Showing 3001 words to 6000 words out of 74791 words
Chapter 2 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
Aliyu yayi ta shiryer-shiryen shi shi kad'ai ba tare da neman shawaran kowa ba sai Baba da yacewa an turashi taraba wani bincike.
Daga manya shi biyu kuma a wurin aiki an bashi pars na tsawon 2 weeks.
Yau jummah tun safe Sani ya had'a kan sojojin da zasuwa Aliyu rakiyi Wanda an hadasu da sabbin Hilux dan sanin hanyar da zasu dosa hilux 6 da sojojin 27 aka had'a sukayi sammako tun sanyin safiya suka nufi hanyar Adamawa Yola,
yayin da shiko Aliyu da Sani jirgi zasubi zuwa cikin Adamawa dan babu na Taraba,
sai na Kaduna 2 Yola suka samu hakan yasa sai dai su diro jihar Adamawa daganan su ma tawagar sojojin dake ta howa a motocin sun iso daga Yolo sai su kama hanyar Taraba da mota.
Su sun tashi tun safe,
suko sai 4 na yamma jirgisu ya tashi zuwa Yola.
4:25 pm jirginsu yayi diran mikiya cikin..!!!!!!
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* pg 3⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*pure moment of life writers*
P.m.l.w
jirginsu ya dira cikin International
Airport na Yola,
bayan d'an wani lkcin matafiyan suka rinqa fitowa d'aya bayan d'aya,
cikin sanyi General Aliyu ya zuro qafarsa tare da shaqar iskar garin Adamawa Yola ,
Sani na biye dashi a bayan shi cikin salon shi na murtuqe fuska suka sauqo yayin da
Airport din ya ke cike da sojoji maqil,
domin ko ya samu tarba daqa shugaban sojoji na jihar Adamawa tare da tarban fadawan masarautar Sarki Muhammad barkind'o,
don karramawa ga jarumin dake sadaukar da ransa domin baiwa qasarsa kariya.
Kai tsaye daga Airport din cikin Yola suka nufa domin kai gaisuwa ga Sarki Muhammad,
daga nan kuwa barrack suka dawo inda nanma suka gaisa sama-sama daga nan suka fito suka kama hanyar Taraba.
Tafiya suke cikin gudu dan su samu su isa da wuri
tunda Yola 2 Taraba tafiyar awa 3 ne
bare su suna tsula gudu,
uwa uba kuma su duk inda suka biya basu hanya ake,
shi yasa 9:00 pm suna cikin birnin Taraba jaligo ja gari na baba Abasu.
Barrack din suka wuce tare da tarbar mutanen jihar
a barrack din ya diro sauran sojojin yayinda ya fita shida captain Sani suka wuce jummu hotel dakin Sani na qasan nashi ,
shi kad'ai ya tare a dakinshi daga shi sai tunanin shi da ya cika mar rayuwa wonka ya samu danyi sannan yazo ya kwanta tare da jawo laptop enshi ya fara aiyukan shi tare da banda umurni ga sojojin da suke qarqashin sa,
haka dai baiyi bacci ba har zuwa 12:30: Am sannan ya d'an rumtsa.
Kashe gari suna idar da sallah suka kammala shirin su suka kama hanyar Gembu,
Tafiya mai dad'i hanya mai cike da abin al'ajibi hanya mai tarin abin sha'awa hanyar da duk fad'in qasarmu ta Nigeria bamu da irinta
hanya mai cike da tsirrei da qoramu da koguna da lambuna tare da sanyi mai dad'in ji yanayi mai sanya sanyi a zuciyar bani Adama
hanyar Gembu 2 Membila kenan.
Shi kam Aliyu zaune yake a bayan yayinda yake tsurawa dajin ido mamaki
yake ganin yadda fulani sukawa dajin qawanya duk inda ya cillah idonshi dabbobi yake gani bila adadin sai mata masu fasa cikin dajin da qoren nono da ka shigo sashin wurin zakaga banbanci matan wurin da sauran matan sauran jihohinmu wannan ba shati fadi bane
matan Gembu sunyi zarrar da tasa sunka doke matan kamaru ma
Kyawun halitta haiba cikar zati uwa uba tsafta duk wanda yasan matan Gembu ya sansu tamkar larabawa suke
fararene tas masu yalwar gashi suna da sura ta haqiqa.
10:00 Am
Suna cikin garin Membila daga nan
Aliyu ya tsaya tare da tara yaran shi cikin sanyi,
ya tsura musu ido d'aya bayan d'aya
da salon bada umurni yace.
"Sani daga nan su Garba zasu tsaya ni da kaine zamu qarisa cikin dajin domin saimun ga yanayin wurin sannan mu shigo baki d'aya".
Cikin bin umurnin suka sassara mai tare da qamewa daga nan,
ya jaqoran cesu zuwa tantin sojin dake kula da dajin Membila sabida yawan kashe fulanin wurin da akeyi.
Sai da ya tabbatar ya sama musu duk abin buqata,
sannan suka wuce shida Sani.
Tafiya ma budin ilimi taken Mahmoud Nagudu,
Tafe suke Sani na mishi hiran yanayin wurin tare da nuna mai tsirrai masu ban sha'awa,
shi kam Aliyu bin hanyar yake da ido cikin mamaki tabbas hanyar Membila abin kallone da bada mamaki,
tafiyar suke Sani tun yana surutu har yayi shiru.
Cikin sanyi ya kalli Aliyu tare da cewa "Oga inaga daga kan dutsen nan hanyar ta tsaya ba ci gaba sai waccar hanyar da muka wuce".
Kai ya d'an juya tare da cewa ka zagaya bayan dutsen nan ta gefen dama akwai y'ar qaramar hanya tabin shanu sai mubi ta wurin"
Haka suka kutsa cikin dajin yayinda suke ta ratsa tsaunuka wani wurin badan Hilux bane da bazai fitaba.
Wasa-wasa sukayi yawo cikin tsaunu kan duk ya zagaye rigar Fulani dake ta wurin baiga rigar Rumoh ba,
gashi da zaran sun tsaya a wasu rigan dan sunyi tabbaya sai su samu ba maza sai mata matan ma yara dan mazan sun tafi kiwo matan ko sun tafi tallar nono shiyasa sai yara suko da yaran sun gansu da yinifon din sojojin da bindiga a hannusu sai su gudu.
A hakan har d'imuwa ta fara dibarsu cikin jarumta Aliyu yacewa sani
" Muyi gaba gancan wani ma ki yayin".
suna zuwa gunshi daga d'an nesa dashi sukayi parking sannan suka fito tare da cire rugunan jikinsu suka bar best sannan suka qarisa gunshi cikin sanyi dan gudun kar ya tsorita Aliyu yai gyaran murya tare da cewa.
"Akuma *BANDIRAWO*, noi layde e dabbaji men"
Sannu dan uwa ya daji da dabbobin mu"
Cikin mamaki ya juya gunsa tare da yin magana cikin fillanci yace .
"Ra ga Allah Surbajo toi yiftu d'on Mi hetayi on"
Kai d'an Saurayi ina kuka fito ban ganeku ba"
Daga nan kuma sukaci gaba da magana cikin fillanci yayinda Sani ko ya bushe a tsaye mamaki yake wai ase dama General Aliyu ya iya fillanci ji yadda ya juye kamar cikin su yake rayuwa shi kam sai murmushi yake dan tabbas Aliyu ya burgeshi ase akwai masu adana yarensu dan irin wannan ranar.
Suko Aliyu zuwa yanzu d'an fullo har ya masoshi tare da rik'o hannushi ya miqa mai sanda cikin fillanci yace.
"Ko zakayi kiwo?"
Ba kin shi kawai ya d'an motsa alamar murmushi sannan yace .
"Yanzu dai tabbaya muke sai wani jiqon in na kuma zuwa sai muyi kiwon ko".
Ido ya tsurawa fuskar Aliyu tare da cewa.
" kai ko bakayi fillanci ba wlh zatinka ke muna kai asalin ba fulatanine gaba da baya,
dan haka ba matsala menene tabbayar?".
Ajiyar zuciya ya d'an sauqe tare da yamutsa fuska yace .
"Rigar Rumoh nake nema".
Cikin tsoron ya zare ido tare da ja baya gani da nunashi yana fad'in.
" kodai kune mutannen birnin nan da kuke zuwa kuna korar mutanen rigar Rumoh! kuna kashe su! kuna kama musu yan matan su! kuna tafiya dasu birnin! sannan Ku sace musu shanayensu! da raqumansu! kuna zalum tarsu?".
Sani ne ya buga mai tsawa cikin fad'a yace.
"Shi wannan mai gaskiya me baya aiki sai na gaskiya shi ba mugu bane shi mai taimakon wanda aka zalum tame".
Cikin tsoron yace "ya zanyi na yarda?".
Qara matsoshi yayi tare da cewa.
" Shin kana jin General Aliyu Muhammad Umar Rumoh?
shin kasan shine shuga ban kare haqqin makiyaya dake cikin fad'in wannan qasa tamu da suke cikin dazuzzuka da tsaunuka? shin ko kasan shine soja na forko d'aya rasa cikin dajin Sambisa ya kuwa ci nasara?".
Shiru yayi tare dayin murmushi ya matso kusa da Aliyu a hankali yace.
"BANDIRAWO ka makaran kana can kana baiwa wasu sashuka na qasarmu ranka dan ka karesu yayinda masu b'arnar sukazo tushenka suka tarwatsa mutanen ciki suka koresu suna kashe na kashewa suka qona na qonawa".
Cikin tafasan zuciya Aliyu ya rumtse idonshi tare da cewa.
" Muje ka kaimu Rigar Rumoh na gani".
Shiru yayi tare da siyayar da hawaye ya kamo hannun Aliyu cikin takaici yace.
*Bandirawo* a inda muke tsayennan cikin asalin rigar Rumoh ce ai an dad'e da watsa rigar Rumoh ta zama wurin kiwonmu yau kimanin shakaru 4 kenan da y'an ta adda suka hana rigar zaman lafiya sabida suka watsasu,
Kaga wadan can rigogin dake kusama
kullum cikin baraza na ake musu kan dole subar nan ".
Jikin jijiyar bishiyan da suke qasanta Aliyu ya zauna tare da dafe kanshi har zuwa d'an wani likaci sannan kuma ya miqe tare da cewa Sani.
" Shi kenan na rasa ma dafa na rasa ma dosa mu tafi Sani zan qare rayuwa ta ba farin ciki".
Cikin sanyi da tausaya mai Sani ya miqe tare da cewa"oga kaqa yamma tayi kuma ba zamu gane hanyar ba mu roqi Gainako ya rakamu".
Matsosu gainako yayi ganin suna tafiya dan Aliyu ya muna baya buqata.
da sauri yasha gaban sa cikin sanyi da jin son shi yace.
"Bandirawo kalli kan dutsen can da wancan qoraman".
Ido ya tsurawa dutsen da saman qoraman sai wani irin farin hayawi ke tashi tuni wurin ya fara rufewa da hayaqin sai duhu ya fara qaruwa".
Maganar Gainako ta kuma katseshi cikin fillanci dai har yanzu yace.
" kaga wannan yanayin shi muke kira da *Labbare* yanayin ne da yake sauqa da zaran yamma tayi dashi muke kwana sai kuma gari ya waye yake fara tafiya da zaran labbare ya sauqa ko dabbobinmu basu fiye gani sosaiba kuma sanyine ke ratsa ko ina sannan tanan baku da hanya fita sai ta bayan dutsen inko nan zakubi dole sai kun kwana a nan kafin ku samu fita sabida yanzu duk ta inda zakubi zaki hadu da hayaqin labbare da kuma makiyaya sun taso kiwo".
Ido Sani ya dan kuma warewa ganin a take wurin ya fara wani irin yanayin duhu da sanyi mai tsananin gaske.
Shi kam Aliyu duk bai ganiba don baijin komai
Amman gani tako ina dabobine ke faso dajin na fita yasa dole yabi hanyar zagayen yayin da Gainako ke binsu a baya tare da sakin wani irin ihu irin na makiyaye da dabobnsu,
aiko sai ga dabobin sun biyishi a baya.
Cikin d'aga sauti yace.
"BANDIRAWO Ku biyoni zan nuna muku hanya".
Jin haka yasa suka rinqa bin shi a baya da motar su.
Tafiya mai dan nisa sukayi
Sai gasu sun fito ta bayan wata rigar Fulani mai matuqar kyau da tsari rigace mai zagaye da ni'imomi da korayen tsirrei ta bayan rigar shukoki ne masu matuqar kyau daga gaban rigar kuma wata koramace mai ruwan garai-garai ke gudana sai dutsen dake gaban qoramar gaba d'aya wurin sai ya banda wani kalan qamshi da ni'imah.
Gainako tsayuwa yayi tare da ajiye sand'ar kiwonsa a wani fili mai farin yashi dake gaban qoramar sannan ya juya gunsu dai-dai lkcin wani farin dottijo ya fito cikin wani gida daga dukkan alamu gidane sai dai yanayin gidane mai zagaye da katanqar manyan duwatsu,
kai tsaye gunsu dottijon ya nufo cikin sanyi da tsura musu ido tare da murmushi
cikin sanyi yace.
(" Surbajo waru d'o")
"D'an saurayi zo nan"
Cikin sanyi suka matsoshi Sani ne ya gaida shi shiko Aliyu kawai bin shi da ido yake .
Cikin sanyi ya juya tare da cewa su biyo shi.
Shi kam Aliyu bin shi kawai yake cike da mamaki inane nan kuma Gainako ya kawosu.
Suna shiga tsakiyar gidan
dottijon yace
"Badd'i waru an e Inna waziri"
Badd'i kizo keda Inna waziri kuzo da madara da ruwa munyi baqi".
dai-dai lkcin wata Yar budurwa mai kimanin shekaru 16 ta fito daga cikin wata bukka riqe da gwaryya a hannuta kanta a qasa tafiya take cikin kula da qoryar karta subuce ta fad'o ta fashe,
tazo dai-dai kan Aliyu da yake sunkuye yana qoqarin kwance but din qafafunshi qoryar tai qasa......
*Wasa farin girki masu karu yanzu muka fara shiga cikin labarin muje zuwa*
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 4⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writers
P.m.l.w
*Dedicated 2 Ummee pinky & Becky Tika tare da Hanan smart*
Ta fad'a gefen shi lokaci d'aya ya d'ago kanshi cikin sauri don jin d'umin madarar shanun da ya ratsashi gashi duk ya watsumar a jikinshi har izuwa fuskar sa.
Harara ya cillah mata cikin murtuqe fuska lokaci d'aya ya had'e gira sama da qasa yana mai binta da wani irin mugun kalloh,
duk jikin sa sai d'iga yake tal-tal da nono.
Ita kuma Bodd'i qasa tayi da kai sai kerma da jikinta keyi kar-kar hatta numfashin ta sai da ya sauya salon harbawan da yake,
cikin tsananin tsoro yana yin General Aliyu baki na rawa ta rinqa d'an ja da baya cikin sanyi tace.
*"Wad'u muyal BANDIRAWO* kayi haquri dan uwa".
Cikin murtuqe fuska ya kuma watsa mata wani mugun kallo da yanayin jin haushin abinda tai mai yaja wani irin ajiyar zuciya tare da jan d'an gajeren tsaki dan haqiqa kunyar dottijon nan yaji ba dan shiba da zai zuba mata mari kam ai ita ba makauniya bace.
Itako tuni ta jabaya gun dottijon cikin fillanci tace.
"Bappa bari na kawo musu wani nono"
To yace tare da cewa.
"Ki kula fa karki sake zubda Wanda zaki kawon."
Kai ta gyad'a mai tare da juyawa cikin sanyi ta komai cikin gidan.
Shiko General cikin sanyi da d'an rad'ad'in zafin madarar ya kalli dottijon cikin fillanci yace.
"Bappa ni yanzu zan d'an watsa ruwa a jikina don na cire wannan kayan".
Toh yace tare da miqewa yana fad'in .
" Toh bari naje na sa a kawoma ruwan d'umi dan sanyin zaima yawa gashi labbare ya fara sauqa ga sanyin magriba ga sanyin yanayin damina."
Kai ya jinjina tare da miqewa cikin sanyi yace.
"A a Bappa ba matsala zanyi ko da mai sanyin ."
Cikin fahimtarwa dottijon yace .
" kai Surbajo mufa sanyinmu ba irin naku bane bazaka iyaba don baka sababa."
Cikin dan murmushi yace.
"Toh ai jikina ba irin naka banne Bappa nifa jinina a tsinke yake ba kamar naka daya fara bacci ba."
Dariya yayi sosai tare da cewa.
"Toh asheko Yau zaka san sanyin Gembu da Membila ya banbanta da na wuraren da ka saba zuwa a dai cikin wannan qasa tamu kam."
A haka ya muna mai wasu randu nan tab'o guda 3 manya suna jere rabinsu duk an binnesu cikin qasa sai samansu kad'an gaba d'aya jikin su sai naso yake da fidda damshin sanyi,
wata qorya ya d'ago daga gefen randar cikin murmushi ya bud'e randar,
da sauri General ya matso cikin sha'awa
yakarb'i y'ar qaramar qoryar yana juya ruwan cikin,
ruwane fari tas har yana wani garai-garai daga tsaye mutun na iya ganin fuskar sa da zanen qasan randar,
d'iba yayi ya cika qoryar sannan ya d'aga cikin fillanci yace.
"(Bappa hato gad'a sudu mai woni)
Bappa ina toilet d'in yake?."
da hannu ya muna mai cikin murmushi da binshi da ido,
she ko shiga yayi cikin sauri don maqariba ta qarato.
Cikin sakin fuska Bappa ya kalli Captain Sani cikin hausar sa da take d'an fita yace .
"Surbajo tashi inkai ka d'akin ku."
Miqewa yayi tare da cewa.
"Toh Bappa bari na d'auko jakar kayan mu a mota."
Bayan ya dawo Bappa ya nufi wani d'an dakin bukka Wanda yake shatin kobo shi dai yana binshi a baya cikin bin tsohon da ido tsohone fari tas mai kyawun fata da gashi sannan da ka ganshi kaga mutun mai sanyin hankali da nitsuwa.
Suna shiga cikin d'akin Sani ya dire jakar General cikin mamaki ya sake baki tare da bin d'akin da ido,
Komai na d'akin tsaf yake sai qamshi yakeyi ba wani tarkace sosai
katifa ce bai girma wacce akayi mata shimfid'a da wani tattausan blanket sannan ga wani blanket d'in kuma har guda 2 a ninke a gefen pillows din da aka jera kan katifar sai d'aya gefen bangon wata y'ar ma daidaiciyar katifarce a jingine sai d'aya
gefen kuma y'an wata kanta ce na mutanen da gaba d'aya cike take da littafai na karatun addinin isilama suna shirye tsaf daga qasanshi kuma wani tattausan sallah yane a shimfid'e sai sauran tsakiyar d'akin dake d'auke da irin kujerun nan na rida sai kuma irin akwatunan nan na zamanin da .
Sani kam yayi nisa a kallon tsarin d'akin cikin shawa tuni ya fara jin sh'awar ya ganshi cikin blanket din nan don sanyin da yakeji yana ratsa mai jiki da jini,
yana cikin tunanin yaji wani irin d'umi mai dad'i wanda ke fidda qamshi mai sanyi.
Kai ya d'ago ganin Bappa da ke ajiye musu kasko mai d'an girma wanda ke cike da rushi jazur dashi,
(Wanda dama duk wacce tasan gembu membila toh kasan tabbas baqo na zuwa forko kaskon rushi suke kawo mai)
Cikin sanyi ya zauna gefen kaskon tare da cewa .
"Gaskiya Bappa sanyin garinku nada dad'i."
Murmushi yayi tare da cewa.
"shiyasa dole muke rayuwa da rushi a d'akin sannan muke shan madaran shanu mai zafi ko kuma ruwan Lipton mai zafi don muke rege sanyin."
Slmar General ne ta juyo dasu cikin mamaki Sani ya bishi da ido ganin yadda yake ta qaqqame jiki sai
d'an bari yake.
kai tsaye kan kujerar ridar ya zauna cikin jin sanyi yace.
"kai Bappa sanyi har cikin hanjina ruwan kamar ruwan qaqqara wlh."
Ido Bappa ya tsura mai tare da cewa.
"Habba dai Surbajo kaifa sabon jinine ."
Kai ya jinjina tare da hard'e Hanna yen shi a qirjinshi kafin ace kobo ya fara rawan sanyi tuquru gaba d'aya jikinshi sai kerma yake yana fidda sautin.
"Shihhhh hahhhhhhh hsshhhhahi."
Ganin sanyin yamai yawa cikin kula Bappa ya tura mai kaskon rushin kusa dashi sannan ya jawo akwatin qarfen dake gefenshi cikin sauri ya zaro wani borgo fari tas mai kauri da laushi
irin borgunan haramin nan ne,
kai tsaye ya,
yana mai borgon sannan ya jawo y'ar qoryar gaban shi ya miqa mai tare da cewa.
"Karb'i kasha madara ce mai d'umi insha Allah kana sha zaka bar jin sanyin ."
Hannu na rawa ya karba ya d'an kurba sai ya kuma cire kai
shiko Bappa ganin bazai sha da yawaba yasa da kanshi ya riqa basho yana kurba kad'an-kad'an har yasha mai d'an yawa a hankali sanyin ya fara raguwar mai,
sai ya tsurawa Bappa ido cikin mamaki a ranshi yake tunani .
iya tsanin shi tunda da Ammin shi ta gujeshi bai tab'a samun irin wannan kulawar ba ya lura cikin qauna Bappa ke