Showing 63001 words to 66000 words out of 74791 words

Chapter 22 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel

kalleshi tare da cewa.
"Bacci nake ji ina zan konta ?."

Lumshe ido yayi tare da nuna mata gefen shi.

Ita kuma sai tsuke baki tayi tare da cewa.
"Ni wurin nan ya min kad'an gashi duk ka ajiye tarka cen woyoyin ka."

Shiru yayi tare da bud'e idanun shi a hankali ya tsurawa fuskar ta ido,
sai ya kuma nuna mata kan k'irjin shi murya a kasalan ce yace.
"Tunda ke giwace uwar birgima zo ki hau kaina ki konta tunda nan duka bazai isheki ba."

Hannu ta fara yarfawa tana d'an buga k'afa tace.
"Ni dai bacci zanyi gashi k'irjin yana ciwo."

Haka ta rink'a mita har kusan 12 ganin hanashi bacci zatayi ya sashi mik'o hannu a hankali ya jawota jikin shi kan k'irjin shi ya kifata,
hannu yasa a tsakiyar bayan ta ya rink'a shafawa a hankali murya can k'asa yace.
"Dere yayi Minali kiyi baccin ki kinji ko."

Kanta ta rink'a juyawa tare da murza k'afafun ta a kan nashi har tana shirin zame mishi towel d'in jikin shi cikin jin bacci tace.
"Hamma kirjina wallahi kirjina ciwo yake min numfashi na yana tafiya."

"Dama kina da ciwon k'irjin ne?."

"A a ni Yau na fara jin ciwon."

Hannun shi ya cusa cikin towel d'in jikin nata a hankali ya cusa yatsun shi biyu ya kamo robar bireziyar nata sannan ya sake shi pet a bayan ta cikin rad'a yace.

"Yaushe kika fara saka wannan abun?."

"Yau ne nafa ta sakawa."

Ido ya lumshe sannan yace.

"Toh zan cireshi dan shine yake saki ciwon k'irjin."

Shiru tayi tana shak'an k'amshin jikinshi .

Shi kuma hannun shi ya saka tare da ture laptop nashi da iPhone nashi can gefen sannan ya murza k'afafun shi ya waresu,
ita kuma ta gyara konciyarta,
k'ara tallabeta yayi tare da had'e hanna yenshi duka biyu kan tsakiyan bayan ta sannan ya balle brzyar ,
a take Meenarl taji gaba d'aya ciwon girjin ya sake sai ji tayi kamar an kunceta .

Shi kuwa a hankali ya tura hannun shi a tsaka nin k'irjin su,
kamo jikin brzyar yayi tare da zaro shi ya fidda shi gefe,
ita kuwa jin zafin zarowan yasa ta d'an d'aga k'irjin ta sama.

Shi kuwa General idanun shi ya rumtse da k'arfi dan k'ok'olwarshi bazata iya juran ganin k'irjin ta a hakaba.

Ita kuwa cikin jin kunya tayi sauri ta kife k'irjin ta a kan nashi k'irjin tare da lumshe ido.

Shi kam General wasu irin ajiyan zuciya ya rink'a direwa a jere a Jere gaba d'aya jikin shi ya rink'a tsuma ida nunshi suka k'asa bud'uwa ya koma tamkar makaho,
sai manneta da ya karayi a jikin shi k'irjin shi na duka tara-tara ba abinda yake fad'i sai.
"Meeenarrhl zaki kashe Hamman kifa."

Itama gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ta k'asa magana dan kab tsikar jikin ta ya mike' tsaye sai yatsun ta ta cusa cikin suman kanshi tana murzawa.

A hankali General ya mirgina ta cikin rawan jiki ya tsurawa fuskar ta ido murya can ciki yace.
"Minalin Hamma ?."
Sai kuma yayi shiru yana sauk'e nannauyan numfashi.

Ita Kuwa mik'e wa tayi cikin rawan jiki ta zauna a tsakiyar gadon ,
shima tashi yayi ya durk'usa tare da jawota gare shi rugume ta yayi da k'arfi sannan ya d'ago fuskarta tare da lumshe ido ya manna lips enshi kan nata cikin wani yana yin ya rink'a sauk'e mata muguwar kasala sai sakewa tayi a jikin shi tare da rugume shi tana lumshe ido tare da murza k'afafun ta,
a haka har ta ture mishi laptop enshi,
Amman ina basuma san ya fad'in ba.

Jawota yayi suka konta sannan ya jawo blanket ya rufe su ,
ita kuwa hannu tasa tana tureshi jin yana kauce zatonta ,
sai kawai ta saki kuka cikin tsoro tace.
"Hammahh kayi hak'uri barni inyi bacci ka barni."

Jin haka ya sashi juyawa da k'arfi ya kifu tare dasa hannun shi d'aya ya rugume ta cikin wani yana yin yace.
"Nah.. Nha.. Nah bar ki kar kiyi kuka Meenarl tunda ba kya so na barki."

Haka suka kwana rugume da juna.

Da Asuba General ya mik'e cikin lumshe ido yaje yayi wonka tare da yin alwala,
masallaci ya wuce dan bin jam'i
shine bai dawo ba sai 7 dai-dai.

A parlour ya samu Meenarl konce kan 3 str fuska ya murtuk'e dan har cikin ranshi yake jin zafin abin da tayi mishi a daren jiya gani yake ko Dr take so.

Fuska a murtuk'e yayi kanta tare da...



By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

5⃣3⃣to5⃣4⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡




*Yebon goni ya zama dole hak'ik'a rigar mutunci kan sanya a zatawa mai sanyashi mutunci kinkai a yebi ki, mu matan arewa muna yebawa da halin ki da shigarki Namecy tawa AISHA LAWAN UMAR jarumar ma aikaci mai mutunci tauraruwar AREWA 24 Garkuwar Fulani ke mik'a sak'on jinjina a gareki🀝😍😘*



Sunku yowa kanta yayi pillow d'in da ta matse a k'irjin ta ya zare a hankali sannan ya d'an durk'usa murya can ciki yace.
"Meenarl a nan zakiyi baccin ai wuyan ki zaiyi ciwo."

Kai ta juya cikin jin dad'i baccin safiyar ga garin yayi lum alamun hadari ga iska mai dad'i ga kasan cewa cikin tsabta ceccen wuri mik'a ta d'an yi a hankali ta kai hannun ta kan,
fuskar shi sajen shi ta shafa a hankali,
Ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya shima hannun shi ya d'aura a kan goshin ta tare zubawa kirjin ido murya a raunane yace.
"Muje kan gado kiyi baccin anjima zan shiga cikin KD zan dauko miki kayan ki."

Ido a lumshe cikin muryar bacci tace.
"Uhmmm Hamma."

Matsota ya kuma yi a hankali yace.
"Na'am Minali ."

Sai ta kuma lumshe ido tace.
"Bacci nake ji Hamma jikina ya mutu bazan iya tashi ba."

Murmushi yayi tare dasa hannu ya gyara mata wuyan rigar ta dake zamewa sannan ya mik'e a hankali hannu yasa ya tallabo ta tare da manata a jikin shi ,
bedroom ya wuce da ita kai tsaye kan gadon ya direta cikin kula yasa mata pillow sannan ya jawo blanket ya rufe ta ,
sai kuma ya juya tare da d'ago laptop enshi da iPhone nashi juyawa yayi gareta ya ajiye su kan y'ar karamar durowar dake gefen gadon ,
a hankali yace.
"Saura kiyi birgima ki turomin laptop na ki karasi min shi haka jiyama da dare kika rad'a min su da k'asa."

Ita dai baccin ta fara tare da tura mishi baya.

Shi kuwa kai tsaye parlour ya koma ya sassake labulayen sannan ya rufe windows d'in sai kuma ya shige kitchen cikin sauk'i ya had'a musu breakfast mai sauk'i sannan ya kimtsa komai,
tea ya d'an had'a sannan ya dawo parlour tare da kunna TV yana kallin CNN,
tea d'in yake sha yana d'an sauri d'an yana son yaje yaci abincin Ammin shi ,
shiyasa ya d'an Sha ruwan tea d'in kad'an sannan ya mik'e ya shige bedroom d'in .

murmushi yayi ganin yadda Meenarl ke takure dan sanyin dake kad'awa ga kuma sanyin AC murmushi ya kuma tare da shige wa toilet a ranshi yana .
"Ai kin saba sanyin garinku ba irin wannan bane."

Wonka yayi tsab sannan ya fito yana fitowa yaje gaban mirror ya kimtsa tsab da sauri-sauri a nufin shi kafin ruwan ya sauk'o ya isa gida.

Yaje gaban durowar da nufin fito da kayan da zai saka,
a dai-dai lokacin kuma ruwan ya sauk'i kamar da bak'in k'woriya ruwan mai sauk'a a hankali sai iska mai sanyi.

Shiru yayi a ranshi yaso sai ya isa kafin ruwan ya sauk'a.
gashi gaba d'aya wani irin duhu ya rufe ko ina.

Parlour ya nufa tare da gyara d'aurin towel d'in dake k'ugunshi,
TV ya kashe sanan ya kashe bok d'in baki d'ayansu,
Komawa yayi ya dauk'o phone nashi yazo parlour kan 3 str ya zauna tare da shiga yanar gizo-gizo a nufin shi ya d'an zauna kafin ruwan ya d'auke .

Shiru ruwan sai sauk'a yake har yafa rajin sanyin na ratsashi gaba d'aya jikin shi yayi bacci kasala ta rufeshi,
Hakan yasa dole ya mik'e cikin yin mik'a bedroom ya nufa yana zuwa ya ajiye woyar sannan a hankali ya konta gefen Meenarl tare da Jan blanket d'in ya rufe su ,
matsawa gefen ta ya kumayi d'an baya son abinda zai had'e jikin su wuri d'aya ,
ita kuwa hajiar birgima daga jin alaman mutun ta k'ara mirgi nowa cikin sanyi ta d'aura hannun ta kan k'irjin shi ,kai ya juya ya kalleta da kyau tabbas bacci takeyi ,
fuska ya tsuke d'an shi harga Allah gani yake muguntan ce ,
kanshi ya juya da nufin cire hannun ta sai kuma kawai yaji ta sake d'aura mishi cinyarta kan nashi cinyar sannan a hankali ta cusa kanta a kafad'an shi,
gaba d'aya ta kanai nayeshi sai faman baccin ta take.


Shiru yayi yana kallon ta ita ko a jikin ta yayin da shiko ta rabashi da nitsuwar shi,
sai ajiyan zuciya yake direwa a kai akai.

Cikin lumshe ido ya juyo gareta baki d'aya ,
hannun shi yasa a hankali ya zuge zib d'in rigar ta ido ya tsura mata yadda ta k'ara k'amk'ameshi
lips enshi ya lasa a hankali ya jawota jikin shi,
manna ta yayi da k'irjin shi da kyau sannan ya jawo blanket ya rufe su da kyau,
sai kuma ya fara sauya salon konciyar tasu da darrusan sa masu wuyan fad'i.

Cikin baccin taji wani sabon salo ido ta bud'e a hankali ta diresu kan fuskar General da ya gama yin mutuwar konce,
a hankali ta fara janye jikin ta murya can k'asa tace.
"Hamma."
Janta ya kumayi tare da cewa.
"Ina zaki je?."
Ido ta rumtse tace.
"Ni baccin ya ishei zan koma parlour."

Matsota yayi sosai yace.
"Me yasa kike son azab tar danine ? me yasa bakya son na rabeki alhalin kuma kece kike fara shige wa gareni."

Kai ta juya cikin rashin son abinda yake matan tace.
"Ni dai wallahi bana so ka barni ."

Mik'ewa yayi sannan ya shige bathroom wonka yayi ciki sauri-sauri,
Yaya fitowa y kimtsa tsab cikin shadda maikalan sararin samaniya ya fito rasa kamar tauraro sai k'amshi yake zubawa ya k'afa hularsa ras ,
ita kuwa dama yana shiga wonka ta dawo parlour.

Parlour ya fito rik'e da tarkacen sa bai kalli ko inda take a yanufi hanyar fita,
ganin haka ta mik'e da sauri ta bi bayan shi tana .
"Hamma Haiydar ina zaka je?."

Bai ko kalleta taba,
cikin sauri taje gaban shi kanta a k'asa tace.
"Ayyah Hamma na ,
ina zaka je ka barni a nan kasan fa ina tsoro kuma ba kowa a gidan."

Fuska a tsuke yace.
"Ni ba Hamman ki bane ai kinsan waye Hamman ki da kike so,
batun ina zanje kuma gidan mu zanje,
zanje gun Ammi na kuma ke kin ce bazaki je gidan muna."

Da sauri tace.
"Toh zanje gidan mu nima."

Ci gaba yayi da tafiya tare da cewa.
"Ban hanaki ba ai gaki ga hanya kije gun Jabeer d'in."

Yana kaiwa nan ya fice tare da Jan k'ofar ya rufe.

Kai tsaye gidan su ya nufa.

Ita kuma yana fita ta koma tsakiyar parlour ta zauna ranta a b'ace ya zaiyi ya barta a gida ita kad'ai haka ta zauna cikin fushin.

Shi kuwa General yana shiga cikin gidan a babba parlour su ya samesu kab dinsu Bappa na zaune a cikin su kamar sarki gaba d'aya zuriyarsa a had'e sai Mama ce da Abdul basa wurin.

Gefen Bappa ya zauna cikin son tsohon yace.
"Bappa barka da rana."
Kanshi ya shafa tare da cewa.
"Barka dai Aliyu ,
ya gida ina Bodd'i na?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Na barta tana bacci tace a gaida Ku."

Murmushi Inna tayi gami da cewa .
"Aliyu ka barta ita d'aya a wancan gida naka mai cike da sojoji ."

Rayhana ce dake gaban Dr Jabeer yana yanke mata farce tayi shiru tana jinsu shiko Dr yanke mata farce yake yana kallon ta cikin k'aunar da ya dad'e yana yi mata a zatonshi Meenarl yake so sai yanzu ya gane Meenarl tausayawa ce a tsaka ninsu.

Aliyu ne ya mik'a mishi hannu suka gaisa .
Murmushi Dr yayi tare da Sosa k'eya yace.
"Hamma Aliyu ai nizan zo na kawo gaisuwa dan ka zama surki."

Kanshi General ya d'an buga tareda cewa.
"Inma tson kana ta zakayi ka sani dai na fika da wattani har 8."
Dariya sukayi baki d'ayansu.

Sannan Ramadan ya kalli General cikin rawan kanshi yace.
"Hamma Aliyu
har Hamma Sani ma ya zama surkin ka ,
d'azu Abban Meenarl yazo ya nema wa Hamma Jabeer auren Rayhana ya kuma nema wa Hamma Sani auren Nafeesat kuma duk an basu saura biki kawai."

Sai ya kuma matso kusa da General tare da karya wuya yace.
"Hamma Aliyu toh ni kuma da Abdul yaushe zamu auru? gaskiya muma a aurar damu? wallahi inba haka ba muyi tawaye dan mun gani da zaman gida ayita maida mu yara."

Gaba d'aya parlour suka kwashe da dariya Captain Sani harda buga tafi,
Bappa ma dariya yake sosai ,
Dr Jabeer ne cikin murmushi yace.
"Ashe yaushe zaku auru?."

Sai suka kuma dariya.
Ya Amir kuwa dariya yake harda rik'e ciki ya jawo Ramadan jikin shi yana.
"Insha Allah kuma zaku auru Ramadan, kaida Abdul zamu kai sadakar Ku a masallaci wata kil a samu masu tayawa."

Daga nan kuma suka cin gaba da dariya .
Daddy da Abba kam sai kallon su suke cikin nisha d'in da happy.

Abdul kuwa dake zaune gaban Mama yana kuka tana kuka tana cewa.
"Abdul na cucu kaina Na bata lahirata Abdul na cucu Ammin Aliyu na bita da sharri gashi ita kuma sai nasara ke bin rayuwar ta,
gata ga mijin ta ga yaran ta ga surkana yenta kowa sonta yake ga yan uwanta da 'ya'yan y'an uwanta gida duk ya cika da family enta ,
nayi asirina rabata da mijnta ba tare da hakkin ta ba gashi asirin ya karya ya barni da tarin zunubai."

Cikin kukan Abdul ya mik'e tare da cewa ni dai zan nemi gafarar yan uwana kema ki nemi gafararsu sannan ki tuba ki koma ga Allah ki kuma kisan duk abinda kikayi Allah na ganin ki ni zanje cikin su kinga yadda kika samun tsanan Hamma Aliyu kalli yadda Ramadan ke sona har kunya nake ji."

A haka ya dawo parlour akaci gaba da yin hira da dariya dashi.

Shi kuwa General mik'ewa yayi ya nufi bedroom ensu a daa yanzu kuma na Ammi ne.

Murmushi yayi ganin an canza mata kayan d'akin sannan suma na dad'in sunan.
A hankali ya zauna gefen ta a kan sallayar da take zaune tana k'ara tun qura'ani mai girma.

Ganin ya zauna ya tonk'oshe k'afafu yana sauraron sautin kara tun nata yasa ,
ta d'an k'ara k'ara tun shafi 3 sannan ta d'aga hannu ta rink'a yin addu'oi ,
shima hannu ya d'aga yana amsawa da Amin-Amin,
suna shafa wa Ammi ta kalleshi cikin sanyi tace.
"Babana yaushe ka iso? ina Meenarl d'in kuma?."

Murmushi yayi tare da lonk'oshe wuya ya gaida ta sannan yace .
"Ammi me kike buk'ata."

Murmushi tayi itama sannan tace.
" ba komai Haiydar duk abinda nake so Abban ka ya gama minshi."

Haka sukayi ta hira cikin soyeyya irin ta UWA da d'anta.

Ahaka Ramadan da Rayhana tare da Dr da Captain da Nafeesat suka shigo suma akayi ta hirar dasu.

Ammi sai nan nan take da d'anta gudan jinin ta.


A haka suka wuni cikin Happy yayinda Bappa ya kara had'a wa General wasu addu,oin a cikin zam-zam ya wuni yana sha.



Bayan sunyi sallan la'asar ne suka shigo gida .

General ya kalli Ammi a hankali yace.
"Ammi a had'a mana kayan mu zan tafi dashi ."

Cikin k'aunar d'an nata ta had'e musu kayyaya kinsu kab sannan su Ramadan da Abdul suka kaimishi su cikin motarsa.

Shine bai tafi ba har 8:28 pm .

Bappa ne d'aya shigo yanzu ya kalleshi tare da cewa.
"Aliyu har yanzu baka tafi ba? ,
ga hadari ya kuma had'uwa."

Nafeesat ce tayi dariya tare da cewa .
" Bappa hadari kuma? da safe akayi ruwa fa."

Ya Amir ne ya mik'e yana cewa.
"August d'in kenan ai."

Abba ne ya kalleshi tare da cewa.
"Kar ruwan ya tsare ka gashi ka kabar Meenarl d'in ita kad'ai."

Haka ya musu allama sannan ya fito ,
har ya shiga mota Ramadan ya fito rik'e da kuloli guda biyu ya bud'e bayan motar ya ajiye mai cikin k'aunar Hamman nashi yace.
"Inji Ammi a kaiwa Bodd'i."
Toh kawai yace sannan sukayi saida safe,
ya shiga mota ya kama hanyan Jaji,
sauri General yakeyi dan baya son ruwan ya tab'a shi shiyasa ya kama hanyar cikin wani irin shauk'i da jin dad'in yana yin garin,
a ranshi yakeji yau zai kasan ce cikin wata rayuwa mai dad'i d'an yana jin wani yanayin da yafi karfin ya jumre.

A dai-dai lokacin da...



By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*BANDIRAWO* page

5⃣5⃣to5⃣6⃣

*Na*
*Aysha Aliyu Garkuwa*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



A dai-dai lokacin da yayi parking a harabar tasu ,
ruwan ya kece kamar da bakin kworriya,
ruwan ne yake zuba da k'arfi sai wolk'iya da rugugi akeyi ,
hannu General yasa ya dafe siterin tare da komawa ya jingina da jikin sit d'in yana kallon ikon Allah ruwane yake sauk'a harda k'ak'k'ara yana jin yadda suke sauk'a kan glass d'in tabbas badan ko bulet bazai fasa glass d'in ba toh da k'ank'aran ya fasa,
Ido ya lumshe cikin jin sanyi na ratsashi lokaci d'aya kuma wutar NEPA ta d'auke gaba d'aya wurin yayi duhu ,
Juyawa yayi ya kalli cikin motar kab ba leima gashi ba jacket ko wani abin da zai saka a kanshi ko a jikin shi,
gashi gaba d'aya sojojin sun shige cikin mafakarsu
A hankali yake fad'in.
"Allah humma saiyi ban nafi an"
sai kuma yayi shiru yana tuno Meenarl ita kad'ai,
zaman ya gyara a nufin shi sai ruwan ya d'an sahirta amman sai kuma kamar karuwa ruwan yake ganin haka yasa dole ya bud'e motar a hankali ya zuri kafarshi wojo,
tsilum ya jishi cikin ruwa ga wani irin sanyi daya ratsashi,
fita yayi cikin k'amk'ame jikin shi ,
gaba d'aya ya jik'e cakab a lokaci kad'an ,
tuni ya fara karkarwa da sauri ya bud'e bayan moton ya d'auko kulolin da Ammi ta had'oshi dasu,
sannan ya tura phones enshi cikin jakar laptop enshi sannan ya rataya a kafad'an shi,
hannu shi rik'e da kulolin ya juya cikin duhun ya nufi cikin gidan tafiya yake cikin duhu sai hasken walk'iya ke haska mishi hanya kad'an-kad'an,
tuni ya fara rawan sanyi,
sai d'iga yake tol-tol ,
da sauri-sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login