Showing 48001 words to 51000 words out of 74791 words
Chapter 17 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
uwarka banza mara tunani kana tare dashi baka San ya sacema yar uwa ba."
Ido ya sake fiddawa cikin rud'u yace.
"Daddy ina Aminan take?."
Zuwa yanzu Barrister ya gama hatsala cikin fushi ya yarfawa d'anshi Captain Sani wani irin gigiceccen mari tare da janyo hanna yenshi fiii har zuwa gaban Meenarl dake tsaye gaban Ummi,
cikin nuna Meernal d'in Daddy yace.
"Sani ga Aminan gatanan itace Aminar itace yar uwarka da muke ta nema itace yar d'an uwana Ibrahim wacce take Gembu Membila."
Kai Captain Sani ya rink'a juyawa cikin zama wani soko yace.
"Daddy wannan itace Amina yar uwata?."
Kai Daddy ya gyad'a mai tare da kallon Meenarl wacce ta tsurawa Sani da Daddyn ido fuska cike da alamun tabbaya,
shiko Barrister cikin kula yace.
"Amina ga d'an uwanki Sani wannan shine Hamma Sanin naki."
Ido suka tsurawa juna cikin mamaki shiko Sani tsoro da firgicin me zai faru anan gaba kad'an, naunauyan
ajiyar zuciya ya sauk'e ido cike firgici baki na rawa yace.
"Daddy kenan Amina itace Bodd'in Bappa sannan itace Meenarl matar ogana General Aliyu Abubakar Umar Rumoh?,
Daddy ya akayi haka ta kasance ina mafita? sannan kuma Amina itace watar Hamma Jabeer na? Daddy kaina kulle na rasa tinanina kamin bayani."
Ido Daddy ya tsura mai cikin jin haushin d'an nashi yace.
"Sani kana nufin dama kasan inda Amina take har kana cewa matar oganka ne?."
Kai ya gyad'a tare da cewa.
"Ehh Daddy nansata muna tare da ita tun randa aka d'aura aurenta da General."
A hatsale Daddy ya rink'a yarfawa Captain Sani maruka masu zafi da gigitarwa har sai da hankali mutanen wurin kab ya dawo garesu.
Sannan Barrister yace.
"Ashe baka da imanin d'an uwana da taka yar uwar da d'an uwanka kana sane Ibrahim har ciwon zuciya ya kamashi sakamakon batan wannan yarin yar sannan kana ganin halin da d'an uwanka ke ciki.
amman wai kana cemin kuna tare wuri d'aya ka barmu cikin rud'u har kuma kana cemin matar ogan kace ita,
waye aura masa ita su waye masu aurar da ita a duniyar nan bayan mu,
ya sato yarinya yazo yana cema matarsa ce."
Dafe fuska yayi cikin rawan murya yace.
"Daddy ka manta ni bansa Amina ba ban tab'a zuwa garin da takeba kuma ko pictures d'in ta tun nayarin tane na sani."
Mari Daddy ya kuma watsa mishi cikin nunashi da yatsa yace.
"Kalli fuska Rayhana ka kalli fuska Amina ko makaho in yashafa yasan yan uwane ,
Amman da yake kai kifeffen mutum ne mai karamar basira ka kasa gano hakan ,
sannan inma baka gane da kamannin su ba ,
Ina pictures d'in Amina da aka baku d'an nemota suma duk basu ganar da kai ita bace?."
Kai yaci gaba da juyawa tare da cewa.
"Daddy wallahi tallahi ban tab'a lura da kamannin Rayhana da Amina ba sai yanzu da ka fad'a,
batu pictures d'inta kuma wallahi tallahi Daddy ban kalli pictures d'in ba d'an muna fita na bawa General su a hannushi kuma shima wallahi bai gansuba d'an a hannun Captain Garba ya dank'a hotunan."
Alhj Ibrahim ne ya rik'e hannun Barrister sanda ya d'aga hannu zai kuma yarfawa Sani mari cikin damuwa da kullewar kai yace.
"Yaya Lawan barshi haka wannan magana akwai rikici a cikin ta dole mu barshi ya mana bayani a hankali."
Ita kam Meenarl sai ido take zarewa cikin mamaki ,
Ammi kuwa kuka kawai takeyi jin wani rikicin da ya had'e da d'anta da yar d'an uwanta ido take rumtsewa jin mugayen furucin da yayanta Lawan ke yiwa d'an nata sai kuka take tare da sheshshek'a Rayhana na share mata k'ollah itama fuskarta cike da hawaye ,
Ita kuwa Ummi mahaifiyar Meenarl kuka takeyi tare da nuna General tana.
"Wayyo Innata ina kike zoki ga wata fuska mai cike da kamannin fuskar da kike begen ganin tsawon shekaru."
Ammi kuwa zuwa yanzu ta durk'usa har k'asa tana fidda sautin kula mai cike da k'unan rai.
Shi kuwa General cikin tsuke fuska ya d'aga hannu tare da yiwa zugar sojojin alama su bashi hanya,
a take suka yi layi tare da sara mishi.
Taku d'aya yayi zuwa biyu yaci karo da Ramadan dake nufoshi cikin tsuke fuska ya tab'e baki tare da ci gaba da tafiyan ,
shiko Ramadan binshi yayi a baya cikin sanyi kamar rad'a yake cewa.
"Hamma Haiydar ni d'an uwanka ne! ni jinin kane! kalli can gacen mahaifiyarmu! da yar uwarmu Rayhana! Hamma Haiydar ina mahaifinmu? Hamma Haiydar nida Rayhana muna begen mahaifinmu."
Shiru yayi cikin son yaji abinda yaron ke fad'a da kyau d'an bai jishi da kyauba.
Shi kuwa Ramadan matsoshi yayi cikin sanyi zayyi magana kenan,
ita kuwa Meenarl ta juyo garesu,
cikin mamaki ta nufu gaban General cikin d'an d'aga murya tace.
"Hamma Haiydar kazo?."
Ido kawai ya tsura mata cikin mutuwar jiki dan kamannin Rayhana da Meenarl din ga maganganun wanna yaron da suke tsananin kama dashi.
Tana isa inda yake hannu shi ta kamo cikin happy tace.
"Hamma Haiydar zo zokaga mamana da babana ga zuriyata baki d'aya Hamma Haiydar ashe Captain Sani Yaya nane d'an uwanane shi shine Hamma Sani na k'anin Hamma Jabeer d'ina gacan goggona k'anwar mahaifi na ga Yaya Ramadan da Anty Rayhana."
Su Alhaji Ibrahim da Barrister kam da Hajia Amina binsu da ido sukeyi cike da mamaki.
Dai-dai lokacin Dr Jabeer yayiwa harabar gidan diran mikiya cikin wani irin yanayi yayi parking,
marfin motar ya bud'e tare da fita da sauri tin kafin ya k'arisa fitowa yake kiran Meenarl yana.
"Bodd'i na inaki ne bangan ki Bodd'i na Hamma Jabeer naki ne ke kiranki."
Gaba d'aya hankalin su ya koma kanshi ,
ita kuwa Meenarl cikin tsananin happy ta sake hannu Aliyu tare da yin tsalle da gudu ta nufi inda Dr Jabeer yake ,
tana zuwa ta mik'a mishi hannu ,
shima hannun ya mik'a mata tafin hannun su suka had'e wuri guda Dr Jabeer d'in yasa yatsunshi ya rumtse nata da k'arfi lokacin d'aya kuma suka yi..
Shi kuwa General idonshi ya rumtse da k'arfi......
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page
4β£3β£to4β£4β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*Wannan shafi sadaukar wane ga mahaifiyar y'ar uwarmu (Feedo Deedo y'ar ficika) Allah ya jik'an Ummah Allahu yasa ta huta muko in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani*
*Resa tum! mara tum! heb'a tum! seya tum!*
*Happy birthday 2 youuu my lovely Sadnaf Allah ya k'aro shekaru masu albarka*
Sai ya kuma bud'e idon nashi ya tsurawa Meenarl da Dr Jabeer d'in ido.
Shi kuwa Dr Jabeer jawo hannun Meenarl yayi suka d'an sunkuyo sai yasa hannu shi ya d'an ja k'afan wondoshi ya d'an nad'e tare da cire takalmin k'afar,
itama cire takalmin tayi sannan ta d'an janye siket d'in ta sama kad'an ta rik'e da hannu d'aya,
matsota Dr Jabber ya kumayi tare da manna k'afarsa da tata k'afar suka dai-dai ta yatsun k'afafun nasu,
hannuta da yake cikin nashi ya kara rumtsewa tare da juyowa suka kalli juna murmushi yayi cikin wasa da kulawa da yanayin da suka saba duk randa suka had'u sai sunyi haka sannan su nad'e k'afa d'ad'd'aya sama kad'an sai su d'an yi taku biyu zuwa uku cikin sigar wasa da shak'uwa.
Ita ma murmushi tayi tare da cewa.
"Hamma Jabeer inka fad'i sweet lede-leda zaka seyo min."
kai ya gyad'a mata sannan cikin wasa suka d'aga k'afafun nasu a tare sukayi taku d'aya ana biyu suka dire tare da sauk'e ajiyan zuciya sai kuma ya juyo gareta ya mik'a mata hannun suka tafa tare da yin murmushi.
Wannan itace d'abi'ar Dr Jabeer ko ince al'ada matuk'ar suka had'u sai sunyi wannan abin dan Dr tuk'uru yake biyewa Meenarl ya zama kamar abokin wasanta na yarinta.
Suna yin hakan sai ta kuma jawo hannu shi da k'arfi har kamar zai fad'o kanta cikin tura baki da salon wasa tace.
"Zo nan Hamma Jabeer zo muje ku gaisa da Hamma Haiydar."
Dariya Dr yayi tare da cewa.
"Wayyo Bodd'in Bappa kinyi k'arfi har zaki kada Hammanki a k'asa."
Sai kuma ya kalleta yadda take janshi tana ta dariya har dimful dinta dake tsakiyar d'an gemunta yana lotsewa.
kallon ta Dr yayi cikin kula da tsantsar farin ciki yace.
"Har wani Hamma Haiydar kika samu bayan mu duk bamu isheki bane?."
Ita dai janshi tayi har zuwa gaban General wanda ke tsaye tamkar an dasashi ko ido ya kasa k'eftawa mamaki cike a ranshi "ashe dama Meenarl tana dariya haka? ashe tana da surutu? ashe ita mai faram-faram ce? ,
kenan shine ya maidata shiru-shiru kenan shine ya cika zasuyar ta da tsoro ta zama ko yaushe a firgice take.
Su Barrister kuwa da Abba ido suka zubawa General da Ramadan dake tsaye gefen shi kamar su ta k'ara fitowa ras.
Shiko Dr Jabeer yana zuwa cikin happy da yanayin godiya da jinjina ya mik'awa General hannu suka gaisa shi a zatonsa General ne ya gano mishi Meenarl d'in,
shiko Aliyu hannun kawai ya bashi cikin sakewar jiki yake binsu da kallo yana sauraron abinda Dr yake fad'i.
" A gaskiya General Aliyu bani da baking yi maka godiya ko nuna farin cikina a gareka ba abinda zance da kai saidai ince Jxkllahu bil jannah nagode ka gano min matata farin cikina."
Ido ya kuma fitarwa woje baki cikin sanyi yace.
"Matar ka? matarka kuma?."
Hannun Meenarl Dr Jabeer ya kuma jawowa cikin yanayin farin ciki yace.
"Eh matata ce kuma k'anwa tace jinina ce ita kuma tintini an d'aura mana aure da ita."
Cikin murtuk'e fuska da b'acin rai ai shi a ganin shi wannan ma ai rainin hankali ne tunda dai shi yasan Meenarl aurenta aka d'aura mai kuma mahaifinta ne ya auramai ita kuma a can taraba cikin dajin gembu Membila iyayenta fulanin daji masu kiwon shanu ma zauna cikin riga,
sannan ya kuma za ace ga wasu sabbin iyaye wai natane me ya had'a Taraba da Kaduna me ya had'a babarbare da ba fillatani tinda yasan Alhaji Ibrahim su barebari ne.
Tsaki ya ja da tuna wad'an nan abubawan,
cikin tsawa da hatsala yace.
"Kai Captain Sani zonan."
Shiko Captain Sani ido kawai ya zaro d'an tabbas yasan ya shiga tsaka mai wuya sannan duk ta inda ya motsa shine shi kuwa yasan lallai anyi aure kan aure,
ciki bin umurni ya matso inda General d'in ke tsaye ya coge sai kad'an yar k'aramar bindigarsa yakeyi.
Ita kuwa Ummi jin sautin muryar General ya k'ara tsananta bugawar zuciyar ta tana tuno woni sautin murya irin na General sak hawaye ne ya k'ara wonke fuskarta tuno tun tana k'arama rebonta da jin wannan muryar.
Ammi kuwa cikin kuka ta d'ago fuskarta tana kallon fuskar d'an nata cikin kuka ta rik'o hannun Rayhana tare da cewa.
"Rayhana kalli fuskar d'an uwanku ji muryarsa ki kalleshi da kyau Rayhana dan komai nashi na mahaifinku ne ba abinda ya rabashi da Abbanku,
farinshi tsawonshi fuskarsa muryarsa gashi kanshi sajenshi fushinsa komai nashi na mahaifinmu ne."
Ido Rayhana ta zuba mishi cikin kuka tace.
"Ammi kenan Ramadan ma da Abban mu yake kama?."
Kai ta gyad'a mata cikin kukan.
Shi kuwa General Captain Sani na zuwa gaban shi ya juya cikin fad'a ya kalli Captain Garba da muryar bada umurni yace.
"Kai Captain Garbage maza kwashi wad'an nan zugar sojojin da ka kwaso kayi woje dasu."
"Yes sir" Captain Garba yace tare da juyawa ya kalli sojojin yace.
"Ku shiga mu tafi."
Shi kuwa Captain Sani kai kawai ya sunkuyar cikin goga k'afarshi a k'asa,
shiko Dr ido ya tsurawa General ganin yadda ya murtuk'e duk annurin fuskarsa ya bace,
sannan ga Meenarl da ya ganin ta wani Sha jinjin jikinta ta nitsu a gaban shi tana wasa da yatsunta,
a d'aya gefen kuma hankalishi ya tafi kan Amminshi goggon shi k'anwar Daddyn shi kenan can kuma ga Ummi dake kuka tana kallon fuskar General d'in.
Shi kuwa General lips enshi na k'asa ya kamo ya matse lokacin da yaga sojojin duk sun tafi sai shi da Abdul sai mutanen gidan,
cikin tsuke fuska ya kalli Captain Sani da yayi k'asa da kanshi rai a bace yace.
"Captain!."
Shiru Sani yayi dan a wannan yana yin fuskar General yana bashi tsoro ,
shiko General jin bai amsa mishi ba ya hatsala shi cikin zafi ya ware hannu shi ya zabga mishi wani gigiceccen mari.
Cikin zafin Marin Captain ya d'aga kai murya a d'an sake yace.
"Na'am."
Meenarl ya nuna tare da cewa.
"Wannan wacece a gare ka ? kuma me had'inta da zuriyar Ku? me ya had'ata da yayanka Dr Jabeer? asani nadai Ku musulmaine ni kuma musulmi ne! amman kaji Dr yana cewe Meenarl matarsa ce? me ya had'a Taraba da Kaduna? meya maida matataaah matar Dr Jabeer?."
shi kam Captain Sani ya rasa bakin magana sai kai yake juyawa,
hakan ya hatsala General yasa shi ya rink'a zuba mishi maruka yana.
"Ina magana kana jina kayi shiru ko wani munafurcin ka koyo."
Barrister Lawan kuwa dashi da Abba da sauri suka zo Abba ne ya kamo Captain Sani shiko Barrister cikin fushi da b'acin rai yace.
"Kai wanne irin tantirin ne? dame kake gadara? da zakazo har gidan da kasace musu yarsu sannan kana dukan d'an gidan shin matsayin hauka ne dan kai General ne sai ka taka wanda make so dan rashin tarbiya toh ka sani da Barrister Lawan kake ja ba sai na gaya maka ba duk mara gaskiyar k'asran tsoro yake a had'a shari arsa da ni bare kai da na kamaka dumu-dumu kasace min yar d'an uwana".
Daga nan cikin b'acin rai Abba ya jawo hannun Meenarl tare da nunata yace.
"General Aliyu wannan y'atace nine ubanta mahaifi."
Sai kuma juya yanuna Ummi tare da cigaba da cewa.
"Gacan maihaifi yarta,
inda kaje ka sace min y'ata kuwa gidan kakanninta ne ma haifan Aisha."
Cikin fushin ya bawa General labarin yadda ya auri Aisha da kuma sanadin zaman Meenarl a can sannan ya karishe maganar da cewa.
" kuma na aurawa Jabeer ita yanzu a matsayin matarsa take."
Kai General ya rink'a juyawa tare da bugawa Captain Sani tsawa yace.
"Kai Sani Meenarl wacece a gareni????."
sannan ya kamo hannun Meenarl ya fizgota....
*Kuyi da wannan hak'uri sisters da nayi niyar yin mai yawa so inada wani uzurine*
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page
4β£5β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*Moh Allah hokki b'uri moh baba hokku*
*Masu tabba yata menene ma,anar BANDIRAWO? toh ga ma'anar BANDIRAWO na nufun D'AN UWA ko Y'AR UWA duk yana d'aukar ma'anar BANDIRAWON*
Kusa dashi cikin tsawa yace.
"Meenarl dai matata tace! kuma matar auren sunnah aure na halal kuma da waliyinta wanda shine madadin uba a gareta kuma aurene da aka d'aura da shaidu kuma ga Sani wanda ya kasance d'aya daga cikin manyan shaidun,
batun y'ar kuce jikar Bappa ce ni duk bansan da wannan zancen ba,
dan amanarta aka bani Bappa ya bani amanarta cikin k'arfin guiwa da yak'inin zan rik'e amanar shi yasa ya aura min ita."
Captain Sani ya kuma fuzgowa cikin hatsala yace.
"Shin Sani kurma ka zama ne ko ka manta lokacin da ka mik'a kudin sadikin Meenarl da hannun ka?."
Kai Captain ya rink'a juyawa cikin sanyi ya kalli General yace.
"Kayi hak'uri oga tabbas ban manta ba tabbas lillahi ni shaida ne kan aurenka da Meenal."
Sai kuma ya juya gun Daddyn shi tare da kallon Abban Meenarl d'in yace.
"Daddy kuyi hak'uri wallahi tabbas General ba sace Meenarl yayiba aura masa ita Bappa yayi kuma aure na suna bisa koyarwan Annabin mu,
Daddy kune kukayi kuskure kune kuka d'aura aure akan aure Daddy General Aliyu ba mutumin banza bane kamar yadda kuke zaton ba,
Daddy ka tuna alkhairan General a kaina,
Daddy kasan General mai mutunci ne a gareni."
Shiru Captain yayi tare da tsurawa iyayen nashi ido cikin fahimtar wa,
amnan ina sunyi nisa bazasu gane ba,
Shiko Dr Jabeer cikin tafasan zuciya ya kamo hannun Meenarl ya fizgota jikin shi cikin tsawa da harzuk'a yace.
"Kuji zancen banza maganar wofi General zaifi ma kyau kaja motarka kabar gidan nan,
dan fad'a kake cikin rashin gaskiya dan Bodd'i tawace matata ce,
in kai a sama ka sameta ni tun tana yar Babynta nake rainonta."
Hannu shi ya d'aura kan k'ahon zuciyarshi tare dacigaba da cewa.
"Meenarl da kake fad'i itace bugun zuciya taπ tun tana k'arama nake dakon sonta a zuciya ta k'anwata ce matata ce."
Daddy ne ya kalli General a fusace yace.
"Ina fatan dai kasan nan ba gidan ubanka bane ? so don haka ka b'ace min da gani yaro ba tarbiya ancema yarinya yarmuce ka tsaya kana zuba mana rashin kunya."
Abba ne ya kalli General cikin takaici yace.
"Aliyu Meenarl y'atace kuma nine ubanta kuma ni zan aurar da ita nike da hakk'in zab'a mata miji."
Sannan ya juyo ya kamo hannun Meenarl ya rik'e tare da cewa.
"Y'ata zomu tafi."
Janta yayi suka nufi cikin gida ita kuwa Meenarl sai juyowa tayi tana.
"Abba Hamma Haiydar baida lfy fa Abba d'an Allah Ku kaishi asibiti,
Hamma Sani kai kasan baida lafiya dan Allah ka gayawa Abban shi akaishi asibiti."
Sai kuwa ta juya gun Dr Jabeer dake binsu a baya tace.
"Ayyah Hamma Jabeer ka duba Hamma Haiydar wallahi baya da lafiya."
Ammi kuwa zuwa yanzu sautin kukanta ya cika wurin ita kuwa Ummi baki na rawa ta tsaya gaban mijinta da yarta cikin sanyi tace.
"Wallahi Abban Bodd'i,
Aliyu mijin Bodd'i ne tabbas aurenta Bappa ya d'aura kubi abin nan a hankali."
A take fuskar Abba tayi jazir dan b'acin rai a fusace yace.
"Toh ya sakar min yata yaje ya rubuta mata takardar sakinta yaron da bansan iyayenshi bane zan bashi auren y'ata waya san asalin shi tunda iya sanina ba a gaban iyayen shi yake ba."
Da k'arfi General ya rumtse ida nunshi cikin tarin bak'in ciki gaba d'aya ranshi ya gama b'aci da zafin furucin da Alhaji Ibrahim da Barrister ke mishi,
lips enshi ya ciza cikin tafasar zuciya ya juya tare da damk'e hannu shi yace.
"Ni dai ba shege bane! ina da asalina! ina da ubana! kuma ni musulmi! ne kuma ni ba tantiri bane! kamar yadda kuke fad'an! kuma ni ba b'arawo bane! bare na sace muku yarku! ga d'anku Sani shi shaida ne a kaina! ba saceta nayiba!,
Meenarl kema kina sane ba saceki nayi ba?! Bappa da kanshi ya dan k'amin hannu ki a cikin