Showing 117001 words to 120000 words out of 135959 words
Chapter 40 - Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel
peach color. “Tubarikallahu masha Allahu….” Big hajiya ta kwace babyn daga hannun Aeezad, ta washe uban baki Tana fadin “sak uban…” Dai dai sauran nurses din suka karaso suka Mika musu sauran babys din guda biyu Aeezad ya amshe aunty hafsat ta amshe dayar, ummih de se kawaici takeyi amma farin cikin da take ciki baze misaltuba se kallon babys din takeyi amma ta kasa amsa, Aeezad kam daya kame diyya ya rungume kam a kirjinsa se hamdala yakewa ubangiji sega hawaye zirr a idanuwansa abinda ya jima yana nema yau Gashi Allah ya basa har uku a lokaci daya, wai yau shine rungume da jininsa….” Ya kuma fashewa da kuka cikin hamdalar ubangiji. Zaka ya matso ya amshi ta gurin aunty hafsat, sbda de na gurin big hajiya bazata ansu ba ta kama ta rike gam kmr ita ta Haifa, se murmushi takeyi , ta leka ta kalli ta gurin Aeezad ya dawo ta kalli ta gurin zaks, ta dawo ta kalli ta hannunta, se washe baki takeyi hakorin makkkanta nata walwali. “Amma de mata ne kou ?” Big hajiya ta tambayi nurses din. “Eh dukkaninsu mata ne…” suka hada baki gun basu amsa. Big hajiya ta dauki kabbara “Allahu Akbar…Ashe rabon yara mata ne , wannan rabo inka matsa ma seka mutu Kai AlhamduLillah…” murna sosai sukayi. AEEEZAD daketa kwallah ya jiyo yace “ya matar tawa?” Daya daga nurse din tace “tana cikin koshin lafiya Yanzu daga ana dama dinketa ne, da an gama zamu fito da ita insha Allahu a kaita dakin da kuke…” Aeezsd farin cikinsa ya kuma ninkuwa Jin nabeelah na cikin koshin lafiya, ya amshe duka yaransa ya rungume, nan take ya musu hudubaDayarsunan mahaifiyarsa data rasu, daya sunan Big hajiya, dayar sunan ummih.ya musu addu’ur’i sosai, se kuka-kuka sukeyi suna yagar hannayensu Nono kawai suke nema. Karfe daya aka fiddo nabeelah ganin halin da take ciki kmr ba rai Gashi kuma se rawa jikinta keyi yasa Aeezad ya big hajiya duka yaran ta Ansha ta kama ta rike kam a kirjinta taki bawa kowa ko daya, har yanzu ummih bata dauki ko daya ba big hajiya tayi bake-bake, dama kmr Tana jira ta Kame yara ta rike gam taki saki. aeezad Ya koma gadon da aka ajiye matarsa, an lullubeta da bargo ya kamo hannunta ya rike gam cikin nasa, Se Wani irin numfashi takeyi, farin cikin da Aeezad yake ciki baze misaltuba a ransa se sa mata Albarka yakeyi, se Addu'ah yakeyi Allah ya tasheta cikin koshin lafiya. ranar haka suka kwana Basu rintsa ba, baby's Kam sede aka Basu madara Daman already an tanadi komi, seda za a Basu madarar ne big hajiya ta bari aunty hafsat ta daukesu, se yawaba akeyi da kyaun baby's din duk kamanninsu Daya da ubansu duk ciki bame kama da nabeelah DUk ubansu Sukayi kmr yayi kaki haka yaran suke , komi na ubansu,. Se washe gari nabeelah ta farka, Taga yaranta, yara har uku kosassu gasu manya manya, farin cikin data shiga itama baze misaltuba se murmushin takeyi Aeezad se godiya yakeyi mata Hadi dasa albarka,. Itama nabeelah tayi hamdalah yafi a kirga. Se yanzu yadawo hayyacinsa ya fara jika nurses din dasuka kawo masa babys din da kyauta ta gigita lissafi, har big hajiya seda ta musu kyautar dubu Dari dari,. Aunty hafsat ta musu kyauta, Zaks ma ya musu kyaututtuka Sosai murnar da suke ciki baze misaltuba, har doctor ma an masa kyauta Sosai wato doctor din daya mata CS din. Komi de se San barka, babys alhamdullahi duk lafiyayyu ne manya manya. A ranar Zaks ya kira daddy ya shaida masa, Aiko sega daddy ko 1h ba Ayi ba da gaya masa ya iso asibitin yaga yara har uku kosassau, farare sol, nan ya hau washe baki, ya kame yara ya rike, big hajiya ta amshe ya dinga Rokonta ta basa su duka yaji duminsu,. Tabasa daya ya amshe jiki na rawa ji yakeyi kmr ya tafi dasu yayita ganinsu har abadan, San da yake musu baze missltuba gasu kmrsu Daya da Aeezad. farin cikin da daddy yashiga baxe misaltuba. Har dare Alhaji sunusi ya Kai a Nan asibitin se yau ya fara ganin mahaifiyar nabeelah se kallanta yakeyi cikakkiyar buzuwace farace sol bakace ma ita ta haifo nabeelah ba,tanada karamin jiki gata da asali doguwar macece kyakyawa Sosai nabeelah ita ta gado gun diri, duk temakon da Alhajin ke mata be santa ba Se yau , Aiko sun gaisa sosai, nan take Alhaji sunusi yayima jikokinsa kyautar kamfanoninsa guda uku,. Nan farin ciki ya kuma kidimewa see godiya Ake masa big hajiya nata kara sa masa Albarka. Ranar se yammaci Alhaji sunusi Ya bar Asibitin. Tin daga ranar kullum se Alhaji sunusi yazo amemakon yaje office dinsa yake zuwa Nan seya jima kana ya bar Asibitin, Sam Hajiya mommy batasan kome ke gudana ba, suna asibiti har yanzu. Hawwa'u aminiyar nabeelh tazo taga babys din ita se murna takeyi, Yan gidansu Zaks ma sunzo sannan Dr salmah ma taxo se taji kmr ta gudu da kyakyawan babys din kullum se an tofesu da Adduah Amma sunashan dauka har zuwa aKeyi ganinsu. Randa akawa nabeelah CS aka Ciro yaran Dr Maryam bata Aiki, se bayan 2days tazo taga yara Masha Allahu gwanin ban shaawah,kullum itama inta shigo setawa yawan Adduah, sometimes ita ke musu wanka, ynzu ko bata duty tana zuwa asibitin sosai, sbda babys din. Sosai Aeezad be bawa nabeelah kulawa da yaransa, yarafa Yan gata ne, ga gatan ubannasu gana big hajiya, gana Aunty hafsat, gana ummih,ga Zaks ma ba a barsa a baya ba, ga Alhaji sunusi ma Kmr ya cinyesu, gana jamaah, kowa sansu yakeyi, daka gansu Dole su shige maka Rai. Satinsu Daya aka sallamesu a asibitin direct sabon gida aka nufa dasu, Woto gidan da Aeezad yayi first night dinsa da nabeelah,. nabeelah ta dan fara samun sauki abinka da CS sauki se a hankali, komide ya zamar mata se a silow ba kmr ace da kanka ka haihu ba,ga ciwon jiki tana fama da, data juya ta kalli babys dinta se taji farin ciki mara misaltuwa.
*Dole amana shari’ah da masu fitarmin da book da masu karanta na sata…Typing is not easy ynzu wlhi drip aka cire a hannuna kuma nayi typing dole, Ina kwance fans kuna raina wlhi…:wlhi bnjin dadih danma jikin talaka🤧 masu fitarwa da masu karantawa.,,,Ba abinda zance sede ince Akwai Allah*
This book is 1k 08101626484
50....
A bangaren su Hajiya mommy seda Sukayi 17days aka sallamesu daga asibitin, dukkaninsu jikinsu yayi sauki, sede har yanzu akwai shadin bulala a jikin na'eema har yanzu be bace ba, da wuya ma ya bace saboda bulalar bame bacewa bace, da hajiya mommy ta kalleta se taji Wani irin bacin Rai, tana kara daura damarar daukar fansa a kan Aeezad din domin bata sassauci a kan yarta, duk Wanda ya tabata seta tabashi,ita ba kanwar lasa bace. Inta tuna Wai Aeezad ne yama yarta wannan cin mutuncin, toh har itama be bari ba, A gaban wad'anda take nunawa ita watace yaci mata mutumci. Bata tunanin a duniya zata yafewa Aeezad da nabeelah wadda a knta yayi musu cin mutuncinnan, dole ta hukuntasu, shima Aeezad seta barsa da mummunan tabon dase ya damesa kamar yadda itama yasa mata damuwa. Karfe goma na dare suna cin abincin dare a kan dinning table, hajiya mommy da na'eema se alhaji sunusi Wanda keta Allah-Allah ya gama cin abincin ya tashi yaje yaga triplets dinnan sun tsaya masa a Rai, dazu Zaks ya kirasa ya sanar masa an sallanesu suna sabon gidan Aeezad din, harma yasa ya tura masa address din gidan, shi Kuma ya turawa dreva dinsa, yau beje ko Ina ba, Yana gidan tin dazu yake dabarar yadda zeyi ya bar gidan Amma hajiya mommy ta tattare ko Ina ta hanasa rawar gaban hantsi, se makirci kawai take kissima masa iri iri, tana kara nuna masa irin cin mutumcin da Aeezad ya mata gaban kawayenta, Gashi labari ya isa har inda batayi tsammaniba, video din da akayi ma har grps aka tuttura da take ciki,. Duk bashi hajiya mommy ta bayar ynzu take Shirin daukar fansar bashin, ai sata gidan barawo rance ne. "Alhaji inasan magana dakai..." Cewar hajiya mommy da tayi mgnr tana ajiye spoon din hannunta. Alhaji sunusi yace "inajinki hajiya...." Cikin isa da iya lafazi na makirci ta fara magana. "Yanzu ya auren me aiki Nan yake da Aeezad? Gabaki daya wannan ai zubar maka da mutumci yayi, ace d'anka na auran me aiki' me aikinma wadda ta rainesa, gaskiya da sake, Kuma kasan bazeyu diyyata ta zauna da kishiya ba.." Ta karashe mgnrta suna hada Ido da na'eema wadda taji dadin abinda mahaifiyarta tace. Alhaji sunusi yayi humming kana yace "To yazanyi hajiya? Kinsan yaran yanzu Ka haifesu ne baka haifa halinsu ba, balle ma Aeezad wlhi na rasa yazan dashi hajiya..." hade Rai hajiya mommy tayi tace "Kamarya? Ka haifesa da cikinsa kace Ka rasa yaza kayi dashi? Wannan ai batsa ce kakeyi, gaskiya bazata sabu ba Alhaji!!'' ta karashe cikin daga murya, na'eema Kam Dena cin abincin tayi, Ubangiji ne kawai yasan a Wani hali take ciki, data tuna da nabeelah matar Aeezad ce, sannan ga cikin jikinta ma na Aeezad din ne, se na'eema taji komi ya fitar mata a rai, ba ita ba har uwarta ma, ita abinda takeji ma ya wuce na Yar tata, a cikin azabar data tanadarma Aeezad harda nabeelah ciki,ta dauki alwashin inde tanada Rai cikin jikin nabeelah bazezo duniya ba. Alhajii sunusi yabi hajiya mommy da Ido, Ba tare dayace komi ba. Cikin fada taci GABA dacewa "Tukunna ma kayi bincike ka tabbatar Aurenta yayi?'' Alhaji sunusi yace "Eh tabbss nayi bincike hajiya, wlhi aurenta yayi...." Wani bakin ciki ya tokare hajiya mommy da na'eema wadda kejin kamar zata kashe nabeelah. "Tsintacciyar mage ai bata mage alhaji,,,Dan kudi ta Auresa kilama so take ta kashesa taci gado, da wuyama in cikin jikinta nasa ne, Alhaji kayi gaggawan sashi ya saketa Kuma ya mata korar kare zuwa kasarsu, shegiya ita kanta fa ta zina uwarta ta haifota...wannan abun ze taba maka martaba cikin abokanka Alhaji, ... " Hajiya mommy ta fadi cikin kissa da makirci. Alhaji sunusi ya jinjina Kai, shide yasan nabeelah ba Yar Zina bace. a zahiri yace mata "Za asan yadda za ayi, Nan Bada jimawa ba..." "Gaskiya Ayi gaggawan yin yadda za ayi. .Kuma ai yakamata ace shi Aeezad din yaxo ya bawa na'eema hakuri Nima ya bani hakuri kan cin mutumcin Daya mana a kan Wannan shegiyar yarinyar jinin karuwai Yar iskar yarinya! Yan kasar gadon asiri!" Alhaji sunusi yace "Dole zezo ya baku hakuri hajiya...." cikin sanyi yake mgna inde Yana gaban hajiya bashi da katafus. "Yayi gaggawar zuwa..." Cewar hajiya mommy. Alhajii sunusi yace "Toh yadda kikace haka za Ayi hajjajuna..." Murmushi hajiya mommy tayi a zuciyarta tace "Aiki na bugaka Alhajin Allah.." Alhaji sunusi ya kalli agogon dake manne a hannunsa kana yace "Zan fita YNzu Amma ba jimawa zan dawo..." Hajiya mommy ta hade Rai kana tace "Ina zakuje? Gaskiya ba yau ba sede gobe?'' "Pls meeting zamuyi da Abokina
Bazan juma ba..." Cewar Alhaji sunusi, da yayi mgnr cikin magiya. Da kyar de hajiya ta barsa ya fita, dreva yajasa zuwa gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na fita na'eema ta kalli mahaifiyarta tace "Mommy yadda daddy yake Miki Nima haka nakeso Aeezad ya dingamin, a maidaminshi se yadda nayi dashi Dan Allah mommy, ita Kuma Yar bura ubar Nan a haukatata, ita da Cikin a kaita can birnin seen ta karashe rayuwarta a can,ita da shegen cikin jikinta,..." hajiya mommy tayi murmushi tace "Me kikeci na bakinki na zuba? Fiye da haka na tanadar ma yarinyar Nan domin nafijin haushinta a kan Aeezad saboda na fahimci duk Dan ita ne ya mana wannan dibar Albarkar, Amma ki kwantar da hankalinki, yarinyar de dagani ta mori malami,,Ina me tabbatar Miki se tayi nadama ai ruwa ba sa'an kwand'o bane,ko kura ta rame ai tafi gaban raini ga Kar'e, sama Tayima yaro nisa sede ya tada Kai yayi kallo, yaro besan wuta ba seya taka, Wani ma yayi rawa balle d'an makid'a, sha ruwan sanyi y'ata kmr kin jika tsumma a ruwa..." Hajiya mommy ta karashe tana Jan kwafa, ko garwashi ta hada ta jefa nabeelah a ciki bata huce ba. "wlhi mommy hankalina baze kwanta ba Sam, bacci ma seda kyar nake yinsa har yanzu Ina San mijina, mommy wlhi bashi da lefi kawai Kiyi azabarki a kan nabeelah, duk asiri ne yasa idanuwansa ya kulle ya mana abinda ya mana, ni ko kashe yarinyar Nan akayi ban huce takaiba, mommy so nake Ayi mata DUk abinda zakiyi mata , ta d'and'ani azabar duniya taji, tinda harta aurar min miji ai dole in mata azaba mommy, gashi sanadinta mutumcinmu ya zube gaban masu mutunci, wlhi mommy kiyayyar da nakewa nabeelah bazata misaltuba.." hajiya mommy tayi murmushi mugunta kana tace "Ai duk kiyayyar da kike mata be Kai wadda nake mata ba naeema, Allah de ya kaimu gobe,in mukaje asibiti Kara duba jikinki, semu wuce gun boka kawai ba a bori da sanyin jiki..." na'eema ta amshe da Amin, kiyayyar nabeelah na Kuma ninkuwa a rayukansu ita da uwarta, sun rasa ma tayaya ta shammacesu.
Seda Alhaji sunusi ya tsaya Yama jikokinnsa shopping sosai na kayayyaki na Alfarma a babban boutique din da Ake saida kayayyakin jarirai Wanda Ake kawowa daga kasashen waje. Seda ya cika akwatina uku da kayayyaki na Alfarma dreva dinsa ya tayasa zaba da wata me Aiki a gurin. Ya biya akasa a booth. Suka sake tsayawa yawa mahaifiyarsa siyayyar kayyan makulashi. t kana Suka nufo gidan Aeezad,. Alhaji sunusi na shigowa falon yaga ga kugun Aeezad gana nabeelah se kara shishige mata yakeyi ga yara duka ukun a kan cinyarta, zaune take kan carpet Kuma ta daura pillow a kasanta, ta zuzzuba duka yara ukun a kan cinya, ta bawa wancan nono ta dawo ta bawa wannan nono, yaran nada lafiyar tsotso Suna tsotso sosai, danma ana hada musu da madara, saboda tsotsonsu yayi yawa, yau kimanin kwanansu takwas da haihuwa Amma sun kware a tsotso. Big hajiya na gefe tana Jira a gama shayar da yaran a batasu, ummih na can gefe itama,Aunty hafsat bata Nan tana gidanta,se wata laure itama tana zaune gefe me Aiki ce, big hajiya tasa aka kawota dazunnan daga gidan hajiya Maryam wato matar d'anta Alhaji abubakar, Se Yau big hajiya ta shaida mata komi Aiko itama ma ta shaidawa mijinta, Abu kmr almara kowa yaji dadin wannan hadin, Daman ita hajiya Maryam ta fara fahimta kwanciyar Aeezad a asibiti. Alhaji sunusi ya gaida mahaifiyarsa ta amsa fuska sake, ya bata kayayyakin ciye-ciyen daya siyo mata, se godiya take masa dasa Albarka, tinda aka haifo yarannan take ganin sauyi a gurin d'anta, gashima tanata ganinsa akai-akai gaskiya haihuwar yarannan yazo da Albarka, haka big hajiya Ke cewa motsi kadan. Ummih ta gaida Alhaji sunusi ya amsa fuska sake, besan meyasa ba inya kalleta se yaji gabansa na faduwa. Daman nabeelah tini ta gaisasa tin shigowarsa Aeezad ma ya gaidasa, ganin yadda daddy keta zuwa Yana duba yaran yasawa Aeezad jin dadih ba kadan ba. laure me Aiki ta gaida Alhaji sunusin cikin girmamawa. Ya amsa Yana kallanta Yace "Wannan fa?'' yayi mgnar da Aeezad. Aeezad ya bashi amsa da "Big hajiya ce tasa aka kawota daga gidan Alhaji daddy,zata dinga taimakawa da Ayyuka..." Alhajii sunusi yace "Toh-toh...Amma an tabbatar ta iya wankan jarirai kou?'' ya juya akalar tambayarsa ga big hajiya. Big hajiyar tayi murmushi tace "kar aje a jefa maka jikoki a ruwan zafi kou?'' duk Yan falon sukayi murmushi ba karamin jin dadih sukayi ba musammanma Aeezad, dadih na nunawa yaran SO na tsakani da Allah Sam ma be iya boyewa. Alhaji sunusi ma murmushin yayi yace "Eh wallahi big hajiya, haka akayi da Yar Abokina ta haihu haihuwar fari aka dakko me wanka, garin gasa cibiya ta kona babyn, big hajiya satinsu uku a asibiti ana fama da babyn ba karamin kuna yayi ba,,, maganin Ayi ai kar a fara, kwara a bawa hajiya ta dinga musu wanka..." Ya karashe mmaganarsa Yana kallon ummih wadda kanta ke kasa. Aeezad yayi hanzarin cewa "Nima haka nace,Amma big hajiya taki, ita ke musu wanka daddy, da kyar take bari aunty hafsat ta musu wasu lokutan . " Alhaji sunusi ya zaro idanuwa yace "gaskiya big hajiya dakin bari an dinga musu saboda naga ke ba Wani gani kike sosai ba..." Big hajiya ta amshe da "uban bana gani! A haka de na raineka, Shima Aeezad din Dan Anki bani shine Amma Dani zan rainesa... Dan haka ni zan dinga musu wankan da gashin cibi har Ayi arba'in banga me rabani da yarannan ba sede mutuwa..." "Toh ai shikenan Allah de ya tsare min..." Cewar Alhaji sunusi big hajiya ta rike Baki tana mamakin ganin yadda d'anta be kawaici a kan yaran Kuma duk kawaicinsa. Duk Yan falon suka amshe da Amin Banda nabeelah data kasa cewa komi se gyangyadi takeyi Ma ita bacci takeji, so takeyi ta gama bawa yaran nono taje ta kwanta. " Hajiya me kula da jikokina, Jeki ce da dreva Dina ya bude Miki but ki kwaso kaya..." Alhaji sunusi yayi maganar da laure Cikin girmamawa bada raini ba wai Dan tana me AIKI. Laure tayi murmushi Hadi dacewa toh ta mike ta fice a falon, a kallah laure bazata wuce 45yrs ba. Ta kwaso akwatunan ta diresu a tsakiyar falon, Nan aketa kallon kayan arziki,. A haka hajiya Maryam da mijinta, da Saif da matarsa suka shigo falon, Daman big hajiya tasa aunty hafsat ta tura musu da address. Cikin murna