Showing 30001 words to 33000 words out of 77020 words
Chapter 11 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
bane, napep suka Hau yakaisu har 'kofar gida, suna shiga falo suka tarar da Hajiya Anty taci kwalliya, wuyan ta da kunnanta Sai qyallin gold suke, matar ta'iya daukan wanka na fitar Hankali,yar Gayu ce ta qarshe, raba Goro da alawa take, ga Kuma kudi Nan agaban ta dami dami, zama Waheeda tayi akusa da ita, jikinta yana gogar Nata.
Tad'auko alawar guda d'aya tana sakawa a bakinta, sannan tacire hijabin jikinta, dogon gashinta ya baiyana,kwanciya tayi tareda d'ora kanta a cinyar hajiya Anty,sannan tace "Anty kayan me kike rabawa"
Ummah tace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba waheeda, kin sameta tana aiki memakon ki temaka mata, saide kihau cinyarta"
Bakinta ta turo gaba cikin shagwa6a tace "Ummah Anty cefa"
"eh saboda Anty ce saiki kashe mata cinya"
Hajiya Anty tayi murmushi tace "Goron saka ranar Yayanku ne, yau ansaka masa rana,su Sa'eed Kuma ankai musu gaisuwa"
Da Waheeda da 'Yanbiyu lokaci d'aya suka matso kusa da Hajiya Anty sukace "Babban Yaya?"
Hajiya Anty ta d'aga musu Kai, haba ai da gudu Waheeda tayi d'akinsa, tura kofar tayi tashiga ta ganshi a kwance, ya rungume Fillo a qirjinsa, cikin murna ta fad'a Kansa tana sakin ihun murna, yana jin yanda aka fad'o Kansa yasan ba kowane zaiyi masa hakaba Sai ita, yatsina fuska yayi sannan ya tureta daga jikinsa yace "Yaushe zakiyi Hankali ne?"
Cikin farin ciki tace "Babban Yaya, Dan Allah da pink colour da blue, dakuma green wanne ne yafi kyau?"
Cikin mamaki ya daga Kansa ya kalleta batare daya tashi ba, yace "meyafaru?"
Dantsan hannun sa takama ta riqe, tace "sonake kafadamin wanne ne yafi kyau saimu dakko ankon bikinka"
Wani irin baqin ciki ne yakama shi,cire hannunta daga jikinsa yayi,ya maida Kansa fillo cikin damuwa yace "ni banason auren"
Bata lura da yanda yake rabata da jikinsa ba tasake matsawa jikinsa tace "Meyasa Babban Yaya?"
Juyowa yayi yana Kallan ta, yace "Akwai yarinyar danake so"
Cikin farinciki tace "wayyo Allah, Babban Yaya Dan Allah wacece?"
Kallan ta yayi yakasa magana, zuciyar sa ce take zugashi akan yafad'a mata, to Amma tayaya zata dauki maganar?, qalubalen dayake gabansa dangane da fad'a mata wannan maganar ba qarami bane
Waheeda tace "Babban Yaya nikake kallo, wacece yarinyar?"
Ajiyar zuciya yayi yace "Sunanku d'aya, kamar ku d'aya"
Wani irin fari tayi da idonta tace "Dan Allah Babban Yaya kakaini wajan ta mugaisa, ka nuna mata ni, kafad'a mata nice qanwarka wadda kafi so"
Lumshe idonsa yayi yabud'e, sannan yace "zan kaiki, Amma karki fad'awa kowa wannan maganar, sirri"
Dariya tayi tace "bazan fad'a ba, Babban Yaya kasan me? Wallahi inaso kayi aure, sonake Naga matarka ta haihu, muga dawa yaran zasuyi kama"
Tashi yayi zaune ya kalleta yace "ke har farinciki kike da bikin ne?"
Tace "sosai ma, wallahi inaso kayi aure"
Cikin wata irin gigitacciyar tsawa, wadda bata ta6ajin yayi mata irinta ba yace "tashi kibarmin dakina, tunda farinciki kike da aure na"
Tace "Babban......"
kafin ta qarasa yatashi tsaye cikin fishi kamar zai rufeta da duka, tana ganin haka tatashi tsaye, jikinta yafara tsuma saboda tsoro, qwalla ce tataru a idonta, tafuto daga Dakin cikin sanyin jiki
Ayi hakuri da wannan ba yawa, muna tayaka murna Babban Yaya π
Bazanyi zagi ba, Amma duk wacce ta karanta batare data biyaba, nabarta itada mahaliccinta, saboda babu yafiyata aciki
Amnah
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandamaπ: Tana fita daga d'akin ya zauna akan gadonsa tareda dafe Kansa da hannun saπ€¦π»ββοΏ½?
Ita farinciki ma take, meyasa bazata fahimceshi ba? Yace sunansu d'aya, yace suna kama, tayaya zai futo fili yafad'a mata gaskiya? Tayaya zata fahimce shi? Mezai fad'awa iyayensu idan suka ji daga inda maganar tafuto?
Kansa ne ya Sara, yazube akan gadon yana fadin "hasbunallahu wa ni'imal Wakeel"
Bayajin zai iya rayuwa batare da Waheeda ba, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, ya cusa Kansa cikin fillo yana kuka babu me lallashi kamar ba Babban Yaya ba π
Tana barin 'Dakin nasa, d'akinsu tashige, ta zauna agefen gado tana Kallan p.o.p din 'Dakin,
'yanbiyu ne suka shigo, intisar tace "kekuma lafiya kikayi wani iri kamar marar lafiya?"
Cikin damuwa tace "Babban Yaya ne"
Ihsan da intisar sukasa dariya, Ihsan tace "to me yamiki Kuma?, kema da rawar Kai daga jin ansa masa rana kika d'iba da gudu kikaje"
Kallan su tayi cikin damuw tace "Wai baya son auren ne"
Inti tace "to yanzu ke menene naki aciki? Hanawa zakiyi? Mema za'ai da wannan Ummin, ni wallahi Bana sonta, kullum kaganta tana magana da maza"
Ihsan tace "wallahi kuwa, inajin su Daddy basu Sani bane shiyasa, nifa shiyasa banyi murna ba danaji ance itace, Amma Waheeda uwar rawar Kai harda tafiya wajan sa da gudu, dama yasani yamiki shegen duka"
Waheeda tayi shiru tana tunani, tana so tace musu yafada mata yarinyar dayake so to Amma Kuma data tuna yace mata sirri, Saitayi shiru, tayi ajiyar zuciya tace "nikam Ina sonta, tunda Babban Yaya zata aura, mutumin dayake taimako na aduk halin Dana kasance tayaya zanqi matarsa?"
Ihsan tace "to Allah yabada sa'a Waheeda, ke kikaga Zaki iya"
Daga Nan sukai shiru kowa da abinda yake saqawa Aransa
Ita Waheeda tana tunanin Babban Yaya, duk yanda zaiyi mata fad'a tana shiga damuwa muddin ta ganshi acikin damuwa, saboda Shima baya barinta acikin matsala, ta damu da damuwar sa sosai, batasan meyasa ba, wani lokacin zai mata hukunci akan laifin da tayi, gashi de shine ya6ata mata rai ta hanyar yimata hukunci, Amma Hankalinta baya kwanciya Sai ta bashi hakura taga ya haqura tukunna, gashi yanzu yana wani Hali saboda auran Ummi, batasan ta wanne Hali zata taimaka masa ba,zuciyarta tabata shawara akan tatayashi da addu'ah, haka ta dauki shawarar zuciyarta
Haka Babban Yaya ya wuni ad'aki yaqi futowa, Ummah Kota Kansa batabi ba, saboda tasan fishin nasa akan aure ne, Kuma aure Kam babu fashi
Washe gari yafuto daga d'akin nasa, yana Sanye da kayan ball, suma 'yanbiyu maza shine ajikinsu, zama sukai afalo kowa yana kokarin saka safa, yanmatan ne suka futo daga d'akinsu suma de kayan Ball d'inne ajikinsu, Amma nasu wandon dogo ne, rigar ma me dogon hannu ce, sa6anin na mazan dayake qanana, fita sukai zuwa filinsu na qwallo dayake gidan, shikuma Babban Yaya yana falon yana saka takalmin sa, gaba d'aya iyayen nasu suna compound suna shan shayi, da hajiya Anty da Ummah dakuma Daddy da Uncle Usman, akan idonsu yaran suka futo zasu fara buga Ball din, Amma babu Babban Yaya, a lokacin harya gama saka kambos dinsa, yana zaune ne yana amsa wayar Abokinsa dayake tambayar sa yaushe zai dawo, yana gama waya da abokin nasa wata wayar tashigo, yayi mamaki da'aka kirashi ta wannan number, saboda ba kowane yasan wannan number tashi ba, dauka yayi tareda sallama daga dayan bangaren akace "Yayanmu Ina wuni? Sunana Didat, qanwarka ce tabani number ka,Ina neman alfarma ne awajanka, maganar Gaskiya Ina sonta, idan kabani Dama inaso na nemi aurenta"
Babban Yaya ya Sosa girarsa guda d'aya yace "Sister na kuma?"
Daga d'ayan bangaren Didat yace "eh Yayanmu, na gansu ne abakin get d'in school d'insu, akwai mutum biyu masu kama d'aya, toba suba, d'ayar nake nufi"
Babban Yaya yana jin haka ya Lumshe Idonsa, cikin ransa yace "Waheeda"
Dafarko har yayi niyyar dakatar da Yaron, but Saiyayi tunani tayaya rayuwa zataci gaba da tafiya Ahaka? Yaushe ne zai daina hanata huld'a da samari? Duk Daren dad'ewa dole zatayi aure, wazai fara fuskanta da maganar datake damunsa?qalubalen dazai fuskanta akan haka ba d'an qarami bane, Kuma itama da alama sonsa take, tunda gashinan ta yarda harta amince a tambayeshi? Cikin Yan seconds yayi wannan tunanin, wani irin huci yayi yafitar da iska me zafi daga bakinsa sannan yace "Babu damuwa zaka iya zuwa"
daga Nan yakashe wayar tashi yafita zuwa compound da d'an gudunsa irin na 'Yan qwallo, acan Gefe ya hangi su Ummah sun baje suna shan Shayi, yana zuwa kuwa suka fara buga ball din mazan da matan, kusan mintuna talatin suka d'auka sunayi Amma Babban Yaya baici ko sau d'aya ba, mamaki ya kama iyayen nasu dasuke Kallan abinda yake faruwa, shida a qasar waje ma suke alfahri dashi akan iya ball, tayaya wad'annan yaran zasu dinga cinsa? Ada idan sunayin ball d'in kowa saduda yake, saboda sunsan comfirm 'Yan team din Babban Yaya sune da nasara, Amma yau Sa'ad da Babban Yaya, da intisar Sai sunci su Waheeda da Ihsan da Sa'eed suke yi.
Sunkuyawa yayi yariqe gwiwarsu, damuwa tataru tamasa yawa, idan ya tuna da maganar Ummi, yatuna da wayar da gayen Nan yamasa akan Waheeda, saiyaji gabansa yafad'i, daga qarshe ma kawai juyawa yayi zuwa falon su, intisar datake jin haushi anata cinsu, tayi sauri ta hura Whistle tace "wasa yatashi" π
Akan idanun iyayen Babban Yaya ya wuce falo yabar yan'uwan nasa, Waheeda tariqe hips d'inta cikin damuwa tana Kallan sa, daga Nan tabi bayansa, saide tana zuwa 'kofar 'Dakin nasa tayi nocking din duniya yaqi bude mata, dole Sai haqura tayi, ta wuce dakinsu.
Washe gari da yamma Ummah tana zaune ad'akinta tana tunani akan rayuwar Naufal, damuwar dayake ciki haqiqa itama tana ciki, yaqi yafuto fili yafad'a mata me yake tsoro dangane da aure a matsayin ta na mahaifiyar sa, duk sa'anninsa sun dad'e da aure, Sai yaushe ne shi zaiyi? Tun yanda ta ganshi jiya cikin damuwa har yanzu Hankalinta yaqi kwanciya, duk yanda yake dason Ball yamaqi yakoma bare tace ball din zata d'ebe masa kewa, Waheeda ce tashigo Dakin tana Sanye da dogon hijabi tace "Ummah zanje bakin get nayi baqo"
Ummah ta kalleta tace "Baqo kuma? Daga Ina kenan?"
Murmushi tayi tace "shekaran jiya nahad'u dashi abakin get din school dinmu, sunyi waya da Babban Yaya ma, shine yace yazo"
Ummah tace "kin tabbatar abinda kika fad'amin gaskiya ne Waheeda yayanku yasan da maganar sa?"
"Allah Ummah yasani"
"to shikkenan kije, Amma karki dade" cewar Ummah
Waheeda tafuto daga d'akin, ta qarasa wajan Didat, yana Sanye cikin shadda Light blue, hular daya saka ta dace da kalar kayan nasa, qarasa wa tayi tareda sallama, ta ajiye masa ruwan roba guda biyu da Lemo guda daya, baba maigadi yataso da sauri yasake gaida shi, sannan suka qarasa wajan wasu kujeru masu kyau Wanda aka qawata wajan da yar qaramar rumfa domin shan iska, Didat ya kalli Waheeda Bayan ya zauna yace "Ranki yadade gimbiya"
Waheeda tace "mudade tare"
Murmushi yayi yace "bakice nayi kyau ba, Bayan duka wankan naki ne, kinsan kafin nafuto daga gida saida nafadama mamana wajanki zanzo, tace nayi kyau sannan tana miqa saqon gaisuwar ta zuwa gareki"
Tace "nagode sosai, Ina amsawa, idan kakoma kace ina gaisheta"
"zataji insha Allah,ni sunana Didat"
Tace "nikuma Waheeda"
Kallan ta yayi yace "sunanki yanada dadi Waheeda, Ina fatan ace kin zamo wani bangaren na cikin rayuwa ta idan kin amince"
Tace "kamarya?"
"Ina nufin kibani Dama Nima adama Dani acikin Jerin masoyanki, Amma maganar gaskiya itace inada kishi sosai akan abinda nakeso, shiyasa ma nakawo miki wannan kyautar"
Yafadi haka yana bata wata leda, saida ta karba Sannan yace "hijabi ne da niqab, dakuma safa, gaskiya Ina kishinki Waheeda, aurenki nakeson yi bawai soyaiya ce ta kawo ni wajanki ba, banaso muyi shekara daya batare da munyi aure ba"
Murmushi Waheeda tayi tace "gaskiya ne, nayarda kanada kishi, tunda gashi kyauta ta farko daka fara min itace da hijab da safa da niqab, Amma Kuma duk kishinka baka Kai Babban Yaya ba" ππ»ββοΈπ³οΏ½?
Cikin mamaki ya gyara zama sannan ya kalleta yace "waye Kuma Babban Yaya?"
Murmushi Tayi tace "nasan cewa kasan Big Brother ko?"
Yace "sosai ma kuwa, waye zaice baisan Shiba? Aini shine 'Dan qwallon dayake mugun birgeni"
Tace "to shi nake nufi, ai shine Babban Yayanmu"
Didat yace "ok, Allah sarki, haba shiyasa Naga gidanku unguwa guda gashinan aljannar duniya" yafad'i hakan cikin sigar tsokana
Waheeda tace "Shima yanada kishi, yafi son muyi karatu karmu kula samari"
Yace "ya kyauta min, inda yabarku Aida Nima bazan sameki ba, nasan da tuni wani alhajin ya dauke ki"
Murmushi tayi tace "nagode, zan koma gida, Ummah tace karna dad'e"
Shima tashi yayi tsaye, ya ajiye mata rafar kudi Yan hamsin hamsin guda daya, aqalla zasu Kai dubu hamsin, daqyar da Fama Waheeda ta d'auki kudin, sannan suka rabu akan zai sake dawowa gobe ko jibi, tanada son kudi Amma Bana hannun mutane ba, saide na Babban Yaya, tasan yayanta ne bazai taba goranta mata a kan hakaba, abinda ta lura dashi shine, shi mutum ne me kishi kamar yanda yafad'a, sannan daga Gani bashida matsala ko kad'an
Da daddare gaba d'ayansu suna zaune banda Daddy, Ummah ta kalli Babban Yaya dake danna waya yana qara Bawa Corch dinsu hakuri akan dad'ewar da yayi,Kallan Ummah yayi yace "Ummah nanda kwana hudu yaran Nan zasu tafi Umarah insha Allah, gaba d'ayansu"
Cikin farinciki Ummah tace "Alhamdulillah, Allah yayima Albarka, to Allah yakaimu lokacin, Kai banda Kai ne?"
Girgiza mata Kai yayi sannan yace "su kad'ai"
Ummah tace "To madallah, Allah yaqara hore Maka,"
Murna suka hauyi gaba d'ayansu, Nan take suka fara zuba masa ruwan godia, Waheeda kuwa jitake kamar taje ta rungume shi Dan murna, Amma babu Dama yanda taga ya d'aure fuskar Nan tana zuwa kusa dashi tsaf zai maketa π
Ummah ta sake Kallan sa cikin farinciki sannan tace"Yauwa yayansu ga wannan kud'in, saurayin Waheeda ne yabata dazu"
Kallan kudin yayi Asheqe sannan yace "ok"
Ummah tace "bangane Okay ba, bazaka kar6a kasa mata Albarka ba?"
Yatsina fuska yayi yace "Ummah dubu hamsin d'in kamar Wanda yayi kyautar bajinta?" βΉοΈ
Mamaki yakama Ummah, sukuwa su Sa'eed dariya suka saka, Sa'ad yace "haba Babban Yaya, dubu hamsin fa, kodan Kai mekud'i ne shiyasa, wallahi Ummi tahuta"π
Wani irin banzan kallo yamasa, lokaci d'aya yashiga taitayinsa
Kafin su qara cewa komai wata yarinya 'yar kimanin shakara 11 tashigo da sallama hannunta d'aukeda wani flask na abinci, ta tsugunna ta gaida su Ummah sannan tace "Wai gashi inji Anty Ummi abawa Yaya Naufal" π
Haushi yakama Babban Yaya, ya kalli yarinyar yayi tsaki a ransa, ko'ina ya zama yayanta harda wani Yaya Naufal,?
Ummah ta saki ranta tace "Allah sarki, to kice ya gode, zai kawo mata kular da Kansa kinji, Allah yamiki Albarka,"
tad'auko fos dinta dake Gefe tabawa yarinyar dubu biyar, yarinyar cikin murna ta karba tafice daga falon
Waheeda ce tataso tabud'e flask din taga abinda yake ciki, sannan tayi murmushi ta kalli Babban Yaya tace
"Babban Yaya farfe...."
kafin ta qarasa cewa farfesu ne, yatashi cikin fishi, yabar falon gaba d'aya, Ihsan da intisar suka zabgawa Waheeda harara suma sukai d'aki, Waheeda ta kalli Ummah cikin shagwa6a kamar zatayi kuka, Ummah ta janyo ta jikinta tace"rabu dasu, idan sun gama fishin zasu sakko"
Washe gari da safe, suna break fast, wayar Daddy tayi qara, yayi mamakin me Kiran nasa, domin kuwa ba kasafai suke waya da minister of Education ba, d'auka yayi Bayan sun gaisa, Daga d'ayan bangaren minister Abdullahi Wakili yace "Alhaji Umar Arabo"
Daddy yayi murmushi yace "ranka yadad'e, kwana dayawa ba'a jinka"
Minister yace "wallahi kasan koda yaushe muna ta Fama da jama'ah, yanzu ma yarona ne Huzaifa yasaka ni agaba lalle lalle saina kiraka"
Daddy yace "a a ikon Allah, Huzaifa ya dawo qasar ne?"
Minister yace "wallahi ya dawo, cikin ikon Allah ya kammala karatun sa lafiya ya dawo, yazo ya sameni ne akan maganar 'yar wajanka, last week yaje 'Dauko sisters d'insa daga school sunyi party na candy, anan yaga yar wajanka Waheeda yace yanaso, shine da yayi bincike yagano 'yarka ce, Kuma kasan akwai sanaiya a tsakani, shine yace ayi masa tambaya aji ko an yiwa wani alqawari? "
Daddy yace"A a babu alqawarin kowa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi "
Daga d'ayan bangaren minister yayi godia tareda kashe wayar
Babban Yaya yanajin wayar da Daddy yake jikinsa yabashi akan Waheeda ake magana, Bai nuna komai akan fuskar saba, lafiya kalau suka gama cin abincin sannan ya dauki key din mota yafice daga gidan
Da yamma Didat yazo tareda abokinsa Mukhtar, yau wankan qananun Kaya yayi, ba qaramin kyau yayi ba, suna cikin zance da Waheeda yace "Gimbiya inaso kije gida ki fad'awa Ummah zamuje shopping idan ta amince"
Babu musu Waheeda ta wuce gida ta fad'a wa Ummah abinda Didat yace, Ummah tace "to karki tafi ke kad'ai, kuje keda yan'uwan ki"
'Dakinsu ta wuce, ta tarar Ihsan na wanka, Sai intisar dake karatu, tare suka futo da intisar basu jira Ihsan ba, suna zuwa kuwa Didat yace "lalle babbar Yaya, yanzu ashe Kuna ciki kun 6uya, ko sau d'aya bantaba ganinku ba"
Intisar tace "Wallahi muna Nan, abubuwa ne sukai yawa, yakake"
"Alhamdulillah, Ina lafiya kamar yanda gimbiya Waheeda take, dafatan de tare dake zamuje shopping din?"
Intisar tace "babu damuwa muje"
Tsayawa sukai suna jira yabud'e musu kamar yanda Babban Yaya yake musu, shikuma harya shiga motar, saida yajuya ya gansu a inda suke sannan yayi murmushi yazo ya bud'ewa Waheeda gaba, intisar Kuma suka zauna Abaya tareda abokinsa, suna hanya abokin Sai Jan intisar yake da zance, tana amsa masa kad'an kad'an, a wajan shopping d'inma Didat Kam kawai binta yake yana aikin kallon ta kamar wani sakarai, itace me za6ar komai, saida yakashe mata kud'i me yawa sannan suka Juyo gida, tun a hanya yaga tana amsa masa daqyar, Sai yatsina fuska take, suna qarasa wa gida kuwa intisar tayi ciki, ita Kuma Waheeda ta tsaya suna sake tattaunawa, Kallan ta yayi yace "Meyake damunki ne? Naga kamar bakya jin dadi"
Yatsina fuska tayi tace "wallahi jinake zazza6i yana son kamani"
Cikin rud'ewa Didat yace "Subhanallah, Amma shine kikai shiru? Meyasa baki fad'amin ba muje Asbiti?"
Tace "Babu damuwa, zansha pracitamol agida"
Didat yace "no, ga Mukhtar Nan yayi miki injection mana, akwai saura acikin motata Ina siya Dama saboda 6acin rana, idan kikaje gida saiki kwanta kihuta, Shima doctor ne"
Cikin damuwa Waheeda tace "no, karka damu wallahi"
Didat yace "a a, tsaya yayi miki please"
Bud'e motar yayi, ya 'Dauko allurar yabawa Mukhtar, Mukhtar ya kar6a yafasa ruwan allurar, ya kalli Didat yace "Ina sirinji?"
Didat yace "aikuwa na manta wallahi babu, but ga Wanda akamin allura dashi ban yarda shi ba, kayi mata dashi kawai"ππ»ββοΏ½?
Kallan Waheeda Mukhtar yayi yace "babu damuwa ayi miki gimbiya?"
Tace "babu damuwa"
Kar6ar sirinjin yayi yazuqe ruwan allurar, sannan yayi mata a hannunta, basu qara ko minti biyar ba, sukai sallama, tajuya zata tafi gida, adede lokacin Babban Yaya ya dawo gidan, fuskarsa ad'aure take babu wasa, ya gansu Amma saiya nuna baima gansu ba, Didat da baisan da shigo war Babban Yaya ba, ya qwalawa Waheeda kira, tana juyowa yayi kissing hannun sa, sannan yahura mata tareda kashe mata ido, yashige cikin motarsa
Babban Yaya yana Kallan su, yakashe motarsa Bayan ya ajiye ta