Showing 6001 words to 9000 words out of 74791 words
Chapter 3 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
mai komai ayyah ashe wanda ya haifeka zai gujeka,
ka rasa sonsu sai wani bare wanda baka saniba zai gwada ma qauna lokaci d'aya yaji qaunar tsohon na ratsashi cikin sanyi yace.
"Bappa maqqariba ta kawo kaifa."
Miqewa sukayi a tare Bappa na gaba suna binshi a baya shi kam General Aliyu da sannan mayafin na jikinshi suna fita a dai-dai qofar gidan suka riski masallaci daga d'an baya kad'an kuma makaran tar alloh ne babba sai qatuwar bishiyar maqqoro daga gabanta kuma wutsiyar dutsen membilan ne wanda daga samanshi ruwa ke kwaranyowa ruwan fari tas gefen dutsen ko garken shanayen Bappa ne bila'adadin da ka juyako tako wanne gefen shanaye ne konce an huhhura musu wuta a tsaka ninsu maganin sanyi da kaska can gefen kuwa lambune mai girma .
Cikin sha'awa Aliyu ya rinqa bin ko ina da kallo har suka shiga masallah cin,
suna idar da maqqariba suka zauna sukayi ta karatu har lokacin isha yayi sannan sukayi ishan bayan sun idar suka nufu cikin gidan
har yanzu dai Bappa ke musu jagora bayan sun shiga ne ya d'auki kaskon ya nufi cikin gida dashi.
D'akin Inna waziri ya nufa tare da yin slm ya shiga y'ar budurwan nan ya samu zaune a gefen gado cikin fillanci yace .
"Bodd'i ina Inna waziri?."
Cikin yanayin ta dayafi kama da sanyi da tsoron laifi tace .
"(Od'o kanderu)
tana kitchen."
Juyawa yayi tare da cewa
"toh zomuje mu kaiwa baqimu abinci."
Binshi tayi har zuwa cikin kitchen d'in nasu,
suka shiga Inna dake rufe akoshin dake gaban ta,
ta kallesu cikin farin cikin tace .
"Bodd'i zo ki d'auki wannan ki fara kaiwa ."
Miqa mata tayi sannan ta karb'i kaskon hannun bappan ta cikashi da rushi ta miqawa Bappa ya karba yana fita ya tarradda ita a bakin kitchen tana jiranshi.
A Jere suka shiga d'akin ajiye musu tayi sannan ta fita,
ta dauko wasu akoshin guda biyu shiko Bappa yana ajiye musu ya fita qofar gida gun d'alibanshi.
Tana dawowa a dai-dai bakin qofar tatsaya tare da yin slm
Sani ne ya amsa gami da cewa.
"ki shigo BANDIRAWO."
A hankali ta shiga ta duqa tare da ajiye musu har zata juya Sani yace.
"BANDIRAWO ke bakya magana ne? ko tsoron mu kikeji?."
Kai ta girgiza cikin sanyi tace.
"a a na gaidaku bakuji bane."
har ya bud'e baki zai kuma magana General ya d'aga mai hannu fuska a murtuqe .
Ganin haka yasa yaja bakinshi ya tsuke.
Itako cikin gida ta koma ta samu Innarta a dakinta tana cin abinci zama tai gefen ta cikin sanyi tace.
"Inna kinga baqinnane?."
Kai ta juya gamida cewa.
"a a Bappa yace yanzu sun gaji ga sanyin da basu saba ba ga dare yayi sai gobe zasu shigo mu gaisa."
Ajiyar zuciya ta sauqe gamida cewa.
"Ni dai tsoron su nakeji gwara ma d'ayan yana da fara'a shiga d'aya kamar mugune baya dariya sai murtuqe fuska."
Dariya tayi gani da cewa
" ke dai kin fiye tsoro."
Haka sukayi ta hira yayinda Bappa ko da yaran sa suke qofar gida .
Su Captain Sani kuwa tunda ya bud'e abinci yaga tuwon farar masane fari tas tare da miyar d'anyen kub'ewa da naman rago ga man shanu da kitse sai qamshi yake d'aya akoshin kuma gasheshshen naman zabbine da yake ta nason mai sai d'aya kuma mai damemmen kunun nono.
Cikin shaqar qamshin yace
"oga wlh abincin nan zaiyi dad'i kar kace bazaka ciba."
Fuska ya d'an tab'e sannan yace .
"Kai dai kaci ni kam banjin kamar zan iyaci."
Dai-dai lokacin Bappa kuma ya shigo cikin fillanci yace.
"Toh bari a kawo ma tea in shi kafi so ga naman nan sai kaci kafin zuwa safe ama abin da kake son."
A dole Bappa ya kawo mai tea din tare da tura mai akoshin naman gaban shi,
cikin sanyi ya d'an kurb'i tea d'in lokaci d'aya kuma ya lumshe ido dan yadda yaji wani irin d'and'ano ga qamshin citta da kanam fari,
naman ya d'an yaga yasa a baki ido ya lumshe tare da cewa.
"Toh Bappa muci tare mana."
Cikin lokaci d'aya Bappa ya sake dasu sukaci abinci suna hira dukda shi Aliyu sai dai ya d'an zuba musu ido ananne Sani yake bawa Bappa labirin wani aiki sukaxo yi kuma ance mutanen rigar da za suyi aikin duk sun qaura daga nan kuma basu mishi wani bayani ba shi kuwa bai musu shishshigin tabbayan su ba,
a nan d'akin suka kwana Aliyu na kan babbar katifar shiko Sani ya shimfid'a d'ayar,
sukayi baccin su cikin blankets masu taushi.
Washe gari bayan sun idar da sallah Asuba suka zauna suka karanta Azkar har gari ya d'anyi haske sannan suka fito cikin girmamawa suka gaida Bappa wanda shiko ya amsa tare da nufar garken shanu,
gamida ce musu.
"Muje ku tayani tatsar nono."
Shi dai Aliyu ya bashi ne kawai dan zumud'in da Sani keyi.
Suna shiga cikin taron shana yen da raquma da tumaki daga can bayan Aliyu kad'an yaji alamun ana tatsar nono cikin qoriya caar caar,
cikin sanyi ya d'an juyo dan ganin wake wannan aikin cikin mamaki ya d'an.......
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 5⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writers
*dedicated 2 Ummu amhumy tare da Billy A A & baiwar Allah amnoor*
Ya d'an kalleta a fakaice ganin yadda take tatsar cikin iyawa da qorewa idonta a qasa kamar wacce ta lumshe su yayinda ta kauda kanta gefe kamar mai gudun kar ta shiqi qamshi nono kanshi ya kawar tare da matsowa gefen Bappa cikin yanayin shi na tsuke fuska ya dan shafa kanshi tare da cewa.
"Bappa yanzu nake son zamu wuce dan tafiyar dake gaban mu tana da nisa."
Matsoshi Bappan yayi tare da miqa mai madarar da ya tatso yanzu sai tururi take yace.
"Gashi kasha maganin sanyi."
Kai ya d'an juya a hankali yace.
"kai Bappa da sanyin safiyar nan mutun ya kama d'ura nono a cikinsa."
Murmushi yayi tare da miqa mai har bakinshi ganin shirin bashi yake a baki, yasa hannu ya karb'a tare da d'an sha,
lokaci d'aya ya d'anji sanyi ya sake sa,
sannan ya miqawa Sani sauran shima ya sha,
Haka sukai ta d'an zagawa cikin garken bayan d'an wani lokaci Bappan ya miqe tare da cewa.
"Bodd'i zomu je cikin rafi da aiki a ciki."
Sannan ya kalli Aliyu cikin kula yace.
" (Surbajo war en yaha) Saurayi zomuje."
Shi kam Aliyu ido ya zubawa Sani ganin azarb'ab'in shi tuni shi har yayi gaba ganin haka yasa ya bi bayan su ta gefen dutsen da suka ratsa
A hankali yarinyar da ake kira da Badd'i ta bi bayan shi suna tafe har suka isa cikin lambun.
A hankali General ya lumshe ido tare da hard'e hanna yenshi a qirjin shi sannan ya rinqa d'an zagawa cikin lambun yana mai mamaki ganin irin ni'imomin da Allah yayiwa ma zauna wannan wurin komai mai sanyi Allah ya basu ba abinda babu a cikin lambun na y'ay'an itatuwa hatta tupa da inabi akwai su kad'an a ciki bar pia kam ayaba lemu goiba abarba kakana maggoro dibino kashu,
gefe d'aya kuma rekene iya ganin mutun.
yana cikin shaqar qamshin da wurin ke fiddawa yaji Bappa na cewa .
"Bodd'i kicire wanda bai qarisa nunan ba sabida su Surbajo zasu tafi dashi kinga kar ya logob'e a hanya da zafin mota."
Gunta ya juyo d'an shi yarinyar Sam mamaki take bashi ita bata mgn sai iya barna da jiqa mutane da nono.
Itako bata ma san yanayi ba dan ko inda yake bata dubawa aikinta take cikin sanyinta banana take yanka manya-manya sai kuma ta koma gefen pia tai ta sinko manya sannan ta juya gun Inabi da tupa suma ta had'a saida ta cika kondon kabar guda biyu manya da fruits sannan tazo ta ratsa gefen shi cikin sanyi ta matso Bappa a hankali take magana shi dai ba jin me take fad'iba,
Amman dai ya lura cikin shogoba take magana abinda shiko ya tsana a rayuwar sa ko dan bai tashi da hakan bane.
Kai ya kawar ganin yadda Bappa ke mata magana cikin kulawa harda kama hannu ta yana hura mata iska ko tofi yake mata ne ma oho musu .
Daga nan kuma ita ta fara fita ta nufi gida shiko Bappa ya kira Sani dake ta cin banana kamar biri yace .
"Sani d'auki wannan kondon mu tafi" shiko ya d'auki d'ayan sannan ya kalli Aliyu yace kai kuma d'auki nonunan ayaban nan mu tafi gida."
Toh kawai yace sannan ya d'auka suka kama hanya.
Bayan sun fito ne yaga kab ba shanayen sai y'an qananan da aka bari dan bazasu iya nisan kiwo ba wurin yayi shal sai korayen tsirrei dake zagaye dasu.
Kai tsaye cikin gida suka shiga Bappa na gaba suna baya har qarqashin bishiyar ced'iya dake tsakar gidan,
Inna na ganin su ta shiga d'aki tare da d'auki taburma ta zo ta shimfi d'a musu sannan ta zauna kan kujerar tsuguno dake gefen wurin, Bappa ne zauna tare da kallon Aliyu da ke zaune gefenshi cikin murmushi yace.
" Inna Waziri ga jikanki mai irin halin Sayyadi naki!"
A hankali ta juyo ta tsura mai ido cikin sanyi tace .
"Surbajo me sunan ka?."
Kanshi a qasa yace.
"Aliyu "
Ajiyar zuciya ta sauqe tare da yin murmushi tace .
*"Aliyu Haiydar* babu rego ko gafalelle Haiydar Jan zaki gadanga kusar yaqi ."
Jin kala manta yasa ya d'ago kanshi ya kalleta lokaci d'aya kuma suka had'a ido da ita sai kuma yayi mamakin ganin hawaye na bin fuskar ta .
Sai kuma yaji abun bai mai dad'i ba sai ya rinqa juya mata kai a hankali tare da cewa.
"Kiyi haquri "
Duk da baisan damuwar taba yaji yana tausaya mata itako sanyi taji da ban haquri shi.
Bappa kam sai murmushi yake tare da binsu da ido a filiko yace.
"Inna Waziri baki kawowa jikokin naki abinci ba gashi sunce yanzu zasu tafi."
Miqewa tayi tare da shiga kitchen ta fiffito musu da abin kari ta jera musu kan taburmar shiko Bappa ya bud'e musa sannan ya biqa musu ruwa a qoryar suka wonke Hanna yensu,
tare suka ci abinncin da Bappa yana mai kallon su cikin qauna.
Bayan sun gama sukaje sukayi wonka suka shirya tsab Sani yasa musu kayansu a mota ga kondunan fruits har 3 ga qoren gon zabbi har 2 ga jara kunan man shanu guda 3 tare da jarakunan nono 2 sannan ya had'asu da qoryan zuma yar asali har guda biyu.
sannan suka shiga cikin gida sukawa Inna sai wata rana har zasu fita suka tsaya cak jin muryar wata tsohuwa cikin matsifa tace.
"Kai Bappa wato har zakayi baqi har su gama zaman su,
ni bazaka ce suzo su gaida ni ba,
Ku kuma baqin muna furci ko Baku San darajan manya ba!
ke kuma muna fuka harda kukan gulma toh wlh ki shirya yaune zakiyi kuka mai dalili Yau zaki mai mata kukan da kikayi shekaru 40 da suka wuce!
Ku kuwa baqi yau zaku san kun shigo inda ba'a fita dan kun tari kan bala'i da kukazo nan garin!
ke kuma Bodd'i ko? Yau kyawun naki zai zama ganimar wasu gara dai!."
Cikin mamaki Aliyu da Sani suka juya suna kallon Bappa da inna wacce tuni take zubda qollah murya na rawa take cewa.
"Dan Allah Lari karki cutarmin da Bodd'i,
Lari kibar baqin nan karki sasu cikin mugun furuci !"
Ido suka tsurawa Bappa cikin tuhuma da neman qarin bayani,
shiko Bappa hannun su ya kamo har zuwa bakin motarsu
cikin sanyi yace.
"Aliyu kar ku tsaya neman qarin bayani ba lokaci ku tafi kawai kar masifan bakin Lari ya shafeku ."
Cikin jin haushi ganin gaba d'aya yadda suka rud'e da kalaman matar ya kalli Bappa yace.
"Bappa wacce ita? kuma me had'inku da ita? me kuma zata yi muku?!"
Hannushi ya kuma ja cikin murmushi qarfin hali yace.
"Aliyu kubar wannan yanki Ku hamzarta kar lokaci ya kure muku."
Ganin bazai basu amsa ba yasa suka juya zasu shiga ,
Sosai Aliyu yai mamaki ganin irin kaya da Bappa ya had'a musu ,
Matsoshi yayi cikin sanyi yace.
"Bappa wannan kaya ai sunyi yawa".
kai ya gyada mai tare da cewa .
" a a Ali bayyi yawaba kai dai kuje sai wata rana."
"Toh mun gode" yace tare da juyawa har zai shiga mota sai kuma ya juyo da sauri cikin mamaki jin hayaniyar shanaye da raquma da suke ta shigowa cikin rigar a guje ma kiyayan na binsu a baya tako wacce kusurwa shigowa suke.
Ganin wannan Gainako da ya kawosu rugar ya nufi Bappa a guje yasa shima ya dawo gaban Bappa .
Shi ko Bappa ido kawai ya rumtse tare da cewa.
"Gainako yau kuma rigarmu zasu shigo ko ? yau ma Bodd'i suke son d'aukewa ko?."
Sai hawaye shar a idonshi shiko Gainako sai haki yakeyi cikin d'auki war numshi da haki yace.
"Bappa sunce in muna son kanmu da lafiyar mu a kai musu Bodd'i!
inko muka bari suka shigo wlh zasu kashemu su qona rigarmu kamar yadda sukayiwa rigar Rumoh."
Kafin yayi magana sai ga mutanen rigar duk sun hallara qofar gidan a gaban su wasu dottijai guda 3 suka kalli Bappa cikin tausaya wa sukace.
"Bappa ka samu Ku fita ta qofar baya kaida Bodd'i dan tabbas ita suke hari."
Cikin tsoro wani matashin da ya iso yanzu yace.
"Wlh suna nan a qofar bayan ma sunce nanda azahar a fito musu da ita da kuma dabbobinmu."
Shi kam Aliyu so yake sumai bayani suko sun k'asa sai b'ari suke.
Bappa ko jin haka yasa ya matso jikin Aliyu hannushi ya riqe cikin rawan murya da neman
alfarma yace.
"Aliyu taima konka nake nema zaka taima ka min?."
Cikin kaushin murya yace .
"Bappa ka gaya min meke faruwa?,
ai taima ko shine aikina kodako zan rasa raina sabida nai alqawatin taima ko kafin na fara wannan aiki nawa Bappa aini raina da lafiyata kan taimakon qasata yake ka gaya min suwaye ke son kasheku?."
Kai ya rinqa juyawa cikin sanyi ya koma cikin gida ,
Jim kad'an ya fito riqe da qura'ani mai girma cikin sauri ya miqa mai tare da cewa.
"Aliyu kayi alqawari tsaka ninka da Allah zaka taimaka min zaka kuma riqe amana?."
Ranshi cike da jarum ta yace.
"Nayi alqawari zan taima ka maka kuma zan riqe amana bazan kuma k'asa taima ka maba."
Cikin jin dad'i yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli mutanen wurin tare da riqe hannun Sani.
" yace Sani Kaine shaidan Aliyu a garinku in kun koma."
Ya kuma juya ya kalli taron mutanen wurin cikin d'aga murya yace.
"Ku kuwa kune shaida na da alqawarin Aliyu."
Kusan a tare su kace
"Ehh".
Murmushi qarfin hali yayi sannan yace.
" Aliyu na baka auren Amina Bodd'i bisa alqawarin da kayi min!
Kuma yanzu za'a d'aura auren!
yanzu kuma zaku tafi da ita!"
Shi kam Aliyu ido ya zaro woje tare da bud'e baki zayyi magana .
Da Sauri
Sani yace.
"Alqawari kayi oga kuma tsaka ninka da ubangiji kai wannan alqawarin."
Yana rufe baki ya juya ya zaro kud'i masu yawa a cikin moto sannan ya d'auki kondon dibino d'aya cikin sauri ya dawo gaban Aliyu daya murtuqe fuska kamar zayyi ruwan jini.
Kud'in ya miqawa Bappa tare da cewa.
"Ga sadakin ta dubu 50 sannan ga dibino kawai yanzu a d'aura Aure,
shi oga namiji ne ya halatta ya karbawa kanshi Aure." .....
Gaddara ta rigayi fata General Aliyu yanaji yana ganin wata gaddarar rayuwa ta auka mai Wanda dole girman alqawari da bakinshi ya karbawa kanshi Auren Amina.
Ana gama daurin Aureb tare da shaidun mutanen rigar Bappa ya shiga cikin gida,
cikin sanyi da tausayawa kanshi da matarshi da Bodd'i ya kalli Inna ba tare da wani baya niba ya kamo hannun Bodd'i tare cewa Inna.
"Kiyi haquri wannan shine mafita kuma wannan itace sabuwar gaddararmu."
Itako Bodd'i sai binshi tai yana riqe da hannuta.
Gaban Aliyu ya tsaya da ita tare da miqa mishi hannuta cikin sanyi yace.
"Aliyu ga matar ka!
Bodd'i kekuma kibi mijin ki!"
Ita kam bata fahimci komai ba a zancen nasu sai dai ta fahimci tafiya zaiyi da ita shiyasa sai hawaye ke bin fuskar ta.
Shi kuwa kamar makaho Bappa ya jashi har cikin mata Sannan Sani ya shiga suka tafi .
Suna fita cikin rugar ta gefen dutsen Membila sai ga motocinsu da suka bari cikin Membila cikin mamaki Aliyu ya kalli captain Sani da neman qarin bayani duk da dai ya gane Sanin ne ya kira su dan suzo su bawa mutanen rugar kariya.
hakan ko yace mai .
"Oga nina kirasu."
Kai ya gyad'a sannan yace .
"Toh motoci 4 su isa wanda sojoji kusan 28 a cikin sannan yace .
mota d'ayar kuma ta juyo su koma tare.
Haka kuwa Akyi matoci 4 suka nufi cikin rugar,
suko su Aliyu sunka nufi Hanyar Gembu
domain zuwa Yola..
A cikin motar kuwa Bodd'i ta.....
By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writers
*Wannan shafi nakune ku kad'ai Sisters In Islam Mmn jhadijah tare da Y'ar mutan wudil sa'a tafi manyan kaya nis@ online writers & Hurairayabo and Feedoh*
Dungu lewa tai wuri d'aya tana mai wani irin kuka mai sanyi da tausayi dan,
gani take shike nan an rabata da tushenta gatan ta ji take kamar an rabata da farin cikin ta,
a ranta take tuna meyasa Bappa baiyi tunanin komai ba ya had'ata da wannan mutumin mai fuskar mugaye,
cikin jin zafin zazzabin da yake shirin rufeta ta d'an bud'e idonta tana mai kallon tsaunu kan da tsirren da suke ketawa yayin da suke bawa rugar tasu baya a take ta saki wani kuka mai cin rai tare da qamqame jikin ta,
ta takure can gefe jikin motar.
Shi kuwa Aliyu ido kawai ya rumtse cikin wani irin zafi da ranshi ke mishi ,
tunani yake shi da yazo neman mafita da samun sauqi sai gashi wani baqin shafi ya shiga cikin littafin qaddarar rayuwar sa,
shin ina zai Ajiye wannan yarinyar da wani matsayi zai nunata ga Mahaifin shi? da yayan mahaifin nashi ?
shin da wace fuska zai nunata ga sauran abokan aikin shi ?,
kai ya kuma juyawa da qara rumtse idon shi tuno Mama da yayi ko me zatace kan wannan batun ! wanne sherri kuma zata bishi dashi !,
shi a wanne yanayin yazo duniya da ya kasance ba mai ji bantan lamuran shi .
Haka yai ta tubka da warwara,
yayin da shiko Sani driving kawai yake,
zuciya yarsa cike da farin ciki ko ba komai yasan insha Allah nan bada jimawa ba Ogan shi zai samu sauyi a