Showing 93001 words to 96000 words out of 171731 words

Chapter 32 - Namijin Zuma Book 2 Hausa Novel Complete

koya mata hankali, bade bata dauki Aurena a bakin komi ba Dani kaina, yau zan nuna miki Aurenki nakeyi wlhi! Ko dan kinga na barki a banza ban miki abinda ze nuna Miki ni mijinki bane kou?” Ya karashe da zafin zuciyata ya kwace hannunsa daga rikon da Zaks ya masa ya fisgota, takalman kafafuwanta suka cire sbda janta dayayi da karfi, nan take ta Taka wata yar kwalba abinka da farar mace kuma kafarta nada Azabar laushi, nan Kwalbar ta fasa cikin kafafuwanta tashige , nabeelah ta fasa wani irin ihu Sam Aeezad bebi ta kanta ba, ya kara jawota kiiiiiiiiii! kafarta na zubar da jini amma Sam be Lura ba shima Zaks be kula ba, a haka yana jawota harya karaso da ita bakin kofar motarsa ya jefata baya, se ihu takeyi Aeezad yasha zallar iskanci ne da wulakanci yasata ihun dan hk bebi ta kanta ba yashiga gaban motar, zaks yashiga ba bata lokaci yaja motar Aeezad ya kafa ruwan matsifa da bala’i. “Baki daukeni a bakin komiba Dani da Aurena dake kanki,Ina kallankine kawai nabeelah, nasan a bnza kk kallona, kawai sbda kin raine ni, bafa kaina ko kanki aka fara Aure mace ta girmi namiji ba, wlhi tinda bake kk haifanba sena nuna Miki waye ni meye matsayin Aurena a kanki yau….ka kaini sabon gidana, wlhi yau sena nuna ma nabeelah ni cikakken namiji ne nafi gaban raini….” Aeezad ya karashe mgnr yana kallon Zaks sbda matsifa duk kamanni Aeezad din ya chanza. “Toh …” Zaks ya amsa da sauri, gudun kar yayi Lefi a dawo kansa. nabeelah ta kara fashewa da kuka jin yace a wuce da ita gidansa , cikin kukan take cewa “wlhi bazanje gidanka ba dan iska kawai, sena nuna maka na girmeki, bazan dauki raininka ba,,,banasanka!” Aeezad ne ya iya fahimtar me take cewa amma Sam Zaks be fahimta ba sbda kuka ya shake mata wuya sosai. Bakin cikin kalmar datace bata sanshi ya kara harzuka Aeezad a kanta, dabadan karfin San da yake mata ba tabbas babu abinda ze Hana ya rufeta da danbura uban duka yanzunnan, ji yakeyi kome ya mata ma be huce ba. , da kyakyawar hannunta data zama mallakinsa ta dauka ta taba wani namiji dashi kuma a gaban idanuwansa, wannan abu yaci masa zuciya. Be kara cewa komi ba sbda bakin ciki har suka isa katafaren gidan nasa. , sabone dal haka komi na cikin gidan sabo ne , tin daga kofar get din gidan abin kallo ne, gidan zagaye yake da matakan tsaro, duk wani gidansa zagaye yake da mata kan tsaro musammanma gidannan nasa yafi kowanne gidansa kyau, yana tsananin ji da gidan tinda ya fara San Aunty nabeelah yasa aka gina gidan dasunan nan zasu zauna kawai be sanar da kowa ba ko Zaks be sani ba kawai de yasan gidan nasa tin ana gininsa, kafin aka gama komi na gidan sabone fil daga waje akayi order dinsu. Ko packing din kirki Zaks be gamayiba Aeezad ya fito daga cikin motar, ba tare da Zaks din yayi packing ba shima yayi sauri ya fito Aeezad na kokarin bude inda nabeelah take Zaks ya dakatar dashi dacewa “dan Allah aboki kayi hkri ka daure ka dai-daita zuciyarka aboki, karka mari mommy pls ko ba komi ita ta raineka, inka mareta zataga kmr dan Tana karkashinku ne yasa all this, last time ka mareta kayi nadama daga baya kuma, pls this time karka mareta , Annabi bece mu dinga dukan iyalinmu ba kmr yaranmu…” Zaks yayi masa mgna cikin sanyi, Aeezad yayi kmr bejisa ba , ya bude inda nabeelah take cikin zafin zuciya ya kara jawota kiiiii kmr tsohuwar mota , sam Aeezad beda control da zuciyarsa inta baci. Dole zaks seda ya dawo tausan mommy dukda tanada lefi. Nabeelah se kuka takeyi , tasake fashewa da wani kuka, saboda jan da Aeezad din yayi mata a kasa, ta Taka kafarta wadda ta kumbure tayi suntum har yanzu zubar da jini takeyi, ta kurma wani irin ihu Tana fadin kafana!! Amma ina Aeezad be fahimci me take cewa ba hk shima Zaks din dake biye dasu a baya be fahimta ba. Yana isa kofar dazata Sada shi da gidan yasa yatsanshi kofar ta bude, still yana jaye da ita har suka iso tsakiyar falon babban katafaren gidan “Aljannarh duniya…” Zaks ya fadi a ransa yana karewa falon kallo komi na falon Onion color ne light and dark. Suna isowa tsakiyar falon dai-dai kan carpet din dake tsakiyar falon ya watsar da Aunty nabeelah kmr kaya, ta fadi kwance kasan falon , Bom-Bom dinta ya matukar amsa sbda ta baya ta fadi ta kuma fashewa da kuka. “Da hannunki kike taba wani namiji daba muharraminki ba…” ya fadi cikin zafin zuciya yana kallon Aunty nabeelah dake kwance Tana kuka duk tabi ta zama abar tausayi a lokaci kankani har wani zazzabi taji ya rufeta ruf, zafin kafarta se ratsata yakeyi. “ ba wanda ze hanan na zaneki mommy , bakin Cikin da kika samin a zuciyata baze misaltuba mommy dole sena zaneki wlhi…” Aeezad ya fadi cikin zallar bakin ciki, ya dagota ze yaye mata hijjabin jikinta ta rike hijjabin, gam sbda ba komi inside ko pant babu. Aeezad yaga fararen cinyoyinta sun bayyana, dukda a cikin matsifa yake amma seda yawu ya cika masa baki na zallar shaawarta, yayi hanzari ya rufe inda ya yaye sbda Zaks dake tsaye, aeezad yasa kansa ta kasan hijjabim nata nan take yaga zindir take bakomi jikinta. “Kai! Wato haka kika fito gun d’ana miji tsirara, ba kaya, sbda jarabar san maza na damunki…!” Ya fadi a bayyane, yadda yayi mgnr ita kadai taji Zaks dake tsaye yana basa hkri beji komi ba, , nan ran Aeezad ya kuma baci. Bece komi ba ya mike zuciya a harzuke ya isa gaban TV daya mamaye bangon dakin yana fadin “ wlhi kin kara jama kanki mommy, sena zaneki yau mommy,,,duk duniya banga wanda ya isa ya hanani na zaneki ba yau mommy…Kai dole na zaneki wlhi mommy!…” ya karashe yana lumsar idanuwa zuciyarsa na tafarfasa, ya fisgo wayar connecting din TV din wato igiyar TV din. Zaks dake tsaye ya zubo masa ido shi mgnar tazama dariya ta basa da haushi wai ze zaneta kmr wani ubanta. Ya juyo a fusace Zaks yaga ba yadda ze hanasa ya daki mommy kuma gaskiya beso ya daketa sbda shi knsa seya dawo yayi nadama. “Pls aboki kayi hkri dan Allah …” Cewar Zaks , ina Sam Aeezad bebi ta cewarsa ba, idanuwansa sun rufe ruf ya biyewa dokin zuciya. Ya daga wayar ze zuba mata nabeelah ta rintse idanuwa sbda tsoro, har tajiyo zafin bulalan a jikinta dukda bata iso jikin nata ba, ta fasa ihu. dai-dai ze zuba mata bulalar idanuwansa suka sauka a kan kafarta data Taka kwalbar wadda jini keta zubowa har lokacin ta kumbura a lokaci kankani ta kusa biyun dayar kafar me lafiya, kasancewar kwalbar ta shige jikinta duka, a memakon ya zuba mata bulalar seya zubawa kansa ya wurgar da bulalar gefe daya ya karasa kan kafar tata a guje, ya dagokafar tata da hannunsa me lafiya , yaga yadda kwalbar ta shige cike se kadan yake hangouta shima seda ya goge bakin gurin inda jini keta bulbula da hannunsa. Me kika taka a kafarki? Meye wannan? Jini har haka,,,meya Samarmin kafarki mommyna,…” ya fadi a rikice yana dauke idanuwansa a kan kafar tata sbda ji yayi tin daga zuciyarsa yake jiyo zafin datakeji na Kafar a jikinta. Nabeelah ta bude idanuwanta ta zubo masa su kmr me iska taga kuma duk yashiga taitayinsa yanzu-yanzu, mamaki yake bata guy dinnan yanzu kmr mahaukaci beda maraba da mahaukaci, itafa tasha dukan ze mata kuma seta tsincesa yana sambatu. “A ina kika Taka wannan tsinanniyar kwalbar? A ina kika takata? A gidannan ne ko a gidan Aunty hafsat? Amma ba karamin zafi kkeji ba mommy….sannu mommy, Nima inajin zafin a zuciyata, sannu mommyna, sannu kinji zaks zoka gani Zaks mommy ta taka wata kwalba ta shige kafarta, zoka ga yadda kafar mommy ta kumbura…zoka gani…” yashiga fadi a haukace yakai harshensa ya lashi dai-dai inda jinin ke zubowa a kafarta, nabeelah ta tsuresa da idanuwa yadda ya lashi kafar tata ya bata mamaki ko tsoron cuta bayayi, kuma ya hadiye Jinnin daya laso zuwa cikinsa, ba itaba harshi Zaks yayi mamaki, zaks ya kara tabbatar da komi Aeezad na iyayi a kan mommy, ashe kalamansa ba iya baki suke ba,? Se yau Zaks ya tabbatar da duk kalaman bakin Aeezad tabbas ze iya aikata komi ya fadi a kn mommy. Karasowa Zaks yayi ya tsugunno yaga tadda kafar tata taketa kara kumbura shima ya tsorata sosai daganin yadda kafar keta hauhawa. “Subhanallahi sannu mommy, amma a ina kika taka kwalbarnan mommy?” Nabeelah tayi shiru ba tare datace komi ba se kwallah kawai takeyi na zallar azabar zafin dake ratsa kafarta zuwa duk jikinta, duk Aeezad ne yaja mata, shi ya jawota ta taka kwalbar. “Kagani kou? Zaks wlhi Zafi takeji sosai, diba kaga yadda taketa kuka, wlhi zafi takeji na ratsata sannu mommy,,,bari in hura miki..” Aeezad ya kara fadi duk yabi ya rikice nan yashiga hura mata gurin da bakinsa. “Sannu mommy… inaga kwalbar na ciki ne ko Aeezad naga kafar nata kara kumbura?” Aeezad daya sunkuya se faman hura mata kafar da bakinsa yakeyi yace “A, kwalbar na ciki, yanzu yazanyi Zaks? Wlhi har cikin zuciyata nakejin zafin datakeji a kafarnan tata… yanzu yaxanyi?” ya fadi yayinda kwallah suka ciko masa idanuwa amma basu zubo ba, se faman hura mata kafar yakeyi da bakinsa. “Dole fa se an cire kwallar inba haka ba kafar zatayi ta kumburi ne…” Cewar zaks.




Am sorry sekun jini da next page insha Allahu.

Manyan mata adingayi ana gyaran kayan oga, 08101626484 is only chart, ko kin kira kashe take in zakise magani zaki iya kirana ta wannan lambar, amma pls masu siyan book Karki kirani kawai ku dubani a chart dan Allah masoyana ina kaunarku more… call 07034685493.

Saadatubintuabdullahi💖

R…32..and..O..33.

*Dan Allah dan zatin Annabi SAW, masu fitarmin da book ku Dena dan Allah badan niba, ku duba kuga mutanen dasuka siya da kudinsu, kunga ko Allah be sakaminba dole ya sakawa sauran dasuka siya da kudinsu, kuma Amanace, duk wanda yaci amana se Amana ta cisa Alfarmar Annabi SAW, masu karanta na sata kuyi hkri ku siya Dan Allah nasan kuna San Book Dina, ku nunamin San ta hanyar siya bata hanyar karanta na sata ba pls….. dubu daya zaki biya ki karanta a salama 08101626484 only chart, in zaki se maganin mata ne is Allow ki kirani ngde, Ina kaunarku masoyana da masu zagina duk ina sanku ngde*

“Tayaya za a cire? Bakaga tanajin zafi bane?” Aeezad yayi mgnar yayin da yakema Zaks kallon mahaukaci, yaci gaba da hura mata kafar da iskar bakinsa. Zaks yace “Se an cire fa dole aboki, rashin cirewar ne yasa kafar ke kumburi sosai sannan shiyasa yake mata zafi sosai….kayi try ka cire mata…” Aeezad da idanuwansa keta kara cikowa da kwallah na tausanta, amma yaki bari yayi kwallar zuwa kuncinsa. nabeelah kam se hawaye takeyi zuwa yanzu ko kukanma tadenayi. Ya kalli Zaks yace “wlhi bazan iya cire mata ba,,,bakaga zafi takeji ba sosai..” Aeezad yayi mgnr da raunin murya. Zaks yayi shiru yanaso yace ya bari shi ya cire mata amma yana tsoro sbda yasan hakan bame yuwa bane, kishin Aeezad ya baci baze yadda Zaks ya taba mata kafa ba. “A ina kika Taka kwalbarnan mommy?” Aeezad ya sake tambayarta duk a kid’ime yake. Nabeelah ta watso masa wata uwar harara, haka kawai taji haushinsa ya rufeta, tunawa datayi da wulakancin dayayi mata wai harda ze zaneta kamar ubanta, ko ubanta tasan baze mulkata yadda Aeezad ke mulkata ba, ya maidata yar iska ba abinda yafi tsaya mata a rai kmr yadda ya jawota kiiiii , kmr wata mara lasisi, shine sanadin wannan azabar da takeji a kafarta, nabeelah batasan abinda ze taba mata jiki kwata-kwata,. Ganin irin hararar daya watso masa ya bashi tabbacin shine silar Jin ciwon nata, nan y tuna da irin Jan daya dinga mata , se yanzu yaji duk haushin kansa ya rufesa. “I’m really sorry mommy, I don’t mean to hurt you, Dan Allah kiyi hakuri, ke kika batamin rai, ta yaya zaki fito tadi kuma bayan Kinsan da Aurena a kanki, ke kika tunzurani, amma kiyi hkri ni na yafe miki ma, kuma nasan nine nasa kika taka kwalbar ko?, wlhi bazan yafewa kaina ba, Zaks nine nasa ta taka kwalbar…amma dukse naci uwar uban masu sharan gidannan da masu sharar gidan Aunty hafsat, meye aikinsu dazasu bar kwalba a tsakar gida, gashinan mommy ta taka, yanzu ya akeso nayi fisabilillahi?” Aeezad ya fadi cikin sambatu Kai kace ciwon jikinsa yake, ko a jikinsa ciwon yake bazeyi abinda yakeyi yanzu ba, se ya juyo ya kalli Zaks ya dawo ya kalli mommy ya dawo ya kalli kafar se ransa ya kuma baci. “Aboki ko a kira doctor tazo ta cire mata? The more kwalbar ke jimawa a jikinta kafarta zatayita kumbura ne kuma ze bata matsala,,,” Cewar Zaks da tunanin hakan ya fado masa rai yanzu. “Doctor mace ko?” Aeezad ya tambayi zaks kishi ya kuma lullube fuskarsa shi a zatonsa ko doctor haphis dasukaxo dashi daga kaduna Zaks ke nufi. “Yeah macece frnd dinace salmah, nagama da nan da gidansu ba nisa….” “Call her, ka gaya mata kwalba ta taka tazo da abubuwan dazata bukata…” Zaks yace okay, ba bata lokaci ya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa, ya lalubo lambar Dr salmah, ringing biyu ta daga, suka gaisa kana Zaks ya shaida mata abinda ke faruwa, salmah tace gatanan zuwa. Zaks ya tura mata address din gidan ta message. Ba jimawa doctor rahama ta iso Zaks ya bude mata tashigo sanye da hijjabi har kasa, hannunta rike da dan karamin box wanda ke dauke da kayan aikin dazata bukata, se car key a dayan hannunta da wayarta kirar Samsung. Aeezad har yanzu se aikin hura mata kafar yakeyi da iskar bakinsa, se faman sannu yake mata kmr me nakuda, se zufa nabeelah keyi dukda sanyin AC dasuke falon a kallah kusan AC shida ce a falon ko wacce kusurwa a falon akwai AC na tsaye, falon nada mahaukacin girma. Aeezad ya dawo ya kalli DR salmah a kallah bazatafi 35yrs ba bata taba Aure ba, tanada matsakaicin tsawo da matsakaicin kyau, chocolate color ce ita baza ace da ita me kyau ba kuma baza ace mata mummuna ba, komi nata normal. tinda ta shigo falon take kallon nabeelah da Aeezad daketa hura ma nabeelar kafa, tin a kallon farko dr salmah ta fahimci tabbas akwai kwayoyin halitta ta soyayya dake wanzuwa a tsakanin su biyun, idanuwan Aeezad basa taba iya boye soyayyar da yakema nabeelah, duk me hnkli ko kuma wanda yasan zafin SO dole ya fahimta inya kallesa. Mamakin wacece ita a garesa ya wanzu a zuciyar dr salmah, ta fara tambayar kanta kanta wacece wannan din? kowa yasan waye Aeezad haka kowa yasan wacece matarsa daya tak wato naeema. Gaidasa dr salmah tayi cikin girmamawa sbda tasan waye shi a kasar, ya amsa kallo daya Yama dr salmah ya dauke kansa, shi ba maabocin kallon mata bane, a kan mommy ne kawai idanuwansa ke narkewa , yanzu ma kwata-kwata ba mata a gabansa. “Wai sannu dole kiji zafin kafarnan sbda kwalbar na ciki ai,,,,” dr salmah ta fadi bayan ta ajiye box din hannunta ta sunkuya Tana kallon kafar nabeelah da Aeezad ya kama ya rike gam, se yanzu dr tasamu ta karewa nabeelah kallo, bata taba ganin me irin kyaunta ba se yau, “masha Allah…” ta fadi a ranta a zahiri tace “Bari na cire mata…” dr salmah ta fadi hadi da bude box din ta fito kayan dazata bukata Kama daga na wanke ciwon har allurar dazata mata. Aeezad ya lumshe idanuwansa ya budesu a kn dr din yace “pls ki mata a hnkli dan Allah na rokeki…” muryarsa fal tausayin Nabeelah yayi mgnr. Dr salmah dake kallansa yadda yayi mgnr ya kara tabbatar mata da santa yakeyi batasan wacece ita ba amma shi tasan wayeshi. “To ranka ya dade…” Cewar dr salmah. Kafar na hannunsa dr salmah ta fara kokarin cire mata kwalbar, nabeelah taja kafarta alamar bataso sbda yadda kafar ta kumbure tasan in aka tabata ba karamin zafi Zataji ba. “Yi hkri ki tsaya my life,,,” Aeezad ya fadi a rude, irin rudewarnan ta zuciyar ne So. Da kyar nabeelah ta tsaya dr ta cire mata kwalbar ta lumshe idanuwanta ta fasa ihu wata iriyar azaba ta ratsata, shi kansa gogan seda yayi kwallah, dr ta wanke mata ta mata Allura a duwawu ta kariya daga daukar cuta, da kyar nabeelah ta tsaya aka mata allurar , seda Aeezad ya riketa, Zaks kam ficewa yayi a falon har aka gama mata Allurar kana yadawo falon. , nabeelah kam ana gama mata allurar ta zube kasan carpet din Tana kwallah , ba karamin wuya Tasha ba , seda aka cire kwalbar daga kafarta taga ashe yar kwalbar nada girma, Aeezad kam kmr kalamansa zasu kare gunce mata sannu,sosai taji sauki da aka cire kwalbar se taji kmr an zare mata rabin ciwon. Nurse din ta bata wasu magunguna wanda zata dinga sha, ta mata sannu Allah kara sauki kana ta fice Zaks ya rakata zuwa Compound tashiga motarta bayan ya dauko kudade masu yawa daga motar Aeezad ya bata Aeezad ne yace a bata, da kyar ta amsa, sbda a ganinta Zaks ya wuce wanda zatama Abu ya biyata, sunyi zaman mutumci dashi kawar yayarsa ce ita kuma kawarsa shima domin suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login