Showing 51001 words to 54000 words out of 74791 words
Chapter 18 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
nawa!, dan Allah
Barrister karka sake cemin bani da asali! ina da Ubana! kuma ya raine ni! Uwata kuwa mutuwa ce ta rebani da ita!!."
Zuwa yanzu nufashin Sa ya fara fizga cikin zafin rai ya fizgo hannun Abdul murya na carkewa ya nuna Abdul tare da cewa.
"Ko a nan wurin ina da d'an UWA! gashi nan ba gidan marayu na rayuba! Captain Sani kai kasan hakan!!!."
Cikin zafi da cushewar zuciya ya bud'e motarsa tare dasa Abdul a ciki shima ya zagaya ya shiga ma zaunin direba cikin zafi ya fizge hannu shi da Ramadan ke rik'e dashi yana kuka kamar yaro cikin kukan yake cewa.
"Hamma Haiydar kana da UWA mahaifiyar ka bata rasuba tana raye Hamma Haiydar ba Abdul kadai bane d'an uwan ka a nan nima d'an uwanka ne ga Rayhana ma y'ar uwarka ce Hamma Aliyuuu ga Ammin mu tana raye Hamma Haiydar Meenarl d'in kanta y'ar uwarka ce."
Ina General tuni ya rufe motar ya figi motar a guje yayi woje k'iris ya rege ya taka mai gadin su gaba d'aya inda nunshi sun makan ce zuciyar sa ta cushe ba abin da yake cewa sai.
"Ammi na Meenarl Ammi na Meenarl itace ta fara cireni a halin da nake ciki na rashin ki,
itanma rashin ki ya jazamin rashin ta."
gudu yake kamar zai tashi sama.
Shi kuwa Ramadan ganin General ya fita ya sashi sakin kuka kamar yaro cikin kukan yazo ya durk'usa gaban Abba da Hamma Jabeer sai ya saki wani irin kuka cikin muryar kuka yace.
"Ammi kiyi hak'uri ki gafar ceni nasan abinda zan fad'i zai b'ata miki rai yau zan gayawa su Abba gaskiya."
Cikin kukan Ammi ta mik'ewa tazo gaban su cikin juya kai tace.
"A a Ramadan a a."
Kai ya juya cikin zubda k'olloh yace.
"Daddy kun ganin ko Abba kalli yadda y'ar uwarku ke kuka da zubda k'ollah kalli har kamar numfashin ta zai yanke,
Daddy shin kasan waye General Aliyu ? Abba,General Aliyu Yaya nane d'an Ammi nane shine d'anta na fari wanda ta haifa a gidan Abban mu shine d'an da kuka rabashi da uwarshi tun yana d'an shekara 4 zuwa 5 gashi da kunnen Ku kunji yana fad'in mahaifi yarshi ta rasu alhalin gata a gaban shi Amman bai ganeta ba kun rab'a UWA da d'anta dan laifin Abban mu ya saketa."
Ammi kam sai kawai ta yi cikin gida tana kuka cur-cur da hawaye,
shi kuwa Dr Jabeer cikin b'acin rai da tarin tausayin Ammin nashi yabi bayan ta.
Daga nan gaba d'aya suka shige cikin gidan,
A babban parlour Dr Jabeer ya samu Ammi tana zaune kan 1 str tana zubda k'ollah yana zuwa gaban ta ya durk'usa cikin tsura mata ido yasa hannun shi ya goge mata k'ollah baki na rawa yace.
"Ammi ke k'anwace ga mahaifi na Amman duk wani gata da UWA keyiwa d'anta ke kinyi minshi tabbas ni nasan kina da wani d'an mai suna Aliyu Ammi wai da gaskene General Aliyu shine d'an uwana Aliyu da kike fad'a min?."
Hannun Dr Jabeer ta rik'e murya na rawa tace.
"Jabeer General Aliyu d'an uwanka ne ka tuna fuskarsa ka kalli fuskar Ramadan."
Cikin sanyin jiki Abba da Daddy suka zauna jiki a mace Abba kam sai juya kai yake yi.
Captain Sani kuwa Kuka yake kamar ba soja ba tamkar yaro k'arami yana juya kai ya kalli Meenarl yace.
"Habba ashe Hamma Haiydar d'an uwana ne jinina ne shi Meenarl ashe ke jinin Hamma Aliyu ne shi yasa mukeyiwa juna wani irin kauna ashe kula da kauna da Jana a jiki da Hamma Haiydar yakeyi ni d'an uwanshi ne shi yasa."
Gaban Daddy ya rarrafa yaje cikin kukan yace.
"Daddy General Aliyu akan Meenarl ya kusan nak'asa wannan d'an uwana nashi duk da su basa son shi amman General shi maison y'an uwanshi ne,
Abba kune sana din sa General cikin kad'aici a rayuwar sa,
kullum sai yayi kukan rashin mahaifiyar shi ashe kune kuka maida shi maraya,
kalli ratar dake tsaka nina da General amman ba tare d'aya duba matsayin shiba ya jani jikin sa Daddy kasan cewa a mata kan soja Aliyu yana mataki na 8 niko ina mata ki na 3 shi General ni Captain amman ya zabeni a matsayin mai kasan cewa tare da shi."
A haka cikin kuka Captain Sani ya basu labarin tun zuwan su Gembu Membila har abinda ya faru tsakanin Abdul da Meenarl har yadda Mama ke cuszuganawa General d'in da yadda yayi ta lura da Meenarl da bata kariya har zuwa kan ciwon da yake kwana dashi.
ya k'ara da cewa.
"General bashi da kowa ba wanda yasan halin da yake ciki nima Meenarl ce ta gaya min sai kuma lura dashi da nakeyi."
Ramadan ne ya mik'e cikin kuka yace.
"Ammi kiyi hak'uri Daddy Ku gafar ceni nagode da kulawar ku nasan zafin abinda Abban mu yayiwa Yar uwarku ne yasa kuka k'i yafe mishi,
toh ni kam da Rayhana mun yace mishi kuma ni zan tafi gun mahaifi na da d'an uwana zanje na kula dashi zanje na jinyacesa zanje na d'ebe mai kewa zanje in cireshi cikin kadaici zanje na gaya mishi Ammin shi tana raye kuma tana sonshi."
Daddy kam shiru yayi cikin kuny'ar uwar tashi shiko Abba tuni sai k'ollah yake dan dama Barrister ya fishi zafi.
Ita kuwa Meenarl tuni ta koma jikin Hajia Amina ta rakub'e sai sautin kukanta dake tashi,
Dr Jabeer kuwa hannun Ammi ya rik'e cikin lallashi yace.
"Ammi kibar kuka insha Allah farin cikin ya dawo gareki."
Ummi kuwa kuka take tana maison kara ganin fuskar General sai yanzu ta gano dalilin da yasa take son Ramadan ashe kama take ganin yanayi da d'an uwanta amman sai yau taga kamar da tafi na Ramadan d'in,
cikin kukan ta bawa Alhaji Ibrahim labarin yadda sukayi da Bappan ta kuma fad'i dalilinta na hana Bappa ya gaya mishi.
Ramadan kam juyawa yayi ya mik'a wa Rayhana hannu cikin sanyi yace.
"Rayhana muje ga d'an uwanmu yana buk'armu a kusa dashi."
Hannu ta mik'a mishi suke nufi woje Captain Sani ma mik'ewa yayi cikin share k'ollah a fuskar shi yace.
"Daddy nima zan bi su Ramadan zanje gun Hamma Haiydar."
Shiru iyayen nasu sukayi har suka fita basuyi ko motsiba.
Kai tsaye gidan su General suka nufa,
suna zuwa bak'in k'ofar get d'in Captain Sani yayi ta dannan hon Amman shiru mai gadin ya lek'a sai ya koma ya share su cikin hatsala Captain ya fito yazo inda yake yace.
"Sajen ka bud'e min get."
Cikin girmamawa Sajen din yace.
"Oga yace kar a sake barinka ka shiga gidan nan."
Kai ya kad'a cikin tausayi dan yasan yau ba mai tausar General d'in ,
su Ramadan kuma da ya gaya musu cewa sukayi .
"Mu banza mubar k'ofar gidan nan ba wallahi anan zamuyi ta zama har sanda zai fito."
Haka kuwa suka coge a k'ofar gidan har zuwa dare in lokacin sallah yayi suyi sallah a masallacin k'ofar gidan.
Ita kuwa Meenarl Dr Jabeer ya tare a gidan yana ta cikata da salon wasan d'aya saba tuni ta sake suna ta hira da dariya Ammi kuwa yayunta sunyi ta lallashin ta duk da hakan,
ita kam Ammi har yanzu hankali ta na kan d'an ta.
10:00 pm Meenarl dake zauna gaban Hajia Amina da Ammin ,
tayi wani irin razana cikin zaro ido ta dafe kirji gaba d'aya jikin ta na rawa tace.
"Momy Hamma Haiydar wallahi daga yanzu ciwon shi ke tashi."
Shiru Ammi tayi tare da sunkuyar da kanta k'ollah na zuba.
Hajia Amina ce tace.
"Insha Allah yau zai samu sauk'e kinga Dr Ramadan yana can gun shi."
Ita dai kife kanta tayi cikin cinyoyin ta.
Shi kuwa General Aliyu tunda ya figi mota ya fito gidan su Meenarl ko idanun shi basa ganin cikin ikon Allah ya kawosu gidan lafiya,
yana yin parking ya bud'e mota ya nufi cikin gida yayin da Abdul kuwa ke binshi a baya cikin tausayawa hak'ik'a yau zuciyar shi ta cika da tausayin d'an uwan nashi a fili yace,
"Hamma Aliyu Allah ya kawo ma farin ciki a rayuwar ka."
Shi kuwa General yana shiga gidan kai tsaye part ensu ya nufa a parlour su ya zame cikin kuncin rayuwar ya kife kanshi kan kujera ya rink'a kiran.
"Ammi! Ammi! Abba! Abba! me yasa baku tuna makomata ba gashi a yau an wayi gari ana shirin shegan tani,
Ammi na me nayi mik'a ni kuwa da kika manta ni,
kin barni na rayu tamkar maraya."
Haka ya rink'a kuka kamar yaro gaba kad'an yau kewar Ammin shi ya zame mai sabo fil a parlour ya wuni cikin kunci sallah kawai ke tayar dashi daga parlourn.
10:00 pm
ya fara jin kasalar tana rufeshi a take sai ga zazzab'in ya rufeshi ciwon ciki ma yace bismillah sai rawan sanyi yake.
Kanshi ya kifa kan gadon cikin azaba da tausa yawa kanshi murya na rawa yace.
"Meenarl bani da lafiya Jabeer shi ya dace da ke me ribata in na zauna da ke bayan nasan banda lafiya banzan cutar da keba,,,
banzan bari ciwona ya zama matsalar kiba Jabeer shine mijinki ni kam Aliyu bani da lafiyar da zan zauna da ke Minali Hamma kece mai kula dani gashi munyi nesa da juna."
Haka ya rink'a rawan jiki da azabebben zazzab'i.
Dai-dai lokacin Abba kuwa da ya Amir motarsu ta iso k'ofar gidan Captain Sani da su Ramadan kuwa suna ganin an bud'e wa su ya Amir gate suna shiga suma suka dannan hancin motarsu cikin gidan.
Abba na fitowa Ramadan ya kalli Captain Sani cikin sanyi yace.
"Abban mu ko?."
Kai ya gyad'a mishi tare da cewa.
"shida ya Amir."
Fita Ramadan yayi cikin sanyi ya je gaban Abba hannu yasa....
By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page
4⃣6⃣
*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*D'erewol gol mi vinddi gol gam nango beldum fulb'e eb'e gonifu had'er duniyaru du, Fulb'e Cameroon eh Fulb'e chardi eh Fulb'e Niger eh Fulb'e Ghana eh Fulb'e laidi am dayirdi am Fulb'e Nagerian min Garkuwa mon on mi sakki on gol d'erewol golfu gol modon,.. Allah accu lawol fulb'e Amin ya Allah*
Kanshi a sunkuye ya mik'a hannu ya karb'i brufcs d'in hannun Abba kanshi a k'asa yace.
"Barka da dawowa Abba."
yana fad'in haka yasa kai yabi bayan ya Amir,
shi kuwa Abba bugawar zuciyar sace ta tsanan ta cikin mamaki da rud'ani dan tabbas yana kama da General amman tafiyar General ba irin nashi bane kuma muryar General ba irin muryarsa bace,
ido ya sake tsurawa Ramadan cikin kallon tafiyarsa sak irin tashi sannan muryar da yaron yayi maganar sak irin muryar sa,
sosai ya tafi duniyar tunani a fili yace.
"Toh wannan yaron kuma waye shi? daga ina yake? me ya kawoshi gidan nan? ."
Captain Sani ne ya jawo hannun Rayhana cikin sauri yazo gaban abban tare da cewa.
"Abba barka da dare."
cikin sauri ya juya gun Captain tare da cewa.
"Yauwa Sani kana gida ne dama? ina ogan naka?."
ya d'an juya ya kalli Ramadan da tuni ya shige cikin gidan,
juyowa ya kumayi cikin bugawan zuciya yace.
"Kai Sani wancan yaron fa waye ne daga ina yak....!."
Shiru yayi ba tare daya k'arisa tabbayar tasaba ya tsurawa Rayhana ido cikin matukar mamaki tabbas bazai mance irin wannanr fuskar ba a rayuwar shi tabbas ko zai manta komai a duniya bazai manta fuskar mahaifiyar shi ba,
hak'ik'a
tunda ya baro rigarsu bai k'ara ganin fuskar da take kama da fuskar Innarshi ba sai a kan Meenarl shi yasa ya jinta har cikin ransa yana sonta bisa gaskiya da kaunar fuskarta dan tana kama da Innarshi sai gashi yau kuwa yaga wata fuskar da tafi kama da ta Innar tashi ido ya tsurawa Rayhana cikin kad'uwa da k'aunar yarin yar yace.
"Sani wannan kuma fa?."
Ita kuwa Rayhana sai hawaye kawai dake bin fuskarta tana kallon mahaifin ta cikin kuka tace.
"Abba ni y'ar kace amman gani a gaban ka baka san cewa ni jinin ka bace ni tsasonka ce Abba ni da wancan yaron da ya shiga cikin gidan sunan shi Ramadan mu y'ay'anka ne da ka saki Ammin mu tana da cikin mu Abba kace mu ba yaranka bane? amman gashi kamannin Ramadan yau zai nunama mu jinin kane Abba yau gamu a gaban ka muna sonka a matsayin ka na mahaifinmu Abba muna son Hamma Haiydar d'an uwana yana buk'atar mu a kusa dashi."
Shi kam Abba tunda ta bud'i baki yaji sautin muryar ta irin ta Innarshi sak sai wani jiri yaji ya d'ebe shi duhu ya rufe mai ido jikin mota ya koma ya jingina kai yake juyawa yana cije lips enshi abinda a gunshi General ya gaji cije lips Abba kam sai jiri yake k'ara gani dan yau tunanin mahaifarshi ya d'arsu a ranshi begen Innarshi da Bappa shi yake tamkar zasu fasa mishi zuciya yau ba abinda yake bege kamar tushensa asalin sa.
Cikin jirin yace.
"A a,
a,a Rayhana Ramadan ku y'ay'anane Allah sarki Fatima data haifeku sai tasa mik'a sunan da yake sunan Innata ta,
ina Ramadan ina sonku yarana."
Sai kuma kawai yayi luu zai fad'i a sume.
Cikin sauri Captain Sani ya tallabo shi tare da rugume shi,
Ita kuwa Rayhana kuka ta saki da k'arfi tana kiran.
"Abba! Abba ! ka tashi mu rayu a sauran rayuwar da ta rege mana."
Sai kuma tayi cikin gida tana.
"Ramadan! Ramadan! Abban mu!."
Captain Sani ne ya tallaboshi suka nufi cikin gidan yana.
"Kai Rayhana kiyi shiru kar ki karawa Hamma Haiydar firgici."
Shi kuwa Ramadan bin ya Amir yake har suka shiga cikin gidan suna isa babban parlour ganin ya Amir d'in zayyi part din Mama yasa shi yin gyaran murya cikin sanyi yace.
"Ya Amir ina Hamma Haiydar?."
Da sauri ya Amir ya juyo dan shi a zaton shi Abba ne dan muryar sak ta Abban sai kuma yayi mamaki Abba ne zaicewa Aliyu Hamma Haiydar.
Ido ya kuma zarowa ganin wannan yaron wanda komai nasu irin d'aya shi da Abba da Aliyu sai dai bai kaisu tsawo ba,
Shi kuwa Ramadan murmushi yayi cikin k'aunar ya Amir d'in ya matsoshi kafa d'arshi ya dafa tare da cewa.
"Dr Ramadan Abubakar Umar Rumoh suna na ,
ma,ana k'anin General Aliyu Abubakar Umar Rumoh,
ya Amir nasan kai kasan Ammi na ni d'an uwanka ne nida Rayhana."
Kai kawai ya Amir yake juyawa.
"Dan tabbas da kaga Aliyu kaga Ramadan kasan ciki d'aya suka konta da zaran kaga Abba kuwa kasan shine mahaifinsu tabbas kuma shi yasan Ammi dan da girman shi tabar gidan kuma yaji zancen ta fita da ciki ta kuma haifi yan biyu.
Kawai sai ya rugume Ramadan d'in fuskar sa cike da happy cikin d'an daga murya yake cewa.
" Daddy! Abba! Mama! Abdul! Aysha! Nafeesat! kuzo ! kuzo! ."
Nafeesat kuwa tunda suka je gidan su Meenarl ta kalli Ramadan da Rayhana ta kuma ga ana ta tara musu zugan sojoji ta zille cikin kuka ta fito kai tsaye mai a dedeta ta tsare ta shiga tare da cewan.
" uguwar sarki."
A nufinta zata je ta gayawa Abban ta sai kuma gashi suna fita layin sukayi kicib'is da motar General Aliyu hakan yasa ta samu nitsuwa don tabbas tasan komin yaya In General yaje zusu sake Abdul,
shi yasa koda ta dawo gida part d'in Anty Aysha ta nufa,
tunda ta dawo take bata labarin abinda ke faruwa toh tun lokacin tana part din su ya Amir d'in dan ita bata fiye shiri da Mama ba sai yanzu da sukaji kiran ya Amir d'in suka fito.
Shi kuwa Abdul tunda suka dawo tare da General gaba d'aya zuciyar shi ta cika da tausa yin Hamma Aliyun nasu cikin sanyi ya shiga parlour Mama gefen ta yaje ya zauna a hankali ya bata labarin abinda ke faruwa,
sannan yaci gaba da cewa.
"Mama Hamma Aliyu bayida lafiya ga tarin damuwa ga rashin Ammin shi gashi Meenarl d'in ma yau bata nan,
Mama inajin tausayin d'an uwana."
Cikin jan dogon tsaki ta watsa mishi harara tare da cewa.
"Toh me had'inka da shi koma mene wallahi ni bani janye guduri na a kanshi."
Mik'ewa yayi cikin tsanan halin mahaifiyar tashi yana fita tare da cewa.
"Mu daiji tsoron Allah wallahi ni ina son d'an uwana."
Ita kam Mama tsaki taja tare da yin dariya mugunta, sannan ta koma ta konta,
ta lumshe idanun ta kenan taji muryar Amir yana zuba musu kira da sauri ta mik'e ta nufi parlour...
Su Captain Sani kuwa a tare suka shigo da Rayhana dake ta kuka tana.
"Ramadan Abban mu."
Da gudu Ramadan ya karisa inda Captain ya kontar da Abba yana ki ranshi tare da bashi taima kon gaggawa.
Su Mama kuwa da Abdul dasu Nafeesat gaba d'aya sun rude sai dai kowa da abinda ya rud'ashi ita mama tsoro Ramadan ya bata shiko Daddy ciwon d'an uwanshi ne ya firgi tashi.
Rayhana kuwa hannun Abban ta rik'e tana kuka shiko Ramadan tafin k'afan Abban ya rik'e tare dasa tafin hannun shi yana murza k'afan Abban a hankali Abban ya bud'e ido cikin rawan murya yayi salati tare da kamo hannun Rayhana sannan ya tashi zaune da k'er sannan ya jawo Ramadan ya rugume su kawai sai ya saki kuka tare da rik'o hannun Daddy murya na rawa ya kalli Daddy yace.
"D'an uwana wad'an nan yara nane yaran da Fatima ta haifamin bayan nasake ta."
Sai kuma ya juyo fuskar Rayhana yace.
"D'an uwana kalli hoton fuskar Innarmu."
Cikin murmushi Ramadan yayi musu
Introduce kanshi da Rayhana ayyah sai kuma Daddy ya rugumi Abba suka fashe da kuka cikin tunanin mahaifarsu.
Ita kuwa Mama zuface ke keto mata tako ina a firgice taja hannun Abdul har parlour ta cikin zare ido tace.
"Abdul ina mafita."
Zame hannu shi yayi tare da zubda k'ollah yace.
"Mama ni yanzu ba Abdul d'in da bane yanzu cikken sunan nake amsawa *Abdulmuminu* ina son y'an uwana wallahi banzan sake cutar da kowa ba."
Sai kuma ya fashe da kuka tare da ficewa ya barta a tsaye .
Abba kuwa da Daddy d'aya Amir dasu Nafeesat da Anty Aysha farin ciki sosai sukayi.
Cikin sanyi Ramadan ya mik'e tare da kamo hannun Rayhana ya kalli Abba yace.
"Abba ina Hamma Haiydar ?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Muje ."
Allah sarki shiko General Aliyu da k'er ya yajowo blanket ya rufe jikin shi yana ta rawan sanyi tare da dunk'ilewa wuri d'aya gaba d'aya yaji abinda su Abba ke fad'a a parlour so yake ya tashi amman ya kasa Fuskar Ramadan da Rayhana kawai