Showing 42001 words to 45000 words out of 171731 words
Chapter 15 - Namijin Zuma Book 2 Hausa Novel Complete
Aeezad ya nemi Transfer zuwa Asibitin 44 dake kaduna, saboda Sam bayason zama a asibitin Aminu kanon sannan bayason komawa katsina saboda wata manufa dake ransa. Karfe shida na yamma zaune suke dukkaninsu a dakin da Aeezad din yake, yanzu ana barin kowa a cikin dakin sbda jikin nasa da sauki, sede kullum ana masa Allurorin saboda matsalar hannunsa. "Kaida na'eema zaku kadunan gobe kou da big hajiya ? Su zasuyi jinyarka..." Cewar Alhaji Sunusi dake zaune Yana facing Aeezad, jin abinda yace yasa Aeezad hade Rai ya saci kallon fuskar AUNTY nabeelah wadda ke kasa zaune kan carpet. "Wace na'eema??' hajiya rafi'ah ta amshe cikin tsiwa tana kallon mijinta dayayi maganar fuskarta dauke da buhu buhun rashin mutunci. "Wace na'eema kika sani bayan matarsa,,, ke kiji tambayar rashin tarbiya..." Cewar hajiya bilkisu data amshe maganar, Alhaji sunusi de yayi Shiru bece komi ba. Yatsina fuska hajiya rafi'ah tayi ta kalli hajiya bilkisu ta watsar kana tace "gaskiya bazata iya jinya ba, saboda itama ba lafiya ce da ita ba neman me jinyarta takeyi ynzu haka, ita inama zata iya wahalar jinya...." Na'eema tayi saurin amshewa da "Aah mommy zan iya wallahi..." hajiya rafi'ah ta gwabeta dacewa "Ke dallah gafara can ,a gidan ubanki zaki iya, kina fama da uban jiki kamar jakar kauye, tayaya zaki iya Wani jinya? Wannan kibar taki ta asara ke kanki ai neman me jinyarki kikeyi, kina motsi da kyar kmr mesa ta hadiye mutum... bazata iya ba wlhi sede ke hajiyar da danginku kuyi jinyar jikan naki, in rashin mutumci ne kowa ma ya iyasa ai..." ta karashe mgnr tana kallon hajiya bilkisu a wulakance. Wani irin bacin rai kalaman Rafiah ya haifarwa da Alhaji sunusi a zuciya, shi ya rasa gane kan gadon me rafi'ah take nufi ne, ada be gane ba Amma yanzu ya gane akwai kiyayyar jininsa a jinin rafi'ah, mamaki da zallar madarar bakin ciki suka kuma cika Alhaji Sunusi, ya kure hajiya rafi'ah da idanuwansa dake cike da bacin ranta dande beda yadda zeyi ne kawai, zamansu a asibitin Nan shi kadai yasan yawan bakin cikinta daya kunsa, gashi yau wai itace kecewa na'eema bazata iya jinyar jininsa ba, Aiko ba aure a tsananin na'eema da Aeezad a tunanin Alhaji sunusi na'eema me jinyar d'ansa ne, kai bama Na'eema ba, ko ita hajiya rafi'ah yaci ace ta tsaya tayi jinyar jininsa meye be mata ba a rayuwa, kaf danginta shine gatansu, cinsu suturar su duk a hannunsa yake, uwa uba ya rike mata yarta ya bata kulawa ta isilamiyya da boko, ya bata tarbiya ya bata komi take bukata a duniya fin yaran Daya haifa da cikinsa abinda yayima na'eema wlhi ko Aeezad mafi soyuwa a ransa bemasa ba. "Hmmm mutum kenan butulu, a maka rana ka tura mutun dare me tsananin duhu...insha Allahu a barmin shi ni kadai na isa zanyi jinyarsa babu abinda ze gagareni na godewa Allah ma da nake raye, insha Allah ba abinda ze gagareni Saniya bata gazawa da k'ahonta...." Cewar hajiya bilkisu dataketa mamakin hali irin na Rafi'ah ita tako ina ba inda za ace Kwara a halinta, ga rashin wayau, ga rashin kunya ga rashin tarbiya, ga uwa uba jahilci, babban abinda yafi damun hajiya rafi'ah shine rashin wayau, ga rashin iya magana Amma ita a ganinta tafi kowa iya magana,. Se yau hajiya bilkisu ta kara tabbatar da hajiya rafi'ah wawiya ce, sbda yadda ta Hana na'eema jinyar mijinta alhalin ita yarinyar tanaso tayi jinyar mijinta,. A bangaren Aeezad Sam Ko a jikinsa shi sema dadih dayaji, shi kadai yasan dalilin jin dadinsa, kawai hakan dasukayi ya masa dai-dai. Zakariyya wato Zaks ya zubawa hajiya rafi'ah Ido a ransa Yana Kara jinjinawa rashin mutunci irin na hajiya rafi'ah da rashin wayau. "Tashi mu tafi Dan ubanki daddawa uwar miji Nan kina ganin irin cin mutumcin da Akamin a family dinnan, har dukana karamin yaro yasoyi ammma ba a masa komi ba, a haka sbda bakisan darajar uwarki ba kike cewa zaki zauna Kiyi jinyarsa bayan a kansa, Nan ba irin zagin da ba ayimin ba,..." Cewar hajiya rafi'ah datayi mgnr byn ta tashi tsaye ta hambari na'eema da maganganganu dole na'eema ta tashi tana turo baki a zahiri wlhi tafiso tayi jinyar mijinta da kanta saboda bata kaunar taga Nabeelah na rabar mata miji. Kaf kowa na dakin ya zubowa Hajiya rafi'ah Ido da na'eema nabeelah Kam a ranta se kara mamakin hajiya rafi'ah takeyi ganin yadda ko a asibiti ma bata sassautawa mugun hali irin nata ba, hakan ya bawa nabeelah tabbacin da wuya hajiya rafi'ah ta shiryu kila seta jita a kabari. Hajiya bilkisu ta jefi rafi'ah da harara kawai takiyin mgna sbda intayi mgnar abun baze musu kyau ba, Sam shi Aeezad beyi mamakin komi ba yasan hajiyar Rafi'ah ba hankali ne da ita ba zata aikata fin hakanma. "Kai kuma gobe inka shirya mu tafi gida toh kase mana fly da wuri kaji na gaya maka..." Tayi mgnr da Alhaji sunusi kamar Wani d'anta. "Toh shikenan..." Alhajin sunusi ya fadi jiki na rawa, inda sabo duk sun saba gani ita kanta hajiya bilkisu ba sabon Abu bane a gunta ,tini tasan aikin asiri ne, domin inba asiri wane mutum, Adduarh ce kawai maganin wannann matsifa na hajiya rafi'ah. zaks Kam Sabon abun ya zamar masa Dan haka ya saki baki kawai Abu kamar acting din film, ba value taki ina. Hajiya rafi'ah na gama fadar hakan ta juya ta fice a dakin da wata matsiyaciyar bag a hammatarta Tasha danyar shadda da mayafi Sam ko swag dinma bata iyaba, har yanzu ruwan bariki be saki hajiya rafi'ah ne, suka fice a dakin yayinda hannu na'eema ke cikin nata, bayan sun fito daga dakin na'eema ta kwace hannunta daga cikin na hajiyar Rafi'ah tana fadin. "Ke komi sekinyi abinda be kamata ba hajiya mommy,,,," "Dan Uwarki da ubanki me nayi dabe dace ba? Shigiya se kibar banza da hofi ba wayau yanci na kwantar miki Amma kike neman min rashin kunyarki da kika saba Yar iska kawai mara tarbiya..." Na'eema ta kara hade lukutar fuskarnan tata wadda ke cike da uwar namomi me tattare da tarin lagwad'ar kitse da kyar Ake ganin kwayoyin idanuwanta sbda azabar kibarta tace "Wani yanci kenan Mommy? Ko kuma de kinaso ki kasheni da raina ba ta hanyar sanya kusanci tsakanin Aeezad dina da waccan ballagazar me Idanuwan karuwai Nabeelah..." "Dallah gafara can, sakarai, Kinga matsalar rashin wayau kou? Inta samu kusanci dashi se ayi y'ay'a?"' cewar hajiya rafi'ah. "Se ya fara santa mana mommy, bakiga yadda yaketa nannan da ita ba kamar ya maidata ciki fa hajiya mommy wlhi ji nakeyi daman inada hali in kashe ta Tsinanniya ta tsufa a gida ta kasa auruwa sbda karuwanfi..." Na'eema ta karashe mgnr a zafafe kishin nabeelah a zuciyarta kmr ze faso ya fito fili. Kallon banza hajiya rafi'ah tabita dashi kana tace "ta yaro kyau take bata karko... Ke yanzu a zatonki a duniyar Nan akwai macen dazata iya Gwafzawa dake a fagenki da AEEEZAD, na miki alqawari har abadan ke kadai zaki rayu da Aeezad, keda kishiya sede ta waje..." "ta waje kuma mommy? Wace irin ta waje? Niko ta wajemma ai banso..." cewar na'eema data amshe a zafafe, bakin kishi nacinta. "ai keda ta wajenma har abadan, ke kadai zakiyita shawagi a gidan Aeezad , ki kwantar da hankalinki diyata..." "Hankalina baze kwanta ba saboda nabeelah, hajiya mommy abinda Aeezad keyima tsinanniyar me kod'adadiyar fatarnan, wlhi mommy bnsanta kwata-kwata.." cewar na'eema. "Ai ita bata isa Aeezad ya mata Wani duba ba, bayan name masa hidima, mema zeyi da ita, bayan ita ta renesa, ke wannan fa dagani ta girmeni ma kawai Dan kyau ne da ita,,, sannan inaga asirine ta masa na amsar kudi kinsan su yan niger dinnan da asirin tsiya ga kwad'ayin kudi, can uwarta zata bugo mata asiri sbda su samu rabonsu, Insha Allahu shima asirin sena karyasa,wuyarta de in koma katsina....." (haka Ake mana sharrirrika ace mana masu asiri , ace mana masu mallake miji, ace mana Yan iska, insha Allahu se Allah ya saka mana)
Nan na'eema ta danji zuciyarta ta natsa ,a fari ta tsorata ganin yadda Aeezad kema nabeelah, ko Rabin zakuwar da yakeyi a kan nabeelah ita Sam baya mata ko kwata. Suka isa mota na'eema tajasu zuwa hotel din dasuke kwana, daman tinda sukazo da 4days na'eema ke jansu a mota, motar Aeezad ce da ita dreva dinsa ya dakko na'eema ranar datazo garin.
Bayan fitar hajiya rafi'ah da na'eema. Alhaji sunusi ya kalli nabeelah yace "to ynzu yadda za ayi hajiya bazaki iya jinyar Aeezad ke kadai ba sede ku zauna keda Nabeelah..." "Ko baka ce ba Daman plan dina kenan..."Aeezad ya fadi a ransa a zahiri se murmushi yakeyi Yana kallon Nabeelah itama dagowa tayi ta kallesa taga Yana murmushi daman tasan haka yakeso Amma ita Sam batason hakanba saboda bata kaunar kusancinta dashi, sbda a kullum cikin gaya mata kalaman soyayya yake, ita Kuma Sam bataso, gashi yanzu ita zatayi jinyarsa, dole tace ita zatayi jinyarsa sbda tasan de Hajiya bilkisu ba komai zata iya ba, wanka kawai hajiyar ke temaka masa yayi, gata da bacci sosai gata da nauyin bacci, gashi a zaune ma bacci takeyi, ta tabbatar in Aeezad be ganin Idanuwan jama'ah abinda ze mata seya shallake tunaninta. "Eh Hakan yayi, wannan yarinya akwaita da juriya da hakuri, Allah de ya mata albarka, ya bata miji na gari..." Cewar hajiya bilkisu datayi mgnr tana kallon Nabeelah dake zaune kasa ta sadda kanta kasa, ba karamin kaunarta hajiya bilkisu keyi ba saboda nutsuwarta da kamun kanta. "Amin ya Allah..." Daddy da Aeezad da Zaks suka amsa, Aeezad shi kadai yasan me yake ayyanawa a ransa da Addu'ah hajiya kaka ga Nabeelah ta karshe.
Washe gari da asubar fari, jirgin Aeezad da hajiya bilkisu da nabeelah ya daga zuwa kaduna. A bangaren Alhaji sunusi da hajiya rafi'ah da na'eema seda sukaga tashinsu Aeezad a jirgin kana suka hau Nasu jirgin zuwa garin katsina, tin a jirgin hajkya rafi'ah ta fara kartawa Alhaji sunusi rashin mutumci khusfa-khusfa, ta zagesa tass bece komi ba se hkri kawai yake basa,. Seda na'eema tayima hajiya rafi'ah magana a kan tayi hkri sbda itama daddyn ya bata tausayi daman itafa duk abinda hajiya mommy kema daddy na wulakanci ba a San ranta ba , ita na'eema da ace ba hajiya rafi'ah da bata da nakasu, koda tanadashi to kadan ne, kuma saituwarta bazeyi whla ba. Amemakon da na'eema tama hajiya rafi'ah magana ta sasautawa daddy da rashin mutuncin da take masa Amma ina sema ta hada da na'eema ta kama musu fada,danma Allah yasa su kadai ne a cikin jirgin daba karamin abin kunya rafi'ah zata ja musu ba, Kila dasede su tsinci lamarin a gidan Tv, a haka ma ya aka Kare kowa na duniya dayasan sunusi Ahamad yasan mijin tace ne a gidansa, se abinda hajiya mommy tace yakeyi. Har suka isa garin katsina hajiya na yayyafawa Alhaji ruwan matsifa a kan wai danginsa sun wulakantata a gabansa yayi Shiru sbda besan darajarta ba, haka de ta dinga wankesa da fada, kai yaude harda zagi ta uwa ta uba, har kwallah seda na'eema tayi sbda zafin abinda tama daddy a gabanta ya matukar konawa na'eema Rai.
**
Kaduna.
Asibitin 44, asibiti ne me girma da manyan likitoci, asibitin ainihinsa na sojoji ne , Da kuma masu hannu da shuni duba da irin gyaran da akama asibitin yanzu Hadi da kwararrun Likitoci na musammanma da aka zuba da manyan sojoji, Sam Asibitin bana zuwan talaka bane.
Wani irin daki aka bawa Aeezad na alfarma, special inda abinda yafi special ma dakin ya Kai, daki Dayane ne dauke da manyan falo guda biyu, daki Dayan gadaje biyune a ciki Daya na mara lafiya Dayan name jinya, ga AC tako ina ga fanka again, ga frij, an zuba komi de na more rayuwa Kai bakace asibiti bane, zakasha ko wata aljannarh duniyar kake. Tinda suka dawo garin mutane ke ziryar zuwa gaida Aeezad din Amma fa wadanda aka yadda dasu, Nan dinma an cikasa da matakan tsaro tako ina sojojine da red eyes da manyan bindigu. Kwanansu hudu baki na zirya, aunty hafsat da mijinta ma sunzo sun kara duba jikin, a ranar suka koma garin katsina kasancewar jirgi sukabi sukaxo, Zaks Kam kwanansa uku daya biyo su Aeezad ya koma garin Kano. Alhaji sadi ma yazo sbda nabeelah, Sam shi besanma zasu dawo kaduna ba seda yaje akace masa an sallamesu zuwa asibitin 44, shine ya biyo nabeelah domin yasamu daman gaya mata ciwon dake zuciyarsa,. Yau dayazo, bayan ya gama gaida Aeezad da jiki, ya amsa da kyar sbda ya kula da yadda yaketa zuwa tin a kanon gashi se kallon nabeelah yakeyi gabaki daya Aeezad ya tsani Alhaji sadi. Alhaji sadi yayi sallama ze tafi yace Nabeelah ta biyoshi waje yanason yayi magana da ita,. A fari nabeelah tayi kmr bata jiba seda hajiyar bilksu ta mata magana kana ta mike ta bisa wajen tana kallon irin kallon da Aeezad ke Aiko mata dashi na rashin mutumci. Seda suka iso bakin motarsa kana Alhaji sadi ya shaidawa nabeelah irin San da yake mata tinda yafara ganinta har zuwa yau, kuma ya sanar da ita shi San Aure yake mata, sannan bayason Aurensu yaja lokaci, kana ya tambayeta meye ra'ayinta. nabeelah tayi Jim tana kallon Alhaji sadi tabbas yakwanta mata a Rai tin randa ta fara ganinsa itama, sbda shidin dogon namiji ne, uwa uba gashi yanada shekarun dagakeso a jikin namiji. "Se nayi shawaraa...." Itace amsar da nabeelah ta bawa Alhaji sadi. "Toh shikenan ba damuwa...yanzu kamar yaushe zaki gama shawarar, kinada waya?'' nabeelah ta daga masa Kai alamar Eh tace "Amma wayar na katsina
.." "okay gobe zan siyo miki wata wayar insha Allahu Samsung kkeso ko I phone?'' Alhaji sadi ya tambayeta se Wani rawar kafa yakeyi. "Aah ka barshi inada waya..."cewar Nabeelah da Sam ita bata saba amsar abun hannun saurayi ba. Murmushi alhaji sadi yayi ya kara yarda da tarbiyar yarinyar sannan yanzu dasuka tsaya daf-daf ya tabbatar Karya baban Noor ke masa dayace masa ita ba yarinya bace, a idanuwansa danya shataf yake kallo ko a maganarta akwai yarinta a ciki,. Da haka sukayi sallahma da niyar ze dawo gobe ko jibi, yashiga mota takoma ciki. Tana shigowa Aeezad ya jefeta da Wani irin mugun kallo yayinda Nan da nan taga ya hade Rai mugun kishi ya turniketa, sbda bakar zuciya ma ya gaza cewa komi, ji yakeyi kmr ya tashi ya rufeta da duka. "Yaro Dan Arziki meya ce miki ne halan?'' cewar hajiya bilkisu. Nabeelah data kalli Aeezad kana ta dawo da dubanta kan big hajiya tace "Sako ya gayamin yace in bawa baban Noor .." hajiya bilkisu tace "Auuu nashama koyace yana ciki ne dana miki murna, yaro d'an Arziki dubafa kiga yadda ya cika ko ina da abubuwan dubiya, yayi mana Sha tara ta Arziki harda manyan kudade..."nabeelah de tayi shiru ta kasa cewa komi sbda uban kallon da Aeezad ke Aiko mata dashi. Bayan hajiya taje alwalar magrib, Aeezad ya tsare nabeelah da tambaya kan me Alhaji sadi yace mata dasuka fita waje, Nabeelah ta hade Rai tace "Sako ya bani yace in bawa baban Noor, ubana..." Kallon ta raina masa hankali Aeezad yabita dashi yace "Shi besan inda ake aika Sako ba seta ke, Basu da waya ne shida baban noor din ?'' nabeelah ta masa shiru, Nan ya shiga matsifa cikin kunci da bacin rai kmr ze rufeta da duka, ko ince kmr yarsa "kawai kinmin karya Mommy, ni zaki mayar yaron goye,,,sekinyi nadamar karyarnan da kikamin wlhi nan bada jimawa ba, sekin sani!.." Nabeelah ta zuba masa Ido kawai tana mamakin wai yau itace Aeezad kema rashin kunya haka, harda ce mata ta masa karya mamaki kawai lamuran Aeezad ke bawa Aunty nabeelah yanzu, gabaki daya batasan meyasa aeezad ya rainata har haka ba, ga azabar kishinta tana gani a cikin idanuwansa. Ranar kwana yayi Yana fushi da ita. Bayan kwana biyu Aeezad yace kar a bar kowa ya shigo gaidasa, nabeelah nata zuba Ido taga Alhaji sadi taji shiru, haka kawai tunanin Alhaji sadin ya addabi ruhinta, ta farajin wasu yanayoyi a kansa. Bayan 5days, da daddare misalin Sha biyu da mintuna na dare, tini hajiya ta baje se bacci takeyi a kan gadon masu jinya, yayinda Nabeelah ke zaune kan Kujera kusa da godon Aeezad Ta daura kanta a gefen gadon nasa, sam batasanma bacci ya dauketaba hannunta na kan cinyarsa batasanma ta daura hannunta kan cinyarsa ba, shikam idanuwansa biyu Sam be runtsa ba tinda ta daura hannunta a kan cinyarsa yaji gabansa ya tashi ya mike zumbur, shifa Daya ganta seya dingajin kamar Wani abu na jawosa zuwa gareta, tsigar jikinsa se yayita mikewa. ya kure face dinta da ido kmr maye yayinda santa ke ninkuwa a zuciyarsa, yanaji hatta da ransa ze iya badawa a kanta, San da yake mata bayajin a duniyar Nan akwai halittar data tabawa wata halitta irin wannan San in Yana ganinta har heart beat dinsa chanzawa yakeyi yadinga bugu da karfi. Tattaba hannunta yashiga Yi, kasancewar bata da nauyin bacci tayi firgigit ta tashi idanuwanta suka sauka cikin nasa Idanuwan dake kanta na jaraba. "Kyaunki nada kyau mommyna,,,..wlhi ina sanki Saboda Allah!." Ya fadi Yana me kara kureta da ido shi kullum kara masa kyau takeyi. Juyawa nabeelah tayi ta kalli hajiya taga se bacci takeyi kana ta dawo garesa ta fara mgna a hankali "Meyasa har yanzu bazaka natsar da harshenka na rashin kunya ba a kaina...kwata kwata ka rainani ka manta ni na