Showing 105001 words to 108000 words out of 135959 words

Chapter 36 - Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel

Ta kallesa ta numfasa, se tsotsar wani d’an karamin kilishi takeyi a bakinta, sbda in batasa wani abu a bakin nata ba se tayita zubda yawu. Ta kuma numfasawa idanuwanta na kansa ta hade rai tace “Nifa gaskiya bazan iya rikon cikinnan ba har yakai 5month ko fin hakan,,,,” Aeezad dake matsar mata kafa ya dakata ya dago ya zuba mata idanuwa cikin rashin fahimtar kalamanta yace “ bangane ba? Kmrya?” Dauke idanuwa tayi a kansa tace “kamar yadda kaji, gaskiya bazan iya yawo ? Da abun kunya ba, bansan da wani ido zan kalli mahaifiyata ba, uwa uba matarka da hajiya mommy, sbda komin daren dadewa nasan se sunji komi , gaskiya Bazan iya ba, kawai zubda cikinnan zanyi wlhi …” idanuwa ya zaro cikin mamakin kalamanta nan da nan annurin fuskarsa ya gushe rannan yayi bakikirin. “Cikin shege ne a jikinki da kk wannan mgnr banzar? Naga ai cikinnan cikinane ni nayishi kona shege ne inasan abuna, balle na sunnah,,,daman shiyasa tinda akace kinada Cikin kika shiga bakin ciki kiketa hade rai? To wallahi wallahi ki kiyayeni, inna karajin kalmar zaki zubarmin da ciki wlhi se raina da naki ya baci…” ya fadi cikin fushi. Tashi zaune nabeelah tayi tana kallansa tace cikin matsifa harga Allah batasan cikinnan .”Wallahi sena zubar da cikinnan ko ka yadda ko karka yadda…” ya kalli kwayoyin idanuwanta, nan ya tabbatar da tabbas da gaske take dan ada ya fara tunanin wasa takeyi. Murya babu alamar wasa yace “Wallahi Billahillazi na Miki rantsuwar d’an musulmai, In kika zubarmin da ciki wlhi wlhi nabeelah kinji na kuma rantsuwa, wlhi sena daureki, kaf danginku ma sena musu daurin rai da rai, ummih ce kawai zata tsira sbda ina ganin darajarta, amma wlhi wlhi dake, da wanda tasa hannu , da wadda ta zubar min da cikina, da asibiti da aka zubar min da cikina, da makarantar da wadda ta zubar min da cikina tayi dukse na hadsu dake duka na muku daurin rai da rai har mutuwarku, bade Tonon asiri kike gudu ba zan tona miki , in kika zubarmin da cikine zakiga jahilci, wlhi se duk duniya tasan komi , kin ganni nan mahaukaci ne tuburan in haukar kikeyi ni na fiki hauka nabeelah, ki zubarmin da ciki kigani, wlhi sena miki abinda harki komawa ubangiji bakiyi tsammani ba…” yana gama mgnrsa cikin matsifada gargadi, a yadsa yake mgnr shima dole zaka fahimci tabbas ze aikata duk abinda yace ze mata a kan ciki. “Wallahi sena zubar sede kayi abinda kace zakayi…” tayi karfin halin fadar hakan Tana kuka wannan karan, ita wlhi harga Allah batasan wannan cikin , da tasanma tana dashi da tin kafin wani yasani zata zubar dashi, suna abu a boye Gashi ynzu asiri ya tono, tunaninta ma mgna ta Kai kunnen hajiya mommy ko naeema uwar kishi, ga mahaifiyarta kuma. “Ki zubar ki gani, wlhi ke karamar yar iska ce, nine babban…” ya fadi cikin fitar hayyaci duk yabi ya rikide ya shiga wani Hali, Jin tace zata zubar masa da ciki, kuma yasan zata aikata. Ya fice a dakin cikin fushi da matsifa, ya tadda big hajiya da hafsat a falo, nan ya shaida musu komi da nabeelah tace, kuma yace su zama shaida ko a mistake cikinsa ya zube wlhi seya daureta da kaf danginsu, yayi rantsuwa ya kuma rantsewa. Aunty hafsat ta fara bashi hkri, Ina bebi ta knta ba ya fice a gidan zuciya a dagule yaja motarsa zuwa gidansa, yama mance yaushe rabonsa da gidan nasa.

Yana fita aunty hafsat da big hajiya suka taso suka nufo dakin nabeelah zaune suka sameta tsakiyar gado tana kuka. Big hajiya ta rufeta da fada kan karta sake ta zubar mata da jininta, ta inda big hajiya ke shiga bata nan take fita ba. Aunty hafsat de se rarrashinta takeyi Tana mata natsiha hadi da nusar da ita zunubin dake cikin zubda ciki, aunty hafsat ta fahimci me nabeelah ke tsoro, sosai tadinga mata natsiha, har tayi shiru amma fa bata jiba. Ba jimawa bacci ya kwasheta abinka dame ciki suka fice a dakin sunata jinjina rashin hankali irin na Aunty nabeelah. Tinda Aeezad yabar gidan be dawo ba sbda ta bata masa rai sosai, shi a ganinsa inde batasan cikinsa, duk San da yake mata ze iya mata abinda batayi tsammaniba, besanma Mommy bata sanshi ba seda cikinnan ya bayyana. Ya fahimci bata kaunarsa bata kaunar me kaunarsa, wai harshi take gayawa zata zubar masa da ciki, yayi bakin cikin wannan kalmar, besan me yayima mommy ta tsanesa haka ba,shi kuma Gashi Allah ya jarabcesa da santa, amma shi kiyayyarsa takeyi , Gashi har gudan jininsa ma ta tsana. A ranar farko taji wani kala data kwana ba tare dashi ba sede tadinga juyo kawai har tayi bacci. A bangaren goganma da kyar yasamu yayi bacci a Daren ranar ya saba da ganinta, ko beci ba inya ganta sanyi yakeji, balle ko beci ba yasha Nono koya taba nonuwa. Washe gari da sassafe aunty hafsat tazo ta dubata sosai, ta bata abinda takeso kana ya fice zuwa aiki, big hajiya taci gaba da dubata. Nabeelah ta Kira kawata hawwa’u kan yaza ayi tasamu wanda ze zubar mata da cikinnan..” hawwa’u tace “What ? Zubar da ciki kuma shi Aeezad din yace ki zubar ne ko meya faru zaki zubar da ciki? Kai nasanma Aeezad bazece ki zubar da ciki ba gaskiya kawata…” aunty nabeelah tace “Ni nakeso na zubar, wlhi bazan iya renon cikinnan ba har in haifesa, Kinsan akwai kalubale a gabana gaskiya bazan iya ba…” hawwa’u tace “Ki fawwalawa Allah komi kawata, Karki zubar da cikinnan, bakisan meke zaki haifaba, dan Allah Karki kashe rai kawata…” hawwa’u tadinga nata natseeha, nabeelah tayi kmr taji amma Sam batajiba, itafa tinda Aeezad yace ta aubar tagani, shikenan tajima tanaso ta zubar da cikin sbda taga abinda da ze mata , wai har ita yake cewa ze daure kaf danginsu, sbda raini danyaga su talakawa ne, nan ta kara daura damarar seta zubda cikin, taga mezeyi. Ta kira doctor salmah ta tambayeta meye mgnin zubda ciki? Doctor salmah tace ita bata zubar da ciki, sbda Tana tsoron kashe rai. Duk wata hanya da nabeelah zatabi ta zubda cikin tabi amma ba mafita, Gashi na halin ta fita, dana ace zata fita ne se taje ko pharmacy ne t
NAMIJIN ZUMA


46....

kafin a kira Assalatu Hajiya mommy ta nufo dakin domin ta tashi nabeelah Sbda ta daura girki da wuri, jiya mutane nata santin abincinta, Sam ma sauran abincin ba a Wani cicciba anficin Wanda nabeelah ta dafa. Ta kira sunanta, bayan ta shigo dakin ta tsaya a kanta,kwance nabeelah take tana kallon Saman dakin ita kadaice kwanciyar datake iyayi, bata ita wata kwanciya bayan wannan. Idanuwa Hajiya mommy ta tsure cikinta nabeelah dashi wanda ya bayyana, Amma se Hajiya mommy Tasha ko idonta ne, dukda taji Wani mummunar faduwar gaba, ta lumshe idanuwanta ta kara budewa a kan cikin nabeelah,. "toko tumbine?" Hajiya mommy ta tambayi kanta da kanta, haka kawai ta tsinci knta da fadawa duniyar tunanin da bata San kona menene ba. Tafi karfin 5mnt tsaye kan nabeelah wadda keta sheka bacci batasanma hajiya mommy ta shigo ba, kaf maaikatan dakin bacci sukeyi kusab su hudu kowacce da d'an gadanta me daukar kafita waya sha biyu, dakunan masu Aiki a gidan tafi daki ashirin Kuma ko wanne da masu Aiki a ciki kusan mutum hudu, shida na Maza shida na mata. Hannu takai ta daki nabeelah a kafada, da karfi, a firgice nabeelah ta tashi zaune idanuwanta suka sauka a kan hajiya mommy, cikin hanzari nabeelah ta kalli cikinta a ranta tayi Addu'ah Allah yasa de hajiya mommy bata gani ba...'' "tashi kije Ki daura girki,,," nabeelah tace Toh ta diro daga kan gadon tana kallon Agogon dakin taga karfe uku ne da Rabi na dare, ko hudu batayi ba, Sam baccin be isheta ba, ji tayi kmr Yanzu ta kwanta aka tasheta, Wani irin azababben ciwo taji kanta nayi, ga azabar ciwon ciki da taji Yana taso mata, ji take kmr ta koma ta kwanta, Amma dole ta lumshe idanuwanta ta bude, ta karfafa jikinta ta fice a dakin hajiya mommy nata binta da kallo haka kawai taji a ranta bata yadda da nabeelah ba, yayinda kiyayyarta ta yawaita a zuciyarta, a sukwane hajiya mommy ta biyota kiching din, se kawai nabeelah ta ganta kwatsam seda gabanta ya fadi, yaga de se binta take da kallo tako ina, zuciyar nabeelah na bugu zuciyar hajiya mommy na bugu, dukkaninsu ba a natse suke ba ba kmr ma nabeelah ita tasan dalilin rashin nutsuwarta ita Kuma hajiya mommy bata sani ba, itade kawai taji ta kasa nutsuwa. "Ai nagaya Miki abubuwan daza kiyi tin Jira kin fahimtar kou? Akwai komi a kitchen din kasa dazaki bukata,..'' cewar hajiya mommy aunty Nabeelah tayi hanzarin amsawa da "toh...na fahimta..." Hajiya mommy ta shiga kare mata kallo, jikin Nabeelah ya fara Neman bari, kanta na kasa a ranta se Adduah takeyi zuciyarta nata fatt fatt fatt. Hajiya mommy ta juya xata fice a kitchen din se Kuma ta juyo ta sake kallon Nabeelah se kawai ta juya ta karasa ficewa a kitchen din haka kawai ta tsinci zuciyarta da saka da warwarar da batasan Kona meye ba a ranta de se tunani takeyi Kmr ciki tagani jikin nabeelah Kuma kamar tumbi,hakade Hajiya mommy tadinga saka da warwara. A ketchin din Nabeelah jiki ya mutu Se Kara adduah takeyi ta fara aikin tanayi tana layi kmr Yar maye, gashi ko Ina a jikinta azababben ciwo kawai yakeyi. Haka tadinga Ayyukan da kyar tanajin mararta kmr zata bude, inda ace da hali ma kwanciya zatayi , ji take kmr ta saka ihu, har akayi asubahi ta tsaya tayi sallar asubah, haka ta wuni tsaye yauma gashi cikinta ba komi se ruwa data sha, Aiko tanashan ruwan taji cikinta ya fara motsi, ada hatta tsorata, Dan haka ta dauki ayaba taci sosai Sbda tsoro takeji kar cikin ya dena motsi, a asibiti in taje awo doctor Maryam nace mata in ciki yadena motsi hanzari akeyi Azo asibiti wato da matsala, harga Allah batasan Wani Abu ya sameta koya samu d'an cikinta. Tukunya shida ta daura a wuta, tana Aikin ne da kyar, innah sadiya tazo ta tayata a tsorace take tayata gudun kar Hajiya mommy tazo ta ganu, sauran maaikatan nso su tayata Amma Suna tsoro. Haka suka gama aikin cikin temakon ubangiji, mutanen suka yawaita a gidan, hajiya mommy se shiga Ake ta alfarma ana fitowa it's a dole matar Alhajin Allah. Nabeelah da wasu Wanda aka dakko Dan serving mutane suke ta serving mutane, hajiya mommy na bakin cikin nabeelah ta zauna, duk inda tayi seta bita da Ido, a ranta kawai bata yadda da ita ba,, nabeelah kanta a tsorace take ga uban ciwo jikinta nayi kafafuwanta sunyi Wani him, sun kumbure, Cikin jikinta yayi lakur saboda azabar yunwa SE a hnkli yake wutsil wutsil Daman a gida haka takeyi in taci abinci se ya hau motsi Sosai in tanajin yunwa se yayi lakur. DUk abubuwan da takeyi hankalinta na kan tunanin Aeezad ta tabbatar yanacan ya kusa hauka,ko seconds yayi beji taba zarewa yake neman yi, Ina maga wuni da kwana gashi Amma Kuma Wani wunin. Allah-allah nabeelah take ta bar gidan Amma Ina ranar ma Nan gidan ta kwana sbda bakin Basu watse ba wasu se jibi zasu watse Yan nesa kenan, wasu ma Yan kusan ne Amma Nan zasuyi sati daya sbda duk sun gama da mazajensu ba yadda zasuyi, itafa Hajiya mommy bata kawance da macen da namiji ya Isa da ita, sede tayi kawance da macen data isa da namiji. Daren Wannan ranar ita knta nabeelah gaza baccin tayi Sbda tunanin halin da mijinta yake ciki, ga ciwon ciki, gana baya, gana jiki Sbda azabar gajiya, duk de jikin ma ya mata ba dadih kmr ba nata ba.


A gidan Aunty hafsat Kam Aeezad nata kira, tin tana daukar tana masa karya, harta kashe wayar kawai Sbda ta rasa ma yazata ce dashi, harga Allah bazata iya gaya masa inda nabeelah take ba, Sbda tsoro, Se Yanzu take datasanima da gaya masa gaskiya tayi tin farko,tana kashe wayarta ya fara Kiran lambar big Hajiya, nanma Aunty hafsat ta dauki wayar ta kashe, big Hajiya se matsifa takeyi, da ace zata gane gidan rafi'ah da tini ta tafi, Sbda de kawai bazata gane bane gashi Kuma aunty hafsat taki kaita ko barinta ta fita ma taki,. haka suka wuni a falo jungum jungum, suna jiran dawowar nabeelah Amma Shiru har dare , gabaki daya se hankali ya kuma tashi, Daman 2days din takeyi in taje gidan ko 1day, Amma Yanzu se aunty hafsat ke gani kmr an gane cikin jikin Nabeelah ne,. Ranar ko part din baban Noor bata jeba, sede tace masa mgni zatasha ta kwanta kawai a part dinta. Nan falo suka kwana zaune, aunty hafsat ta rasa yazatayi tunaninta ya kasu kashi kashi. big Hajiya tasakota gaba da matsifa da bala'i, gani takeyi kamar lefin tane, se fadi takeyi "Meyasa Baki tasoni ba?ai da dakikaga zuwan rafi'ah ni dase ki tasoni Ina dai-dai da ita a Wannan Karan bazan daga mata kafa ba wallahi bazan bata fuska ba, daman insda cikinta,bata isa ba tayi kadan, ga dumbin rashin imani rafi'ah yarinya da ciki kusan wata takwas a wata takwas kadan ne babu, Nan a asibiti ko wahala ance ba aso tadingayin aikin whla,, saboda Allah fa, wlhi da lefinki hafsatu da lefinki, Allah yasani, Yanzu in mijinta yadawo miza ace dashi? Ubangiji ya Allah ka tsare cikin jikin yarinyar Nan..." Aunty hafsat sede ta rafka uban tagumi ta zubowa big Hajiya ido kawai ,ita kanta tayi nadamar ma bari nabeelah ta fita a gidan, tayi Dana Sani yafi sau dari, se Yanzu take tunanin daman cewa tayi nabeelah bata Nan tana garinsu, itade ubangiji ne kawai yasan ma a Wani hali take ciki yanzu, tashin hankalinta ma Aeezad kwara na big Hajiya DUk me saukin ne, ita yanzu big hajiya maganarta kawai ta cikin jikin Nabeelah ne,, ta tabbatar duk yanayin da suke ciki be kai kwatan yanayin da Aeezad yake ciki ba , shida ma be garin kenan, duk inda yake Aunty hafsat tasan hankalinsa yanacan a tashe,.

A bangaren Aeezad tinda ya kira Aunty hafsat yaji ta kashe waya hnklinsa ya tashi ya kira big hajiya itama bugu daya tayi aka kashe wayar, Nan take zuciyarsa ta Kuma tsinkewa, yashiga tunanin ko Wani Abu ne yasamu mommynsa, yayi innalillahi wa'inna ilaihirrajun yafi sau dubu, ji yake zuciyarsa na mugun bugu kmr zata fashe, a jikinsa yakeji Wani Abu yana faruwa da bangon zuciyarsa wato mommynsa , tunanin meya sameta da yayi yafi dubu? Kawai de ya fahimci dole Wani Abu ya samu mommynsa, aunty hafsat Kuma taki gaya masa, tabbas akwai abubuwan da take boye masa, shi komade mutuwa tayi ne mommy tasa? Se Kuma ya girgiza kai, yasan da mutuwata tayi dole ne a kirasa a gaya masa,. Ya kira wayar nabeelah data Aunty hafsat data big hajiya yafi sau dubu uku,. Wuraren karfe daya na dare ya fara tunanin barin garin zuwa garin katsina, Zaks ne ya dakatar dashi da kyar,ya dinga basa baki,, duk abubuwan dake faruwa Zaks na gefe, shine ya dinga kwantar masa da hankali kan ya bari giobe sesu kama hanyar zuwa katsina,. Gabaki daya Aeezad ya fita a hayyacinsa, Idanuwansa sunyi red sosai, ga uwar rama yayi, a lokaci kankani, tin randa bejita ba , har Yanzu ko ruwa be shiga cikinsa ba, bakinnan nasa yayi fari fattt, labbansa sun bushe rakayau idanuwansa sunyi narai-narai sun kankance Sbda damuwa, ji yakeyi kamar ya fashe da kuka,ya tabbar in Wani Abu ya samu mommynsa tabbas seya kusan mutuwa, shi da a taba masa mommy kwara shi a tabasa, da asa mommynsa kuka kwara shi asashi Kai inda halima a kashesa ko a nakasashi, duk ze dauka inde a kan mommy ne,.har bugun zuciyarsa ya chanza,haka ke kara bashi tabbacin Mahadin zuciyar tasa Bata cikin koshin lafiya. Be bar Kiran Aunty hafsat ba, da big hajiyar da lambar mommynsa, har safiya kamar yasamu aikinyi, haka ya kwana kira wlhi ko gajiya bayayi,Kuma amsar daya ce duk wayoyin kashe suke.washe gari tin adubah yaso subi fly suje katsina , sede an tashi da yanayin hazo, ta yadda jirgin sama bazeyu ya tashi ba,har wuraren karfe daya, Aeezad na Jira yaga ko hazon ze sauka Sbda bayajin ze iya bin mota zuwa katsina, gani yake kmr ze shekara a hanya basu isa ba. kawai jirgi yakeso yabi, duk lissafinsa ya kare Sbda baya hayyacinsa, ji yakeyi kmr ya kulle idanuwa ya bude ya gansa a gidan Aunty hafsat yaga meke faruwa da mommynsa. "Zaks aunty hafsat batamin adalciba...in Wani abu ne ya faru da mommyna,kwara a gayamin , kaga Yanzu fargaba na neman kasheni wlhi ji nake kmr zuciyata zata buga, mommy kawai nakeso nagani, wlhi inaso inga mommyna zaks, ko jinta nayi a waya baze wadatar Dani ba, so nakeyi kawai na ganta, mutuwa zanyi in Wani Abu ya samar min ita, wlhi har Aunty hafsat bazan bari ba in Wani Abu ya samu mommyna, saboda da gan-gan, ta kashe wayarta Kuma na tabbar tana sane, tinda harta amshi ta big Hajiya ta kashe again,,gaskiya akwai matsala! Akwai Wani Abu ba asone a gayamin kawai zaks,,Amma Ubangiji na Nan,insha Allahu mommyna tana Nan da Rai ita da babyna na cikinta..." Aeezad ya fadi da disasashiyar muryarsa wadda ta narke Sbda tashin hankali, da tsantsar fargaba, Ya kalli Zaks, wayarsa na hannunsa still se Kiran aunty hafsat yakeyi da lambar big Hajiyar data nabeelah shiru har yanzu, hankalinsa yafi na uban kowa tashi a ranar haka yake gani,. Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login