Showing 150001 words to 153000 words out of 171731 words

Chapter 51 - Namijin Zuma Book 2 Hausa Novel Complete

ta shaida mata abinda tagani Amma Abu yakici yaki cinyewa,. Seda Ta jima tana wayar kana ta ajiye wayar, Kuma bata tsaya jiran cewar naeemar ba ta tashi ta nufa hanyar fita tana fadin "bari inje part din baban Aeezad..." Ta fice ba tare data tsaya jinn me na'eema zatace ba. Haka na'eema ta tashi ta fice a dakin, ta nufa part dinta da aka ware mata a gidan da tunani a ranta tayi wanka ta kwanta, kawai so takeyi ta tabbatar da dagaske cikine jikin nabeelah, domin itade idanuwanta ciki suka ganar mata. A bangaren nabeelah a tsorace take Sbda ta fahimci an fara Gane da ciki jikinta Aiko a tsorace take. Da yamma misalin karfe hudu da Rabi,falon Hajiya mommy cike yake taf da jamaah kaf kawayenta be yanzuma se na'eema, khady bata Nan tana gidanta tazo dazu da azahar zuwa karfe uku ta tafi. Nabeelah keta zirga zirga a Falon tana jide musu manyan tray cike da kayayyakin lambu na Motsa baki, wato kayan fruits nau'ila daban daban. Kusan seda ta kawo tray tara wannan ne na taran shine wanda ta ajiyesa a kan table din gaban Hajiya mommy wadda suke zaune gata ga Hajiya naja'atu, se na'eema hajiya mommy din akasa a tsakiya. Bayan nabeelah ta ajiye tray din a kan table din su hajiya mommy, tayi-tayi ta tashi Amma ta gaza tashi, saboda kafarta data makale , seda ta tsugunna sannan ta ajiye tray din, kafarta ta rike gam, tayi tayi ta tashi ta kasa. Hajiya mommy da na'eema da hajiya naja'atu suka zubo mata ido. "Lafiya kika zauna kinata kallonmu kmr kinsamu TV,,,," hajiya mommy ta fadi tana kallon Nabeelah a wulakance. Na'eema ma ta kureta da ido, the more tana kallanta se taji zuciyarta na azabar bugu. "Kafata ce ta rike..." Nabeelah ta fadi a tsorace, sbda yadda hajiya mommy ta mata mgnr, zabura tayi ta mike da duk karfinta da kyar tasamu ta tashi tana Nishi da haki, ji tayi kmr an rike mata kafar ta-ta cikin hanzarin ta bar Falon. Na'eema da hajiya mommy suka kalli juna Sbda cikin dasuka gani baro baro a jikin nabeelah. Hajiya naja'atu ma ta gani tin shekara jiya datazo tagani, Amma we tayi shiru a tunaninta sun sani, ynzu ma tanaso tace Wani Abu Amma tayi shiru. Na'eema ce tace "Mommy naga Wani abu...." Ta fadi yayinda zuciyarta ke bugu, kowa hankalinsa na can suna kallan TV Kuma suna hira Dana kusa dasu, Hajiya naja'atu Kam idanuwanta na kan TV. Hajiya mommy da itama zuciyarta ke mugun harbawa, ta kalli na'eema tanaso tayi Mgna Amma ta kasa magana. Sede ta tsinci bakinta dacewa "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Itace kalmar dataketa maimaitawa , Apple ne a cikin bakinta Amma ta kasa hadiyewa sede ta fiddosa waje, ta ajiye a gefen tray din. Dai dai Nabeelah ta dawo falon da Wani tray din ta ajiyesa a dayan table din Wanda shi kadai ya rage ba'a ajiye tray din a Kai ba. Zuciyar Nabeelah se bugu takeyi, bugun da bata tabajin irinsa ba ta juya zata bar falon, cikin hanzari hajiya mommy ta mike ta kawo mata hijjabinta ta baya cikin zafin nama. nan ta dakatar da ita sbda shakurewar datayima wuyanta data RIKO mata hijjabi har kakarin amai tashiga yi, nan take hankalinta ya kara tashi bugun zuciyarta ya kara yawaita, seda d’an cikinta yayi wata iriyar mummunar harbawa, ta cire hijjabin jikinta kawai sbda neman shidewa da takeyi ta zube kasan kafafuwanta cikin dimauta da tashin hankali mara misaltuwa, bata ma hayyacinta Sam sbda tashin hankali, takai hannu ta rufe cikin jikinta, shi kawai take ji. Nan idanuwan kowa na falon ya dawo kansu dan ganin meke faruwa. hajiya naja’atu tayi hanzarin cewa “hajiya meye haka zaki shakurewa mace meciki wuya? Kuma tsohon ciki bayan da kyar kake numfashi in kanada tsohon ciki , aise kisa numfashinta ya daukee….” Hajiya naja’au batasan mugunta ita Sam. . Juyowa tayi ta kalli naeema wadda tini itama ta mike tsaye, a tare ita da naeema suka kalli hajiya naja’atu suka hada baki gun cewa “Ciki?” Naeema seda ta dafe kirjinta sbda wani azababben bugu da yakeyi. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” Itace kalmar da nabeelah ta fadi a zuciyarta, ubangiji ne kawai yasan a wani Hali take ciki so takeyi tayi kuka ko zata samu nutsuwa a zuciyarta amma ta kasa, yaude asirinta ya gama tonuwa, d’an cikinta kuwa se azababben motsi yakeyi, motsin dabe taba irinsa ba se yau, in kasa ido har ta saman rigar jikinta zakaga harbawarsa, takai hannu ta RIKO kasan cikinta hadi da rintse ido, ta sadakar yau, daman jiya kwana tayi muggan mafarkai, ta RIKO cikin jikinta gam, a ranta Adduah takeyi Allah yasa kome ze faru ya tsaya a kanta kawai kar a taba mata ciki, yau ta tabbar har kasheta hajiya mommy na iyayi,. "Cikin shege! Haba biri yayi Kama da mutum, amma cikin shege a family din Alhaji Sunusi,, tabdijan!” Hajiya mommy ya fadi afirgice, zuciyarta na tsananta bugu, ta rasa dalilin dayasa takejin tashin hankali a kan cikin jikin yarinyar. Sbda tashin hankali Nabeelah taji kmr zuciyarta ta fito fili, se azabar bugu takeyi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta taji dadih, ji takeyi kamar zuciyarta zata buga, se Adduah takeyi, ta rasa ma Wacce Adduah zatayi sbda tashin hankali tayi kasa da kanta, danma ubangiji ya rufa mata asiri, ta basu baya . Hajiya rafiah ta karasa ta juyo ta da ita ta yadda zata fuskanceta sosai ta tabbatar tabbas ciki ne a jikin yarinyar.ta kurama cikin jikinta ido , idanuwan nabeelah na kasa, jikinta se kakkarwa yakeyi ta tallabo cikinta ta rike sosai kmr za a kwace mata shi, ita cikin kawai takeji batajin ta kanta, abinka da zuciyar uwa, cikin se mugun harbawa yakeyi, hankalin nabeelah inyafi dubi seda ya tashi. A kallo uku hajiya mommy ta tabbatar da ciki ne a jikin nabeelah kuma tsoho, ta tabbatar kuma hafsat nada masaniya a kan cikin, koma menene da bakinta zata fadi sbda ba karamar azaba zata mata ba yau. Naeema ta matso daf da nabeelah nan ta kara ganin cikin baro-baro, ta kuma dafe kirji, tashin hankalin data Shiga baze misaltuba, ta kumajn tsanar nabeelah sosai, haka itama hajiya mommy nan take ta kumajin tsanar nabeelah sosai. Kowa de ya zubo ido amma Sam basu fahimci meke faruwa ba. “A gidan uban wa kika samo ciki? A gidan wa kika samo cikin shege? Yau se kinci uwarki da uban ubanki, yau sekin gayamin cikin waye wannan jikinki? Inmates hafsat ce ke Miki kawalanci yau duk senaji komi…” Hajiya mommy ta fadi cikin tsawa da karad’i. Jikin nabeelah ya kuma daukar rawa, ta kumayin kasa da kanta, hajiya mommy ta kuma tambayarta cikin tsawa “Cikin waye ga jikinki?” Nabeelah ta kasa mgna se azabar bugu da kirjinta keyi ta lumshe idanuwanta gam gam. “ bake ake tambaya ba dan ubanki! Ni daman na tsaneka wlhi, ne kaunarki ma bansansa,,, yau sekin gaya mana wani dan iskan ne ya miki ciki? Zakiyi magana kose jikinki ya gaya miki…” naeema ta fadi jikinta na tsuma, ji takeyi kmr tayi ball da ita da cikin jikinta, inda Hali ma Tana iya zama ajalin cikin jikinta, kawai taji ta tsani cikin sosai. Nabeelah tayi shiru ta kasa cewa komi kawai se kukan zuci takeyi,jikinta se kara rawa yakeyi.. hajiya rafi’ah a hasale tace “Dan ubanki uban wa ya miki ciki? Shegiya karuwar banza, daga yau zamanki ya kare a nan gidannan, zakiyi magana ko baza kiyi mgna ba yar iska ta kama ciken shege ta rike, dan kutmar ubanki ki gayamin uban wa ya miki cikinnan na jikinki?” Nabeelah ta girgiza Kai ta kasa mgna kawai se yanzu taji kwallah masu zafi sun wanke mata fuska,. Hajiya rafi’ah ta dagota da hannu daya ta wanketa da uban marirrika guda hudu, a Dukkanin kuncinanta biyu. Zafin Marin ya shigeta amma ta kara RIKO cikinta sosai ta fashe da wani irin kuka mara hawaye na zallar tashin hankali, se ihun haka kawai takeyi. “Uban wa ya miki ciki?” Hajiya mommy ta kuma tambayarta, still tana rike da bayan wuyanta ta riketa gam ta bayan wuyanta. “Bazaki gaya mana uban wa ya miki ciki ba?” Cewar naeema hajiya rafi’ah ta Ansha da “jeki ciromin wayar injin wallahi yau nice ajalinki da cikin jikinki, Nima ai ba kaunarki nake ba, dan kutmar ubanki yau zan kasheki na kashe banza na kashe hofi ba abinda aka isa Amin…” naeema ta nufa kitchen domin ta ciro bulalar jikin babban injin nika dake kitchen din kasa, ba bata lokaci ta ciro belt din jikin injin nika ta dawo falon, da zabgegen belt din. har lokacin hajiya rafi’ah na rike da wuyan nabeelah ta baya, naeema ta miko mata belt din injin ta amsa, ganin tana shirin zubawa nabeelah uban belt din yasa hajiya naja’atu saurin tasowa ta iso ta rike bulalar kowa ya kasa dktar da hajiya rafi’ah, se kallo kawai sukeyi se yanzu suka fahimci meke faruwa wato cikin shege yarinyar tayi? Dukkaninsu azabtar da yan aikinsu sukeyi dan haka se cewa sukeyi “Gaskiya hajiya Karki sassauta mata dan kutmar ubanta, shaggu masu aiki yan iska mayun mata, duk fatsikaine …” sune muggan kalaman daketa fitowa daga bakunan mutanen. “Karki daketa da wannan bulalar pls hajiya, kodan Albarkacin cikin jikinta…koda na shegen ne ki kyaleta pls, Karki kashe ta in kika kasheta Allah vaze barki ba, iya wuya karka dau hakkin wani kwarai tsakaninka da ubangiji inyaga dama ze iya yafe maka…” Cewar hajiya naja’atu data rike bulalar belt din hannun hajiya rafi’ah. Fisge bulalar hajiya rafiah tayi tana fadin “wani albarkaci Cikin shege ke garesa? Dan kutmar ubanta yau ita da cikin shegen duk nice ajalinsu, ko Alhaji sunusi inya shigo falonnnan be isa ya hanani na kashe yarinyar nan ba, tin fa Tana karama take gidannan, so kk ta Batawa gidan mijina suna? Tayi kadan dan bura ubanta,,,” hajiya mommy ta karasheta tana sakin nabeelah daga rikon datayi mata, ta turesa kasan tile din falon ta hankadata seda ta mirgina ta buge kanta da kujera, Sam nabeelah taki yadda cikinta ya bugu hkn ne yasa ta bugu a kai, nan take se goshinta ya kumbura sbda ta bugu sosai abinka da farar fata batasan whla. Hajiya rafiah ta daga bulalar ta fara shimfidama nabeelah a jikinta da karfi, zafin bulalar ya shiga nabeelah ya ratsata tako ina ta fasa ihu cikin fitar hayyaci tana me basu hakuri. Amma ina ai kmr Tana zuga ta, naeema ta jawo wayar wuta, tashiga zubawa nabeelah, yazamana su biyu ke bugunta da naeema da hajiya mommy,. Hajiya naja’atu de taga abu yafi karfinta taja gefee, tana tausaya wa nabeelah, yan falon de se zugawa sukeyi. Ita kam nabeelah dukta rikice se basu hakuri takeyi dukta rikice Gashi ta kasa motsawa ta gudu dagan inda take, se ihu takeyi kawai Tana kakkare cikinta, nan naeema tafi bugu, ita kam hajiya mommy tako ina kawai Kai mata dukan takeyi da karfinta tana dukanta tana Haki sbda da karfi take bugunta. “In har bazaki gaya mana wani shege ya miki cikin shege ba, sena zama ajalinki wannan cikin sede ki haifo shegen cikin naki a kabari..,” Cewar hajiya mommy. Yan falon se kara se zugawa yakeyi cikin sigar gulma, hajiya naja’atu ita kadai ce keta aikin bada hakuri taki daddara, ita de gaskiya da sauran imani jikinta. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya tako ina. Hajiya naeema da hajiya mommy se aikin dukan nabeelah sukeyi wadda keta ihu har yanzu, tini jikinta ya rufe da azabar zafi sbda sun faffasa mata jiki tako ina, har fuskarta ta fashe se jini kawai ke fita a fuskarta da wasu sassa a jikinta , rigar jikinta me Haske ce, dukta baci da jini,farar fatar nan tata tayi red sosai ba karamin duka suke mata ba, a zuciyar nabeelah ta kudirta ko kasheta zasuyi bazata gaya musu waye uban cikin ba, sbda ta tabbar in sukaji, tabbas wuta kawai zasu hada su sata ciki.

Hayaniya Alhaji sunusi yaji wanda shigowarsa gidan kenan, ya fito daga mota yaji hayaniya tayi yawa, cikin hanzari ya nufo part din hajiya rafi’ah sbda ya fahimci hayaniyar bata lafiya bace, yana shigowa falon yaga abinda ke faruwa, kokarin dakatar da hajiya rafiah yayi amma taki dakatawa tayi ma kmr bata San ya shigo falon ba, shi Sam bema kula dawa ake dukanba balle ya kula da cikin jikinta. Kawai de yaji hajiya nata fadin “Sekin gayamin ubanwa ya miki cikin nan na jikinki?” Sune kalaman dake fitowa daga bakin hajiyar, nabeelah kam tin Tana ihu ana ji har muryarta ta disashe yazamana tana ihun amma bame ji. daman kwance take kasan tiles din se kara rirrike cikin jikinta takeyi, har yanzu duk azabar da takeji ta kasa sakin cikin jikinta. Duk yadda Alhaji sunusi yaso
Ya dakatar dasu abu yaci tura , yayi-yayi ma ta tsaya ta masa bayani amma ina, seda kyar naeema ta tsaya ta masa bayani se yanzu ne ya kallah yaga ashe nabeelah ce ga uban cikin yayi Totso a jikinta, naeema na gama masa bayani suka ci gaba da bugunta kmr wadda tayi musu wani mummunar kisan kai, Kai kace Ubangijine ya aikosu su daketa. Alhaji sunusi ya zubawa nabeelah ido cikin mamaki, shide dan bayadda zeyi ne amma a ransa yaji bayason dukan da Ake mata, dukda lefin datayi babba ne amma shi a ransa beji ya tsaneta ba,. Duk yadda yaso ya dakatar dasu abu yaci tura, yan falon de se kallonsa sukeyi daman duk sun San shi Mijin tace ne Sam basuyi mamakin danya Hana matarsa taki hanuwa ba a bainannassi. Hajiya rafiah bata taba bawa Alhaji sunusi rai ba kmr yau ganin yadda yayi-yayi ya hanata abinda takeyi ta masa bansa a karshe ma sede ta daka masa tsawa tace “Ba ruwanka kaji kou!! In bazaka iya gani ba ka fita!” Yaji zafin yadda ta masa hakan a gaban kawayenta, inda sabo yaci acee ya Saba Tasha masa hakan yafi a kirga a cikin mutane, ba kmr ma kawayenta, amma na yau ya masa zafi sosai.





Paid book ne 1k 08101626484


NAMIJIN ZUMA



47.....

Ba karamin gudu Aeezad yasa dreva dinsa ke shararawa ba a kan shantalelen ti-tin daga Kano zuwa katsina,. Duka motocin tawagarsa kawai gudu sukeyi a kan Ti-Ti. gabaki daya Aeezad Gani yakeyi ma Kmr basa sauri, yakagu yaga mommynsa, gashi zuciyarsa nata azalzalarsa a kanta, a jikinsa yaji kawai Wani Abu na samunta, ji yayi har jikinsa da komi na jikinsa ciwo yake masa, zuciyarsa se uban Zababbaka takeyi ya rasa dalilin hakan, cikin mummunan baccin Rai ya tsinci kansa mara misaltuwa, kawai kuka yakeso yayi sbda yaji sassaucin matsifar dake zuciyarsa a kanta, ji yakeyi daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa zafi rakayau Kmr ana zuba masa rushi. "Ya hayyu ya kayyum,,,!'' itace kalmar data fito daga bakinsa se Nishi yakeyi shi kadai yasan a Wani hali yake ciki. Zaks dake gefensa se Aikin kwantar masa da hankali yakeyi Yana fada masa kalamai masu sanyi Amma Ina be saurarensa sema yaji ya cika masa kunne Yana Neman hada masa tunaninsa biyu, shi Kuma yafi bukatar yayi tunani guda daya Rak a halin da yake ciki wato tunanin mommynsa shine ne abincin ruhinsa. Dasuka fara shigowa katsina suka tadda uban hold of, Aeezad ji yakeyi kmr ya sauka ya taka Zuwa gidan Aunty hafsat, harya fara kokarin sauka zaks ya rikesa da kyar ya hkra., sojojinsu suka sauka suka tsayar da kowa su suka wuce.
Karfe biyar dai-dai motocinsu sukayi packing a farfajiyar gidan Aunty hafsat, a tafkeken packing space din dake gidan.
Big hajiya da Aunty hafsat dasuke zaune jingum jingum a falon har yanzu ba Wanda yasawa cikinsa abinci har kwara big hajiya tasamu tasha tea, duk matsifar baccinta, yanzu baccin ya xamar ma big hajiya sede barawo. aunty hafsat taji karar shigowar motoci Cikin gidan, a matukar razane ta mike , ta lega Nan taga fitowar AEEEZAD daga mota, Daman tin kafin ta leka jikinta ya bata shine. "na bani yauni nashiga uku! Ina zansa rayuwata!'' itace kalmar data fito daga bakin aunty hafsat yayinda zanin atamfar dake cikinta ke niyar faduwa ta rikosa da kyar, daura zaninma ta kasa seda kyar se fama takeyi ta daurasa Amma Yana subucewa Sbda tashin hnkli , inside zuciyarta se azabar lugude kawai takeyi,ta tabbatar in Aeezad yazo bega Aunty nabeelah ba ita ze bawa lefi, big hajiya ta bata lefi ma Ina maga uban gayyar. "Meya faru kk fadin kin shiga uku? Me kika gano? Ko wani Abun ne yasamu Cikin jikin yarinyar?'' big hajiya dake zaune ta mike tsaye cikib tashin hankali take jeroma hafsat tambayoyin. "Aee.....za...d....ne,,,ya,,,da,,,wo"" aunty hafsat ta Fadi bakinta na rawa, ta cire dankwalin atamfa dake kanta ta ajiye kasa, azabar zafi da tiriri kawai taji brain dinta nayi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta se Fadi takeyi ta bani, Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Kam ta fadeta yafi a kirga, bata kai wata take daukat wata. Big hajiya a ranta taji dadin dawowar Aeezad, waNi farin ciki ya lullubeta, Daman kashe wuta seda ruwa, in ruwan beyi ba a Kasheta da wuta, Wani lokaci lalaman baya kashe bala'i, wuta seda wuta. Aunty hafsat na daga tsaye cikin mummunar fargaba da tashin hankali, big hajiya ma na tsaye,. Ya turo kofar falon da karfi kmr ze cireta, seda Aunty hafsat ta Kuma tsorata taci uwa zuciyarta zata buga, Nan take Wani zazzabi ya lullubeta, ta kama rawar d'ari, ko a iya Haka tashiga Azaba zazzabin da takeji bata taba jin irinsa ba se Yau. ya Sako kafafuwansa Wanda suke sanye da farin cilifas irin na Yan hutu, Sam ma besan silifas bane a kafarsa, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login