Showing 93001 words to 96000 words out of 135959 words
Chapter 32 - Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel
school,San yanzu babu Wani laulayi laulayi, Amma har yanzu abincin da takeci su takeci bata iyacin komi, jefi jefe anasa mata drip sbda taji kwarin jikinta. Yaude da kyar nabeelah tadinga lallamar Aeezad sbda ya koma bakin aikinsa ogansa nata kiransa, beso Amma haka ya tafi ya barta byn ta bashi gindi yaci sosai, daze tafi seda yayi kuka, Sam beso ya tafi ya barta, zuwa yanzu an gama siyayyar baby, kayayayyakin da aka siyama babyn yafi a kirga drowers uku manya ya siyo Kuma duk an cikasu da kayayyakin daxe dauki maza da mata.
da kyar nabeelah ta lallashesa sosai ta rakasa har bakin mota, yayinda securities sunfi mutum dari na tsaronsa sbda a mota ze tafi garin kanon sannan shida Zaks zasu tafi. Bayan ya shiga motar ya kamo hannunta , ta tsuresa da ido, idanuwansa fal kwallah yace "Mommy ki kulamin da babyna Dan Allah, sati Daya zanyi in dawo na Baki amanar babyna, daga can zanje American in karoma babyna kayayyaki dukda babyn nawa ta boye kanta taki bari aganta, Amma inasan ran insha Allahu mace zaki haifa mommy,,,," nabeelah tayi murmushi karfin hali gani takeyi kmr inya tafi bazasu sake haduwa ba. "Ka kyale babbynnan da kaya kayayyakin sunyi yawa, wasuma har abadan baza a sasu ba sbda sunyi yawa pls ka bar kudinka haka Nan ba abinda fa baka siya ba,,," Aeezad yayi murmushi yace "Bakomai ai inasan maman babyn ne, Shiyasa nake san babyn, ke bakisan wai zan iya bada komi nawa Dana mallaka ba a kanki mommy..." for the first time dataji tanaso ta furta masa kalmar soyayyar kmr daga sama tace "Wallahi Ina sanka!" Wani irin mummunan bugu zuciyarsa tayi, be taba tsammanin A rayuwarsa mommy zata fusta masa kalmar SO ba, wasu sassanyar hawayen farin ciki suka wanke ma Aeezad idanuwa ya kara damke hannunta cikin nasa yace "Mommy kina sona? Yau kece kike furtamin kalmar soyayya? Wow! Wlhi Ina sanki, Ina Kara sanki, Ina Miki Azababbiyar kaunar, ke rayuwata ce, wallahi da in rasaki kwara in rasa rayuwata, saboda Rashinki a cikin rayuwata Yana iya haifarmin da mutuwar azaba, har kwara inyi mutuwar farat Daya, Amma inna rasaki mommy mutuwa zanyi bayan nasha wahalar jinya,, Ina rokon Ubangiji a kullum innasa goshina a sujjada, Allah ya barni dake, Allah yasa mu mutu tare, sbda in kika mutu kika barni bazan jure rashinki ba mommy, Ina rokon Ubangiji ya karamin sanki, sbda sanki shine dadih me fidda sinadari a cikin rayuwata!I love you Naji dadih yau kin furtamin kalmar SO zanyi tafiya cikin farin ciku, Kiyi min adduah inyi juriya da hakurin rashinki a kusa dani, ina sanka ki kulamin da maniyyina daya zama gudan jini a mararki, I wish in iya Kai 1week dinma bandawo ba da wuya,, ko mu tafi tare? " Nabeelah tayi shiru yayinda kalamansa na soyayya suka ratsata, duk abinda ya fadi direct daga zuciyarsa yake fitowa. "Ki shigo mu tafi mommy, daga can semu wuce America a Miki CS acan,," ya fadi cikin magiya kawai beso ya tafi ya barta. Nabeelah ta girgiza Kai tace "aah, ni bazanje ba,
Nafiso na haihu a Nigeria kusa da kasata,ba asan yadda hali zeyi ba..." Aeezad ya
Ya kula tinda cikinnan nata yakai wannan watannin take a karaye, cikin karfafa guiwa yace "Zaki haihu lafiya insha Allahu mommy na, Ina gefenki, za ayi Miki CS insha Allahu zamu rayu tare sekin haifamin yara ashirin ..." Murmushi nabeelah tayi, da kyar tasamu ya saki hannunta, sukayi sallama da Zaks, suka fice a gidan se daga mata hannu yakeyi itama tana daga masa. Seda taga ficewarsu kana ta juya zata koma ciki, taga baban Noor ya fito daga part dinsa, kallo daya ya mata yayi hanzarin dauke idanuwansa a kanta shi tsoronta yakeji ynzu tin abunnan daya faru da abokinsa alhaji sadi, Daman Kuma ba karamin tsoron Aeezad baban Noor keyiba, basa shiri Sam da Aeezad, inya gansa sede shi baban Noor din ya gaidasa Amma Sam shi Aeezad baya gaidasa kawai jininsu be hadu ba, ya rasa dalili, ynzu Kam shida nabeelah se kallon nesa kallonma na tsoro, Yadda yake ganin Aeezad na gidan gun nabeelah kullum shike kara tsorata Baban Noor a kan Aeezad. Nabeelah ta gaidasa ya amsa , cikin hanzari ya wuce ya shiga motarsa ya fice a gidan, nabeelah ta shige ciki, zuciya fal kewar mijinta, Nan falo ya ta zauna gun big hajiya da Aunty hafsat kasancewar yau Sunday bata zuwa aiki, Nan suka wuni suna hira, se dare tashiga daki ta tadda miss call din Aeezad yafi miss call hamsin, daukar wayar tayi ta kirasa, bugu daya Aeezad ya daga,, "Ina kika ajiye wayar inata kiranki Wife?'' cewar Aeezad daga cikin wayar,. Nabeelah tace "Tana daki Wlhi Nima inataso in kiraka Muna falo ne munata hira dasu big hajiya,," AEEEZAD yace " Shine xaki bar mijinki cikin tashin hnkli inata kiranki, Baki kirani ba kinji Yana Isa kano? Toh na isa lafiya my wife and I miss you, ,," "am sorry pls..."cewar nabeelah "Ai bakya lefi ya abun dadihna?:'' nande suka shiga hirar soyayya. seda sukaci juna a waya kowa ya kawo, har karfe biyu na dare kana sukayi sallahma da juna, Aeezad so yayi su kwana suna waya.
After 2days da tafiyar Aeezad kullum cikin waya suke. Yau karfe goma na safiya, nabeelah nakwance tana bacci, ta kashe wayarta danta samu tayi bacci yau, sabuwar shekara Ce yau new year 1january yau ba aiki. Kmr a mafarki nabeelah taji aunty hafsat na tabata, ta bude Idanuwan ta a kan aunty hafsat bakinta dauke da Addu'ah a kwanakinnani tana yawan muggan mafarkai.,kallo Daya nabeelah tayima aunty hafsat ta fahimci tashin hankali kwance kan fuskarta, tasan bata taba tashinta in tana bacci ba se yaj, hasalima ko TV ba a kunnawa asa volume in tana vacci. "Mommy tashi Maza ki dakko zumbulelen hijjabi kisaka hajiya mommy Ce tazo, wai kindena zuwa mata Aiki duk bayan weeks,se hauka takeyi tana shouting, kinsantade mahaukaciyar banza,ihunta ne ya tasheni a bacci, danma Allah ya temakeni bata San dakinki ba dasede ki ganta a knki, ubangiji ya rufa mana asiri dase taga komi..." aunty hafsat ta karashe maganarta tsoro na Kuma bayyana a kan fuskarta, jikinta har Neman fara rawa yakeyi gani takeyi kmr asiri ya gama tonuwa yau. yauce rana ta uku da hajiya mommy taxo gidanta, Daya a haihuwar noor, biyu a haihuwar Nasmah, se yau da maman Noor ke tunanin tsautsayine ya kawo hajiya mommy gidan.
This book is 1k 08101626484.
[18/07, 6:58 PM] +234 701 497 9567: NAMIJIN ZUMA
43….
Kowa ya ankare da yanayin da nabeelah tashiga amma babu wanda yabi ta kanta , sbda farin ciki, Aeezad yafi kowa farin ciki ji yakeyi kmr bashi ba, kmr a mafarki, ya kamo hannun doctor tace “pls doctor are you serious nabeelah na, nada ciki?” Doctor da fuskarta ke dauke da mamakin wai basu san da cikinba? Harshi me cikin, abun ya bata mamaki har tsawon 4month. “Yeah sir cikine da matarka har tsawon wata hudu…” juyowa Aeezad yayi ya kalli nabeelah wadda bakin ciki ya turniketa kmr zata hadiye zuciya ta mutu sbda bakin ciki da kunya, ita Sam bata shirya amsar cikin d’anda ta raina ba, kuma ma da wani ido zata kalli duniya? “AlhamduLillah…” Aeezad ya fadi a bayyane, idanuwansa suka ciko da kwallar farin ciki mara misaltuwa, nan take ya zube yayi sujjadar godiya ga ubangiji , yana kuka yanama Ubangiji godiya daya bashi abinda ya jima yana nema., tako ina yasan Aurensa da mommy ya cika, daurin Auren da Akayi a babban masallacin sultan bello, inda Aeezad yace shine waliyyin amarya seda akazo daurin Auren Malam yace ai bazeyu wanda ze auri mace yazama waliyyintaba, a nan de babban malamin yazama shine waliyyin amarya a matsayinsa na babban me shari’ah kuma babban malami a masallacin, Zaks shiya zama waliyyin ango, shi tamkar dan uwa na jini yake ga Aeezad.
Bayan haka, kuma ya sanar da mahaifiyar nabeelah bayan tazo dubasa a asibiti dabeda lafiya, dayake ummih me fahimta ce kuma burinta nabeelah tayi aure, nan ta fahinta kuma ta amince, amma taace “Dangin baban nabeelah sune damuwa zasu iya cewa basu amince ba…” Aeezad yasan su sbda ya taba zuwa gaidasu dayaje kasar shida mommy, dan haka ya bawa ummih kudade dayawa yace inta koma gida ta basu injisa duk sun sanshi sbda dayaje ya jikasu da kudi sosai, yanada alheri, shi a kn mommy ba abinda baze iya ba. Duk a boye sukayi hakan, kuma ya shaidawa ummih karta gayama nabeelah kuma karta nuna mata, ummih ta musu addu’ur’i sosai, dasa Albarka kuma ta barwa cikinta sbda batasan dalilinsa dayace karta nunawa nabeelah ba, ita a duniya sun gama mata komi shida mahaifinsa , ba abinda Aeezad
Ze nema a gareta bata masa ba in har tanada iko da abun, kuma da abun kunya ai kwara irin wannan Auren dade a kawo mata abin kunya, kuma ta kula Aeezad nada rawar kai ze iya aikata komi, Gashi koda kashe nabeelah yayi basu isa su masa komi ba, saboda yanada kudi kuma yanada power ita a bangarsn ummih Aeezad ya gama mata komi sbda wannan tamkar rufa mata asiri yayi daya auri yarta. Da ummih zata tafi har lambar limamin daya daura musu auran ya bata kuma ya kirasa a gabanta ya tabbatar mata da tabbas shiya zama waliyyin nabeelah, kuma akwai shaidu dayawa. ummih taji dadih sosai,dana koma Niger ta sanar da yan uwan mahaifin nabeelah a fari sukace basu aminta ba, seda ta fada musu waye Mijin da kuma abun Arzikin daya basu kana suka amince da Auren suka sa albarka, daman Sam ba mutanen kirki bane su , basu taba taimaka mata dako Sisin kwabo ba bayan rasuwar Mijin nata, kuma suma tankar yan uwa suke a gareta, sbda Auren zumuncine tsakaninta da baban nabeelah. Shiyasa shifa Aeezad hankalinsa kwance a kn nabeelah babu wanda ya isa ya hanasa zaman Aure da nabeelah, yanzu de mahaifinsa ne matsala, shima kuma be maidasa matsala ba, sbda malamin babban me shariah ne, yasan daddy ma ba dmwa bane hajiya mommy da naeema suna babban case din dake gabansa.
, big hajiya se washe wawulo takeyi tace Alhamdllh yafi sau ashirin, aunty hafsat kam baki har kunne, ita knta doctor da nurse din se murmushi sukeyi, suna Tayasu farin ciki, nabeelah kam ta hade rannan gam, se tunanin tunani takeyi, kan asirinta ya tonu a duniya, zuciyarta ta cunkushe Sam bata farin ciki ji takeyi daman cikin ya bare ynzu, babban tashin hankalinta yazata kalli mahaifiyarta da wannan abun? Uwa uba kuma Dangin mahaifanta da Alkhairi baya kawosu gidan. Se kallan big hajiya takeyi Tana kallon aunty hafsat su se murna sukeyi ba kmr ma uban gayyar da tinda yayi sujjada be dago ba, seda yayi 10mnt yana kuka, kana ya dago , AlhamduLillah taki barin bakinsa, ya karaso ya rungume aunty nabeelah se faman godiya yake mata cikin sambatu, be taba farin ciki kamar wanda yake ciki ba a yau. Nan take yayima doctor kyautar kujerar hajji, itama nurse ya mata kyautar kujerar hajji,. Suka dinga godiya nurse harda kwallah sbda farin ciki, daki de ya rikice da farin ciki Aeezad se murna yakeyi aunty hafsat da big hajiya ma ba a barsu a baya ba, nabeelah kam bakin ciki suke kara mata in suna murnar nan ta kasa hada ido da kowaccensu sede tayita satar kallansu kmr barauniya. Har wuraren 2;pm kana doctor ta fice a dakin ita da nurse se murna sukeyi kafin doctor ta fita tace da Aeezad ya sameta a office zuwa gobe. Ranar de kwana akayi ana farin ciki da murna, har seda sukayi sallar asubahi kana suka kwanta, drip din daman ya kare tin asubahi aka cire mata, ta kwanta ita kan ta kasa bacci, se kallan cikinta takeyi, tana ayyano yadda za ayi ta rabu da wannan cikin kaddarar dan ita bazata iya da wannan abun kunyar ba. Tini aeezad ya Kira mahaifiyar nabeelah ya sanar da ita, tayi farin ciki sosai, duk nabeelah bata sani ba, daman shi yana boyewa ne sbda iya wuya kar nabeelah ta gudu ta barsa, yasan akwai matsalolin a gabansu yana tsoron in komi ya bayyana kar nabeelah ta koma Niger ta barsa, ynzu kuwa yasan bazata iya barin gidanba sbda tana tsoron inta je can mexatacema mahaifiyarta. After 2days , Aeezad na bawa nabeelah kulawa ta musammanma ji yake da ita tamkar kwai, ya rasa Ina zesata dan murna, aunty hafsat da big hajiya sun fahimci nabeelah bata murna da samuwar cikin shide gogan Sam be fahimta na farin ciki ya hanasa ya fahimta a ganinsu Aunty hafsat kenan , basusan yana ankare da komi ba. Kwanansu uku a asibitin aka sallamesu bayan doctor ta jaddada ma Aeezad banda sex ya barta harnan da 1month, sannan Banda aiki dayawa, banda Yawan tafiya me nisa, sannan adinga barinta tana samun bacci sosai, a takaicede an bata bed rest. Aeezad har rubutawa yayi sbda beso ya mance ko abu daya gudun kar cikinsa ya zube ji yakeyi daman ana daukar Cikin ya dauki abinsa ya rike kayansa,. Zaks ma tini yasani shima yayi farin ciki sosai, dashi aka dinga jinyar nabeelah a asibitin, , kafin Subar asibitin Aeezad yayi kyauta kudi yafi millions of naira. kyauta kawai yadingayi kmr besan zafin kudi ba. Har gida seda yasa aka sake ma maman nabeelah sabo a niger ya zuba mata kayan alatu, bayan sun isa gida yau kawai nabeelah taga mamanta ta kirata ta tambayeta ya jiki, nabeelah tace dasauki, daman tasan bata da lafiya tin randa aka kaita asibiti Aeezad ya sanar da ita aiko se Kira takeyi dasuna asibitin nabeelah ta kula mahaifiyarta na Cikin farin ciki amma batasan Kona meye ba. , nunawa kawaj Ummih keyi kmr batasan komi ba. Ummih tace tayima Aeezad godiya..” se a nan nabeelah kejin ya chanza musu gida har mota yasiya ma ummih da dreva, ta kallesa se kimtsa dakin yakeyi tinda suka dawo yake tsaye sbda beso tayi aiki duk abinda yasan zatayi seya yakeyi da knsa, ita kuma Tana zaune a gefen gado ynzu aunty hafsat da big hajiya suka fita a dakin. Godiya sosai nabeelah ta masa, kan abin Arzikin daya ma mahaifiyarta. Aeezad ya kalleta yayi murmushi yace “Abin arziki ai yana jikinki mommy, fatanade ubangiji yasa ki haifamin yarona ko yarinyata lafiya, Allah ya miki albarka wlhi na kara sanki, ke sanadin Alkhairi ce a rayuwata…” ba tare da tace komi ba ta koma ta kwanta, ita duk haushin komi takeji, Gashi cikinnan tinda ya bayyana se amaye amaye, wai a haka ma dan an kakkara mata drip sosai, Gashi ba komi take iya ciba , abubuwan dake shiga cikinta Kala hudu ne,, daga tasha zuma se taci kilishi , se taci ayaba, se ruwan sanyi, ba abinda tafi bukata kmr ruwan sanyi tana kaunarsa, Gashi ance ta rage sha. Wata iriyar kulawa Aeezad ke bata ta musamman, kullum yana manne da ita, big hajiy da Aunty hafsat ma suna bata kulawa sosai ba kmr ka big hajiya , wuni takeyi Tana dafa mata abubuwan ciye ciye na gargajiya wasu taci wasu ta kasa ci, har kwarama dambu inta mata dambun masara tanaci sosai, tinda aunty hafsat ta mata bayanin Aurene tsakaninsu da Aeezad ba zina ba, tamata bayani sosai yadda zata gane, aiko nan ta kara San nabeelah da d’an cikinta, itafa ko ada batasan nabeelsh yanzu Tana santa sbda Tana dauke da cikin jinintan, daman ba yawa ne dasu a family dinba, Gashi big hajiya naso taga jininta sunyi yawa sosai dan haka ita d’a kona shege ne tana so inde daga jininta ya fito, ballema tanasan Aeezad sosai, nabeelah tazama yar gata a gidan, duk jarabar Aeezad ya kyaleta sbda tanada ciki, amma daurewa kawai yakeyi ta kula da hakan, inya ganta se yayita kallo, wanibin har yawu yake dalalarwa. Sau uku hawwa’u na zuwa dubata tin zuwan farko ta fahimci ciki ne da nabeelah , Gashi aeezad yaki basu guri su zanta, se yau da nabeelsh ta masa dabara tace yaje ya Siyo mata gwaiba, shine ya fita ya basu guri su zanta da hawwa’u. Yana fita nabeelah ta kalli hawwa’u tace “Wai cikine Dani na Aeezad? Da wani ido zan kalli duniya ni nabeelah!” Nabeelah ta fadi kmr zata fashe da kuka, ta kuma kyau da fresh ga wata uwar kiba tanatayi ba lallai ka gane cikine jikinta ba sbda cikin yabi hips da nonuwa. Hawwa’u da farin ciki a kan fuskarta tace “Nafaga kayan arziki, wannan ciki ai d’an gata ne, tako ina naga lelebki akeyi musammanma agun Miji…” tabe baki nabeelah tayi tace “lelen me, bayan an cuceka kou..” fuska dauke da rashin fahimta hawwa’u tace “Kmr ya? kina mgna sekace cikin shege, pls kidena irin wannan abun gaskiya, wani na nema ke kina nuna kmr bakiso tin rannan na kula, se wani abubuwa kkeyi, keda ya kamata kiyima Allah godiya ga miji ya baki Danye sharaf, ga ciki ya baki cikin gaggawa…” nabeelah ta kuma hade rai sbda ta fahimci hawwa bata San me take ma tsoro ba. “Da wani ido zan kalli ummih? Babban bala’inma yazanyi dasu hajiya mommy da matarsa naeema…wlhi ban shirya daukar bala’innan yanzu ba..” hawwa tace “Au baki shirya ba, amma shine kika dinga gwale gindi anaci? Kinga wlhi ki nutsu nabeelah , ki bar tunanin wadannan, domin ynzu rabo ya rantse ba abinda suka isa suyi, in rabo ya tsinke daraba bacewa takeyi, ki rungumi mijinki da cikinki kawai Aunty nabeelah, ba abinda su hajiya mommy suka isa su miki tinda basu hana faruwar wannan kaddarar ba aiko kinga ba yadda zasuyi dame zuwa…” nabeelah tayi shiru kawai badan taji abinda hawwa tace mata ba, duk natsihar daya mata a banza, har tabar gidan, washe gari ta tashi tanata fushi abu kadan seta hau