Showing 30001 words to 33000 words out of 74791 words
Chapter 11 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
samun sukuni gaba d'aya hankalin shi ya koma kan Aminan shi ,
a haka ya wuni cikin far gaba ko abinci ya kasa ci ,
dere nayi wani sanyin zazzab'i ya fara ratsa shi hakan yasa da wuri ya konta bayan yayiwa Uncle saida safe ,
konci yayi amman ya kasa bacci,
daya rumtse idon shi sai ,
Fuskar Meenal yake gani cikin halin damuwa ga zazzab'i ga rashin konciyar hankali haka tasa ya mik'e yayi al'wala ya fara nafilfili yana nemawa Meenal d'in shi tsari daga dukkan abin cutarwa tsakanin mutum da aljan'
haka ya kwana kan k'afafun shi har sai 4:42 ya tafi masallaci ,
Bayan anyi sallan Asuba an idar Alhaji Ibrahim ya shaidawa liman akwai d'aurin auren da za'ayi ,
hakan yasa liman ya tsaida mutane daga fita masallaci ya shaida musu akwai d'aurin aure yanzu nan,
Shi kuwa Dr Jabeer labarin d'aurin auren ya sama mashi kuzari kad'an tunda yau za'a malla kamishi Amina a matsayi matar sa shiko yayi alk'awarin jiran ta koba dad'e koba jima zai jirata kuma yanzu ya fara k'aunar ta da nemota dan gani yake duk jami'an tsaron nan na banza ne ba gano mai ita zasuyi ba.
Cikin sanyin safiya da sa'ar dake ciki aka d'aura auren Amina Ibrahim mai dala (Meenal ) tare da Doctor Jabeer Muhammad kan sada ki dubu 50 tare da shaidawar dubban al'ummah dake rayuwa a ugguwar tasu da kuma yawun Malam Salisu Abduljalal limamin masallaci kenan ...
Bayan sun koma gida,.
hajia Aysha tare da Hajia Amina basu yi mamaki abinda ya faruwan ba dan sun san Alhaji Ibrahim mai dala kaifi d'aya ne in yace ehh tofa ehh d'inne sannan in yayi alk'awarin toh da izinin Allah sai ya cika,
shi kuwa Dr Jabeer cikin happy ya rink'a gayawa abo kanshi.
Alhaji Ibrahim ne zaune a d'akin shi ,
Hajia Aysha tayi sallama cikin sanyi taje ta zauna a k'asa kan carpet kusa da k'afafun shi kanta ta jingina jikin gadon
cikin sanyi ta kalleshi ya zauna ya dafe kanshi da hannu bibbiyu sai hawaye da ke bin fuskar sa ,
kanta ta sunkuyar yar cikin tausayawa kanta da mijin nata murya na rawa tace.
"Alhaji kayi hak'uri ka daina zama cikin irin wannan halin wannan yarinyar Allah ne ya bamu ita kuma ya fimu sanin yadda muke sonta da k'aunarta kuma shi ya b'oye mana inda taken da halin da ta shiga,
dan Allah kabar kukan nan mu fawwalawa Allah lamarinsa muci gaba da yimata Addu'a Allah ya baya nar mana da ita ya kuma kare mana ita a duk inda take Allah yasa tana hannun nagari."
Kai ya sunkuyar cikin rawan murya yace.
"Aysha Amina itace kad'ai y'ar da Allah ya bani ban rayuwa da ita wurin d'aya ba dan nayiwa Bappa alk'awarin na bar masa ita gashi tashi d'aya Bappa yace an d'auke ta an tafi da ita kinga ko, ko nace bazanyi kuka ba nayi k'arya."
Shiru tayi tana tunanin ko ta gaya mishi gaskiya tunda ita tasan gaskiyan maganar.
Lokacin da suka je Membila kamar yadda suka saba su duba yarsu su kawo mata duk wani abin buk'ata na rayuwa,
Hajia Aysha tana shiga cikin gida Lari kishiyar Inna tana ganinta ta kwashe da dariyar mugun ta,
harda ker keta Hajia Aysha kam tsoro ne ya rufeta matuka dan tasan Lari bata dariya sai abu ya b'aci ,
gashi Lari irin mutanen nanne masu bak'in abu a kan harshensu wanda in sunyi furucin yakan iya aukuwa wanda a musulunce ake ce musu masu kambbun baka,
tabbas kuwa mun san kambbun baka gaskiya ne,
toh hakan da Lari ta gane sai take bin kishiyar ta da yarta da jikarta da mugun baki.
Ita kam Hajia Aysha a firgice ta shiga d'akin Innarta,
halin da ta samu Innar a cikine ya bata tsoro,
cikin firgici da kulawa ta matso kusa da mahaifiyar tata wace tun randa Bappa ya d'aura Aure Meenal da General suka kuma tafi tare tun wannan ranan take kuka cikin k'unci da tsoro halin da jikarta zata shiga gashi tana tuna wanne hali Alhaji Ibrahim zai shiga ciki ga tausayi yawa y'artan,
cikin kuka ta rik'e hannun Hajia Aysha tana bata labarin yadda abin ya faru ,
haka yasa gaba d'aya suka riccab'e da kuka suna cikin kukan Bappa ya shigo gefen Hajia Aysha ya zauna cikin zubda k'ollah yace.
"Ki gafar ceni Ayshatu banyi haka dan cutar da Bodd'ina ba nayi haka ne dan na kare mutuncin ta na tsera tar da ita daga hannayen udawan nan da suka addabi Fulanin Gembu Membila su kashemu su sace mana yaran mu mata su kora dabbobinmu suna zalum tarmu gomnati ta sani bata d'auki mataki a kaiba sun maida mu tamkar bayin su! ko mu fulanin daji wanda ke bin shanaye da zamanrugogi bamu da hak'k'ine kan shuga banni mu ? ko dan mu a dazuka muke zama ? shiyasa ma zauna cikin birane basa tausaya mana ? basa kula matsalar mu ? ko mu ba raine da muba?."
Sai kuma yayi ta zubda k'ollah cikin cewa ban san me zan cewa Alhaji Ibrahim ba akan rashin y'arsa ince mai na Autar da ita ga wani bak'on da yazo mukayi kwana d'aya tan da shi?."
Cikin kuka Hajia Aysha ta rink'a girgiza kai murya a disashe tace.
"a a Bappa kar kace mai Autar da y'ar shi kayi ga wani wanda baka saniba in yaji haka zai ga kamar baka damu da y'ar shi bane zaiga kamar sakaci kayi da ita Bappa kawai muce mai dauketa akayi mu kuma cemai jami'in tsarone suka d'auke ta ,
daga nan in mun koma a zuba masu neman ta har Allah yasa a gane ta."
Da fari Bappa yak'i yarda da wannan tsarin,
toh ganin yadda ita Aysha take tsoron fuskar tar mijin ta da maganar yasa dole ya yarda ,
a ranshi kuma yake tunanin ya tabbata wotaran Aliyu zai dawo da Meenal daga nan sai ya cewa Alhaji Ibrahim jami'in tsaron d'aya tafi da ita ya dawo da ita..
haka suka gayawa Alhaji Ibrahim yayi kuka har ya godewa Allah.
( toh kunji fa dalilin dayasa Alhaji Ibrahim bai san Aure aka yiwa y'ar shi ba sannan ya kuma d'aura mata wani auren,
yake kuma ganin shi sace mishi y'arshi akayi..
Shiru Hajia Aysha tayi tuno yadda sukayi da iyayen ta kawai sai ta kasa fad'a mishi gaskiya dan tana tsoro zaice ta muna furcesa haka suka zauna sukayi ta kukan su ....
General Aliyu kuwa tunda aka idar da sallan asuba jikin shi a mace ya dawo gida,
cikin sanyin jiki ya zauna a parlour tare da lumshe idon shi ya resa wanne yanayin ya kaji,
yana cikin hakan yaji sautin muryar Minalin Haiydar tana kuka k'asa-k'asa kamar bazai ta shiba sai kuma zuciyar shi ta kasa daurewa ya mik'e jiki a mace ya shiga d'akin..
Gefen gado ya ganta zaune tana kuka dafe da kanta,
matso ta yayi cikin sanyi yace.
"Meenal meke faruwa?."
Kai ta d'ago cikin zunda k'ollah tace.
"Hamma Haiydar."
Sai kuma tayi shiru
cikin k'arin macewar jiki ya kalleta dan duk duniya mutum biyu ke ki ranshi da Haiydar Abban shi sai Ammin shi da ta guje shi sai yanzu kuma da yaji Meenal na ki ranshi da sunan.
Murya a sanyaye yace.
"Meenal me kike so? meke damun ki?."
Cikin kuka tace .
"Kai na Hamma Haiydar kaina zai fashe."
Ido ya tsurawa goshin nata tare kama lips d'inshi na k'asa yana tsotsa .
Jin taci gaba da kukan yasa ya d'an sunkuyo kanta hannushi na hagu yasa ya tallabe k'eyarta sannan ya d'aura tafin hannun shi na dama kan goshin nata ya danne tare da fara murza wurin,
cikin azaba da gigita ta rik'o hannayen shi tare da sakin kuka mai cin rai tanayi tana janye hannayen shi,
shi kuwa k'ara dirza wurin daya kumburan yakeyi dan ya samu ya bace,
cikin sakin k'ara da k'arfi ta sank'alo wuyanshi tare da komawa baya zata k'wace kanta ,
aiko cikin rashin kuzari ta fizgo General sai gashi ya fad'o kant........
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page 2β£5β£to2β£6β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*Tabbas wannan babu shakka (MOH ALLAH WUJI FURD'ATA, MOH ALLAH HOKKI B'URI MOH BABA HOKKI)*
Pml
Kanta cikin wani irin sanyin jiki da jini ya mirgina gefe tare da konciya rigin gine kanshi na kallon saman d'akin yayin da k'afafun shi kuwa ke reto a kasan gadon hannu shi d'aya kuma yana kan cikin ta,
so yake ya d'auke hannushi daga kanta amman ya kasa kuzarin shi duk ya tafi dan dama tun sanyin safiyar yake jin kasala ba abin da ke aiki a jikin shi sai zuciyar sa dake harbawa idon shi ya lumshe cikin sauke ajiyan zuciya daga nan ya kasa ko motsi mai k'arfi ,
a cikin ranshi kuwa sam bawai jin dad'in wannan yana yin yakeba gaba d'aya ya resa me kemai dad'i.
Ita kuwa Meenal shiru tayi tare dasa hannu ta rufe kan goshin nata zuwa kan idon ta sai hawaye dake bin fuskar ta sam ita bata san hannushi na kanta ba dan zafin da kanta ke mata shiyafi komai a gareta hawayen take zubdawa tare da fara sheshahekan kukan.
A hankali ya fara jin sautin kukan ta mai sanyi wanda sai in mutum ya kasa kunne zaiji,
shiru yayi tare da murza yatsatsa ma nunuyiya da babbar yatsarsa a hankali ya fara jin kuzari idonun shi yake son bud'ewa amman sunyi mishi nauyi dole ya k'ara lumshe idon cikin sauk'e ajiyar zuciya sannan ya tattaro sauran kuza rinshi ya mirgino ya juyo ya konta gefe d'aya yayin da fuskar sa ke fuskantar ta,
cikin k'arfin hali ya bud'e idon a hankali sannan ya tsura mata idon yana kallon ta,
ganin kukan take tayi,
cikin sanyi yasa hannun shi ya jawo nata ta mirgino ta fuskan toshi suna kallon juna har hancin General na tab'a goshin ta ,
cikin sanyi ya bud'i baki tare da cewa.
"Meehnarl."
Ido ta bud'e tare da tsurawa bakin shi ido,
shi kuwa gashin giran ta yake kallo jin bata amsaba yaci gaba da cewa.
"Meenarl kiyi hak'uri ki daure kinji ko murza miki wurin zanyi in kin daure na murza shi sau d'aya dai zai b'ace gacan magungunan ki nasha dana shafa insha Allah zai bari kinji ko?."
Rau-rau tayi da ido cikin zubda k'ollah ta tura baki tare da cewa.
"Hamma Haiydar zafi nake jifa"
Numfashin ya sauk'e tare da cewa.
"zan miki a hankali kinji ko."
Idon ta d'an d'ago ta kalleshi cikin tsoro da d'an zare ido tace.
"A hankali sosai fa?."
lumshe idon yayi tare da d'aga mata gira d'aya.
kai ta juya tare da tsuke bakin ta tace.
"A a ni ka amsa min da baki."
Yunk'uri yayi ya zauna tsakiyar gadon tare da nad'e k'afafun shi yana fuskar tarta yasa hannu ya kamo hannun ta d'aya ya jawo ta zaune itama ta nad'e nata k'afan ya zama suna fuskantar juna kusa da kusa cikin muryar da tafi kama da mai yin rad'a yace.
"Ehh a hankali zan miki,
Amman kar na fara ki fara kuka ko ki tureni kisa nima na fad'i na fasa kaina."
Cikin d'an tsoron dai tace toh .
"Da hannu d'aya zakayi kar tare min kaina da d'aya hannun."
Fuskar ta ya d'an kala a fizge sannan yace .
"Toh matso."
Matso shi tayi har guiwar ta tana gogan nashi sai kuma tana yarfa hannu alamun tsoro.
Shi kuwa mamaki yake irin wannan raki da tsoro ga shegen mita duk ita d'aya,
hannushi ya d'ago zai kai kan goshin nata ,
ita kuwa sai kawai ta sa hannu ta kamo hannun nashi yasunta tasa cikin tafin hannushi ta matse tana.
"Wayyo zafi wallahi tsoro nake ji."
Shi kam General Aliyu shiru yayi tare da tsurawa hanna yensu dake had'e wurin d'aya ido ko k'eftawa ya kasa sai kallon ta yake yadda ta dage tana murza mai tafin hannushi,
ganin yayi shiru yana kallon hannun ta yasa tayi k'asa da kanta cikin sanyi ta zare yatsunta daga nashi hannun,
sai ta d'an d'ago kan ta tura mishi tare da cewa.
"Ayyah Hamma Haiydar a hankali fa."
Gira d'aya ya sake d'aga mata sannan ya d'ago hannushi ya manna kan goshin nata ,
ido ta lumshe tare da yarfa hannu tana.
"Shiishhhh wayyohhh."
Cikin sanyi da sanyin tafin hannun nashi ya fara goga k'ulun goshin nata,
ita kuwa tuni sai hawaye da shan yaji take sai shishita takeyi ,
jin yana murzawa da d'an k'arfi sai kawai tasa hannayenta ta rarumo cinyoyin shi ta rink'a damk'ewa da yamutsa shi tamkar mai yi mishi tausa,
Sai ta matse cinyar sa tace.
"Hahhhhhhyi shihhhhh wahhyi Hamma Haiydar zafi."
Shi kuwa sai sauk'e ajiyar zuciya yake yana ce mata.
"Oh sorry Minali kiyi hak'uri daure kinji ko? saura kad'an."
Kuka ta kara saki jin k'ara murza wurin yake sai ta fara fizge kanta tana yin baya,
shiko ganin haka yasa shi d'ago hannushi ya tallabe k'eyanta dan ya murza wurin da kyau,
ita kuwa jin haka yasa ta k'ara matse cinyoyin shi cikin zafi da kuka tana .
"Wayyo Hamma Haiydar zafi."
Bai kula taba sai murza wurin yake,
Cikin zafin tayi yunk'uri ta afka kanshi cikin k'irjin shi tasa kanta sannan tasa hannu ta zagaye k'ugunshi ta k'amshin k'am jikin ta sai kuma ta saki kuka .
Shiko General wani irin numfashin ya furzar tare da rumtse idonshi sannan ya gyara zaman shi tare da sa hannushi a kan bayan ta yana shafawa a hankali cikin yanayin lallashi tare da cewa.
"Gud gerl sannu ko Meenarl kinyi k'ok'arin sannu kiyi shiru ya isa bazan k'ara murza wurin ba ya b'ace kinji ko."
Ita kam shiru kawai tayi tana jin kan goshin ta yana zut-zut lafewa tayi a jikin shi,
shi kuwa shiru yayi ba tare da tuna komai ba.
A haka har zuwa d'an wani lokacin sannan ya janye jikin shi tare da tureta gefe ya mik'e ya nufi parlour ba tare daya juyo ya kalleta ba.
ita kuwa madubin jikin kan gadon ta juya tana kallon fuskar ta,
murmushi tayi cikin goge k'ollan fuskarta taji dadi kumburin ya b'ace.
Shi kuwa yana fitawo parlour da niyar zai kira Captain Sani yazo ya ai keshi ya samowa wanna yarinyar abin da zata ci,
yana fitowa parlour ya samu kulolin abinci da filas wanda Anty Aysha ta
kawo,
kan kujera ya koma ya zauna cikin tsuke fuska da d'an d'aga murya yace.
"Meenarl ."
shiru bata amsaba,
"Meenal" ya kuma kira a karo na biyu.
Tana jinshi ta mik'e da sauri ta fito parlour,
cikin sanyi tazo gaban shi ta d'an zauna gefe,
fuska ya kuma tsukewa sannan yace.
"Zauna kici abinci."
Shiru tayi tare da sunkuyar da kai ,
A d'an fusace ya tura mata kulolin sannan yace.
"Kici nace ko."
Ganin yadda ya murtuk'e fuska yasa ta jawo filas d'in cikin sanyi ta zuba d'an ruwan tea a cup sannan tasa a baki tana d'an sha a hankali,
har tashanye sannan ta ajiye cup d'in tana kallon idon shi,
shiko ledan maganin ta ya jawo sannan ya b'alli d'aya ya mik'a mata,
ba musu ta karb'a tare da tsiyayo tea d'in ta had'iye maganin a haka yayi ta bata da k'waya d'ad'd'aya tana had'iye maganin da tea ,
shi kuwa mamaki yake yadda take shan tea kamar ruwa duk da dai na yanzu kam shan dolene.
Mik'ewa yayi rik'e da wani d'an farin roba gabanta yazo tsuguna sannan ya bud'e robar ya lakato maganin ya rink'a shafa mata a goshin nata,
yana gamawa ya mik'e tare da cewa .
"Zo ki konta kiyi bacci."
Baki ta d'an tura sannan tace.
"Toh"
Haka kamar dole ta konta ,
shi kuwa wonka yaje yayi sannan ya fito parlour ya kimtsa ya fito tsab cikin bedroom d'in ya koma gaban mirror ya tsaya tare da fesa turare,
har ya juya zai fita sai kuma ya dawo bakin gadon cikin tsurawa fuskar ta ido,
baccinta take cikin takurewa wurin d'aya kamar maijin sanyi,
kai kawai ya girgiza sannan ya jawo blanket ya rufeta,
ya juya ya fita.
Parlour Mama ya nufa cikin tsuke fuska sallama yayi tare da tsayuwa bakin k'ofar,
cikin tsana ziryan a idon Mama ta kalli ya Amir da ya amsawa sallaman General d'in ,
shi kuwa Abdul rumtse idonshi yayi cikin jin tsanar d'an uwan nashi wanda a halin yanzu baida burin daya wuce daukar fansa .
Shi kuwa a tsaye ya mik'awa ya Amir hannu suka gaisa sannan ya kalli Mama fuska a d'an yamutse yace.
"Ya Abdul da jiki."
"Ban saniba mugun d'an gidan mugaye wallahi a jutyi zuwa rafi dai tabbas wata ran tulu zai fashe wallahi tabbas akwai ranar nadama."
Baki ya tab'e sannan ya juya ya fita.
Yana fita ya Amir ya mik'e yabi bayan shi suka fitoh tare suna fita ya kira Captain Sani akan zasu biya gidan Alhaji Ibrahim su karb'i pictures d'in yarshi da aka sace d'in su rik'e dan pictures d'in zasu tai maka daga nan kuma zasu wuce Jaji.
Suna shiga gidan Alhaji Ibrahim Captain Sani yana gaba General yana binshi a baya,
a dai-dai bakin k'ofar General yaci karo da.....
*Kuyi hakurin da wannan sisters*
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page 2β£7β£to2β£8β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*YELAN BANDIRAWO MA KHAIRUJI NUMIN BANDIRAWO MA KHAIRUJI WANNU BANDIRAWO MA DO'A KHAIRUJI, TOH ALLAH JAB'I A LARAI KHAIRUJI D'ER HABARUJI KHAIRU HAMAD'A BE BANDIRAWO MAD'A TO EN NUMI ENFU EN BANDIRAB'E*
Pml
Da wani dan saurayi wanda bazai wuce sa'an Abdul ba cikin wani irin yanayi yaron ya zubawa General ido tare da mamaki cike a ranshi,
shima General d'in kallon yaron ya d'an yi cikin mamakin wannan abu sosai yake mamaki bin yaro yayi da ido jin yadda yaron ke magana.
"Ayyah sannu ban lura da kaiba ne."
Ido ya runtse cikin son tantance kalan muryan yaron wanda gaba d'aya ya tsaya mai cikin rai,
ganin shiru su duk ba wanda ya kuma magana sai budurwar dake bayan d'an saurayin tayi magana cikin kallon General.
"Kayi hak'uri bandirawo."
sai ta kuma kallin Saurayin wanda ke bin General da ido kawai tace,
"Ramadan mu tafi kaga lokaci na tafiya fa."
Saurayin da ta Kira da Ramadan ko,
sai ajiyan zuciya ya sauke tare da yin murmushi ya shafa sajenshi sannan ya nuna fuskar General ya kuma nuna tasa fuskar,
sannan ya matsa gefe tare da jan hannun budurwar nan yace.
"Zo mu tafi Husaina ta."
Janta yayi suka fita ta gefen General ita kuwa sai yarfe hannu tayi tana cewa.
"Can tafi da yawar ka wallahi ka dena kirana Husaaina inba