Showing 45001 words to 48000 words out of 74791 words
Chapter 16 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
ya gaida Abban ne ya mik'e tare da cewa.
"Abba bari in wuce Jaji akwai sojojin da zan sallamah zasu tafi borno."
"Toh Haiydar Yau ina Sanin naka?."
"Yana gidan su Abba nima ba dadewa zan yi ba yanzu zan dawo shiyasa ba sai na tafi da shiba."
"Toh" kawai Abban yace,
ita kuwa Meenal mik'ewa tayi rik'e da cup d'in tea da sauri tabi bayan shi cikin kula tace.
"Hamma Haiydar ga tea kasha kafin ka tafi."
Bai kulata ba bai kuma juyo ba,
da sauri tasha gaban shi tare da mik'a mishi cup din tace.
"Ayyah Hamma Haiydar kasha tea nasan inka tafi baza ka nemi abinda zaka Ciba."
Kai ya juya zaiyi magana ,
tayi maza ta manna mai cup d'in a bakin shi.
Ido kawai ya tsura mata ganin yadda ta dago k'afafunta sama tare da d'aga hannu kafin ta samu cup d'in ya isa bakin shi,
a haka ta rink'a bashi yana kurba har ya sha rebin tea d'in,
sannan yasa hannu ya janye hannun ta cikin kallon juna ya manna mata kiss a goshi sannan ya fice da sauri yana jin dad'in yadda take kula dashi..
Yana fita Nafeesat ta shigo Abba ta gaida sannan ta kalli Meenal cikin murmushi tace.
"Meenal yau ne zamuje kitson ko?."
Shiru tayi tana tunanin yau dinma bata gayawa Hamma Aliyu ba kuma ya hanata fita kuma gsky tana son yin kitson,
Jin tayi shirun ne Abba yace.
"Zaku je mama Nafeesatu ai barin kai a tsefen ba dad'i."
Cikin jin dad'i tanaga ta samu madafa ko Hamman ta zaiyi fada zata ce Abba ne ya barta,
tana happy tace.
"Eh zamuje ."
Haka kuwa akayi 11:00 na safe suka gama shirin su tsab suna fitowa suka samu Abdul yana shirin fita a motar shi,
ganin su ya sashi yin murmushi mugunta cikin mugun nufi yayi...
*Sisters wata k'il gob'e bazaku samu ba dan gobe zan koma fatan Allah ya maida in lafiya*
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* pg 3β£8β£to4β£0β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*Damoni na damoni! gidd'o mo fina laramo! gaid'o mo fina sukoyo ladde Allah yama d'um! Kinkid'i kakkad'a! ki d'oidi yalete! yoriki tenete! ki b'ibb'e sammete! b'enduki yamete! Mo Allah hoinani wala ko sad'in ta d'um!*
Gunsu kai ya kauda gefe cikin muryar munafurci yace.
"Nafeesat fita zaku yine?."
Kai ta d'an d'ago ta kalleshi tare da gyad'e mai kai alamar .
"Ehh", sannan tace .
"Gidan kitso zamu je."
Ita kuwa Meenarl kai ta kawar gefe cikin rashin son ganin Abdul d'in dan har ga Allah tsoro yake bata.
Kanshi a sunkuye yana k'okarin kunna kid'i cikin motar sa tare da zuge glass d'in motar sama tare da cewa.
"Ku shigo in sauk'e ku tunda nima fitan zanyi."
Shiru Meenarl tayi tare da tuno Hamma Aliyu yama hanata fitan fa kuma sannan ta fita fitanma kuma da Abdul,
itako Nafeesat cikin kula ta kalli Meenarl d'in a hankali ta kamo hannunta cikin yak'ini da karfin zuciya dan ita tanaga har abadan Abdul bazai kuma gigin tab'a Meenarl d'in ba dan ya horu horo iya horo,
ita kam Meenarl kai ta rink'a juyawa cikin sanyi tace.
"Nafeesat ni bazan shiga motar shiba."
kallon ta Nafeesat tayi cikin jinjina kai tace.
"Wallahi Meenarl har abadan Abdul zai kasance mai tsoron ya kuma cutar dake kuma gani gaki insha Allah bazai miki komai ba,
kuma wallahi Abdul yanzu ya canza kinga yana jin tsoron Hamma Aliyu."
Ita dai tsayuwa tayi cikin d'an farga ba,
tana ji Nafeesat ta kamo hannuta suka shiga motar,
suna shiga suka rufe,
shiru tayi cikin jin bugawar k'irji da tsananin firgici da tsoro gaba d'aya zuciyar ta sai duka yake tara-tara.
Shi kuwa Abdul lumshe ido yayi tare da sauk'e ajiyar zuciya yana murmushin mugunta da kanne ido a ranshi yake fad'in.
"Meenarl kinyi gaggancin shiga motata kinyi wautar saurin mance waye Abdul,
Nafeesat kinyi wauta da kike tunanin Abdul zai gani ya k'yale."
A haka ya figi motar a 100 suka fito tare da daukar hanyar tudun wada,
inda ita Nafeesat bata damu ba don tanaga ai hanyar zata b'ulle dasu inda zasuje d'in,
ita ko Meenarl shiru tayi tare da maida hankalin ta kan titi don sam ita bata samu nitsuwa ba kallon titin take da kyau har ta manna fuskarta da jikin glass din ta yadda wanda yake wojema zai ga fuskarta ras,
shiko Abdul a ranshi murna yake a nufinshi zaice bari ya biya gidan abokin shi dasu daga nan zai samu ya aiki Nafeesat bakin titin ta seyo mishi katin woya kafin ta dawo kuwa hak'arsa zata cimma ruwa murmushi yayi cikin mugunta da jin dad'in yana mai yarda da kanshi.
Gudu yake kamar wanda zaiyi doguwar tafiya gudun yake ba tare daya tuna a cikin gari yake bafa.
Gudun yake har ya kamo titin dake bi ta k'ofar gidan gwamnan garin Kadunan ba tare da tuna komai ba ya saki kid'i da gudu kamar mai tashi sama,
a haka har ya isa dai-dai wurin da sojojin dake tsaron kofar gidan ba sassauci ya danno kanshi zai wuce ba tare da tuna ya taka doka ba,
Captain Garba dake kan titin bai kula da motar tasuba har saida yazo gab dashi karar yadda yake gudun ne yaja hankalin Captain Garban cikin murtuk'e fuska da tsarewa irin nasu na sojojin ya d'ago kanshi tare da sa hanccin bindigarshi yana yin k'asa dashi alamar ya tsaya,
shiko Abdul a take tsoro ya rufeshi a zaton shi akan Meenarl yake tsaida shi tunda Meenarl matar ogansu ne ya kuwa tuna sarai randa suka ci ubanshi da duka harda Captain Garban a cikin su,
abinda Abdul bai saniba (su kam basuma san akan me General yasa sukayi mishi duka ba a wancan ranar don basu san Meenarl a gun General ba a zahiri sai pictures dinta da General d'in yasa Captain Sani ya reba musu a matsayin ana neman ta ta bata ne, yayin da shiko General har yau bai kalli pictures enba).
Shiko Abdul tsoron ko kar Meenarl d'in Captain Garban ya gani yasa yake tsaida shi ,
yasa yaki tsayuwa sai k'ara gudun da yayi,
yayin da shiko Captain Garban Abdul na figar motar ida nunshi suka sauk'a kan fuskar Meenarl dake ta d'an zare ido dan a zaton ta tunda taga sojojin kar Hamma Aliyu yana cikin su,
cikin sauri Captain d'in ya juya kan kalandun da suka manna a d'an wurin yana mai kallon fuskarta Meenarl ido ya zaro cikin mamaki ganin tabbas ita ya gani cikin motar nan da ta d'an wuceshi kad'an.
Cikin zafin nama ya d'aga bindigarshi sama ya saki harbi 3 a jere hakan yaja hankalin sauran sojojin ganin ogan su na sake harbi,
shiko Captain cikin gudu da zafin nama yayi tsalle ya fada cikin hilux d'in su dake Jere a wurin cikin tsawa ya kalli sauran tare da cewa.
"Maza Ku shigo Mubi waccar motar."
D'aya daga cikin sune ya kalleshi lkcin da suke tayar da moticin yace.
"wacce mota d'aya oga ai motocin nada yawa."
A fusashe yace.
"Waccar black C,R,V d'in can."
Aiko cikin sakin sautin jiniya da k'aran bindigoginsu suka bishi a guje shiko Abdul,
cikin tsoro da firgici da tsinkewar zuci ya k'ara gudun nashi zuwa 180 gaba d'aya jikin shi sai b'ari yake zufa na keto mashi tako ina dan har ya mutun bazai manta azabar da yasha a hannu wadan nan mugayen sojojin ba gudu yake cikin neman ceton rai,
Ita kuwa Nafeesat cikin mamaki ta ke kallon shi baki na rawa tace.
"Ya Abdul wannan wanna irin gudune ka tsaya mama ka rege gudun nan a cikin garifa muke zaka kashe mune?."
shi dai gudun kawai yake sai zare ido yake yana kuma kallon su Captain d'in ta cikin madubi,
ita kuwa Meenarl tuni ta tsinke da gudun da yake kawai sai ta rink'a kuka tare da salati tana.
"Wayyo Allah na wayyo Hamma Aliyu shike nan Abdul zai marka d'amu a kan titi dama saida ka hanani fita ashe kasan abinda Abdul yake shirin aika tamin."
Shi kam Abdul kai ya rink'a juyawa cikin tsoro yana.
"Dan Allah kiyi shiru wallahi ba abinda zan miki Meenarl ki kalli bayan mu sojojine ke bina kuma in sun kamani zasu kasheni."
K'ara mai k'arfi Meenarl da Nafeesat suka sake tare da k'amk'ame juna jiki na rawa,
dan k'aran fashewar tayarsu da sukaji a lokacin da Captain Garba ya harbi tayar.
Fuuuh iskar tayar ta rink'a sacewa Wanda dole motar ta tsaya yayin da ababen hawan dake kan titin kab suka tsaya.
Dai-dai lokacin suko sojojin suka iso tun basu gama tsayuwa ba Captain Garban ya diro cikin hilux d'in tare da sa kai cikin motar Abdul d'in,
shi kam Abdul tuni yayi mutuwar zaune,
ita kuwa Meenarl ba wai tsoron sojojin take jiba dan tasan duk wadan nan bazasu wuce abokan Hamma Aliyu ta bane a zatonta zasu kwace tane daga hannun Abdul,
Ita kuwa Nafeesat gaba d'aya ta firgita tana jin tsoron karsu kashe mata d'an uwa.
Captain yana bud'e motar ya wani irin rarumo Abdul.cikin zafin nama ya fizgoshi woje,
cikin hatsala da tuhumarshi da sace y'ar Alhaji Ibrahim mai dala,
ya rink'a zuba mishi maruka ba k'akk'autawa har sai da Abdul din ya zube k'asa daga nan kuma ya rink'a butin dashi a kan titin yana tattakashi,
shi kam Abdul zuwa yanzu ba abinda yake sai ihu da neman taimako yana kururuwa,
Nafeesat ma da ta fito cikin motar sai kuma take tana .
"Ku bar shi me ya muku zaku kashe min d'an uwana."
Itama Meenarl fitowa tayi tana zubda k'olloh dan Abdul ya bata tausayi matsosu tayi cikin kukan tana.
"Dan Allah karku kasheshi ba kyaufa kisan kai."
Shi kam Captain Garba cikin zafi ya cukuikuyo Abdul d'in sannan ya tura shi cikin hilux d'in sannan ya dawo gaban Meenarl d'in ya kamo hannuta ya bud'e gaban motar yace.
"Shiga ciki ."
Sannan cikin sassaita fushinsa ya kalli Nafeesat tare da cewa.
"Zo ki shiga."
Cikin tsoro ta shigo sannan ya shiga tare da figar motor suka tafi kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim suka nufa yayinda sauran hilux 3 ke biye dasu a baya wanda cike suke da sojojin,
tin kafin su isa Captain ya kira Dr Jabeer yashai da mishi sun gano matarsa da ake nema kuma sun kama Wanda suke zaton shine barawon.
Shi kuwa Dr Jabeer da yake cikin Zaria cikin asibitin cika tuni ya fito ya nufo cikin Kaduna zuciyarshi cike da farin ciki a d'aya gefen kuma fargaba yake kar dai yaje ya samu ba Ita bace.
Shiko Captain Sani suna can cikin gidan Alhaji Ibrahim d'in a inda yake kiran su Ramadan su zo.
Su kuwa su Ramadan da Ammi tare da Rayhana Motar su na shiga gidan hilux din sojojin na biye dasu a baya.
Shi kuwa Alhali Ibrahim wanda yake tare da yayanshi Barrister Lawan suna Parlour Alhaji Ibrahim din woyar da Dr Jabeer yayi ya shaida musu anga Meenarl kuma yanzu haka ana kawota gida yasa suka fito farfajiyar gidan.
Kusan a tare suka firfito cikin motocin suna fitowa Meenarl ta zaro ido cikin tsananin mamaki da kad'uwa ido ta zaro woje cikin rikicewar tunani ta nufi gun Babanta cikin cikar mamaki baki na rawa tace.
"Babahhhhhh Babahh."
Sai ta kuma kalli Barrister Lawan ido zuru-zuru tace.
"Daddyyyyyhh."
Baki ta kuma bud'ewa cikin tsantsar farin ciki dan ganin Hajia Amina da Hajia Aysha Wanda suka fito yanzu don jin sautin jiniya a cikin gidan yaki k'arewa.
Cikin tsantsar farin ciki ta nufi Hajia Amina jiki na rawa ta fad'a jikinta cikin kad'uwa tace.
"Alhamdulillah Momy yau gani a gaban Ku."
Sai ta kuma saketa ta nufi jikin Ummin ta cikin dariya tace.
"Ummi bakya farin cikin ganina ne.?."
Ita kam Nafeesat tuni ta zama tamkar gunki tana sake da baki tana mamakin ina Meenarl tasan wad'an nan mutane?.
Ammi kuwa da Rayhana cikin kad'uwa da tsantsar Happy suka nufi gaban Meenarl d'in.
Ita kuwa Meenarl tana ganin Ammi ta saki Ummin ta cikin kaunar k'anwar mahaifin nata ta rugume Ammin baki na rawa tace.
"Ammi na ina Hamma Jabeer na Ammi ina yake ban ganshi ba."
Ita kam Ammi sai dariya take da hamdala shi kuwa Ramadan cikin had'a fuska da yanayin fushi yace.
"Bodd'in Bappa wato ni bakiyi kewa taba?."
tana jin muryan Yaya Ramadan d'in nata ta juya gunshi cikin murna da salon su na wasan d'an Goggo da y'ar kawu ta mik'a mishi hannu suka tafa tare da cewa.
"Kai Yaya Ramadan ai kasan Hamma Jabeer na shima yana sona."
Ita kuwa Rayhana ture baki tayi cikin kaunar k'anwar tata tace.
"Ai dama ni na sani Bodd'i ni da Hamma Sani baki wani damu da muba."
Da sauri ta saki hannun Ramadan ta rugume Rayhana cikin fara'a tace
"Anty Rayhana inason ku wallahi duk da bansan Hamma Sani ba ina son shi a raina."
Gaba d'aya haka suka cika da tsantsar farin ciki da murna.
Nafeesat kuwa ta bushe a tsaye.
Abdul kuwa Barrister Lawan yace a dakashi har sai ya fad'i wanda ta saceta tunda shi yace ba shi ya kawo ta garin Kaduna ba.
Cikin azaba da rad'ad'i Abdul yace.
"Wallahi ni ba satota nayi ba d'an uwanane ya satota shi ya kawota gidan mu san ina ya samota ba yace matarsa ce kuma wallahi zai kasheni in ban maidata gida ba kuyi hak'uri zan kirashi zai zo."
Cikin tsawa Captain Garba yace.
"Maza kirashi ."
Jiki na rawa ya zaro wayarsa dake cikin aljihun wonddon shi ya kira General,
Wanda a lokacin ya fito office nashi kenan zai koma cikin Kaduna,
kamar bazai amsa kiran ba sai kuma ya d'an zaro woyar a aljihun yinifon d'in nashi ,
ganin Abdul ne ke kiranshi ya d'an yi mamaki sai kuma ya d'aga kiran tare da cewa .
"Uhum."
Shi kuwa Abdul cikin kuka da tsoro yace.
"Hamma Aliyu zasu kasheni sun kamani sun k'wace Meenarl wai yarsu ce sun saceta Hamma Aliyu kazo karsu kasheni su kashe Meenarl."
Cikin tsananin fushi da hatsala yace.
"Kai banza kamin bayani su waye ne? kuma a ina suke? a ina suka samu Meenarl d'in? yanzu kuma ina? banza kayi min bayani."
Cikin tsoro yayiwa General bayani da kwotoncen gidan,
su kuwa Captain Garba tuni sun cika gidan da sojojin da y'an sanda,
suna shirin cin uban wannan Hamma Aliyun da Abdul ke kiran.
Shi kuwa General cikin zafi da fushi ya kalli yaranshi dake binshi a baya yace.
"Tafiya Kaduna zamuyi Ku fito da sauri."
Binshi a baya sukayi cikin gudu suka shishshiga motacin nasu sannan suka nufi cikin Kaduna .
Shi kam General gaba d'aya a hatsale yake hakan yasa ya gane kwotoncen Abdul amman sam bai tuno da cewar wannan gidan da akayi mashi kwotoncen d'in gidan su Captain Sani bane har suka shiga shiga cikin gidan.
Dai-dai lokacin Captain Sani kuma ya fito harabar gidan.
A dai-dai lokacin kuma General Aliyu Abubakar Rumoh ya bud'e motarsa cikin cikar haiba da sura ya fito,
Tsayuwar motar tasace taja hankalin mutanen wurin baki d'aya,
Ramadan da Rayhana kam wani irin farin ciki ne mara adadi ya rufesu yayin da Ammi kuwa tuni ta zuba mai ido fuska cike da k'ollah sai kirjinta dake harbawa.
Hajia Aysha kuwa mahaifiyar Meenarl Ummi kenan,
ganin Aliyu ya razanata ya cika mata zuciya da zulumi dan tunda yake zuwa basu tana kad'uwa ba,
Ido ta zuba mai tana kallon kwayar idanun shi dai-dai lokacin...
By
*Garkuwar Fulani*
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page
4β£1β£to4β£2β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*La shakkah Moh Allah wuju furd'ata wallahi Moh Allah seini b'uri sembe innu adamajo suna d'um*
Lokacin da ya fito ya tsaya fuska a murtuk'e,
shi kuwa Abdul yana ganin shi ya mik'e cikin wahala ya nufeshi tare da cewa.
"Hamma Aliyu zasu kasheni zasu tafi da Meenarl."
Alhaji Ibrahim kuwa ido ya zubawa Aliyu cikin mamaki tare da cewa.
"Kana nufin shine ya sacemin yar tawa?."
Shi kuwa Barrister Lawan cikin tsantsar hatsala ya kalli tarin sojojin dake gabansu yace.
"Maza Ku juya kuje ku canzawa wannan d'an banzan kamannin Ku sumar min dashi asume nakeso ku fita dashi daga cikin gidan nan."
Juyawa ya kuma yi a hatsale ya kalli Captain Sani da yake tsaye cikin kullewar kai da cushewar tunani ya zama tamkar wani soko,
ido yake bin Meenar da Rayhana yana zaro ido woje shi baima lura da oganshi da ke tsaye ba cikin murtuk'e fuska.
Tsawa Barrister ya buga mai cikin takaici yace.
"Kai Sani tsayuwa kayi yanzu nake so ku koyawa wancan hankali.
Su kuwa sauran zugar sojojin da yan sandan gaba d'aya cikin zafin nama da hatsala suka nufi inda General yake tsaye ya hard'e hannuyen shi a k'irji ya koma ya jingina da jikin motarsa tare da hard'e kafafunshi ya coge cikin isa.
Shi kam Abba shiru kawai yayi yana kallon yadda sojojin suka nufi General d'in da gudu,
shiko Barrister Lawan cikin fushi yake basu umurnin su bugeshi sai sun sumar dashi.
Suko sojojin da sukazo da General sun san duk masu nufo kansu d'in yaran General d'in.
Ita kuwa Ammi hannu tasa ta dafe k'irjin ta fuska cike da k'olloh gaba d'aya jikinta na rawa,
Shiko Ramadan wurin General d'in shima ya nufa Rayhana kuwa Ammi ta matso cikin rawar murya tace.
" Ammi kin ganshi ko kinga Hamma Haiydar d'in ko."
Itako Meenarl gaban Umminta ta koma tana kallon yadda Ummin ke juya kai tare da kad'uwa.
Gaba d'aya sojojin suna zuwa gaban shi suka yi wani irin tsayuwa a tare cikin mugun tsoro suka d'ad'd'aga hannu suka sara mashi tare da buga k'afafunsu a k'asa,
ji kake rib-rib suna "yes sir ".
Mamaki ne ya rufe Barrister ganin duk sunje suna saramishi sun k'ame k'am sun tsaya a gaban shi cikin yana yin suna jira ya basu umurni su aikata.
Shi kuwa Captain Sani da Captain Garba sai ido suka tsurawa juna cikin tsoro,
Barrister kuwa ganin Sani na tsaye gim yasashi hatsala cikin fushi ya juya gun Sani da Garba yace.
" wai shi waye shi da Ku sojoji bazaku aikin ku a kanshi ba ko shi yafi k'arfin doka shine fa ya sace Amina,
shiwaye a k'asarnan?."
Cikin yin k'asa da murya Garba yace.
"Shine Brgdl General Aliyu Abubakar Umar Rumoh soja mai kula da rund'unar sojojin na k'asa baki d'aya."
Tsaki Barrister yaja cikin takaici yace.
"Wannan mai halin sace yayan mutane shine wai aka bawa wakilcin tsaron wannan k'asa tamu?,
an bashi daman aikata b'arna son ranshi,
yaro ne aka d'auki wannan matsayi aka bashi ba dole ya maida mata abinda yaga dama ba,
tunda ya samu dama ga k'uruciya ga matsayi ga kud'i ga kyau ga rashin mafad'i dan wannan da ganin shi zaiyi taurin kai da izzah."
Shi kam Sani baki ya sake cikin mamaki da rashin ganewa yace.
"Daddy General me yayi muku?."
Cikin tsawa Barrister yace.
"Shine ya sace Amina yar