Showing 24001 words to 27000 words out of 74791 words

Chapter 9 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel

tana k'ok'arin cire hannushi da ya rufe mata baki tare da yin zillo da cure-cure da k'afafun ta sai kai take jujjuya mai cikin rauni da zare ido alamar ya jik'anta,
ina shiko mugun yayi nisa baya jin k'ira sai tsura mata ido da yayi cikin lasar lips enshi murya a sab'ule yace.
"Ki nitsu ki kontar da hankalin ki nima zan biyaki ba wai a banza zanyi ba ke tunda zaman karuwan ci kikeyi me naki nan zab'en wanda zakiyi harka dashi abu na kud'i,
kinga zamuyi abinmu ba wanda ya sani daga yau kuma duk randa Hamma Aliyu baya nan,
ni zan kasan ce tare da ke."

Ido ta k'ara zazzarowa jin irin furucin da yakeyi mata cikin rashin imani,
ganin baida imani da tsoron Allah yasa tasa hannu bibbiyu ta rink'a dukanshi tako ina duka take kai mai da yagushi kamar kare,
Ashiko maye azzalumi sai mak'aleta yake yi kamar biri yasa hannushi ya danne mata baki tare da matse mata kai yana ta k'ok'arin jawota jikin shi.

Cikin tsoro ta bud'e bakin ta da k'arfi takoyi sa'a yatsun sa sukayi cikin bakin ta da iya k'arfinta ta tak'ark'ara ta dasa mai wani irin gigiceccen cizo,
har sai da taji k'amshin yatsun suna k'as-k'as a take kuma taji alamun jiki a bakin nata.

Shi kuwa Abdul cikin wani irin gigita da azaba ya fisze hannushi tare da dirowo k'asa cikin tosku yasa hannu d'aya ya rik'e kanshi d'aya hannun da ta cizan kuma sai yarfashi yake jini na zuba d'is-d'is hannun sai rawa yakeyi kar-kar sai wani irin juya kai yakeyi cikin azaba.

Ita kuwa Meenal tun da ta samu ya sake ta ya sauk'a kan gadon,
itama ta diro cikin zafin nama da rawan jiki a guje ta nufi parlon gudu take har taje ta sake gora kanta da jikin durowar d'akin,
Amman duk da haka bata juyo ba tana gudun ceton rai sai rik'e kan tayi cikin azaba ta zund'uma ihu baki na rawa tana.
"Wayyo Allah zai kashe ni Ku ceceni wayyo Anuty Aysha kizo ki tai maka min."

A haka ta nufi parlon cikin azaba,
shima a guje yabi bayan ta,
ganin yana binta yasa cikin zafin nama ta doshi k'ofar fitan cikin rashin sa'a tana zuwa ta samu k'ofar a gark'ame yake,
bugawa ta kamayi cikin k'arfi da razani sai kuka take cikin neman ceto buga k'ofar take tana juyawa tana kallon yadda ya nufota a guje gaba d'aya jikin ta sai rawa yake kar-kar numfashi ta na fuzga ga goshin ta da ta k'ara bugewa da jikin durowa tuni sai jini yake zubdawa,
tana ganin ya iso gareta gashi duk ihun da takeyi da k'iran ba wani motsin taima ko sai kawai ta d'ora hannun ta a kai ta saki wani irin kuka mai cike da abin tausayi kuka take cikin azaban tsoro.

Yana zuwa ya sa k'afa ya taliyeta aiko tayi k'asa gim kan tayis ihu ta kuma kurmawa cikin azaba ta fara neman taima kon Allah da kiran sunan Bappa da inna cikin azaba ta kuma kurma ihu lokacin da ya shak'o wuyan ta ya mik'ar da ita tsaye,
baki na rawa tace.
"Wayyo Bappa Na wayyo Abba na wayyo *Hamma Jabeer* ina kake gashi yau za'a keta min haddi Hamma Jabeer ina kake Kaine fa kayimin alk'awarin kare min mutuncina wayyo dan uwana Hamma Jabeer Yau za'a keta haddin k'anwar ka Amina shin ina kake ne?."

Cikin rashin imani ya kuma k'ara shak'e mata wuya cikin zalumci yace.
"Ni kika zubdawa jini a jiki toh wallahi ki sani yau sai na azabtar dake iya azaba tarwa sai na keta miki haddin da kike fad'in yau ba Jabeer zaki kira ba ko ubanki ne a nan sai na ketaki,
kiyi ihu har ki mutu ba mai jinki bare ya kawo miki taima ko sai Mama ita kuwa cemin zatayi in k'ara ba rawan kai kikeyi ba in kinga Hamma Aliyu yana nan ba har zai targad'a min hannu a kanki ko? yau zan k'unsa mai bakin ciki da sai ya kusan halla kashi."

Sai kuma ya zabga mata wani irin wawan marin da yasa taga tauraro mai wutsiya atake sai ga jini a bakin ta janta ya kuma yi ya hankad'ata kan 3str
fad'awa tayi cikin azaba yayin da ta sake yunk'uro wa ta mik'e tana layi cikin kukan tace.
"Dan Allah dan son Annabin mu ka barni kar ka cutar dani zuciya ta zata bug'an zan mutu."

Mari ya kuma yarfa mata tare da shak'o wuyan ta yace.
"Yau ba mai ceton ki a gidan nan dole na mu'amalan ceki dole ne."

Kakari ta fara cikin zare ido da ficewar numfashi dan jin kamar kasheta zaiyi cikin wahala ta saki k'ara mai k'arfi murya a disashe tace.
"Wayyo Hamma Jabeer ina kake? Wayyo Hamma Haiydar ina ka tafi ka barni,
k'anin ka zai kashe ni? Hamma Haiydar kaci amanar da Bappa na ya baka ka kawo ni inda za'a kasheni Hamma Aliyu Haiydar ni kenan k'waya d'aya tak Abba na ya Haifa amman dan mahimmancin cika alk'awari ya barni na rayuwa cikin rigar Fulani gaban kakana Bappa a zaton Bappa kai mai amanane kamar Abba na shiyasa ya had'a ni da kai dan ya tseratar da raina a gun udawan da suke k'ona mana rigogi su kashemu su tafi da dabbobin mu ashe kaima inda za'a kashe ni ka kawoni?."

Kukan take cikin azaban yayin da ya jawo ta da k'arfi ya han kad'ata cikin bedroom d'in ta fad'i gim a bakin gadon,
shi ko mugun ya tsaya yana b'alle botur d'in rigar sa.

Ganin yana matso ta yasa ta saki wani irin k'ara tare da rumtse idonta sannan ta rink'a kurma k'ara da k'arfi tana.
"Hamma Haiydar! Hamma Jabeer!.."


Doctor Jabeer dake zaune gaban Alhaji Ibrahim ne ya rumtse idon shi cikin wani irin mutu wan jiki da yakeji a hankali ya kalli Alhaji Ibrahim baki na rawa yace.
" Abba bani number General Aliyu."

Mik'a mai phone d'in shi yayi,
karb'a yayi tare da d'auka number General d'in,
k'iranshi yayi a take kuma k'iran ya shiga.


Shi kuwa General Aliyu Haiydar tun da suka zo cikin Jaji ya wuce office nashi ya zauna ya k'asa tab'uka komi sai wani irin tsinke wan zuciya da yake ji har yaji gaba d'aya jikin shi na rawa,
haka kawai kuma sai yaji kamar ana rabka mai k'ira sai kunne shi kemai dumm can kuma sai ya rink'a jin fargaba abinda ko a fagen yak'i baya jin haka.

A haka ya kasa komai dole ya mik'e jiki a mace ya fitoh yana fita ya ranshi suka mimmik'e suka sara mai ba tare daya kallesu ba yacewa Captain Sani su tafi,
kai tsaye gidan shi suka nufa suna zuwa Esther ta kawo musu abinci Amman sam ya kasa ci,
a take kuma sai yaji hankalin shi ya koma kan Abban shi a fili yace.
"Toh ko Abba name jikin shi ya tashi."

Cikin kula Sani yace .
"Oga ka k'ira Abban mana ai zaifi."

Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da cewa
"Shawara mai kyau."

Yana k'iran Abba bugu d'aya ya d'aga cikin kula yace.
"Abba kana lafiya?."
Dariya yayi cikin k'aunar d'an nashi yace,
"Lafiya ta lau Haiydar kun isa lafiya ko?."

Ehh yace mai sannan sukayi slm ajiye phone d'in yayi tare da watsar da tsinke war zuciyar da yake jin.

Yana Ajiye phone din k'iran Dr Jabeer ya shigo,
da fari kamar bazai amsaba sai kuma ya amsa.
Suna gaisa wa Dr Jabeer yace.
"Kana magana da Dr Jabeer ne yayan Captain Sani naka."

"Ayyah nagane ka Doctor ."

Cikin sanyi Jabeer yace.
"Dan Allah General a tsanan ta nema da bincike plxx kar wani abu ya faru da matata kuma k'anwata Amina wallahi tsoro nakeji kar a cutar min da ita."

Cikin sanyi da kontar mai da hankali yace.
"Insha Allahu ba abinda zai sameta kuma za'a ganeta kudai ku dage da addu'a."

A haka ya kontar mai da hankali sannan ya katse k'iran,
bedroom ya tafi a niyanshi yayi bacci Amman kuma sai yana jin fargaban na k'aruwa amman sabida hali irin na maza sai ya share ya konta tare da lumshe idon...


A gida kuwa Abdul ne cikin rashin imani yayiwa Meenal........

By
*Garkuwar Fulani*πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*BANDIRAWO* pg 1⃣9⃣to2⃣0⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Pml

Wani irin shak'a ya mata tare da mik'ar da ita tsaye sannan ya ingizata kan gado,
a gigice ta fad'a kan gadon yayin da guywarta ta bugu jikin gadon lokaci d'aya ta fara ganin wani irin duhu na rufe mata ido jikin ta gaba d'aya ya kama rawa cikin rawan jiki ta sule ta zame k'asa jikin gadon tasa hannunta ta k'amk'ame cikin tattara k'arfinta baki d'aya har jijiyoyin wuyan ta na tashi ta dunk'ule ta had'a k'irjinta da guiwowin ta, ta kafa kanta jikin gadon,
tare da sakin wani irin kuka mai cin rai.

Shiko Abdul ganin niyarta na dunk'ulewa yasa yayi ta zuba mata mari da gora kanta da jikin gadon yana.
"Shegiya taurin kai ko? toh wallahi zaki jawa kanki kisa ko ki mik'e da kanki ki hau gado ki bani abin da nakeso ko na kasheki".

Cikin wata iri yar murya tace.
" kashe ni ! ka kasheni nace nafi muradin kisan a gareka mugu azzalumi tantiri la'anenne."

Ba tare da ta rufe bakin taba yayi wani irin gora kanta a jikin gadon ji kaka gum da k'arfi,
wai ina dalili zata la'anceshi'
Zafin buga kan da yayi cikin azaba ta rink'a addu'a da kurma ihu tana kiran Hamma Jabeer Hamma Aliyu a jere a jere.
"Wayyo Hamma Haiydar wayyo Allah na wayyo dan uwanka zai kashe ni zan mutu Hamma Aliyu kaci amanar yardar da Bappa yayi ma Hamma Aliyuuuuuuuuuuuuu."


General kuma yana lumshe idon sai wani irin baccin fargaba ya saceshi baccin yake cikin tsoro da bugawar zuciya,
a cikin baccin Allah ya nuna mai halin da Meenal ke ciki har k'iran da take zuba mashi,
abin kamar mafarki kamar ido biyu dan kamar a fili yake jin k'iran da take k'wada mashi,
sa juya kai yake ya kasa tashi ya kasa bud'e ido.

Shi kuwa Abdul yanzu ya samu ya b'amb'aroto daga jikin gadon ya cillata kan gado sannan ya zuge bel din k'ugunsa ya zare dogon wondon ya cilla gefe sannan ya nufi kanta haik'an k'adaran,
ganin haka yasa ta rumtse ido cikin k'arfi tace.
'Hamma Haiydar Allah ya isa min kai ka jamin Hamma Haiydarrrrrrr."


Jin wannan k'iran General Aliyu Abubakar Rumoh,
yayi wani irin firgita jikin shi na rawa ya mik'e tsaye gaba d'aya illahirin jikin shi b'ari yake kar-kar hatta jijiyoyin kanshi dana hanna yenshi idanun shi sun kad'a sunyi jazir sai zufa ke tsatstsafo mai tako ina.

Daga cikin d'akin ya fito a gigice cikin tsawa da k'arfi yake zubawa Captain Sani k'ira ba k'ak'k'autawa k'i ranshi ya a jere-ajere cikin kid'ima yana.

"Captain! Captain! Captain! Sahniiihhh ".
Shiko Captain Sani yana parlon ya b'ink'ire kan 3 str yana bacci sam duk k'iran da ake mashi baiji ba.

Shiko General ya fitowa parlour cikin zafin nama da hatsala ya tak'ark'ara ya zabgawa Captain Sani wani irin gigiceccen marin daya sa,
Captain mik'ewa cikin azaba da tsoro baki na rawa yace .
"Sir lafiya meke faruwa?."

Cikin zafin nama yayi gaba tare da cewa Captain.
"Banza kawai mai baccin asara,
ka biyoni maza yanzu zamu shiga cikin kaduna nan da minti 5 insha Allah inaso in ganni a gida."

A firgice Captain Sani ya bishi cikin gudu yana,
"lafiya kuwa?."

A fusace ya juyo cikin nuna shi da bindiga tare da cewa.
"Banza parrot kayi sauri ko na fasa ma kai ."

ya fad'a yana nunashi da bindiga,
cikin gudu Sani ya fad'a cikin motar General
BMW 7series mota mai bala'in gudun tsiya,
yana shiga shima General ya tada motar ya danna hon d'in ta wanda yake sanarwa da sauran masu saran Brigadier general Aliyu Abubakar zai fita,
ai ko a take sai ga Hilux kusan guda 8 sun bisu a baya,
gudu General yakeyi kamar zai tashi sama zuciyarsa sai harbawa takeyi tara-tara.

Cikin minti 6 sai gasu cikin Kaduna daga nesa in anji jiniyar su sai a rink'a kaucewa ana basu hanya ganin irin gudun da suke ya bawa mutane tsoro sosai,
duk motocin an tsaya a na jiran su wuce a cikin wad'an ke tsaye harda motar ya Amir dasu Anuty Aysha ,
Nafeesat ce ta kalli ya Amir cikin zare ido tace,
"Ya Amir Hamma Aliyu ne fa meke faruwa yake irin wannan gudun?."

Cikin rud'u ya Amir d'in shima yabi bayan Hilux din a guje.


Abdul kuwa yana zuwa kan gadon zai danne ta tayi yunk'uri cikin tattara sauran k'arfin ta,
ta mik'e ta sauk'a kan gadon ,
k'ara ta saki da k'arfi tare da durk'ushe wa dan ta k'asa tsayuwa dan ya buga mata guiwowin nata rarrafe ta rink'ayi cikin kuka da k'iran Hamma Aliyu ta nayi tana juyawa tana kallon yadda yake matso ta yana k'ok'arin zame gajeren wonddon dake jikin sa,
ganin har ya isota ya durk'uso kanta yasa ta rumtse ido dai-dai lokacin da ta gaggara ta fito parlon tare da cewa.
"Hamma Aliyuuuuuuuu!."

Dai-dai lokacin kuma General Aliyu yayiwa babban parlour nasu diran mikiya cikin gudu tamkar wanda zai tashi sama dan ko parking bai k'arisa yiba ya fito motar,
jin ihun ta da k'iran shi da takeyi yasa ya nufi part d'in nasu cikin azabebben fushi da hatsala gaba d'aya jikin shi b'ari yake kamar an buga mishi tambarin yak'i.

Yana zuwa ya murd'a k'ofar yaji a rufe take ,
cikin fushi da rud'ani yayi baya-baya ya sake tahowa a guje ya had'awa k'ofar naushi d'aya sai ga k'ofar ta bud'u.

Shiga yayi cikin zafin nama yayin da Anuty Aysha da Nafeesat da ya Amir suke biye dashi,
dai-dai lokacin kuma su Abba ma suka shigo cikin gidan.


Yana shiga ya hangota durk'ushe tana rarrafe , ita batama lura da shiba shiko Abdul yana d'ago kai ya kalli General da yadda ya juya kamar zaki, kawai sai ya d'ora hannu a kanshi tare da rawan jiki ya rink'a komawa baya-baya yana jan gajeren wonddon shi sama.

Ido Aliyu ya zazzaro waje cikin firgici da tsoro ga jikin Meenal da ya gani duk jini fuskar ta duk tayi jazir da jini ta kumbura sintim cikin razani yayi kanta tare da cewa
"Meenarrrrl ! me yayi miki ?."

Jin muryar shi yasa ta juyo da sauri don, da kallon Abdul take ganin ya fasa,
tab'ata,
tana juyowa taga Hamma Aliyu cikin k'arfin hali da dauriya ta mik'e a guje da dink'isa k'afar cikin kuka ta nufoshi tana.
"Wayyo Allah na Hamma Haiydar ka ceceni zai keta min haddi."

Ganin ta nufoshi ne shima yayi maza ya bud'e mata hannu cikin gudu ta fad'a cikin k'irjishi tare da rugume shi,
shima ruggume ta yayi cikin matseta a k'irjishi kamar za'a k'wace masa ita matseta yayi tsam a jikin shi yana wani irin numfashi,
da ker ya b'amb'arota sai a yanzu yaga ashe a sume take,
cikin razani ya talla bota ya mik'ata hannun Anuty Aysha dake tsaye gefen shi,
tana karb'ar ta
shiko ya nufi kan Abdul gadan-gadan cikin wani irin takun da yafi kama dana zaki ,
shiko Abdul zuwa yanzu ba fuskar Aliyu yake gani ba fuskar zaaki yake gani a jikin Aliyun yana dumfa roshi,

Cikin tafasar jini da zuciya da jiki Aliyu ya rarumo shi wuyan shi ya shak'o cikin k'arfi wanda a take Abdul ya fara wani irin kakari da zazzaro ido waje tuni numfashi sa ya fara tafiya,
shak'e wuyan Aliyu yayi har jikin shi na rawa kar-kar bai sakeshi ba har sai da yaga fukarsa tayi jazir sannan ya d'aga shi sama cikin jujjuya shi ya man nashi da k'asa,
cikin azaba Abdul ya saki wani irin gigiceccen ihu da kururuwa tare da rik'e wuyan shi da kokkoson shi ,
ba sararawa General ya rink'a butin dashi tamkar k'olloh naushe yakeyi tun cikin parlon su har ya fito babban parlour su inda Mama tayi kanshi cikin bala'i da da masifa fad'a take tana.
"Aliyu hauka ne a kanka kashe min d'an nawa zaka yi kaje ka gama d'ura giyar ka shine za kazo ka kashe min yaro toh Wallahi ka tari bala'i ka samu ka joganowa zuriyar Ku kab tashin hankali wallahi ko ubanwa ya tsaya ma sai an d'aura min kai ."

Ina aishi Aliyu baya tare da ita bol kawai yake bugawa da da Abdul yana tatta kashi a haka har ya fitar dashi farfaji yar gidan cikin huci da tafasan jini fuskar nan kamar zata fad'o k'asa ya shak'o Abdul wanda zuwa yanzu ko kanshi baya iya tsayar wa, shak'eshi yayi cikin k'arfi ya cilla shi tsakiyar yaran shi dake kollon su cikin tsoro,
cikin bada umurni yace.
"Gashi Ku canza mai kamanni ."

aiko kamar ma yunwatan zakuna sukayi kan Abdul dukanshi suke kamar zasu halla kashi ,
Mama kam ganin Aliyu ko inda take bai kala ba kawai sai ta kurma ihu ta nayi tana burburwa ta fad'i gaban Daddy cikin masifa,
ta nuna Aliyu d'aya shigo yanzu kai tsaye kitchen ya nufa yana zuwa man gyad'a ya tuttila cikin kasko gas ya kuna cikin k'ure gudun shi ya d'ora mayin a take ya fara tafasa yana damuwa kamar kolta,
bai fitoha sai daya d'auko kaskakon yana fita ya nufi waje inda Abdul yake ta rusa ihu,
ita kuwa Mama tana ganin ya fito da kaskon soyeyyen mayin gyadan ta fasa wani irin kuka tace.
"Daddyn Abdul kana gani Aliyu zai kashe mana yaro d'an k'afa zai kashe amman ka zauna ka sunkuyar yar da kai me kake nufi barin shi zakayi ya kashema d'an ka Aliyu wato tak'ama kakeda kai Soja ne tsinenne mara imani."

Cikin tarin bakin ciki da kunya Daddy yace.
"Rukayya kin cuceni kinci amana ta kin b'ata min tarbiyar d'ana! shin Rukayya sai yaushe zaki bar cutar dani da d'an uwana ."

Sai kuma Daddy ya dafe kanshi cikin kuka kamar yaro yace.
"Wayyo ni Aliyu ina zan kai wannan kayan kunya da bakin ciki ashe d'ana mazina cine mazina cin ma kuma zinar ma da matar Aure matar auren ma matar Aliyu d'an uwanshi,
Rukayya Allah ya isa ni ban bawa Abdul irin wannan tarbi yarba kin cuceni kin cuci d'anki,
Aliyu ka kashe Abdul ko ma samu mu cire najasa a cikin zuciyar mu,
Rukayya ki sani ina sane ke kika had'a tuggun da kika rab'a d'an uwana da matar sa sannan kika maida musu d'an su marayan dole, wannan gidan da muke ciki kin sani gidan d'an uwana ne amman masifar ki da sherrorin ki yasa gidan yafi k'arfin shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login