Showing 165001 words to 168000 words out of 171731 words
Chapter 56 - Namijin Zuma Book 2 Hausa Novel Complete
fuska sake, ya bata kayayyakin ciye-ciyen daya siyo mata, se godiya take masa dasa Albarka, tinda aka haifo yarannan take ganin sauyi a gurin d'anta, gashima tanata ganinsa akai-akai gaskiya haihuwar yarannan yazo da Albarka, haka big hajiya Ke cewa motsi kadan. Ummih ta gaida Alhaji sunusi ya amsa fuska sake, besan meyasa ba inya kalleta se yaji gabansa na faduwa. Daman nabeelah tini ta gaisasa tin shigowarsa Aeezad ma ya gaidasa, ganin yadda daddy keta zuwa Yana duba yaran yasawa Aeezad jin dadih ba kadan ba. laure me Aiki ta gaida Alhaji sunusin cikin girmamawa. Ya amsa Yana kallanta Yace "Wannan fa?'' yayi mgnar da Aeezad. Aeezad ya bashi amsa da "Big hajiya ce tasa aka kawota daga gidan Alhaji daddy,zata dinga taimakawa da Ayyuka..." Alhajii sunusi yace "Toh-toh...Amma an tabbatar ta iya wankan jarirai kou?'' ya juya akalar tambayarsa ga big hajiya. Big hajiyar tayi murmushi tace "kar aje a jefa maka jikoki a ruwan zafi kou?'' duk Yan falon sukayi murmushi ba karamin jin dadih sukayi ba musammanma Aeezad, dadih na nunawa yaran SO na tsakani da Allah Sam ma be iya boyewa. Alhaji sunusi ma murmushin yayi yace "Eh wallahi big hajiya, haka akayi da Yar Abokina ta haihu haihuwar fari aka dakko me wanka, garin gasa cibiya ta kona babyn, big hajiya satinsu uku a asibiti ana fama da babyn ba karamin kuna yayi ba,,, maganin Ayi ai kar a fara, kwara a bawa hajiya ta dinga musu wanka..." Ya karashe mmaganarsa Yana kallon ummih wadda kanta ke kasa. Aeezad yayi hanzarin cewa "Nima haka nace,Amma big hajiya taki, ita ke musu wanka daddy, da kyar take bari aunty hafsat ta musu wasu lokutan . " Alhaji sunusi ya zaro idanuwa yace "gaskiya big hajiya dakin bari an dinga musu saboda naga ke ba Wani gani kike sosai ba..." Big hajiya ta amshe da "uban bana gani! A haka de na raineka, Shima Aeezad din Dan Anki bani shine Amma Dani zan rainesa... Dan haka ni zan dinga musu wankan da gashin cibi har Ayi arba'in banga me rabani da yarannan ba sede mutuwa..." "Toh ai shikenan Allah de ya tsare min..." Cewar Alhaji sunusi big hajiya ta rike Baki tana mamakin ganin yadda d'anta be kawaici a kan yaran Kuma duk kawaicinsa. Duk Yan falon suka amshe da Amin Banda nabeelah data kasa cewa komi se gyangyadi takeyi Ma ita bacci takeji, so takeyi ta gama bawa yaran nono taje ta kwanta. " Hajiya me kula da jikokina, Jeki ce da dreva Dina ya bude Miki but ki kwaso kaya..." Alhaji sunusi yayi maganar da laure Cikin girmamawa bada raini ba wai Dan tana me AIKI. Laure tayi murmushi Hadi dacewa toh ta mike ta fice a falon, a kallah laure bazata wuce 45yrs ba. Ta kwaso akwatunan ta diresu a tsakiyar falon, Nan aketa kallon kayan arziki,. A haka hajiya Maryam da mijinta, da Saif da matarsa suka shigo falon, Daman big hajiya tasa aunty hafsat ta tura musu da address. Cikin murna suka karaso aka gaggaisa, duk hankalin kowa na kan baby's,har rige rige sukeyi gun daukar babyn, se Masha Allahu kawai suke cewa Alhaji abubakar yace "Ashe haka ya kasance,,,Toh Allah yasa Albarka..." duk falon suka amsa da Amin nabeelah de a zuciya take ta Amsawa da Amin de. Nan de falo ya kicime se ganin babys akeyi da kayayyakin Arzikin da Alhaji ya siyoma babys din duk sunyi kyau kmr siyayyar mace. Big hajiya taji dadin ganin iyalansa a hade, anata nishadi,matar saif ta dauke babys ta rike sun bata shaawah sosai ta taba haihuwa Amma yaran sun rasu har Sau biyu,ji takeyi kmr a bata babys din ta tafi dasu. "Kowa de ya hallara, banda tsatson tsiya, Allah de wadaran hali irin na Rafi'ah...Sanusi bakayi sa'ar mata ba, Ubangiji de yasa da raina na ga ka auri mace ta arziki.." Big hajiya ta Sako wannan maganar ana cikin Hira. Alhaji sunusi yayi Shiru kawai shida kansa yasan macensa bata kirki bace Amma ba yadda zeyi ne. "Dafatan de baka sanar da ita an haihun ba?'' tayi mgnr da Alhaji sunusi again. Ya daga mata Kai alamar Eh. "Toh kar inji kar in gani, domin kana sanar da ita wannan haihuwar,seta shiga ta fita ta kashesu, danma kullum se uwarsu ta musu Azkar An tofesu tako ina, bade mutum ba ko aljan be isa ba Insha Allahu, mun rike ubangijin da baya bacci, kema nabeelah ki dinga yawan askar din safe da rana da dare, koda Baki da tsarki, ki dinga zama da Alwala da''iman kinji kou?..." Nabeelah tace "Toh..." Daman kullum cikin Alwala take da Azkar, Kuma tana tofe yaranta da Addu'ah safe da yamma da dare, kullum se uwarta tace ta dafe kansu Daya bayan Daya duk safiya ta dinga ma yaranta Addu'ah. "Alhamdulillahi da zuwanki zuriahta nabeelah, kinada ibada ba abinda mugu zeyi dake..." Cewar big hajiya. Hajiya Maryam tace "Kwarai kuwa....insha Allahu ma zan amso musu maganin kariya Ayi musu wanka dashi itama uwar tayi wanka dashi gobennan, zanzo na kawo da safe zan aika kanwata ta amsa da safe se inzo in kawo insha Allahu..." big hajiya da ummih suka hada Baki gun mata godiya. Har karfe Shadaya na dare suna gidan nabeelah ta mike sbda bacci takeji sosai zata nufa dakin da Aeezad yace Nan ne nata, shi Kuma dakin da yayi first night dinsa da ita Nan ne nasa. Aeezad ya mike ze bita Hajiya Maryam tace "Kai Kuma Ina zaka?'' ba kunya Aeezad yace "Bacci mukeji nida ita,..." hajiya Maryam ta bude baki tace "Au tare kuke kwana dame jego?'' big hajiya ta amshe da ''Kadan kika gani, ai wannan yamafi babys din, danma bakiga Abu ba a asibiti, Kai wannan yaran jarababbe ne..." Nabeelah najin haka ta karashe shigewa dakin da sauri sbda kunya. "Toh Ina zan kwana fisabillahi big hajiya?'' kowa ya zubu masa Ido Sam bashi data ido. Hajiya maryam tace "To ai haihuwa tayi ko jego taKeyi tana bukatar hutu? Sannan de Ai Doctor ta gaya maka ka'idojin CS kou? " Ya daga Kai yace "Duk an gaya min gimbiya hajiya,Ai bance Wani Abu zan mata ba, wlhi ki kyale sharrin big hajiya..." Alhaji sunusi yayi kasa da kansa jin abinda d'ansa ke fadi,, se kawai ma ya mike ya musu Sallahma yayi kissing jikokinsa dake hannun big hajiya kana ya fice a gidan, a ransa bega lefin d'ansa ba domin be Yar a kasa ba inde jarabar bukatar macece, Amma su sunada kawaici akasin shi Aeezad,. Duk yadda aka tasosa da Baki seda ya shiga dakin da nabeelah take harta fara bacci taji an rungemeta, zatayi mgna ya kame bakinta ya tsotsa, ya tura mata hannu cikin nono kmr shine babyn, gashi yaki sakar mata Baki tayi magana. Soyayyarta na kuma ratsasa, a haka bacci ya kwashesa seda yayi bacci ta kwace bakinta cikin nasa ta cire hannunsa a cikin nonon,sbda tasan dole big hajiya zata shigo ta kawo mata yaran. Ta matsa nesa dashi, bacci ya dauketa. Se shabiyu hajiya Maryam suka bar gidan,big hajiya ta nuf dakin da Aeezad da nabeelah suke da babys a hannunta, tana fadin Dani suke zancen. Itama Nan daKin ta kwanta tsakiyar Aeezad da nabeelah, danma gadon uban fadi be dashi se mutun biyar su kwanta basu matsu ba,babys Kuma Daman an riga an shirya musu gadonsu Nan ta kwantar dasu, Aeezad Yana farkawa yaga big Hajiya a tsakiyarsu, Allah yaso be Kai mata raruma a nono ba, girgiza Kai kawai yayi a zuciyarsa yace "Nida matata..." Kawai ya tashi ya bar dakin ya koma dakinsa, big hajiya ta masa kora da hali Wanda yafi kora da sanda, ya saba kwana yana tattaba nono yanzu Kuma se a hnkli besan yaze kasance ba. ummih Daman an bata dakinta can ta kwana, Daman ita ba Wani bacci take ba, ibada take tayi tanawa yarta da jikokinta Addu'ah,toh ynzu ta Kuma kara zage dantsi gun musu Adduah,.
Washe gari tin da duku-duku Hajiya mommy da na'eema suka bar gidan ko asibitin Basu fara Zuwa ba, suka nufa gurin boka can cikin daura. Bokan na ganinsu ya kyalkyake da dariya irin ta wad'anda aka Cirewa Imani gabaki daya yace "wato magana ta fito Kenan...tinda na ganki da yarki asiri ya bayyana,,,,hahahahahaaaaaaa.." se yanzu naeema ta Kuma tunawa da abinda bokan yace Ashe tin lokacin ma da auren Aeezad da nabeelah, da ynzu Wani labaarin akeyi ba wannan ba Amma tunaninsu ya bace, in Abu ze faru de baka da tsumi baka da dabara. Hajiya mommy ta bude baki zatayi mgna bokan ya dakatar da ita dacewa "Aita haifa wannan Cikin yau ma yaran kwanakinsu tara....hahahaha duk Ina biye da taurarinku, a taurarinki nake ganin meke faruwa, Aiki aka mata aka cire mata yara Yan Uku!!!'' ya kwashe da dariya dajin ya amsa. Dukkaninsu hantar cikinsu ta kad'a suka kalli juna, Hajiya mommy seda ta tsugunna sbda tashin hankalin tace "Yanzu shikenan inya mutu komi na yaran ne Kou boka mu Kuma se abinda Muka gani?" Bokan yayi dariya yace "Da wuya ma kugani .." a wannan karan itama na'eema seda ta tsugunna, dukda ita bayan kudin da takeso tanasan mijinta ma, . Hajiya mommy ta daura hannu a ka tace " Nashiga uku ni rafi'atu! Wace iriyar matsifa ce ta tinkaroni nida diyyata ...ynzu yaza ayi boka? ka temakeni boka ka kashemin yaran first ita uwar a haukatata, irin haukan dazata dinga yawo tsirara, sannan asa mata warin tamkar warin sabon ZAWOOO, inda hali ma asa mata Fiye da haka... A fara Dasu Daga baya Ayi ta uban gayyar... " Bokan ya kyalkyale da dariya yace an gama. Se yayi Shiru na wasu dakiku, kana ya kuma fashewa da dariya yace "Zeyi wahala wannan aikin domin kullum Cikin Azkar suke da yaran, dadin dad'awa dukkaninsu suna wanka da Wani magani Wanda bamu Isa muje kusa dasu ba,, sede ku bari in an samu damarsu a aiwatar da wannan aikin...." Na'eema ta fashe da kuka kawai, tana rokon boka ya temaka mata, ko kashe nabeelah ne yayi ita da yaran. Hajiya rafi'ah itama ji take uwa ta fashe da kukan Amma ta dake tasan aikin babba ne tinda har boka yace aikin ze wahala. "ka temakamin boka, bani dame temakona sekai boka, ka dubeni boka, ka rufamin asiri boka, karka bari suka karshena, banasan wannan yaran da uwarsu duka, gabaki daya komi nawa na neman kalacewa..." (hajiya rafi'ah ta mance da duk duniya bame taimakonmu se Allah) Boka ya kyalkyale da dariya yace "duk karki damu hajiya, ke zakiga bayansu, kin taba ganin nasa Abu a gaba banyi galaba ba? Zanta bibiyarsu harse nayi galaba a kanku ki kwantar da hankalinki....kuje gida kuyi bacci kawai..harshi uban gayyar bazan barsa ba, sena dawo dashi ga yarki tamkar yaro mara wayau... ." Ya Karashe Yana kwashewa da dariya. Nande hajiya da na'eema suka dinga magiya boka yace karsu damu, suka ajiye masa uban kudi suka koma gida na'eema ke driving motar, Amma hankalinta tashi yake, dukkaninsu bame mgna kowacce tashin hankali ya shafe tunaninta. Ranar ko asibitin Basu jeba, dukkaninsu ji suke damn mutuwa sukayi da wannan Labarin. Ranar haka suka wuni jugum jugum kamar an Aiko musu da sakon Mutuwarsu yanzu-yanzu. Alhaji Sunusi ya kula da yadda suke kmr marasa lafiya ko abinci basuci ba. Ya tambayi Hajiya mommy lafiya de ko tace masa lafiya Lau kawai Amma inside Abu na nukurkusarta, ta kula alwalar safe na Neman kaita la'asar, ta raina d'an hakki gashi ya shiga idonta ya addabeta da yawo Tako Ina. Ta tambayi Alhaji Sunusi nabeelah ta haihu Ashe? Nan Alhaji yayi mamakin yadda akayi taji Amma seya Waske yace shi be sani ba, ya nuna mata ma besan mgnr gudun kada Allura ta tono garma. Ranar de bacci gagarar Idanuwan Hajiya mommy da na'eema yayi, Abun har ya fara basu tsoro da mamaki, wai me Aiki tazo har gida ta Aure ma yarta miji, tsohuwar mace, kuma ya juyawa yarta baya ita da take sabon jini ya komawa tsohuwar mace. wannan abun a duba ne, ko yanzu nabeelah ta gushe tasama na'eema da Hajiya mommy bakin Cikin da baze gushe ba har abadan, Kai Wani abun fa dole sede insun kwanta Dama, basuga abinda zasuyima nabeelah ba su samu sassauci..
Karku manta Muna saida kayan gyaran Aure akwai pridal package manyan mata Kuma ba a barku a baya ba kuzo ku gyara jikinku a sabanta jiki. 08101626484
This book is 1k 08101626484
NAMIJIN ZUMA
51....
Bayan dawowarsu Asibitin da kwana hudu aka fara shirye-shiryen suna, Anata shirye-shirye domin so akeyi Ayi bikin suna irin wanda ba a taba irinsa ba a kaf duniya.anata tsare-tsare da Aunty hafsat, tini har an kama kaf hall din dake cikin garin katsina, tin ana saura 3days sunan Yan ukun, w'anda Aunty hafsat ta musu Lakani da Manaal itace me sunan Mahaifiyar Nabeelah, Mushfiqa itace me sunan Big hajiya, Mahnoor itace me sunan mahaifiyar AEEEZAD,. Alhaji Sunusi ya kuma wa yaran akwatunan fitar suna kowacce dozing-dozing, kana yayima nabeelah akwati biyar cike da kayayyakin alfarma. Aeezad Kam kayan fitar suna akwatunan dozing biyu yayima nabeelah, yaransa Kuma ya musu dozing biyu-biyu DUk daya seda aka mata akwati dozing biyu na zallar kaya na Alfarma kawai. Yawancin kayan da Aeezad yayima nabeelah a fitar sunan kusan Shima yayi irinsa. ana saura 2days sunan tafiya ta kamasa zuwa Kano haka dole bdan taso ba, ya bar yaransa da nabeelah da santa ya kuma ninkin ma ninkin a zuciyarsa. Seda ya Isa garin kanon yaga Ashe kiran a kan Alhaji rabi'u ne da tawagarsu, Wanda aka kamasu a gurin Wani boka matsafi, sun kashe wani sun kai masa zeyi tsafi a kan a raba Aeezad da duniya, shine akaje kama bokan saboda n kama wata mata asibiti taje satan jarirai, dataji duka shine tace bokan ne ke sata Wannan sana'ah tsawon shekaru ashirin tana masa Wannan Aiki na satar jarirai a asibitoci. Da akaje kama bokan shine akaga su Alhaji rabi'u sun kawo gawar mutum namiji d’an shekara Ashirin da uku. Daman sojojine sukaje kamo bokan. Da aka kawosu office sukaji duka shine suka fallasa komi har barin dasuka kaiwa Aeezad, komi akayi recording aka bawa Aeezad yana isowa garin kanon yaji, yayi mamakin meyasa suke binsa da bita da kulle bayanshi besanma da zamansu a duniya ba, tare suke aiki amma su Sam besan da zamansu ba, su kawai burinsu su kashesa Alhaji rabi’u ya maye gurbin kujerar Aeezad. Nande aka tura Alhaji rabi’u da tawagarsa kotu, duk yadda sukaso su kubuta beyu ba, nande aka yanke musu hukuncin daurin rai-rai a gidan yari,. Allah yasa mufi karfin zukatanmu.
Kwanan Aeezad daya a kanon ya dawo garin katsina, aka cigaba da shirye shiryen suna daza ayi gobe insha Allahu,. Zuwa ynzu hajiya mommy da naeema suna samun labarin komi ta hanyar wata kawar naeema sumayya wadda take kawar hawwa’u ce aminiyar Nabeelah da ita ake komi, ita kuma da sumayya take zuwa komi ta haka Hajiya mommy ke samun labarin komi. Ranar suna Ansha shagali Amarya da Angon Karni se shiga sukeyi ta alfarma, jarirai ma se shiryasu akeyi, daga safe zuwa rana sun chanza kaya yafi kaloli talatin, sutura kawai ta alfarma suke sawa,. Ummih ma Alhaji sunusi ya mata kayan fitar suna akwati biyar, yayima big hajiya ma akwati biyar, yayima aunty hafsat ma Akwatuna biyar. Kowa se shiga yake ta Alfarma, . Tako ina mutane ne makil a gidan wasu ma ba asan daga ina suke ba. Nabeelah Tasha makeup, daga shahararriyar ne makeup dinnan Hajiya Yasira (Gayu). Ga kunshi tasha ns design , tako ina walkiya takeyi Gashinan na kanta yasha gyara ta kashe dauri, duk inda tabi camera kawai ke daukarta photo , ita da mijinta da Yaranta da duk abokan Arziki, big hajiya kam ta Kama yara ta rike gam. Zaks ma ba a barsa a baya ba, abu nasu maganin a kwabesu, shima Gashi ga Dr Salmah, da family dinsa,. Hajiya maryam kam da zuriarta a gidan suka kwana Dazu aketa hidindumu, Alhaji sunusi ma se yabar gidan ya dawo yanata kallon jikokinsa, dasuka fito sharr sukayi kyau. Besan kyaun ummih ya shahara ba se yau datasha simple makeup ita yace ta zubo masa abincin gidan sunan shida abokansa dasuka kebe a wani babban falon, ta kawo musu abinci iri iri da drinks. Alhaji sunusi se binta yake da kallo Tasha doguwar riga wadda ta bayyana dirinta, a dire take sosai komi ya fita zarr shaawah, Alhaji sunusi yaji kmr ta zauna karta fita a dakin. Babban Amininsa Alhaji adamu ya fahimci irin kallon da Yaga yanama Ummih, se Adduah yake a ransa Allah yasa abinda yagani da idonsa ya bayyana a zahiri, duk cikinsu kowanne ya dace macen Arziki amma Banda Alhaji sunusi kuma duk yafisu nagarta da kudade, Gashi mutum na gari Sam bashi da nakaso. Da daddare akasha dinner wanda ya tara manyan mutane, Kama daga kan maza zuwa mata, duk wasu abokan Arziki sun hallara, manyan yan jaridu sunzo se dauka sukeyi akayi hira da Aeezad a ranar ne ya bayyanawa duniya nabeelah matarsa ce domin mutane da dama basu sani ba, aiko a Daren akasa duk wata dauka da akayi A manyan Gidajen talabijin da Manyan Accounts din TikToks. Manyan kyaututtuka aka dinga rabawa a taron tunan, daga 13promax zuwa XR aka dinga rabawa a gurin dinner, harda motoci aka dinga rabawa game rabo. duk wanda yazo to tabbas yasamu kyautar atamfofi masu hotunan Aeezad da nabeelah da Yan ukunsu kyawawa da waya se wadda de kayi sa’ah 13promax or 12promax or 13mini zuwa XR de, ko motar, harka ake ta Alfarma. Alhaji sunusi ya fitar da dukiya a sunan shiya dauki nauyin kyaututtukan da aka raba agun sunan, Sah shida da raguna