Showing 18001 words to 21000 words out of 74791 words
Chapter 7 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
sai wani irin lumshe ido takeyi can sai kuma wasu siraran hawaye dake bin fuskar ta.
cikin tsurawa fuskar tata ido yaga tana wani irin layi kamar mai maye,
tayi wani luuu zata fad'i,
ganin haka yasa cikin sauri ya rik'o hannun ta,
ta fad'o jikin shi sannan tasa hannu biyu ta zagaye k'ugunshi sai kuma tayi lib kamar maiyin bacci.
Haka tasa dole yaja jiki a hankali ya zauna bakin gado da ita,
ita kuwa sai k'ara mik'ewa tayi ta narke a jikin shi,
a hankali ya rink'a sauk'e ajiyan zuciya tare da lumshe ido,
cikin nitsuwa ya kuma bud'e idon ya tsura su kan fuskar ta,
Baki ya tab'e tare da jan dogon tsaki sannan ya mirgina ya matsa gefe,
ita kuwa sai ajiyar zuciya ta sauk'e tare da gyara konci yar ta,
taci gaba da baccin cikin sauk'e ajiyar zuciya.
Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki a hankali ya shiga cikin toilet d'in,
jiki a mace ya samu ya watsa ruwa sannan ya fito,
gefen gadon ya zauna hannushi rik'e da towel yana goge suman kan shi,
tare da kafeta da ido har zuwa wani lokaci kollon da yake mata ne yake k'ara kashe mai jiki,
da k'yer ya samu ya d'an shafa mai sannan ya shirya cikin galila mai matuk'an kyau kalan sararin sama niya sai farin takalmi da farar hula,
wani irin kyau shigar tayi mai kalan kayan da takalmin da hular sai ya fita tamkar adon sararin samaniya,
kyawun surarsa da cikar haibarsa ya k'ara fitowa ba abin da yakeyi sai k'amshi da shek'i farar fatar sa ta k'ara fito da cikar haibar sa.
Yana gamawa ya dawo gaban gadon ya tsaya yana kallon yadda take rawan sanyin,
a hankali yasa hannushi kan wuyan ta,
jikin zafi kamar wuta,
shiru yayi yana tunanin ko me zayi mata? gashi ko ruwan tea d'in ta na jaraba bata shaba yau.
Kai ya kad'a tare da fitowa parlour,
a tsaye ya samu Captain Sani na jiran shi,
yana ganin shi yayi gaba har ya fita sai ya kuma juyowa jin ba alamun ogan nashi na bayan shi,
yana juyowa ya ganshi ya fito kitchen rik'e da filas da cup ya nufi bedroom d'in,
shi kam Sani murmushi yayi tare da juyawa ya fita yana jiran shi cikin mota.
Shi kuma General kan durowar gefen gadon ya ajiye mata sannan ya juya ya fita,
a babban parlour ya samu Abba da Daddy sunyi shirin su na tafiya masallaci da yake yau jumma'a ane in sun tafi tun safe sai dare suke dawowa tare suka fito ,
a hara bar gidan suka samu ya Amir ma da Anuty Aysha tare da Nafeesat zasuje anguwa,
a haka suka shiga motocin suka fita suna fita motar Abdul kuma tana shiga,
wani irin murmushi mugun ta Abdul yayi tare da cije lips d'in shi sannan ya kuma lasar lips d'in binsu da ido yayi cikin happy ganin duk sun fita mutanen gidan gashi ita kuwa Meenal tana cikin gidan,
cikin sauri yayi parking jikin shi har yana rawa ya nufi cikin gidan..
Su Abba suna fita masallaci suka wuce,
Su ya Amir ko Zaria suka tafi.
Suko su General kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim mai dala suka wuce,
suna isa kai tsaye cikin gidan suka wuce da jagoran Captain Sani,
gidan Alhaji Ibrahim gidane mai girma cike da alfarma da kayan k'awa na rayuwa.
Wani Babban parlour suka shiga bayan sunyi slm an basu izinin shiga,
suna shiga Captain da General Sani suka wuce gaban Alhaji Ibrahim wanda ke konce kan wani tattausan carpet suka zauna,
cikin girmamawa General ya gaida shi tare da cewa.
"Uncle ka rege tunani dan gudun kar ya cutar da kai."
Cikin rawan jiki irin na mara lafiya ya yunk'ura ya zauna tare da rik'o hannun wani mata shi mai cikar zati Dr Jabeer Muhammad wanda d'an uwan captain Sani ne uwa d'aya uba d'aya,
kuma shine wanda Alhaji Ibrahim yayi niya da alk'awarin aurawa yarshi Amina kuma ko yanzu da ta bace bai fasa niyar saba acewar sa tunda bata rayuwa cikin birniba burinshi ya aurawa Jabeer ita dan Jabeer yaro ne mai mutunci da sanin ya kamata ga tausayi kuma dama tun Amina tana k'arama in sunje Membila sai yace itace matar sa shiko Alhaji Ibrahim yayi alk'awari kuma shi Alhaji Ibrahim irin mutanen nanne musu kaifi d'aya fad'a da cikawa ne.
Yana tashi zaune ya kalli General cikin sanyi da rawan murya yace.
"Aliyu na kasa mantawa na gaza daurewa kuka na ina Amina take? ko a wanne halin take ciki? ko ya lafiyar ta?."
Sai ya kuma yi shiru cikin sanyi ya rik'o hannun Dr Jabeer sannan ya kalli su General da sauran mutanen dake parlour yace.
"Ita min kena d'aya tak gashi azzalu mai sun d'auke min ita gashi mahaifiyar tama kullum sai kuka."
Cikin tausayi General yace.
"Insha Allah Uncle zamu maida hankali kan ne mota kuma zamu d'auki mataki."
Shi kam Jabeer sai hannu ya mik'awa General tare da share k'ollan dake bin fuska shi murya na rawa cikin sanyi yace.
"General kuyi duk abinda ya dace ko nawa ne wallahi zamu kashe dan samun dawo war farin cikin mu,
Amina itace burin rayuwa ta itace sanyin idanniya ta bazan iya rayuwa inba itaba ban tab'ayin 2 weeks ban ganta ba duk rintsi a sati sai naje Taraba na ganta Amman gashi yanzu har tsawon wata d'aya ban san halin da take ciki ba."
Sai kuma ya juya gun Alhaji Ibrahim cikin kukan yace .
"Uncle dan Allah gobe a d'aura mana Aure da Amina ni ko bata nan na yarda a d'aura mana aure kuma duk halin da zata dawo a ciki na amince da ita a matsayi mata."
Kuka yake yana magana lokaci d'aya kukan nashi yasa Uncle d'inma kuka Captain Sani shima sai kuka Hajia Amina ma sai kuka yayin da Aysha ko mahaifiyar Amina take cikin gidan bata wurin,
sai wata yarin y'ar budurwa wacce itama take ta kukan wui-wui harda majina a hanci kuma sai kallon General take cikin zubda k'ollah,
da kyer Uncle ya kama hannun Dr Jabeer yace.
"Insha Allah gobe za a d'aura muku auren."
Cikin kukan ya kalli General da Captain Sani numfashi ya furzar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.
"Aliyu na tsani duk wanda ya nesan tani da y'ata ji nake inama ace gani gashi wallahi ban ma sannan wanne irin abu zan mishi ba,
rok'ona a gareku in Allah yasa kuka kamashi kar ku barshi da hankalin shi a mai dashi yadda bazai taba gane banbanci tsakanin mace da namiji ba bare ranshi ya tuna mai ya sace wata."
Kai yake gyad'a mai cikin k'arfin guiwa yace.
"Insha Allah ."
A haka sukayi ta bawa Uncle hak'uri da bashi baki Dr Jabeer kam kamar wanda aka yiwa mutuwa.
Sai lokacin sallah suka tafi masallaci daga nan kuma suka wuce cikin Jaji.
*Abdul*
kuwa cikin farin ciki da mugun ta jikin shi har yana rawa ya kutsa kai cikin ......
By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣4⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writers
*Dedicated to Anty Sis*
Kitchen suka nufa,
Anty Aysha na ganin su ta kalli Meenal cikin murmushi tace.
"Meenal ya gida?."
"Alhamdulillah Anty Aysha ya aiki?."
"aiki kam na kam mala ma yanzu zan je in shirya kan dainin ne."
Kula ta d'auka cikin sanyi tace.
"Nafeesat d'ebo sauran mu tafi."
Tare suka shirya komai tsab sannan suka koma parlour Anyt Aysha suka zauna suna d'an hira yayin da Nafeesat da Anty Aysha ke ta janta a jiki,
har zuwa azahar ganin lokacin sallah yayi ta mik'e tare da cewa.
"Anty Aysha zan tafi lokacin sallah yayi."
Cikin kula tace.
"Toh muyi sallan a nan mana sai muci abinci in yaso sai ki tafi ,
wota k'il ko zakiyi bacci ne."
Murmushi tayi sannan Anty Aysha ta ce mata .
"Muje ciki kiyi al'wala."
Murmushi kawai tayi tare da binta a baya.
Bayan sunyi sallah ne suka zauna suka d'anci abinci suna d'an hira,
kafin su ankara har 3:13 pm tayi ganin haka ta mik'e cikin sauri tana cewa .
"Kai bari in tafi ."
Nafeesat ce ta kuma tsaida ta a dole tayi sallah bayan sun idar suka kuma shiga kitchen tare suna shiga kitchen d'in itama ta zage suna ta aiki tare dan tana son gane kan kayayya kin aikin ba laifi kuwa ta fara ganewa gashi Anty Aysha na janta a jiki Nafeesat kuwa duk abinda zasuyi sai tayi mata bayanin yadda ake sarra fashi,
dad'i sosai takeji a wannan d'an taraiyar da sukayi dan ta d'auki darusa da yawa ta fara gane komai bugu da k'ari dama ta iya girki kam tsab.
Suna cikin kitchen d'in har zuwa 5 dai-dai zuwa lokacin kuwa sun kammala komai.
*Mutan Katsina kuwa*
har sun iso cikin gida
A gajiye Abba ya zauna a parlour part d'in nasu,
yayin da suka wuce babban parlour gidan kuwa ba kowa dan Mama da Abdul sun fita yawon mugun tarsu ya Amir kuwa da Daddy basu dawo gida ba tukun.
Captain Sani ne yaje ya kawo musu ruwan sanyi tare da zama gefen Abba yana .
"Abba sannu."
"Yau wa Sani sannu kai ma dan ai kaine mai tuk'in ka fimu gajiya."
Shi kuwa General wucewa yayi cikin bedroom yana shiga yayi shiru a nufin shi ya saurara ko tana cikin toilet d'in,
shiru ba motsi hakan yasa ya matso jikin k'ofar a hankali ya dan buga k'ofar ,
shiru ba motsi tsaki ya d'an ja sanna ya murd'a marfin tare da d'an lek'awa,
wayam ba kowa ganin haka yasashi juyawa cikin tsuke fuska kitchen ya shiga nan ma bata ciki ganin hakan yasa ya fito a fusace kai tsaye tsakiyar babban parlour yaje ya tsaya tare da tsurawa tsakiyar parlour ido cikin d'aga murya tare da tsuke fuska ya fara aika mata kira.
*"MEENAL"*
sai kuma ya d'anyi shiru tare da k'ara had'e fuska dan yasan yanzu Mama zata zo tayi rashin mutuncin nata.
Jin shiru bata amsa ba yasa ya fara antaya mata kira ba k'ak'k'auta wa a jere- a Jere.
*"Meenal"*
*"Meenahhl*"
*"Meenahhhl*"
Abba da Captain dama tun yadda suka ga ya fita a fusace suka bishi da ido sannan kuma suka jiyoshi yana ta rabka k'ira,
Sai suka mik'e tare da biyo bayan shi ganin ya tsaya ya coge yasa suka tsaya suma tare da zuba mai ido,
fitan su yayi dai-dai da fitowar Meenal d'in daga cikin kitchen d'in cikin tsoro da rawan jiki ta nufi gunshi tana mai kallon yadda ya tsuke fuska tana zuwa sai ta tsaya gaban shi tayi k'asa da kai tana fidda numfashin tsoro,
Anty Aysha da Nafeesat ko na biye da ita a baya ,
dai-dai lokacin ya Amir da Daddy suka shigo,
suna shiga sai ga Mama da d'an kanzagin ta Abdul.
Duk tsayuwa sukayi cirko-cirko suna kallon yadda ya tsareta a gaba yana hukun tata da ido.
Ya Amir ne cikin mamaki yace.
"Daddy kalli Abba a gidanmu yau."
Daddy kam da sauri ya k'arisa gaban d'an uwan shi cikin k'aunar juna suka gaisa ya Amir ma ya iso tare da gaida shi .
Nafeesat ce ta k'arisa gaban General d'in cikin tsoro murya na rawa tace.
"Ayyahhhhh Hamma Aliyu kayi hak'uri wallahi muna kitchen ne muna taya Anty Aysha aiki."
Kai ya d'an dago ya kalleta ,
ganin yadda ya cilla mata wani irin kallo yasa tayi k'asa da kanta cikin sanyi ta juya gun Abba,
gai dashi tayi cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Ayyahh Abba kacewa Hamma Aliyu ya rink'a barin Meenal tana zuwa muna zama gashi muna taya Anty Aysha aiki kaga dama aiki ya mata yawa kuma Meenal zata ji dad'in zaman mu zamu d'ebe mata kewa."
Kai Abba ya jinjina cikin sanyi yace .
"Ba damuwa insha Allah zai barta."
Nafeesat kam sai dariya tayi tare da jawo hannun Meenal cikin raha tana cewa.
"Meenal kizo ga Abban mu shine Baban Hamma Aliyu dama yana Katsina yaune yazo."
Gaban Abban suka tsaya cikin sanyi ta d'an durk'usa a hakali tace.
"Sannu da hanya Abba ."
Cikin fara'a Abba yayi maza yace.
"Taso Meenal ni mahaifi ne a gareki ni ba surki bane a gunki,
ki d'auken kamar mahaifin ki,
Allah ya muku al'barka."
Cikin jin dad'i tace.
" Amin Abba ."
Itama Anty Aysha ta matso tare da gaida Abba cikin happy ya amsa tare da cewa.
"Aysha kema kinga kin samu y'ar uwa ko,
Ke Meenal ai zakina zuwa kina taya Aysha aikin ko?."
Murmushi sukayi baki d'aya sannan suka amsa da cewa.
"Ehh Abba."
Shiko Abdul duk maganar da akeyi idon shi na kan Meenal gaba d'aya ya zauce a kanta sai binta da ido yake baki a sake kamar soko tunda Nafeesat taja hanunta zasuje gaban Abba,
yabi k'ugunta da ido har yana lasan lips d'inshi ganin yadda gaba d'aya take tafiya cikin wani salo a ranshi yake jin ya samu garab'asa har gida a hankali yace.
"Nagode Hamma Aliyu ka kawo min ganima nima dole na d'ana."
Ita kuwa Mama wani irin tsuke fuska tayi cikin salon rashin mutun ci da bak'in cikin dawowar k'anin mijin nata,
sannan ga tsanar Aysha da Meenal da take ji cikin bak'ar magana ta kalli Aysha tace.
"ai in mace nason ta samu,
masu taya ta aiki haihuwa zatayi in ta isa ke kina nan baki da aiki sai ci sai k'aton kashi banza mai maceccen zuciya."
Sai ta kuma juyawa kan Meenal cikin gyatsine tace.
"Lallai karuwan ci ya fara samun lasisi tunda har ubban korton naki zai baki wurin zama,
ko da yake ba bak'on abu bane ai shima ubban zaman banzan yakeyi a katsinan,
uwar ma waya san ko yanzu haka tana *TAPA* jigon y'an iska."
Wayyo General Aliyu gaba d'aya ya kejin jinin sa na tafasa zuciyar sa na soyuwa ji yake kamar zai had'iyi zuciya ya mutu gaba d'aya jikinshi har b'ari yake cikin fushi ya nufi gaban Maman."
Abba ne ya kirashi cikin d'aga murya yace.
"Kai Haiydar zo nan banson jin koma daga bakin ka."
ai ya k'asa magana sai juyowa yayi ya rab'a gefen Abban kai tsaye bedroom ya wuce ya kasa zama ko tsayuwa sai zirga-zirga yake ranshi na tafasa.
Ita kuwa Mama dariya tayi cikin jin dad'i sannan ta juya tare da jan hannun Abdul suka tafi.
Ya Amir kuwa da Daddy hak'uri sukayi ta bawa Abba shi ko Abba murmushi kawai yayi tare da jansu Abban da ya Amir d'in yana mai basu labarin yadda akayi auren General da Meenal,
fatan alkhairi sukayi tare da sanya albarka .
Anty Aysha kuwa hannun Meenal taja tare da cewa Nafeesat.
"Ku zomuje mu sharewa Abba d'akin shi."
D'akin Abba na cikin part d'in Aliyu Amman inya zo yawan ci a parlour yake zama,
gashi yanzu ko General ya tare a parlour koya za'ayi ne rai?.
Shara sukayi tare da goge mai komai sannan suka fito tare da bawa Meenal hak'uri da halin Mama.
Shiko General da k'er ya samu ya sarrafa zuciyar sa,
sannan ya watsa ruwan tare da yin alwala sannan ya fito suka tafi masallaci.
basu dawoba saida sukayi ishah.
Suna dawowa Daddy yasa kab suka zauna a babban parlour yayin da Meenal da Anty Aysha da Nafeesat suka shirya musu abinci, tsarin gidan kenan duk tare suke had'uwa a parlour suci abinci.
Ita kuwa Mama ta samu damar yi musu cin fuska kenan.
Shi kam General a cike yake tab ya k'asa cin abincin dan shi dama In dai ba Abban shine yazo ba bai zama a cikin,
sai harara yake cillawah Meenal itako tana kauda kai.
Hira sosai Abba yayi tayi da Daddy tareda Ya Amir da kuma Nafeesat da Meenal a parlour nasu shi kuwa General so yake ya keb'e da Bodd'i ya casata dan koma menene itace ta jaza masu da tabi dokar sa ai hakan bazai faruba,
shi yasa yace shi bacci zaiyi.
Hakan yasa suka watse hirar tasu Abba ya nufi d'akin shi,
Suma su Daddy duk suka tafi part nasu.
Suna fita ya rufe k'ofar sannan da sauri yabi bayan Meenal d'in yana cije lips d'in shi,
yana shiga cikin bedroom d'in..........
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* pg 1⃣5⃣ to 1⃣6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writers
Gaban ta yaje ya tsaya,
ya tsare ta da ido yana matso ta,
itako tana ja da baya har ta zauna gefen gado,
k'afar sa d'aya ya dago ya taka gefen ta cikin fad'a yace.
"Ke ba a isa dake bako? duk abin da kika ga dama shi zakiyi ko ?
toh wallahi ni zanyi maganin rashin kunyar ki sai anyi magana kiyi ta zaro ido kamar tsohuwar mayyah."
Ita kam sunkuyar da kai tayi tare da zubda k'ollah cikin sheshshek'ar kuka .
Ranshi ne ya k'ara b'aci ganin shi ba abin da ya mata kuma ta sashi a gaba tana kuka dan muna furci.
Cikin fad'a ya damk'o hannun ta cikin masifa ya mik'ar da ita cikin k'uluwa ya nunata da d'an yatsa sannan tare da tsare ta da ido yace.
"Wallahi ki had'iye kukan ki maza rufe min bakin me nayi miki da kike min koke-koken muna furci kin iya rashin kunya kuma kice kar ayi miki magana ."
Kai ta rink'a juyawa cikin son had'iye kukan amman ta kasa sai hawaye shar-shar .
Tsawa ya kuma buga mata cikin k'ara matse hannun ta yace.
"Ki had'iye kukan ki da wahayen ki muna fuka yanzu me nayi miki?."
Cikin kukan ta d'an d'ago ta kalleshi tana girgiza kai,
baki na rawa cikin kukan tace.
"Kayi hak'uri ka gafar ceni."
Sai kuma kukan ya kufce mata kuka mai cike da k'unan zuciya kukan take har kamar numfashi ta zai d'auke gaba d'aya jikin ta sai bari yake da ker take cewa.
"Kayi hak'uri bana son fad'a ina tsoron tsawa kaina na juyawa."
Ido kawai ya tsura mata cikin mamakin ganin yadda gaba d'aya ta rud'e tana kukan cikin cushewar numfashi da k'unan zuciya gaba d'aya ta ke d'an layin jin kanta na juyawa."
Cikin ta kaici ya kuma watsa mata tsawa.
"Kada Allah yasa kiso tsawan wato ke gaki mai iya fidda kai ko ji muna furci toh wallahi ki kiyaye ni ko na fasa miki kan naki da tsawan."
yana rufe baki ya hanka d'ata gefe ya juya ya nufi gaban durowa.
Ita kuwa hannu tasa ta kama kanta cikin firgici da tsoro kukan da take ne ya cusa numfashin ta sai jiri a take sai duhu ya rufe mata ido sai ga jiri yu-yuh yana d'ibar ta.
Blanket ya zaro tare da juyowa zai d'auki pillow,
Ido ya tsura mata yana tsaye ba tare daya matso ta ba ganin tayi tangal-tangal zata fad'i yasa ya d'an matso ta cikin rashin sa'a kafin ya isoma ta fad'i k'asa kanta ya buga jikin gado ta kuma sulewa k'asa a take goshin ta yayi wani irin k'aton k'ulu sai wani irin kuka ta kuma