Showing 57001 words to 60000 words out of 74791 words
Chapter 20 - Bandirawo Book One Complete Hausa Novel
dashi kan katifar Bappa Ramadan ya d'ebo magungunan shi zai bashi .
Cikin fahimta Bappa ya matse matar tashi kai ya juya cikin sanyi yace.
"Ramadan ciwon Aliyu bana asibiti bane wannan ciwon kura'ani ne da add'a maganin shi."
K'ara damk'o wurin Bappa yayi tare da matsewa da k'arfi.
cikin wani irin.....
*Allah Yau da k'er nayi typing d'inga*
By
*GARKUWAR FULANI*
πππππππππ
*BANDIRAWO*
page
4β£8β£
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
πππππππππ
*Fulb'e BANDIRAB'E am mi hofni on*
Zafin da sanyin zazzab'i General ya k'ara dunk'ulewa tare da kamo hannun Bappa ya rik'e murya na rawa yace.
"Bappa marata zata tsinke! sanyi zai kasheni! Bappa kaina kamar zai fashe!."
Cikin tausayawa Bappa ya shafa kanshi tare da girgiza mishi kai yace.
"Insha Allah yanzu zaka rebu da wannan ciwon In Allah ya yarda zaka samu waraka a jinyarka da zanyi maka yanzu."
Kai Bappa ya d'ago ya kalli Ramadan cikin shak'uwar dake tsaka ninsu da yaron yace.
"Ramadan tashi kaje cikin gida,
kace Inna Waziri ta baka zam-zam da ganyen magariya sannan ta baka da farar zumanan ta had'oma da ruwan d'umi."
Cikin sauri Ramadan ya mik'e tare da cewa.
" toh."
Yana shiga cikin gidan d'akin Inna ya shiga cikin sauri ya shaida mata aiken Bappa.
Rayhana najin haka ta mik'e tare da cewa.
"Jikin Hamma Haiydar ko? ."
Kai kawai ya gyad'a mata tare da karb'an goron zam-zam din da sauran abubuwan ita kuwa Rayhana ta karb'i akoshin zuman,
sanan Innan ta kallesu cikin kulawa tace.
"Ku kai da sauri bari in d'ebo ruwan d'umin zan kawo."
"Toh kiyi sauri Inna." Rayhana ta fad'a lokacin d suke fito tsakiyar gidan.
Ita kuma Inna ta nufi kitchen d'in su har zasu fita,
suka d'an tsaya cikin had'e fuska Ramadan ya kalli Lari kishiyar Innan dake musu tsaki tare da cewa.
"Muna fukai kunzo ko kai wannan yaron na tsani ganin fuskar ka."
A hatsale Ramadan yace.
"Wallahi ki rik'e mugayen furucin ki ni ba Inna da Bappa bane wallahi sab'a miki zanyi in kin saba fad'in mugun zance toh ki kiyayeni ina gab da casaki banza kawai mai bak'in baki."
Shiru tayi d'an har ga Allah tana shayin Ramadan da kuma jin tsanarsa dan fuskar sa na tuna mata 'ya'yan Inna da tayiwa mugun baki suka watse suka bar garin."
Ita kuwa Inna cikin sanyin ta tace.
"Ramadan ku tafi kuje Bappa na jiran Ku."
Juyawa sukayi suka tafi,
ita kuwa ta shiga kitchen d'in ta d'ebo ruwan d'umin ta bisu a baya.
Suna shiga d'akin Bappan ,
Ramadan ya mik'a mishi goran zam-zam d'in tare da y'ar k'aramar k'oriya tare da k'anyen magariyar ,
karb'a yayi da sauri ya tsiyayi zam-zam d'in cikin k'oriyar sannan ya d'auko ganyen magariyar k'waya bakwai sannan ya zauna dirsham tare da tonk'oshe k'afafun shin cikin nitsuwa da cikar tajwidi tare da tauhidi ya fara karanto addu'oi irin su,
Ayatulkirsiyu Qulhuwa Falak'i Nasi amanarrasulu tare da had'e yatul shifa baki d'aya yana tofi a cikin ruwan zam-zam d'in .
Sannan ya kalli General d'in dake rawan sanyi kar-kar har hak'oranshi na bugan juna yasa hannu ya damk'e cikin shi.
Cikin sanyi Bappa ya juya gefen Ramadan dake ta gyara rufewa General jiki da blanket cikin tausayin su yace.
"Ramadan taima ka mishi ya zauna yasha ruwan zam-zam d'in nan."
"Toh" yace tare da yunk'urowa ya tallab'o Aliyu cikin dauriya General d'in ya zauna tare da cewa.
"Zan iya fa ba sai an d'agani ba."
Mik'a mishi y'ar k'oriyar Bappa yayi tare da cewa.
"Kasha tare da bisimillah."
Kai ya gyad'a yayi bisimillah sannan ya k'afa kai ya shanye kab.
Yana ajiye k'oriyar a hankali ya fara yin gyatsa yana mai rik'e cikin sa sai gyatsan yakeyi ba k'ak'k'au tawa tuni ya rink'a jin bugun zuciyar shi ya tsanan ta sai tsinke wan zuciya a hankali rawan jikin shi ya k'aru amman kuma ya kasa konciya sai cikin shi d'aya damk'e da k'arfi yana wani irin mik'a cikin juya kai ya damk'e hannun Bappa da hannu shi d'aya yace.
"Bappa cikina marata zata fashe Bappa kaina na juyawa,
Bappa cikina."
Inna da yanzu ta shigo cikin mamakin ganin Aliyu ta matsoshi tare da cewa.
"Aliyu gadanga k'usar yak'i kaine,
Aliyu ina Bodd'i na ina take?."
Kai ya murza cikin zafi yace.
"Inna Bodd'i tana wurin iyayen ta Inna ga Ramadan shine shaida na bar Bodd'i gaban iyayen ta na barta cikin lafiya na meda amanar da Bappa ya bani."
Fuska a karye Bappa yace.
"Habba Inna waziri ki barshi mana yaji da ciwon shi yanzu ki had'a min zuman nan da ruwan d'umin ki bani in bashi.",
Cikin sauri ta had'e farin zuman a cikin ruwan d'umin sana ta d'an sa zam-zam ta jujjuya cikin kula ta mik'awa General tare da cewa karb'i kasha."
Gaba d'aya jikin shi rawa yake ya k'asa karb'a sai Ramadan ne ya karb'a ya saka mishi a baki.
shi kuma yayi bisimillah sannan ya shanye.
Ajiye k'oriyar Ramadan yayi tare da tsura mishi idanun jin yadda yake sauk'e ajiyan zuciya a kai akai sai zufa a take tuni ya rink'a atishawa a jere har sau 7 sanna ya rink'a fad'in .
"Alhamhadullih."
Rayhana kam sai mumurshi takeyi tana kallon yadda lokacin d'aya jikin shi ya bar b'ari shiko Ramadan da Bappa suma ,
hamdalan sukayi ,
Inna kuwa sai mik'a mishi zuman tayi zallan farar Zuma wanda tana cikin sak'arta ma tace.
"Karb'i ka rink'a lasa."
Ido ya tsura mata ita da Bappa sannan yasa hannu shi kan mararshi da dazun nan yake da tauri kamar dutse sai gashi yanzu-yanzu wurin yayi normal.
Karb'a yayi yasa yatsarshi tare da laso zuman,
murmushi yayi ciki sanyi yace.
"Ramadan daga Yau kai ba Dr bane,
Bappa ne babban doctor mu kaji wallahi gaba d'aya yanzu ba abinda ke min ciwo Alhamhadullih yau naji sauk'i."
Dariya Ramadan yayi tare da cewa.
"Alhamhadullih B'iyaye na."
Kamar wasa rahanar ubangiji yawane da ita tuni General yaji shi garau,
Inna da Rayhana suka shiga cikin gida suka kawo musu abinci,
Bappa kam tasa Aliyu yayi a gaba kamar yaro sai da ya bashi abinci yaci cikin kulawa shiko General yaji dad'in abincin dan yasha man shanu,
Inna kuwa ruwan Lipton ta had'a mishi ta bashi,
gaba d'aya suna zaune a d'akin Bappan,
cikin tura baki Ramadan yace.
"Wallahi na lura yanzu Hamma Haiydar kawai kuke so ni kun wani shareni."
Dariya sukayi gaba d'ayansu shiko General Murmushi yayi cikin k'aunar d'an uwan nashi cikin murmushi ya d'an bugi kafad'an shi yana.
"Ai kai d'an gatan Ammi ne ni ba masu sona sai Bappa da Inna ."
Haka sukaci abinci suna raha.
Bayan sun nitsu ne a daren Ramadan ya kalli Bappa cikin nitsuwa ya bashi labarin abinda ya faru baki d'aya.
Sannan yaci gaba da cewa.
"Bappa meyasa lokacin da ka had'a auren Bodd'i da Hamma Haiydar ba kayi tunanin wani abu zai iya faruwa ba? Bappa baka ji tsoron Habba Aliyu ba?."
Shiru Bappa yayi tare da komawa ya zauna ya jingina jikin gini
yanata tunani a hankali yace.
" kusan tun bayan tafiyan Bodd'i kullum cikin tunani nake
Harga Allah nayi iya tunani na dazaiyi akan masu son cutar da ita dan na kareta amma babu mafita sai yadda nayin, koda ace nayiwa ALIYU kwatancan mahaifin ta dan ya kaita badole bane yazama inya kaita yakaita lafiya ba dan komi na iya faruwa kasancewar Bodd'i mace ce wacca ta amsa mace, gashi kuma ALIYU namiji kuma shed'an yana iya samishi wani abu tunda shima mutum ne babu Wanda ya wuce jarabawar ubangiji."
Ajiyan zuciya ya sauk'e tare daci gaba da cewa.
"Aura mishi ita danayi itace mafita dan koba komi ina yiwa yaron kyakkyawan zato, hakan yasa komi yazo cikin sauki, aure darajane dashi mai girma wanda insha Allah adalilin auren zata iya gamuwa da mahaifinta,
Sannan kuma ni nasan Bodd'i yarinyace mai biyayya nasan zata yiwa Aliyu biyeyyah zata kuma yi hak'uri zama dashi na kuwa san Bodd'i bata da musu ko gardama,
adalilin haka ina sakaran sake haduwa da ita cikin farin ciki da zuriyya dayyiba,
tun a lokacin kuma na lura da Aliyu yana cikin damuwa a rayuwar sa duk da bai gaya min ba amman na lura yana buk'atar mai shiga rayuwarsa dan tausaya mishi."
Shiru yayi tare da kamo hannu General yaci gaba da cewa.
"Aliyu sana din had'a ka da Bodd'i da nayi ya jazama matsaloli ,
sannan kuma yayi sana d'in had'uwar ka da mahaifiyar ka da k'annen ka,
sai rashin fahimta dake tsananin yayun mahaifiyar ku da mahaifin ku,
Ni kuwa Insha Allah gobe goben nan zamu wuce tare daku da Inna waziri zanje Insha Allah za dai-dai ta tsakanin su Ammin ku zata koma gidan Abban ku."
Shiru Inna tayi tare da cewa .
"Tabbas su Alhaji Ibrahim basu kyauta ba ai ko dan rik'e musu yarsu da kayi da a mana da zusu bar maka ita a matsayin matar ka kuma tunda shi Sani ya gaya musu Bappa ya d'aura muku Aure ko mu bamu isa da ita bane?."
Cikin sanyi Bappa yace.
"Batun auren su kuwa wannan hurumin bana kowa bane tunda aurene akayi a kan Aure kuma wannan matsalar a kawai maslahar ta cikin addinin mu na musulunci dan addininmi bai regemu da duhun komai ba."
Cikin sanyi General yace.
"Bappa me yasa Baku gayawa iyayen Bodd'i aura min ita kumayi ba?."
Kai ya jinji na cikin nadaman abin yace.
"Wannan shine kuskuren da nayi dana yarda nabi shawarar mahaifiyar Bodd'i ita kuwa tace a fad'i hakan ne dan tana ga kar mijin ta yaga banyiwa yarshi adalci ba ko na aurar da ita ga wanda ban sani ba,
amman ni nasan nayi kuskure ka gafar ceni."
Kai ya juya tare da cewa.
"Bappa baka yimin komai ba,
kuma Insha Allah gobe iwar haka muna jihar Kaduna."
Haka suka kwana cikin tsantsar farin ciki, da k'aunar juna.
washe gari da sassafe suka kama hanyar Kaduna,
tafiya kuwa tayi kyau General ke jan motar sai Ramadan a gefen shi Bappa da Inna da Rayhana kuwa suna baya.
11:00 pm dai-dai General ya kutsa hancin motarsu cikin Jaji yayinda gaba d'aya sun cika da gajiya,
bayan sun shiga Ramadan ya jido musu ledodin kayan cima da General ya lodo musu,
ya kawo musu Inna da Rayhana d'aki d'aya suka shiga suna shiga ko ruwan basu shaba suka konta idanun cike da bacci jiki dauke da gajiya.
Ramadan ma tuni ya b'ingire yana bacci Bappa kuwa saida yayi nafilfilinshi sannan ya konta.
Shi kuwa General wonka yaje yayi sannan yazo ya konta tare da k'ura'ani a hannu shi karatu ya rink'a yi cikin sanyin saiti,
jin bacci na fin k'arfinshi yasa yarufe karatun tare ajiye kura'anin,
sannan ya koma ya konta,
cikin hamdala ya matse mararshi tare da cewa.
"Alhamhadullih yau gani lafiya ta lau ba ciwo har na manta na tab'a ciwon ma."
Ido ya rumtse da k'arfi tare da matse cinyoyin sa cikin ranshi yace.
"Allah ka yaye min wannan raunin shawa'an da ke damuna dan tabbas yaji sauk'i amman kuzarin shi da saura.
Haka yayi ta Addu'a.
Washe gari bayan sunyi wonka Rayhana tayi musu girke-girke sukaci suka sha sannan suka nufi cikin kaduna.
Abba kuwa shima da Daddy bayan sun gaba shawarwarin su ,
Captain Sani ya dauke su ya nufi gidan Alhaji Ibrahim dasu.
Shima General kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim d'in ya nufa dasu dan a cewarsa lokacin da yaje ya jajubo maganar auren Abban shi bai sanina haka kuwa zai warware abin ba tare da sanin Abba .
Motarsu General nayin Parking sai ga Motarsu.....
By
*Garkuwar Fulani*
πππππππππ
*BANDIRAWO* page
4β£9β£to5β£0β£
*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*
πππππππππ
*Wannan shafi d'uggu ruggum d'in shi nakine ke kad'ai Khaleesat Haiydar Allah bar zumunci da k'aunah ina al'fahari dake, MI YID'I MASIN KHALEESAT*
Dr Jabeer shima yayi parking,
Ido Aliyu ya tsurawa motar Dr Jabeer d'in cikin takaici,
Meenarl ya haggo zaune a gefen Jabeer daga dukkan alamu tare suka fita kuma yanzu sunka dawo tsaki ya jaa cikin murtuk'e fuska yayi shiru yana matse siteri,
Bappa kuwa da Inna da Rayhana shiru sukayi dan basu san me yasa shi jan tsaki ba kuma ya tsuke fuska ya k'i ya bud'e musu motar,
Shiko Ramadan shima kallon motarsu Meenarl d'in yake tare da son fitowa dan sauri yake yayiwa Meenarl albishir da zuwan su Bappa.
Ita kuwa Meenarl shiru tayi tana kallon Hamma Jabeer d'in nata da ya rik'o hannun ta yana murza yan yatsunta cikin wani salon ya k'ara juyowa gareta suna fuskar tar juna cikin sanyi yace.
"Bodd'i na ina sonki inason kasan cewa tare da ke inason farin cikin ki,
me yasa kike k'untatawa kanki akan Aliyu ai da ya damu dake yadda kika damu dashi da bazai iya korarki ba,
Bodd'i nifa d'an uwan kine na jini ki dawo da zuciyar ki gareni zan soki zan kula dake zan riritaki."
Shiru tayi fuskar ta na cike da k'ollah tace.
"Hamma Jabeer,
Ni ina tausayawa Hamma Haiydar bashi da lafiya kullum dere baya bacci kuma ba mai taimaka mishi sai ni."
Sai hawaye shar-shar a fuskarta tana juya kai.
Shiru Dr Jabeer yayi zuciyar shi cike da k'aunar ta yasa hannu ya tallabe hab'arta k'ara matsota yayi tare dasa hannun shi ya share mata k'ollah.
Shi kuwa General da k'arfi ya rumtse idanun shi cikin k'ara matse siterin yana mai juya kai.
Ganin haka yasa Ramadan dannan pin d'in bud'e motar sannan ya bud'e ya fito tare da bud'e wa su Bappa da Inna suma suka fito,
shima kainshi a sunkuye ya bud'e ya fito cikin tsuke fuska.
Suna fitowa ,
Meenarl ta wore ido cikin tsananin mamaki da farin ciki cikin sauri ta fito tare da yin gudu tana zuwa ta rugume Inna cikin kewar juna Inna ta rugumeta Bappa kam sai murmushi.
Ita kuwa Meenarl sai hawayen farin ciki,
sai ta kuma sake Innar tayi cikin gida da gudu tana.
"Ummi! Ummi ina kike ? Ummi ga Bappa na da Inna ya Ramadan ya kawo minsu."
Su kuwa bin bayan ta sukayi suna dariya a babban parlour suka tarar da mutanen gidan baki d'aya,
cikin farin ciki da k'aunar juna suka gaggaisa.
Shiru Bappa yayi ganin Aliyu bai shigo ba cikin kula ya kalli Ramadan dake gefen Ammin su yace.
"Kai Ramadan ina Aliyu ."
"Yana woje yace shi bazai shigoba tunda masu gidan basa so."
Cikin girma Bappa yace.
"Shima ai nan gidan sune."
Sai kuma ya mik'e ya fita yana zuwa kai hannun shi ya kamo yayi cikin gida dashi suna shiga parlour.
Ammi da ta zubawa k'ofar shigan ido tana ganin shi ta rink'a sauk'e ajiyar zuciya tare da tsura mishi ida wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata cikin rawan murya tace.
"Haiydar."
Shi kuwa General Kanshi a sunkuye yabi Bappa dake rik'e da hannu shi ,
gaban Ammin yaje ya ajiye shi sannan ya zauna gefen shi cikin kula yace.
"Aliyu ga mahaifiyar ka gata a kusa da kai gata a gaban ka."
Shiru Aliyu yayi tare da tsurawa yatsun k'afafun ta idanu lokacin d'aya yaji wani irin karayan zuciya gaba d'aya sai yaji zuciyar shi ta raunata.
Ita kuwa Ammi hannu tasa ta jawo kanshi ta d'aura kan cinyarta yayinda kan Ramadan yake kan d'aya cinyar Rayhana kuwa ta rakub'e a jikinta,
cikin sanyi ta d'aura hannun ta kan tsakiyar kan Aliyu baki na rawa tace.
"Aliyu Haiydar ina sonka d'ana ina tunako ako wacce rana ban tab'a yin sallah na idar ba tare da nayi maka Addu'a ba Ammin ka tana sonka kaine farin ciki na
Nagode wa Allah daya kare min kai."
Shi kam General manna kanshi yayi da jikin Ammin kamar mai tsoron kar a saceta a hankali yaji hawaye masu zafi irin hawaye da yake ji a duk randa bagen mahaifiyar shi ya dame shi,
ita kam Ammi fad'ar farin cikin ta bazai yiwu ba,
General kuwa zuciyar shi cike da k'aunar mahaifiyar shi a d'aya gefen kuwa har cikin ranshi yake jin zafi da haushin yayun mahaifiyar tashi dan su suka mishi Katanga da ita tun yana k'arami suka mai dashi marayan dole.
Bappa ne ya gyara zama cikin halin girma ya kalli Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim sannan ya kalli mahaifi yarsu a hankali yace.
"Wannan shine babban kuskuren da mutanen mu sukayi a wanna zamanin, aiki da zuciya fushi da tunzura a duk inda aka samu saki ya gifta a tsakanin ma'aurata,
mata kin forko da za d'auka shine hak'uri sai kuma a duba darajan Aure sannan a koma a duba makomar yaran dake tsakanin dan gujewa aikin dana sani,
babu wani riba cikin yin fushi dan anyi saki a reba uwa da d'an ta domin ko a shariyance yara suna gefen uwane har sai sun shekara 7 yanzu kai Lawan ribar me ka samu daka reba y'ar uwarka da d'anta kalli hawaye dake bin fuskar ta,
kalli illar rebesun da kukayi yasa Aliyu ya rayuda Bodd'i tsawon lokacin Amman baisan y'ar uwarsa bace itama bata sani ba,
kuna ne manta a can gefen bakusan tana kusa da kuba."
Shiru sukayi baki d'ayansu dan tabbas gaskiya Bappa ke gaya musu,
gaba d'aya zuk'atan su sun cika da nadama,
Barrister kuwa har cikin ranshi yake jin kunyar y'ar uwarshi.
Haka Bappa yayi ta musu nasiha da fad'a da nuna musu illar yin fushi dan an saki y'ar uwarka kace zaka rebata da yaran ta.
Gaba d'aya sun maida hankali kan Bappa shi kuwa cikin girma ya sake gyara zama tare da yin gyaran murya yace.
"Ibrahim wai ka d'aura auren Aminatu da Jabeer."
Cikin sunkuyar da kai Alhaji Ibrahim yace.
"Ehh Bappa na d'aura musu Aure ."
"Yaushe ka d'aura musu auren?."
"Bayan munje Membila lokacin da kukace an saceta toh damuka dawone da wata 1 na d'aura musu auren tunda shi Jabeer yana sonta."
Kai Bappa ya jinjina cikin kafeshi da ido yace.
"A lokacin kana da yak'inin Aminatu tana rayene? a lokacin kana da yak'inin zata dawo ne?
kasan inda take a wanna lokacin ne?.
Ajiyar zuciya Alhaji Ibrahim ya sauk'e tare da jin saurin tabbayoyin Bappa sai kai kawai yake gyad'a wa tare da cewa.
" a a,
bani da sanin wannan Bappa."
Gyaran murya Bappa ya kumayi sannan ya kallesu baki d'ayansu tare da cewa.
"Lawan ana d'aura Aure da babu ne? ana d'aura Aure da wanda ba san inda take ba?."
Cikin goge zufa Barrister yace.
"A a tabbas ba,a d'aura auren da babu matar ,
Amman nima wallahi Ibrahim bai gaya minba sai kawai cemin yayi ya d'aura musu