Showing 36001 words to 39000 words out of 74791 words

Chapter 13 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel

Abban ta haihu sabida kar ya samu Magaji kaga in baida yaro da zaran ya mutu Daddy kune zai gajesa kaga d'en duk dukuyarshi ta zama tawa nida Ku y'ay'ana,
toh amman don jaraba da taurin kai saida wannan jarabebben d'an nasu Aliyu yazo duniya gashi ya fito d'an namiji ta yadda duk zai kwakwashe gadon,
toh shine yanzu banson Aliyu ya haihuwa tunda ko ubanshi ya mutu ya gaji dukiyar toh in baida y'ay'an dole kune zaku gajeshi daga nan dukiya ta zama tamu,
kaga dama shi Daddyn Ku ba abin da yake dashi yana nan kamar b'eran masallaci fak'aru alal larurati kawai."

Ido ya ware cikin jin hud'ubar shaid'aniyar uwarsa,
cikin zak'uwa yace. "toh Mama ya kikayi ki rab'a iyayen Hamma Aliyu?."

Murmushi tayi cikin yarda da kanta tace.
"Yanzu kan zan tafi gidan boka mai gobe da nisa dan ya fara min aiki a wannan rana sai gaba zan baka labarin yadda na rabasu a sauk'ak'e."

Ido ya zura mata tare da mik'ewa yana tafiyar yan kaciya yasa hannun ya d'an dago jallabiyar sa karta fameshi,
Ita kuwa mayafinta ta yafa sannan suka fito parlour anan ya tsaya itako ta wuce gidan bokan nata Wanda yake can cikin k'auyen Zaria kauyen ma a bayan garin.

Tana zuwa ta samu gidan a cike da mata anata bin layi gidan boka ya zama tamkar asibiti,
Itace bata samu shi gaba sai goshin maggariba tana shiga bokan ya kalleta cikin yin shu'umin dariya yace.
"Hajia zulai a gidan lallai mugunta ta motso."
Zatayi magana yayi maza yace.
"Kiyi shiru nasan meke tafe dake amman kinsan sharad'in aiki na dole yau nine matsayi mijin ki kuma kinsan abinda zamu aikata."

Kai ta jinjina tareda cewa.
"Ba dai buk'atata zata biya ba?."

Cikin zare ido yace .
"Sai dai in ban miki wonka ba."

Kai ta jinjina tare da cewa.
" na yarda"
Dariya yayi tare da cewa.
"Toh a wannan Daren zan tura aljana kasalau ta zuba mishi kasala da sanyi mai tsanani da zazzab'i ta yadda bazai iya yin nafilfilin daya saba yi da karatu k'ura'ani da azkar da yake duk sai ya kasa yi kafin mu samu nasara a kanshi."

*Wa iyazubillah ya Allah ka tsare mana imanin mu hak'ik'a wannan abu ya yawa ita a cikin matan wannan zamini*


Shi kuwa General bayan anyi sallan ishah ne ya koma kan 3str ya konta,
Captain Sani ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Sir ya kamata mu koma cikin Kaduna ko?."
Kai ya jinjina tare da rumtse idonshi ,
can kuma sai ya mik'e tare da rarumo..

By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page

2⃣9⃣to3⃣0⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*MOH ALLAH HOINANI WALAH KO SAKLATA D'UM*

*Wannan shafi nakune Ku kad'ai Anuty Kausar (Kausar m hassan) & Maryam S bello msb tare da Jannart Lamod y'ar gatar Garkuwar Fulani*


Pml
Key d'in motar sa ya d'auka tare da ficewa yana cewa Captain.
"Kai tashi mu tafi "
mik'ewa yayi tare da binshi a baya suna fita harabar ajiye motocin ya mik'a mishi key d'in sannan Captain ya bud'e mishi marfin motar ,
shiga yayi ya zauna tare da lumshe idonshi sannan ya jingina da jikin kuje ran kamar maiyin bacci,
shiko Captain jiniyar motar ya tayar cikin tsuwa da shaidawa mazauna wurin General zai fita,
hannu Aliyu ya d'aga mishi tare da cewa.
"Ya isa bance ka gayya toh min kowa ba,
mu tafi kawai."

Shiru Captain yayi tare da figan motar suka fito a guje,
suka kama hanyar Kaduna.

Ita kuwa Meenal ranar kusan a parlour ta wuni tare da Abba ita ta shiga kitchen tayi musu girki irin namu na fulanin daji wanda yasha man shanu,
Abba na tafiya masallaci ita kuma ta koma cikin bedroom tare da rufe k'ofar,
kai tsaye toilet ta shige tare da yin wonka tare da al'wala tana ,
fita ta d'an zauna gaban mirror gashin ta kawai ta d'an tace sannan ta tubke gashin sai kuma ta murza d'an turaren humran da Anuty Aysha ta bata,
man baki ta d'an shafawa pink lips d'in ,
ras ta fito gonin sha'awa nan ma ba kolliya tayiba ,
wota y'ar doguwar riga ta dauka mai laushi da sulb'i rigar bakace mai dan tsukekken k'ugu sai dan gajeren wondo mai taushi tasa tare da zura rigar sannan ta yane kanta da gyalen rigar ras fuskarta ta fito cikin tarhan wanda dama ta iyashi ras dan Hamma Jabeer ya koya mata kasan cewar irin kayayyakin yake saya mata yana kuma cewa suna mata kyau,
sallah tayi sannan ta d'auko k'ura'ani mai girma ta rink'a karatu cikin muryar ta mai dad'in sauraro,
har zuwa wani lokaci sannan ta rufe tare da jero addu'oin Azkar tare da shafe jikin ta,
cikin dan k'arfin guiwar da jin tsoron da takeji ya regu ta koma kan gado ,
konciya tayi tare da yin shiru tana fidda numfashin a hankali
tana cikin hakan taji motsin mutun a parlour,
shiru ta k'ara yi ko zata ji anyi magana tsorone ya fara diro mata jin anyi shiru ba magana gashi tasan in Abba ne zayyi gyaran murya inko General ne yana shigowa zai nufi cikin bedroom d'in inko yaji a rufe ne toh zai fara kiran.
"Meenarl "
"Meenarl"
kanta ta kuma mannawa jikin pillow tare da yin zuru-zuru da ido,
tsoro ne ya kuma rufeta jin karan k'iran woya wanda ta shaida karar na woyar Abdul ne,
tsore ne ya rufeta a take gaba d'aya jikin ta ya fara rawa,
shi kuwa Abdul da yake lellek'a cikin gidan har ya samu ya shigo parlour nasu ya fara k'ok'arin zare key d'in k'ofar tasu jin karan k'ira ya shigo woyarsa ya sashi fita a firgice cikin sauri gudun kar wani ya ganshi ,
ta bayan windowta ya koma tare da amsa k'iran ganin Mama ce cikin rad'a yace.
"Mama har yanzu baki dawo ba? kinsan fa Daddy zaiyi fad'a."

Tsaki ta d'an ja tare da cewa.
"In ya dawo kace mishi naje gidan Hajia ta zan kwana sai gobe zan dawo bata jin dad'i ne."

Fuska a had'e yace.
"Toh shike nan ai, ki gaishe ta."

"Toh" kawai tace tare da katse k'iran ta shiga d'an bukkan bokan ,
tana shiga ya mik'a mata hannu tare da cewa .
"Zo mu fara aikin mu dan sai mun fara namu kafin aljana kasalau ta fara nata aikin,
cikin d'auke war imani da rashin tsoron Allah Mama ta matso kusa da wannan k'azamin bokan suka rink'a aikata k'azamin aiki mai matuk'ar muni da bala'i,
yayin da shaid'an yake mata hud'ubar zakiyi nasara.

Shi kuwa Abdul tunda sukayi magana da Mama har zai koma parlour sai ya jiyo karan tsayuwa motar General,
hakan yasa sai ya juya cikin sauri da ware k'afa ya koma part din Mama yayin da Nafeesat ko take part din Anuty Aysha..

Ita kuwa Meenal tuni tsoron ta ya dawo sai numfashi take a hankali,
Shi ko General suna isa ya fito ya nufi cikin gidan ,
yayin da Captain Sani ko ya nufi part d'in Abdul.

Yana shiga cikin gidan yaji gidan shiru ba motsin kowa haka tasa ya wuce cikin sanyi kai tsaye ya wuce parlour Abba,
sallamah yayi tare da cewa.
" Abba kayi bacci ne?."

Ido Abba ya bud'e jin muryar d'an nashi cikin kula yace.
"Haiydar ka dawo ne? shigo mana."

Shiga yayi tare da zaunawa kusa da Abban a hankali yace
"Ehh Abba yanzu na dawo,
naga gidan shiru duk har kunyi bacci."

Cikin kula yace .
"Toh tashi kake ka shiga sai da safe ko."

"Toh" yace tare da mik'ewa yana.
"Sai da safe.".

Yana fitowa parlour bakin k'ofar bedroom d'in yaje ya tsaya tare da murd'a k'ofar gim,
yaji k'ofar a rufe ,
"Meenarl "
Ya kirata cikin d'aga murya wanda cikin tsoron ta jiyo k'iran kamar a mafarki a hankali ta tashi zaune,
Shi kuwa a hatsale ya kuma watsa mata kira.
"Meenarl"
"Meenarl".

Da sauri ta mik'e tana zuwa ta murd'a key d'in k'ofar ,
shiko tun kafin ta k'arisa murd'a key d'in ya tura kofarda d'an k'arfi,
cikin rashin sa'a k'ofar ta dawo ta buge mata kai saida ta koma baya-baya zata fad'i,
cikin jin zafin ya fame mata goshinta ta juya ta zauna kan gado tare da dafe kan nata tana .
" wayyo kaina ni kam naga ta kaina."

Tsaki ya ja tare da tab'e baki a fad'ace yace.
"Wallahi kin fiye rakin banza da wofi,
sannan kinji ina k'iran ki kowa na jina kekuma kin wani b'ingire kina bacci."

Shiru tayi tare da zuba mishi ido fuska na zubda k'ollah,
bawai dan zafin buguwar bane zafin rashin tausayin da yake goda matanne ya sata kuka.

Shi kuwa toilet ya shige tare da jallabiyarsa a hannu yana shiga ya d'an watsa ruwa tare da yin alwala sannan ya zura rigar ya fito tare da d'an k'ara min towel a hannushi yana goge suman kanshi,
yana fitowa gaban mirror ya tsaya tare da murza towel din a kanshi sannan ya d'an shafa mai a jikin shi sama-sama sai kuma turarukan da ya feshe illah hirin ikinshi dashi gaba d'aya d'akin ya d'ebi wani irin k'amshin mai dad'in shak'a.

ita kuwa Meenal har yanzu zaune take tana kuka k'asa-k'asa ga hawaye cur-cur suna zuba daga dukkan alama bacci take ji amman kukan ya hanata tayi baccin ,
ta cikin mirror ya tsura mata ido tare da tsuke fuska a ranshi ko yana Mamaki yadda kuka baya mata wuya yanzu inta ga dama sai ta hanashi bacci da wannan kukan,
tsaki ya d'an ja tare da sa hannu ya tatsi maganin ta na shafawa a goshin,
cikin kauda kai yaje bakin gado ya tsaya a gaban ta,
a hankali yasa hannu ya d'an d'ago fuskar ta sannan ya d'an matso maganin tare da sunkuyowa yana murza yatsun sa biyu kan goshin nata,
kan nata ta janye tare da komawa tsakiyar gadon tana yarfa hannu tare da cewa.
"Shiihhhi wallahi zafi."

Bai kula taba sai haurawa kan gadon yayi tare dasa hannu ya jawo nata da nufin ta matso ya shafa mata,
ita kuwa cikin jin d'an zogin maganin ta zame ta konta tare dasa hannu ta kare goshin nata.

Shi kuwa yunk'ura yayi da niyar ya sauk'a ya barta da ciwon ta dai-dai sanda yasa guiwar sa zai tsalla kata ya sauk'e k'afafun shi,
a dai-dai lokacin a take yaji wani irin sanyi ya ratsa shi wanda gaba d'aya tsikar jikin shi ta mimmik'e wata iriyar muguwar kasala ta rufe shi ta yadda hatta lips d'in shi yaji sun mishi nauyi a take jikinshi ya fara wani irin rawa da tsuma cikin kasala mai tarin yawa,
ya zame kan gadon ya konta jiki na rawa konciyar yayi a hargitse k'irjin shi zuwa cikin shi ya kifa kan pillow sannan yasa hannushi d'aya ya zagayo k'irjin ta k'afafun shi kuwa suna kan nata k'afafun,
ido ya lumshe cikin kasalan da sanyi tare da jin tsinkewar zuciya ,
hannushi yake son janyewa ya kasa kuma sai kawai rawan sanyin daya fara yana ta duk'unk'u newa.

Ita kuwa Meenal jin yadda ya matseta yasa ta tattaro k'arfin ta zata yunk'ura hakan yasa ta zame kan pillow sai gashi shima ya mirgino tare da had'e k'irjin su wurin d'aya,
tsoro ne ya rufeta jin yadda yake numfashin da fizga kai ta d'an d'ago ta kalleshi cikin tsoro tace.
"Me haka Hamma haiydar?."

Cikin sanyin murya ya fara magana.
"shhhhh Meenarl sanyi nakeji rufeni rufemin jikina."

Ido ta zaro cikin Mamaki ganin yanzu yanzu lafiyar sa lau sai gashi yanzu kuma sai rawan sanyin yake yi.

Yunk'uri tayi zata zare jikin ta daga gareshi ,
sai kuma taji ya k'ara shigewa jikin ta yana.
"Shhhhhhhihhh sanyi nake ji Meenarl zazzab'i shhhihh kija blanket ki rufe ni."

Cikin tausayi tasa hannu ta janyo blanket d'in ta rufe shi ,
shiko sai k'ara shigewa jikin ta yake yi yana murza k'afafun shi a jikin ta cikin kasalan ya rink'a tura hannayen shi yana mik'a da had'e su cikin blanket d'in.

Ita kam Meenal ba abinda take yi sai cewai .
"(Isa ) sannu" .

Lokaci d'aya zazzab'i mai zafi ya rufeshi gaba d'aya jikin shi sai wani irin tiriri yakeyi jikin yayi zafi tamkar wuta.

A haka yayi ta rawan sanyi da dunk'u lewa cikin jikin ta.

Haka ya kwana cikin wahala da kasala da zazzab'i da tsinke war zuciya,
shine bai samu sa'ida ba sai da iskar asuba ta fara kad'awa tana ratsa ko ina.

A hankali ya fara jin sauk'i sai kuma kasalan dake damun shi,
ido ya bud'e tare da kallon yadda suke konce cikin jikin juna ita kam Meenal baccin take cikin mak'aleshi,
ido ya tsura mata ganin yadda ta d'aura kanta kan k'irjin shi ta mirgina k'afafun ta kuma tsakiyar cinyoyin shi yayin da gaba d'aya rigarta ta tartare ta dawo har kan cikin ta sai d'an gajeren wonddon dake jikin ta hatta cibiyarta a fili take daga sama kuma ta matse mai k'irjin sa da nata,
shi ma en duk jallabiyarsa ta nad'e cinyoyin shi kab a woje fatarta na gogarta sa sai hannunta d'aya akan cikin shi.
Shiru yayi yana mai jin sauran kasalan a jikin shi so yake ya mirgina ta k'asa ya kasa sai murza k'afafun shi yakeyi,
ita kuwa motsin shine ya sata ta d'ago kanta cikin bacci ta kife kanta kan nashi kan bakin ta dai-dai kan nashi ta woni tsuke bakin ta tura shi ,
bakin shi ya bud'e cikin sanyi da nufin ya tasheta,
aiko sai ga lips d'in ta cikin bakin shi
ido ya lumshe cikin janye numfashi ya d'an kamo lips d'anta na k'asa ya d'an ciza,
cikin tsoro da firgita tasa hannu ta tallabe kanshi tareda janye bakin ta,
ido ta tsura mishi cikin tura baki tace.
" wallahi ba kyau yin mugunta."

Ido kawai ya tsura mata a ranshi ta bashi dariya amman sai kawai ya d'an kamo lips d'inshi ya fara tsotsa,
ita kuwa cikin kiciniyar tashi takeyi daga kanshi,
shi kuwa ya matseta da hannu d'aya sai ya kuma tura d'aya hannu tsaka nin cinyoyin su yana lalubo jallabiyar sa a nufin shi ya jawo ya rufe cinyoyin shi karta ganshi a hakan
ita kuwa ido ta zaro jin yanata tura hannushi a tsaka ninsu,
shiko ya samu ya jawo ya rufe jikin shi sannan ya d'auke hannushi a kanta,
jin ya sake tan yasa ta mirgina ta konta ta bashi baya tare da tura mishi k'ugunta,
Robar gajeren wonddon dake jikin ta ya tsurawa ido ganin yadda hips d'anta ya ciki a ciki har wonddon ya matseta,
Ido ya lumshe tare da sa hannushi kan k'ugunta yatsun shi biyu yasa ya kamo roban sanna ya sake,
pet ya fetta mata shi tare da jawo duguwar rigarta yana rufe mata cinyoyin ta,
Ita kam tsalle tayi tare da dirowa kasa tana shafa inda ya fetta mata roban,
shi kuwa cikin kauda kai ya mik'e yaje yayi al'wala sannan ya fito ya nufi masallaci,
itama alwalan tayi tana ta mota sannan tazo tayi sallan.

Sune basu bar masallacin ba sai 7 dai-dai ya shigo cikin gidan shida Abban shi a parlour suka same ta ta shirya musu abin shan tea ,
Abba ta gaida tare da bashi tea d'in,
shi kuwa General sai ta kalleshi sai tayi saurin sunkuyar da kanta,
a haka har suka gama shan tea d'in Abba ya mik'e ya nufi parlour shi,
itama Abban na tafiya ta mik'e tayi cikin bedroom ensure,
Shima mik'ewa yayi cikin zafin nama yabi bayan ta,
suna shiga yayi kanta tare da matse....


Ramadan kuwa shida Rayhana tun jiya suna dawowa gida cikin tsere suka nufi part din Ammin suna shiga suka sameta da bak'in hakan yasa dole suka koma part din Ramadan suka rink'a magana kan wannan mutumin da suka gani,
jira sauk'e bak'in su tafi suko bak'in sai tara harda rebi suka tafi,
Wanda tuni su Rayhana anyi bacci,
haka yasa Ramadan yana fitowa masallaci sallan Asuba,
kai tsaye d'akin Ammi ya wuce,
bayan ya gaida ta cikin kad'uwa yace.
"Ammi....

By
*Garkuwar Fulani*
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* page 3⃣1⃣ to3⃣2⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Wannan shafi sadaukar wane gareki k'anwata ta gari har kullum kina raina Ummee Garkuwa 😍😘*



Pml
yace.
"Ammi kin san abin da muka gani kuwa jiya da hantsi?."

Murmushi tayi cikin kula tare da maida hankalin ta kan d'an nata gudan jinin ta mai sata farin cikin mai share mata k'ollah a duk sanda suka koranyo a fuskar ta mai cike da tunani da bagen wani abun da ta rasa.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Me kuka gani Ramadan har ya rud'aku haka?."

Ido ya tsura mata tare da yana yin mamaki yace.
"Ammi jiya ba munje gidan uncle Ibrahim duba jikin shiba?."

kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Ehh."

Matsota ya kuma yi tare da rik'o hannun ta cikin shak'uwa da mahaifiyar tasu yace.
"Ammi jiya a gidan uncle ni da Rayhana mun had'u da wani Soja a dai-dai k'ofar shiga part d'in uncle Ammi kin ga yadda Sojan nan yake kuwa?."

Ido ta tsura mashi tare da girgiza kai cikin son jin k'arshen maganar.

Cikin muryar mamaki yace.
"Ammi dana ganshi zuciya ta tayi ta bugawa tsikar jikina gaba d'aya ya rink'a tashi idona sai rawa suke a kan kaman nin fuskar sa hankali na kuwa ya tashi Ammi."

Rik'o hannunshi tayi cikin tsoro kar d'an nata yayi gamo ne tace.
"Ramadan me ka gani a fuskar sa? shi mutun ne ko aljan?."

Kai ya jinjina tare da sauk'e ajiyar zuciya a hankali yace.
"Ammi ina da tabbacin mutun ne shi,
Ammi kamannin fuskar Sojan nan ya bani mamaki da tsoro,
Ammi komai fa na fuskarsa da halittarsa irin nawa ne,
Ammi hatta farin mu irin d'aya ni dashi Ammi hatta k'wayar ida nunshi irin nawa ne,
Ammi hatta sajen dake fuskar sa irin nawa ne ,
Ammi wallahi ko yatsun hannushi irin nawa ne,
Ammi kamata da wancan Sojan yayi yawa har takai kamar da nakeyi dashi wallahi ko Rayhana da muke tagwaye bamuyi irin wannan kamar ba,
Ammi tsawo kawai da d'an k'iba ya fini alamun ya d'an girma ni a haife,
Ammi wallahi kwana nayi ina mafarkin shi yana kuka yana k'iran sunan ki yadda muke kiran ki Ammi shima haka yayi ta k'iran cikin mafar kina,
Ammi shi kad'ai na gani a mafarkin yana rayuwar kad'aici ba wanda ke kusa dashi dake nuna mai k'auna ko kulawa sai wata budurwa ita kuma tayi nesa dashi sai wani haske da yake tsaka ninsu sai kuma na haggo wani duhu a hannun wata mata tana turawa cikin hasken daga gefen shi kuma Hamma Jabeer ne yana jan hannun wannan budurwa."

Sai hawaye cur-cur a fuskar sa murya na rawa ya kifa kanshi jikin gadon ,
wanda Rayhana ke konce tana jin duk abinda suke fad'a tuni itama sai kuka take yi sun had'a kai wuri d'aya suna kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login