Showing 57001 words to 60000 words out of 171731 words

Chapter 20 - Namijin Zuma Book 2 Hausa Novel Complete

zata nufa dakin, cikin hanzari Zaks ya karasa gareta ya fara bata Hkri cikin dadin lafazi “Aunty kiyi hkri Karki shiga kina kuka big hajiya tagani asiri ya tonu, kinga in asiri ya tonu matsalar zatafi shafarki mommynmu shide Aeezad kam nashi kadan ne, bama zeji komi ba sbda duk ya zama wani Kala, shi wannan baya hayyacinsa, bama a maganarsa…” nabeelah ta dakata da kukanta hadi da juyawa ta zubowa Zaks ido hawaye ya wanke mata fuska tace “Kana ganin rainin da Aeezad kemin kou Zakariyya? Ya mance ni na renesa gabaki daya ya rainani, yanzu waini zema wannan cin mutumcin, sbda ina aiki gidansu …” ta karashe hadi da kara fashewa da kuka. Nan tausanta ya kara ninkuwa a zuciyar zaks ba karamin tausanta yaji ba “kiyi hkri mommy,, harga Allah be miki Adalci ba, dande ba halin in fadi ne,,,kiyi control kar big hajiya ta gane wani abu,,,,” daurewa tayi ta goge hawayenta dake zirya kan kuncinta amma Sam hawayen sunki Dena zubowa,. “Kiyi hkri mommy…” Cewar Zaks, bude baki tayi zatayi mgna ta kasa sbda wani sabon kukan daya Balle mata ta kulle bakinta, bakin ciki mara yankewa na cinta inside,. Zaks ya shiga bata hkri cikin tattausar lafazi, a hankali ta fara Jin sauki a zuciyarta, hawayenta suka rage Yawan zirya. Bayan fitarta motar Aeezad ya jingina bayansa da kujerar motar se murmushi yakeyi, jinsa yake ba abinda ke damunsa yau, kmr an masa bushara da Aljanna, se murmushi kawai ya saki kmr Wawa, yana kallonta ta glass Zaks ya tareta, Tana kuka , koda beji me Zaks kece mata ba yazan hakuri yake bata, dan haka yayi luf yaki fitowa se kallonta yake daga kasa zuwa sama yana murmushi, a zuciyarsa yace “kayannan fa yanzu duk nawa ne, kayan Alatu na jikin mommyna Alaji!!….” Ya fadi yana kara lumshe ido, se hadiye yawu yakeyi, “kayan Alatu, iya kayan alatu…” ya kara fadi hadi da fitowa daga motar se murmushi yakeyi, ko sadda ya auri na’eema yacita beyi kwatan farin cikin dayake ciki a halin yanzu ba,, amma yau beci ba besa ranma za a basa yacin amma farin cikinsa baze misaltuba , shifa ko be hauta ba AlhamduLillah aide ya aureta ko. Karasowa yayi inda suke tsaye Zaks nata bata hkri cikin girmamawa, tini tadena hawayen da takeyi, ta koma kukan zuci, Tana ganinsa ta nufa ciki , ta tsanesa yanzu , bata taba tsanar wata halitta ba kmr Aeezad din, ko san ganinsa batayi, shi kam ko a jikinsa murmushi,.“Hakuri kake bata kou?” Aeezad ya tambayi Zaks yana murmushi. Zaks yace “eh, wlhi Tana ta kuka kmr ranta ze fita, ka dauki hakkinta wlhi Aboki…” Zaks yayi kasadar fada ma Aeezad din haka, murmushi Aeezad yayi hadi da kallon Zaks din yace “Nima ta jima Tana daukar hakkina Ai, kwara ita iya kuka tayi, ni inna rasata rayuwata zan rasa wallahi Aboki…” Zaks ya kallesa Cikin mamakin kalmarsa ta karshe, yasan Abokinsa baya karya duk abinda ya fadi to tabbas gaskiya ne. “Kai baka hango kalubale da bala’i da matsifar dake gaba, you have to be thinking before you do gaskiya Aboki…” Cewar zaks. Aeezad ya tabe baki yace “duk wani bala’i da matsifar daze faru, wlhi wanda nakeji a zuciyata a kanta yafi haka, koda za a watsamin fuel a watsamin ashana wuta ta tashi dani, wlhi duk rad’ad’in zafin wutar dazanji baze kai zafin da nakeji a kan San Aunty nabeelah ba, ni kawai ko kasheni za ayi a kashemu nida ita I don’t care, zuciyata ita kawai takeso a kaf fad’in duniyarnan…” Zaks ya sauke Ajiyar zuciya yayinda idanuwansa suka kasa sauka a kan Aeezad , Fuskarsa da idanuwansa tini suke gaskata duk abinda ya fito daga bakinsa,.”Yaushe ka fara mata wannan SAN?” Zaks ya tambayesa shifa har yanzu abun mamaki yake basa hadi da daurin kai. “Muje ciki…” Aeezad ya fadi ba tare daya bawa Zaks amsar tambayarsa ba, suka fara takawo zuwa cikin, tako ina haskene a asibitin Kai kace safiya ce. “Baka amsamin tambayata ba pls Aboki…” Cewar zaks. Aeezad yayi murmushi yau de murmushi yaki gushewa a kan fuskarsa mutumin dase yayi 3month beyi murmushi ba kullum fuska a gimtse . “Tinda uwata ta haifoni duniya aka mika mata ni ta raineni na fara santa….ban San santa nakeyi ba se kwanaki, kawai ni naji I can’t live without her…ita kadai ce ke chanzamin mood inna ganta, komi nawa kawai itace a zuciyata… wlhi duk duniya ba wanda ya taba soyayyar da nakewa Aunty nabeelah, in ban ganta ba kmr zan hauka, in tana gabana se in mance da komi na rayuwar duniya, banganin kowa se ita …” zaks daya saki baki lamarin ya fara bashi tsoro abu kmr aikin sihiri, kai ko sihirine tabbas samun wanda ze irinsa da wuya. “Ka dakko dala da gwauron dutse…” Cewar Zaks dake hango matsifun dake gaba. “Babban dutsen America na dauka na tarihi kuma ko nauyinsa banji, nauyin santa dake raina ya wuce nauyin a dauramin kaf nigeria a kaina….wallahi da ace san aunty nabeelah zahiri ne kowa na gani da kogin maliya za acemin a fagen santa…” “base ka fadi ba ni shaidane, idanuwanka da kaf gabobinka sun gaza juriya a kan boye santa…” Cewar Zaks. Aeezad ya amshe da “Tabdijan! Karamin so ake boyewa nata yafi gaban a boye, inna boye ai sede a Wayi gari aga gawata…” Zaks ya amshe da “I see, abinda kakeyi a aikace ya wuce kalaman da kake fadi,, ka zama kmr ba kaine commander of army ba, kawai ga kanan ne Alhajin Allah me ciki bakwai…” Zaks ya karashe hadi da kwashewa da dariya Aeezad ma dariyar yayi yace “dabadan kawaici dakai zuciya nesa ba da tini na mata ciki hansin!…” zaks ya kara kwashewa da dariya hadi dacewa “zaka aikata din hakan, inde a kan mommy ne …” dai-dai suka iso Cikin falon suka samu big hajiya da nabeelah zaune kasa big hajiya na zaune kan kujera. Tana ganinsu ta zubu musu idanuwanta masu cike da tashin hankali. “Wai Ina kukaje min ne da jikanane, na fita na dubaku tako ina ban ganku ba, likitoci sunzo yafi a kirga , gabaki daya kun dagamin hankali har waje na fita nemanku, naga banganku ba ki nabeelah ma bangani ba,,,,se yanzu ita nabeelah ta dawo duba kuga idanuwanta duk sun kumbura sunyi luhu-luhu, inagama kuka tayi, inata tambayarta meya faru tace bakomai, tacemin kuna waje gakunan shigowa,…” Zaks da Aeezad suka kalli juna , karasowa Zaks yayi ya zauna kasan carpet , Aeezad ya zauna kan kujera Zaks ya zubowa big hajiya idanuwa hadi da jinjina Kai yace “Bari, bari, bari, wayyohhh! Hmmmm kede big hajiya, wani luntsumemen hatsarine ya afku a nan gaba damu kadan, jirgi da mota katafila suka so su hade,, shine mukayi sauri muka isa muka hana faduwar hakan, amma fa dukda haka, mutane dari uku da saba’in da digo tara da mita uku ne suka jiggata…. Shiyasa kikaga mommynmu nata kuka, duk Imani ne ya ratsata ganin irin mummunan hatsarin daya wakana….” Zaks ya shimfido mata karya, abinda da tsufa nan take ta amince ta dauki sallallami da salatittika ta karanta fatiha yafi sau ashirin kana ta fara kwallah Tana fadin “Wayyo , Allah ya jikansu C Allah ya bawa iyalensu hakuri, Allahu Akbar da anyi mutuwa dana tuna da mijina Na Allah, Allah yajikanka na Allah…” seta kara fashewa da kuka. Aeezad kam wata iriyar dariya ya kwashe da ita kasa kasa, nabeelah kam se binsu takeyi da ido ita abinda yake damunta yafi gaban tayi dariya, duk tabi ta rakube, Aeezad se kallonta yake yana karkashe mata ido daya kmr tsohon karuwan namiji, ita kam dasun had’a ido seta balla masa harara. “Kiyi hkri hajiya, dukkaninmu lokaci muke jira…” Cewar zaks. A fusace big hajiya ta dago kai hadi dacewa “Kuke de jira, shege ja’irin yaro, sede ku mutu ku duka ku barni …” Zaks da Aeezad suka kwashe da wata iriyar dariya data kasa boyuwa daman big hajiya bata kaunar mutuwa. Nan ta hadesu ta fara sirfafo musu zagi, seda ta musu San ranta kana ta mike zata nufa daki se taci karo da waya da kudin da Aeezad ya watsar nan kasan. Sam Dazu big hajiya bata Gansu ba sbda tashin hankalin bataga jikanta ba. Ta tsugunna ta dauka kudin da wayar ta juyo ta nunawa musu Tana fadin “kunga wasu makud’an kudi, da wayar salula irin wadda saifu jikana na gurin wannan d’an ke rikewa…ko ku kuka yar?” Zaks ya amshe da “Aah inaga ganima ce ta isoki har gida, daga sama ta fad’o inaga na wad’anda ke cikin jirginnan ne dasukayi hatsari suka mace…” big hajiya ta amshe da “kwarai kuwa, Allah ya bani Arziki har gida, kaga irin wannan wayar ta yaran zamani ce, , ga kudi masu yawa dalar Amurka ce wannan na ganeta,,kaga dabadan wannan d’an ba ai tini na bude shagon ice a GRA kusa da gidan shi wannan d’an, inada kudi dayawa nayi-nayi wannan d’an ya hana in bude shagon saida icce,,,,,” “icce kuma big hajiya…” Cewar Zaks Aeezad kam se dariya kawai yakeyi. Big hajiya ta zaburowa zaks “Eh iccen mana dan kutmar ubanka, ai sana’a tace tin Na Allah mijina nada rai, nidashi ai sana’ar muce saida icce a daji muke yowa…” Zaks da Aeezad suka kara kwashewa da dariya big hajiya ta nade ledar kudinnan bayan ta jefa wayar ciki ta saka a cikin lalitarta dake cikin zani ta mayar ta kulle se murna takeyi , domin hajiya akwai San abun duniya , ita har yanzu kudi basu zama bakinta ba. “Uwarku da ubanku kukewa dariya, shegun yara masu Kama da yara maza a zamanin fir’auna,!” “Muna godiya hajjaju, ai girmanki ne kiyi komi ba komi…” Cewar Zaks daketa dariya har lokacin. Hajjaju ta miko masa dakuwa hadi dacewa “Kaci uwarka da ubanka kaida godiyar, shege da idanuwanka irin na tsinannun zamanin farko, da Kai kmr na bazawarin karuwa…” Zaks ya kuma kwashewa da dariya hadi da dunkule hannu ya kara Rissinawa yace “Ina kara godiya hajjaju ikon Allah…” big hajiya batabi ta kansa dan ganin yana neman haukatata, daman tasan halinsa shakiyyin yaro ne na bugawa a jarida. Ta maida dubanta kan nabeelah tace “Taso muje ciki diyyata, kiyi hkri kinji, kai wannan diyya da imani kike har yanzu jimami kikeyi kenan…” Zaks ya amshe da “Eh kede bari big hajiya ai mommy Zuciyar fal take da imani hadi da madarar rauni…” big hajiya ta amshe da “Tabbas, duba kaga yadda farar fuskarta tayi ja-jawur kai kace a fuskarta hatsarin ya faru…” big hajiya ta fadi Tana tsurawa nabeelah ido wadda ta tashi tsaye, se Mika takeyi Aeezad kam idanuwansa na kan monuwanta, dataketa bankarosu tsigar jikinsa se tashi takeyi, ji yakeyi kmr yaje ya duddumbesu. Zaks ya amshe da “Ai mommy nada fadin zuciya me cike da imani…” Cewar zaks daya fadi yana jinjina Kai. Big hajiya ta amshe da “wayyo…” nabeelah ta kalli zaks ta gallara masa harara harshi haushinsa taji tanaji. “da girman kujerarki gimbiya me mulkar farar zuciya…” Zaks yayi mgnr da Aunty nabeelah, bayan ya kula da aiken hararar da nabeelah ta masa, nabeelah da Aeezad ne kawai suka fahimci me zaks ke nufi amma big hajiya bata fahimci komi ba, a zatonta shakiyyancine kawai irin na zaks, suka shige cikin dakin big hajiya da nabeelah. Aeezad ya kalli Zaks yace “Kai zanci kutmar ubanka fa in kana hadawa da iyalina a iskancinka…” Zaks yayi dariya yace “da girman kujerarka dawisu me mulkin mallaka,,,sannu Mijin mommy kuma mahaifin mommy kuma mahaifiyar mommy, sannu waliyyin mommy shugaban yan iskan duniya, me ciki bakwai…” Aeezad ya kwashe da dariya hadi da watsoma zaks wani gangariyar ashariya, Zaks ya kwashe da dariya. Aeezad ya mike yana dariya ya kalli Zaks yace “Dan iska, kaje ka Kira doctor yazo yasamin drip Dina na yau na farajin hannun namin zafi yanzu…” Zaks ya mike hadi dacewa “okay …” yana fadin hkn ya fice , Aeezad ya nufa cikin dakin.

Ranar gabaki daya nabeelah batayi bacci ba, Zaks nan ya kwana a falo, ita kam ko rintsi batai ba, kafin Safiya tayi ta kara fice wa a hayyacinta har Rama tayi, ita banzan jikine da ita, tashin hankalin awa biyu ka seya ramar da ita, ba wani jikine da ita ba kayane na Alatu kawai gareta tako ina , irin kayan da dole in namiji ya ganta hankalinsa ya tashi, ko mace ta kalleta seta tabbatar nabeelah macece ta bugawa a jarida macece wadda ta Riga ta Kama kasa tanada komi da namiji ke bukata a jikin mace. Washe gari da safe Zaks ya bar asibitin zuwa karfe sha biyu hauwa’u tazo, da manyan baskets masu dauke da manyan warmers , abinci ta kawo musu kusan kala biyar da farfesu nau’i daban-daban kala uku, sannan da drink kala uku shima. Dole nabeelah tayi feeding Aeezad badan tanaso ba, hauwa’u na ankare da nabeelah tin zuwanta ta fuskanci tanada damuwa ba haka ta barta ba jiya Gashi bataga alamar wayar da Alhaji sadin ya bata ba, daman hauwa’u tasan za a rina hakan. Bayan nabeelah ta gama bawa Aeezad abincin hauwa’u tayi dabara taja nabeelah waje,. “Kawata Meya Faru daga jiya zuwa yau kinyi fige-fige…” hauwa’u ta tambayi nabeelah bayan sun fito wajen sun kefe gun wata bishiya. Nabeelah tace bakomai..” hauwa’u ta tsareta da tambaya, badan nabeelah taso ba se dan bata da yadda zatayi yasa ta kwashe komi ta sanar da Hauwa’un, bata boye mata komi ba. “Tabdijan!!” Hauwa’u ta fadi tana me jinjina lamarin ita kanta jinta take kmr a mafarki. “Kaddara…” hauwa’u ta fadi a bayyane se kallon nabeelah takeyi. “Wlhi aurennan be dauru ba, tinda ba amincewa ta yayi Auren yaudara dani, kawai danni ba kowa bace zemin haka, dan Ina aiki a kasansu …” nabeelah ta fadi Tana sharar kwallah. Hauwa’u tace “Wallahi kawata Aure ya dauru sede kiyi hkri bade an tara shaidu ba , kuma kmr yadda kikace, har kinji komi a kunnenki sannan A masallacin sultan Bello , masallacin da babban masallaci ne, bazeyu ayi yaudara a dakin Allah ba, wallahi Aure ya dauru, ke da kanki ma kinsani, tinda kinada zurfin karatu a koyarwar Addinin musulunci, dande kawai tashin hankali baze barki ki fahimci hakan bane… kawai kiyi hkri Aunty nabeelah komi kaddara ce, ki duba kiga mazan dasuka dinga nemanki kikaqi Aurensu, wannan fa duk a cikin zanen kaddararki ce, Ubangiji ya riga yace Aeezad ne ze aureki…” nabeelah ta kara fashewa da kuka tana fadin “Wallahi be isa ba, wlhi ban yarda da wannan Auren ba, musulunci bece ayi zalinci ba…na raine shi da hannuna in auresa in me dashi, wlhi nafi karfin aurensa, karya ne be Aureni ba, ban amince ba…” nabeelah ta fadi Tana me kuka kmr ranta ze fita, ta dinga sharewa da gefen hijjabinta. Hauwa’u ta dinga bata baki dan ta kula bata hayyacinta, tadinga rarrashinta, ita kanta hauwa’u tashin hankalin datake ciki baze misaltuba tabbas A wannan Lagon Aeezad yayi gaggawa kuma bema nabeelah adalci ba, shide kawai yabi San zuciyarsa ne da San ransa, a wata siffar kuma hauwa’u ta dauki hakan kaddara ce, kuma duk bawa be isa ya kaucewa kaddararsa ba, amma fa akwai babban wasa a gaba, akwai kalu bale masu yawa, hauwa’u ce kawai tasan meke kasan ranta ta tabbatar akwai babbar matsala. Ranar ma Haka hauwa’u ta wuni asibitin har dare kana nabeelah ta rakota waje , nanma hakuri da ban baki hadi da natseeha akan yadda da kaddara hauwa’u tayitama nabeelah kmr yadda de ta wuni Tana mata natsihar, kawai nabeelah jinta takeyi amma batajin kome za a mata a duniya zata amince da Auren Aeezad a kanta, yaudara kawai ta maida hakan. Hauwa’u ta hau napep ta wuce a zuciyarta tana jinjina lamarin ita kanta abun ya bata tsoro nabeelah ta koma Cikin asibitin Tana kwallah Tana sharewa gabaki daya ta gaji ma da kasar kawai so takeyi taje kasarsu taga mamanta ko zata samu samu sassaucin abinda ke ranta. After 2days tini hawwa’u ta koma katsina.

gabaki daya nabeelah taki sakin jikinta kullum se kuka kawai ko bacci bata samu tayi, big hajiya duk Tasha tausayin ne ke dawainiya da ita har yanzu se natsiha take mata kan tayi hakuri ta cire hkn a ranta. Hankalin Aeezad kam kaf a tashe yake, daya kalleta se hankalinsa ya tashi ganin kukan da take tayi, ga shadin yatsunsa na Marin daya mata har yanzu be baje ba a kan fuskarta, se bata hkri yakeyi yana lallaba, hajiya nashiga toilet seya taso daga inda yake ya iso inda take dan yanzu tadena zama kusa dashi Sam kullum tana rakube a lungu, yayi ta bata hakuri amma Sam taki hakura, ko saurarensa ma bataji, a kwana biyun harshi kansa gogan ya rame, Marin dayayi mata ne kadai yake nadamarsa amma Sam be nadamar Aurenta da yayi, yasan aurenta da yayi ne yasata a damuwar da take ciki, shi kam daya kalleta se yaji ddh,. Ko abinci se hajiya tayi da kyar nabeelah keci. A satin Alhaji Sunusi da hajiya rafi’ah sukaxo hadi da aunty hafsat, jirgi daya suka biyo sukaxo ganin jikin aeezad din. Kallo daya Aunty hafsat tayima nabeelah ta tabbatar Tana Cikin damuwa me tsanani, haka hajiya rafi’ah ma kallo daya ta mata ta fahimci tana da damuwa dadih ya rufe hajiya rafi’ah , Gashi ta fuskanci kwata-kwata nabeelah bata ta Aeezad yanzu kobi ta kansa ma batayi, farin ciki goma da ashirin ya kashe hajiya rafi’ah, ita a zatonta Aikinta ne yaci a kan nabeelah , komawarta katsina tini ta Kai sunan nabeelah gun bokanta tace a raba nabeelah da Aeezad inma asiri tama Aeezad din a karyashi boka yace an gama. Toh zaton hajiya aikin ne yaci a kan nabeelah. Tini Hajiyah ta fita waje ta kira yarta dake Egypt , tanaso ta dawo amma uwar ta hana itade hankalinta na kan mijinta uwarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login