Showing 21001 words to 24000 words out of 135959 words
Chapter 8 - Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel
mutuniyar kirki ce sbda tanada fuskar mumunai, Aiko ya hadata da Alhaji sunusi, sukaje neman Aure a jahar daura , ita haifaffiyar yar daura ce,mahaifinta cikakken bakatsine Bashi da sana'arh data wuce wankin hulah da ita yake ci Yake ciyar da iyalansa matansa hudu yara talatin da uku, rabin yaran nasa mata ne kuma duk karuwai ne dasun samu namiji yadanse musu abun dadih to shikenan se su mallaka masa martabarsu, babbar yayarsuma batai aure ba tana can cameron tazama uwar karuwai,. Rafi'ah na ciki daga manyan yan iskan yaran Audu, tin tasowarta takeda kwad'ayin Tsiya, Aiko tadinga bin Maza suna bata kudi, da kyar malam Audu me wankin hula ubanta yasamu tayi aure bayan yasama mata mijin Aure Wani babban amininsa, ta auresa tadinga gana masa azaba sbda bashi da kudi, bakin cikinta ya kashe mas'udu ,ya mutu ya barta da yarinya yar shekara goma sha biyu wato na'eema, a daddafe rafi'ah tagama takaba ta bazama yawon siyasa hadi da yawon bariki 2 in one. akwai wata babbar kawarta asiya itama bazawara ce. ita tabasu shawarar su Kai photos dinsu gidan me dalilin aure shine suka Kai, cikin sa'ah rafi'ah tasamu mijin Aure wato Alhaji sunusi. Dukda Alhaji sunusi yaga talakawa ne su rafi'ah na gidi, Sam be damu ba a tunaninsa ze samu kwanciyar hankali da ita. Aiko sati daya da Auren sunusi da rafi'ah komi na rayuwar Alhaji ya chanza, rafi'ah ta kwaso Rabin danginta takawosu gidan daman tin randa aka kawota a matsayin Amarya taxo da yarta Na'eema wadda bata da kunya ko kadan idanta tsakiyar Kai, bata bin maza ammafa sam bata da tarbiya. Tin Alhaji sunusi na magana a kan wasu abubuwan da rafi'ah keyi marasa kyau har yazo yadena mgnr ma baki Daya, rafi'ah ta shanyeshi tass be iya komi,gashi bata kaunar yaransa, sbda ta kula yana san yaransa. Aeezad ne kawai ya zame mata kadangaran bakin tulu. Tinda zuwan na'eema ta kyallara Ido a kan Aeezad tace ta kamu da Azababbiyar soyayyarsa, tin baya kulata harya dawo ya fara kulata,shima ya kamu da Azababbiyar kaunarta, zuwa lokacin tini yazama soja shida Zaks sede shi Aeezad ya fito da babban mukami yafi Zaks, Asalin sunan Zaks (zakariyya),. Tin lokacin Aeezad na tare da Esther, da akasa ranar bikinsu da na'eema ne Aunty nabeelah ta matsa dole Aeezad ya rabu da Esther , itama se lokacin tasan suna tare da Esther din, Tasha fama sosai kafin Aeezad ya rabu da Esther. Esther yar asalin osun state ce, tanada tsananin kyaun fuska Amma sede a jiki bata da shape, Aiki ne ya kai Aeezad can osun din suka hadu da Esther iyayenta nada kudi Allah ne kawai ya jarabceta da soyayyar Aeezad har tabiyosa garin Kano suka dinga sha'anin rayuwarsu kusan 1yr suna tare, Aeezad ne ya fara bare Esther a cikin leda. Yanajin dadinta Sbda nabeelah kawai ya rabu Da Esther ta koma gidansu bayan sunyi kaca-kaca, a zuciyarta har yanzu bata bar sanshi ba, kawai ja da baya tayi tasan dole akwai ranar daze nemeta ko ita ta nemeshi. Zuwa lokacin tini Hafsat yayar Aeezad ta gama karatunta na low ta hadu da Wani babban Dan kasuwa sukayi aure daman ta kosa ta rabu da gidan ubanta sbda ba dadih kwata-kwata Tin zuwan hajiya rafi'ah ta rikita gida, ta raba Sunusi da uwarsa ko gidanta baya zuwa, ta rabashi da Dan uwansa Daya tilo Alhaji Abubakar Wanda keda iyalansa yaransa hudu biyu mata biyu maza,, Sam Alhaji Abubakar be rabu da Dan uwansa ba duk yadda Rafi'ah taso su rabu abun beyu ba, time to time Yana zuwa da iyalansa gidan su gaisa ya tafi dasu, Sam baya damuwa da Amsar karnukan da hajiya rafi'ah ke musu, ita Sam bata kaunar taga kowa ya rabi gidan inba ita da danginta ba, kaf Yan uwanta Da kawayenta sun maida gidan Alhaji sunusi kamar gidan ubansu, hatta wanda yayi sanadin aurenta da sunusi wato alhaji hamza seda rafi'ah ta rabasu da sunusi . A haka Aeezad ya Auri na'eema Daren farko kawai yasamu ya kusanci na'eema 2tyms,daga lokacin be kuma samun abinda yakeso ba kullum na'eema na gidan hajiya mommy, hajiya mommy kuma liyafa taci gaba tini ta bude manya manyan kantuna wanda akeji dasu a garin katsina, ta shiga tura na'eema kasashe saro kaya domin ita hajiya rafi'ah bazeyu taje ba sbda ba boko, na'eema ce tayi karatu Sosai daman kuma kasuwanci ta karanta, itace a kan komi na kasuwancin hajiya rafi'ah ita bata San komi ba, ba Arabi ba boko, a haka itama na'eema take gina nata kasuwancin. Auren Na'eema da aeezad Ba abinda yasawa Aeezad se dumbin bakin ciki, ada bashi da wata damuwa seda ya Auri na'eema yashiga tashin hankali mara misaltuwa, nabeelah ce kawai ke bashi hakuri a kan na'eema wallahi da tuni ya saketa, nabeelah tace wlhi inya saketa bashi bata, shine fa Aeezad ya shiga taitayinsa kawai yaci gaba da hkrin zama da Na'eema Amma fa Yana cikin bakin ciki, tin Yana 20yrs yayi Aure Amma Auren mara amfani, gashi ba halin yayi mgna se kallo kawai. Hajiya rafi'ah kuwa duk yadda ta kaiga San ta haihu da Alhaji sunusi, Allah beyi ba, ko bari bata taba samu dashi ba,tabi bokayen harta gaji.
A bangaren Hafsat ta haifi yaron farko yaci sunan Alhaji sunusi ake kiransa da Noor, hajiya bilkisu tazo ta zauna da ita hartai arba'in, haihuwar ta biyu ce datayi tace a kawo mata Aunty nabeelah sbda hajiya bilkisu takuma tsufa sosai. tinda nabeelah tadawo gidan bata koma ba, daman tagaji da zaman gidan hajiya rafi'ah, sbda kiyayyar da rafi'ah ke nuna mata ya shahara, ita ke kaf girkin gidan, sam bata kaunar taga nabeelah ta zauna,ta tsaneta tsana me tsanani,haka itama na'eema ta tsani nabeelah sosai, har marinta ta tabayi Aeezad ya rama mata, Aiko ranar ansha fada a gidan , rafi'ah tace dole se Nabeelah ta bar gidan Aeezad yace baze yuba,, da kyar akayi settling problem din. Nabeelah batayi karatun boko ba Amma tayi na islamiyya har ta sauke alqur'ani a gidan, Amma batasan komi ba a kan karatun boko ba sede ta iya hausa kadan-kadan, tana saving number sosai Nabeelah takeson karatun boko tin tana karama Amma Allah be rubuta zatayiba. Sun taba zuwa da Aeezad kasarsu sau biyu ya rakata yaga mahaifiyarta wadda a ynzu tana iya komi da knta sede kullum cikin shan magani take, Aeezad ya yaba da dattako irin na mahaifiyar Nabeelah, Nan ya nemi madaidaicin gida yase mata a birnin niger ya zuba mata kayan Alatu, Ya Kaita unrah da hajji,. murna gun nabeelah baze misaltuba, sosai kima da darajar Aeezad ta karu a kwayoyin idanuwanta, saboda darajar mahaifiyarta da Aeezad ke gani yasa nabeelah Kara kaunar Aeezad tasawa ranta itama insha Allahu wata rana seta biyasa da ALKHHAIRINSA gareta, sede tasan har abadan ba wannan ranar saboda bata da abinda zata biya Aeezad dashi a rayuwarta. Sosai Nabeelah kejin dadin zamanta a gidan Hafsat, a fari de tasamu cikass ta yadda mijin hafsa ya fara nunawa nabeelah so na aure, taki yarda da hakan, shi kuma mijin hafsa ya kamu da soyayyarta,yadawo yace ko bazata Auresa ba ta bashi kanta domin ya riga ya kwad'aitu da surar jikinta, a Nan nabeelah tashiga tashin hankali, daman tin zuwanta gidan ta fahimci Baban Noor din nada neman mata, lokuta da dama in hafsa ta tafi Aiki har mace yake kawowa gidan su gama abinda zasuyi su tafi, Sam nabeelah bata sanar da Hafsa ba, kuma tayi alqawarin bazata sanar da ita ba har abadan, shima kuma baban Noor din ya kula nabeelah nada sirri shiyasa har yake wannan iskanci, a karshe yadawo kanta wai ze aureta yaga babu nasara yadawo yana nemanta da iskanci, Aiko nabeelah tace wlhi in be rabu da ita ba zata sanar da matarsa komi, Sam baban Noor ko a jikinsa domin yasan da wuya kota gayawa matarsa ta yarda, sbda ya gama mata komi, be raketa da komi ba,shi mutum ne me rike gida sosai ko cokali hafsa bata taba siya ba a gidan shike komi, aiki datakeyi raayinta ne, Amma duk month seya mata salary ita da yaranta, akwaisa da kokari, Amma sede yanada azabar neman mata,har yanzu kuma matarsa bata Saniba, domin yana bata so da kauna be taba chanza mata a fuska ba daze nuna yana neman matan waje ba. kalubalen Aure nada yawa, babu macen dake samun 💯 a dakin aurenta dole seta samu nakaso a wasu abubuwan sede Adduarh kawai yanayin mazan yanzu marasa control se hkri. Da Adduarh nabeelah tasamu ta kaucewa kaidin baban noor, amma fa har yanzu da kwad'ayinta a ransa,ita kuma nabeelah wannan shine kalubalenta nazaman gidan Hafsat gashi intace zata tafi hafsat zata dasa question mark a kan nabeelah, Dan haka dole ta jure daman ita damo ce sarkin hakuri, ba kasafai ka fiye gano damuwar taba, tanada dauriya da juriya.
Gameson littafin namijin zuma da Namijin duniya ze biya 1500 a wannan account din 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank cantact 08101626484.
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
*NAMIJIN ZUMA*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Free page group.
SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)
Free page6
Jin muryarta ya haifar masa dajin Wani irin sanyi me sanyaya ruwan jiki, ya sauke ajiyar zuciya 2tyms a jere ya lumshe Ido ya sake budewa kana yace. "mommy bani da lafiya wallahi..." Ya fadi a shhagwabe kmr me Shirin fashewa mata da kuka. Ya saba mata shagwaba Amma wannan Karan Se taji abun ya mata gatsal kmr bata saba ji ba. "Subhanallahi Meya sameka?" Ta fadi cikin sanyin murya sabanin farko data daga wayar. "Wani Abu nakeji mara dadih a jikina da zuciyata..." Ya fadi Yana mejin Sanyi a jikinsa kaso Dari na abinda ke damunsa ya ragu zuwa tamanin sbda muryarta kawai dayaji, shide be tabajin abinda yakeji ba a kanta kamar na yau,ada inyaji muryarta ba haka yakeji ba. "Kamar me babyna? Banason abinda ze dameka pls,, Ba munyi magana dakai ba a kan kan ka denasa damuwa a ranka Dan Allah kayi Adduarh itace maganin komi na rayuwar duniya, haba Jarumina!" Ta fadi tana mejin yanayi mara dadih a jikinta sbda ko a muryarsa ta tabbatar da Wani Abu na damunsa Amma setasha ko damuwarsa da na'eema ce. 'ajiyar zuciya kawai Aeezad ke saukewa yana me sauraronta kawai shi kadai yasan meke damunsa, shide yasan ba dmwar na'eema bace a wannan karon kuma besan meke damunsa ba. "kaji babyna !'' ta fadi jin yayi shiru sede ajiyar zuciyarsa kawai take juyowa ta cikin wayar. "Naji mommy insha Allahu zanyi Addu'ah kema kiyi min pls ....'' ya fadi cikin sanyi. Nabeelah ta jinjina tabbas yasa damuwa a ransa sbda muryarsa ta nuna alamar nadama a ciki duk yayi sanyi shida bakinsa be mutuwa Amma yau murus take jinsa, ko maganar batsa babu a bakinsa. "Zanyi maka kaji na mamansa..Amma se kayimin promise zaka denasa damuwar komi a ranka Dan Allah ka dinga sanyayawa a kan komi hkri fa maganin zaman duniya ne ..." ta karashe cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali. "Thank you,,, proud of you ..." "Nima ina alfahari dakai na mamanshi...Ka kwanta kayi bacci kaga time ya tafi dare yayi sosai ko baka koma kanon bane?" "No na koma..." "Okay Allah ya bada sa'ah ya tsareminkai gabas da yamma kudu da Arewa..." "Amin ya Allah mommyna..." "Seda safe ka kwanta zuwa 3 or 2 katashi kayi sallar ka gayawa ubangiji damuwarka nima zan tayaka Kai kukanka , Allah shike mgnin damuwowinmu..." Aeezad ya kara sauke ajiyar zuciya yace "Insha Allahu nagode mommyna sweet dreams.." ya karashe badan ransa naso ba, haka kawai ya tsinci kansa da rashin San ta ajiye wayar. "Nagode babyna bye..." Ba tare data jira cewarsa ba ta katse wayar,. Bayan ta katse wayar ya kasa cire wayar daga kunnensa seda wayar tayi 5mnt a kunnensa yana mejin muryarta na masa gizo, ya cire wayar daga kunnensa ya kure Screen din wayar da Ido, ya shafa creen din wayar ta kawo haske, picture dinta ne kan lock screen dinsa, tana zaune a farfajiyar hutawar gidansu, sanye take da doguwar rigar atamfa tasha daurin ture kaga tsiya yayin datai murmushi har wushiryarta ta bayyana, ba karamin kyau tayi ba, sumar goshinta ta kwanta luf-luf. Wani irin murmushi ne ya subuce masa yayin dayake kallon picture din nata kamar Yana gabanta haka yakeji a zuciya da kwanjinsa. "Kinada kyau na matsifa mommy!" Ya fadi yana me kara kureta da idanuwa, be taba sanin tanada kyaun daya wuce lissafinsa ba se yau. Bude wayarsa yayi yashiga gallery dinsa ya fara duba picture dinta da yaketa mata ba tare data sani ba, kaf wayoyinsa itace take cika masa gallery kuma duk photos din da yake mata ba tare da saninta yakeyi ba, itace a kaf lock screen and home screen na kaf wayoyinsa, sunyi fada da na'eema yafi a kirga a kan hakan tayi tayi ya cire yaki cirewa, har hajiya mommy seda na'eema ta gayama, hajiya mommy ta kira Aeezad Ta tambayesa meyasa zesa kaskantacciya a screen dinsa..." Aeezad yayi mata banza, Nan ta rufesa da bala'i da matsifa tace dole seya cire kaf pictures din nabeelah a wayoyinsa, cikin Mulki Aeezad yace " am sorry hajiya mommy Wallahi bazan cire ba, ai kowa abinda yakeso shi yakeyi... Kuma in zaku lura ai a matsayin uwa mommy take a gurina..." Sam hajiya mommy bazata iya jaa da Aeezad ba Dan haka ta kyalesa kawai ita kanta Tsoronsa takeji wasu lokutan sometimes data gansa se taji zuciyarta na yawaita faduwa kwarjini yake mata, dole sede ta bawa na'eema hakuri a kan hakan. Dadin karawar abinda ya kara dasa musu kiyayyar Nabeelah a ransu kenan saboda ganin yadda Aeezad ya bata muhimmancin fin komi na rayuwarsa. Seda ya Kai 2:am Yana duba picture dinta haka kawai kallonta kesa masa nishadi,. Mikewa yayi ya nufa toilet ya dauro alwala ya fito ya fara jero sallolin dare Yana me Adduah Allah ya yaye masa abinda ke damunsa , danyafi tunanin boyeyyen ciwo yakeyi Wanda shi kansa besan Kona menene ba. Har seda yayi sallarh asubahi kana ya kwanta bacci ya barawo ya figesa, bashi ya tashi ba se 9:am, ya shirya ya tafi office 11:am. A office dinma yau kmr jiya se tunani tunani kawai yakeyi , ya kirata a waya yaci saah ta dauka bugu daya,, wuni sukayi suna waya, har ya bar office din, a voice dinsa nabeelah ta fara fuskantar kamar ya soma chanzawa, nutsuwar dole ta fara shigarsa.
*Katsina state*
Zaune suke a falon hajiya mommy kusan su biyar, hajiya mommy se kawayenta manyan mata su uku manyan mata ne kamar Hajiya mommy, Dayar ce karama wato na'eema . Duk kaninsu sunada kiba sosai, ba kamar ma ita karamar cikinsu, dukda a zaune take hakan be hanani gano itadin gajera bace, sede fara ce sol, bata da kyau kwata-kwata ga kananun Ido, gashi duk tayi kiba tako ina, irinsu ne akewa lakani da badan fari ba se bola. Zaune suke sun Sa table a tsakiya Wanda ke cike da kayayyakin motsa baki se sanyin AC da AC kawai keta ratsasu tako ina masu Aiki nata hidima dasu, sauran ukun duk Aminan hajiya mommy ne na bugawa a jarida, kallo daya zaka musu kasan sunci sun tada Kai, tinda hajiya mommy ta Auri Alhaji sunusi Ta dena kawance da talakawa sede Yan gayu masu kudi kawai. Hajiya mommy dake zaune kan kujerar 1ctr tana facing na'eema dake zaune da wayarta kirar iPhone 13promax a hannu tana kallon TikTok. "Ke tinda Allah yadawo dake lafiya ya kamata ki koma dakin mijinki Ko zuwa gobe ne..." na'eema dake kallon wayarta ta dawo da dubanta kan Hajiya mommy dake maganar ta tabe baki cikin mamaki tace "Ai benan mommy Na tambayi me gadi ta waya ya gayamin ya koma kano ai.. kuma ma ko Yana Nan gaskiya bazan koma yanzu ba. " Hajiya mommy ta amshe da "Dole ki koma saboda kinsan de mijinki ba hankali ne dashi ba, na fuskanci ya fara kosawa gaskiya, danma Allah ya rufamin Asiri uban a tafin hannuna yake .." Cewar hajiya mommy. Kaf kawayen hajiya mommy suka kwashe da dariya Hadi da hada baki gun cewar "Da kyau ta gurina ai bakya wasa..." hajiya mommy tayi Wani farr da Ido tace "ina zan tsaya wasa,,, ai kaf gidannan d'anne ya zamar min. Kadangaran bakin tulu....ita kuma wannan wawiyar tasha nono ta zubar Sam ta kasa maidasa kmr masa a tandaa." Hajiya mommy ta karashe mgnrta tana kallon na'eema. Hajiya naja'atu babbar Aminiyar hajiya rafi'ah ta amshe da "ta yaya zata maidasa kamar masa kullum kina kan aikata kasashen waje sarin kaya?" Na'eema ta amshe da "Gaya mata dai mama.. " cikin tsiwa tayi maganar daman bata da alamar kunya ko a Ido.. "A gayawa uwar ubanki me dattin talauci..." Hajiya mommy ta amshe da kundumoma na'eema manyan ashariya. Na'eema ta hade Rai tana kunkunai. "In ban aikaki kasashen wajen saro kayayyakin ba ubanki dake kabari zan aika ya saromin shigiya kawai! Yar bura uba, Nan dattin talauci ne ya kashe ubanki! shegiya Dan uban ubanki tashi ki barmin falona kuma gobennan ki shirya ki koma gidanki ,in mijinki yadawo ya taddaki gidansa,karki jamin yazo ya gayawa ubansa, tin uban be tafuka Wani Abu yazo ya tafuka a kansa, tinda azabar sonshi yakeyi kamar hauka.." cike dajin haushi da bakin ciki na'eema ta tashi ta bar falon ta cika fam ta batse, a rayuwarta ta tsani yarfi kuma mommy ta matsifar iya disga mutum a cikin