Showing 6001 words to 9000 words out of 77020 words

Chapter 3 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete

mutane Sai addu'ah suke masa shikam saide yayi murmushi yace "Amin"

Sa'eed ne ya karbi Brief case din hannunsa yace "Sannu da zuwa Babban Yaya"

Yace "Sannu Sa'eed, kaje da wannan kudin ka can zasu zuwa Naira Please"

Yace "to Babban Yaya angama"

Sa'ad yabude masa Bayan motar yashiga, yana shiga ya Lumshe idonsa tareda dafe Kansa
Su Sa'ad da Sa'eed suka shiga gaba, suka tada motar Sai hanyar gida, suna hanya Sa'ad dake driving yajuyo ya Kalle shi yayi murmushi tareda fadin "sannu Babban Yaya, gidanka zamu wuce ne kokuma gida?"

Batare daya bude lumsassun idanunsa ba yace "no, muwuce gida kawai, I want to see my mother"

Babu Wanda yasake magana acikinsu, saida suka qarasa gida sannan Sa'eed yafice daga motar yashiga wata motar yafita wajan canji,
Babban Yaya da Sa'ad Kuma suka tsaya gaisawa da ma'aikatan gidan.

Karfe hudu daidai, gaba dayansu yanmatan su uku suna falo kowacce Sanye cikin uniform din islamiya Mai launin light blue, sungama shirya wa Ihsan ce kawai bata saka hijab ba

Intisar tadubi Waheeda "Waheeda Dan Allah ki Ara mata hijab din, inda taga Nata ai bazatace ki Ara mata naki ba"

Yatsina fuska tayi tace "tabdi, ai saikuyi Kuma,dazu dazunnan tagama cemin marar Hankali ta6a66iya, tayaya zata saka kayan ta6a66iya?, kunifa Bari kuji banida mutunci akan kayanaaaaaa" taja naaa din sosai sakamakon tozali datayi tashi a bakin kofa yana qoqarin shigo wa falon nasu,dayake itace take kallon bakin qofa, sukuma ita suke kallo suna roqarta hijab,lokaci daya taji tanemi nutsuwar ta tarasa, taji kanta yasara tundaga qeyarta har zuwa goshinta, fuskar Nan tasa atamke, yahade girar sama data qasa, shikkenan magana ta qare, tasan yau takade har ganyenta, yaji labarin meta aikata

lokaci daya tanutsu, cikin tsananin ladabi ta kalli Intisar tace "kidauki hijab din nabaki duka, kinga wannan dayan bashida guga, Bari nadaukeshi, kekuma saiki dauki gogaggen" ๐Ÿ˜‚

Cikin falon ya qaraso, qamshin turaren sa ne yasa yanbiyu juyawa cikin sauri,suna ganinsa suka juya suka kalli Waheeda, Sai yanzu suka gane abinda yasa ta basu Aron hijab din.


Wajan sa suka nufa cikin ladabi sukace "Babban Yaya sannu da zuwa"

Hannunsa ya daga musu kawai,tareda zama acikin kujerun dasuka qawata falon nasu masu launin dark green, cikin murna suka tafi Dakin Ummah suna qwala mata kira, suna zuwa suka tarar tana toilet

Kallan Waheeda yayi wadda ta qame a wajan tun shigo war sa, yamiqe tsaye batare daya kalleta ba yace "ke biyoni"

Gabanta ne yake wani irin bugawa dak! dak!, tafiya take tana binsa Amma jitake kamar batada nauyi, jitake kamar iska zata Iya dagata sama,suna shiga Dakin nasa wani irin qamshi yadaki hancinta,Dakin ya qawatu da manyan pictures dinsa, dayawa daga cikinsu duk da kayan ball yayi photon, qamewa tayi daga Nan bakin qofa saboda bai bata iznin qarasowa tsakiyar Dakin ba, takunkumin dayasa a hancinsa yafara cirewa sannan ya kalleta yace"Kneel Down here"

Cikin sassarfa taqaraso cikin Dakin tazube gwiwarta aqasa tareda daga hannayenta sama, zama yayi agefen gadon yafara cire takalmin qafarsa, sannan ya tashi tsaye yacire rigar jikinsa, farar fatar jikinsa ta bayyana, murdaddan Hannunsa yasake futowa sosai, duk abinda yake idon Waheeda quriiii akansa, tunda taga yafara cire Kaya take qarewa surar jikinsa kallo, cikin ranta tace tunda Naga yafara cire Kaya inaga yau zamu raba raini, hukuncina nayau yafi qarfin duka saide dambe ๐Ÿ˜‚

Wayarsa ce tayi qara ya dauka tareda bude fridge din Dakin ya dauki ruwan gora, sannan ya dawo ya zauna, cikin aji yayi sallama yana fadin "wake magana?"

Daga d'ayan bangaren akace "ranka yadade Big Brother, Shema'u ce, Shema Lady, yanzu na bude data ne, sainaga Ana bada labari kazo, ashe ka shigo gari yau"

"no, qaryar Yan media ne kawai Shema, banzo ba"

Fari tayi da idanunta, taji shi ne kawai, Amma bata yarda ba, cikin salon yaudara tace "Big B. Kenan, saika ganni kawai" qit takashe wayarta, wayar ya janye daga kunnansa ya kalli screen din wayar, aiko saboda wayar data kashe masa yanzu koda ace tazo, bazai saurareta ba, saboda ba'a kashe masa waya saide yakashe

Tashi yayi yafara kokarin janye dogon wando jeans din jikinsa, har boxer din yafara bayyana yajuya ya kalli Waheeda yaga ta qwara masa ido tana Kallan sa ๐Ÿ˜‚, saiya fasa cirewa yamiqe tsaye yana mata wani irin kallo, cikin sauri ta runtse idonta, saida yaga tarufe idonta sannan ya qarasa cire jeans din, dagashi Sai gajeren wando yashige cikin toilet dinsa, tanajin shigarsa tayi wata irin ajiyar zuciya sannan tasauke hannunta qasa, sau dayawa tana mamaki sosai dangane da tsakanin ta da yayan Nata, kamar bashine yayanta me sonta ba, bazata taba manta lokacin dazai dauketa ya goyata abayansa yana zagaye compound din gidan da'ita ba, Amma tunda ta girma, komai ya sauya, yadena wasa da'ita, yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, idan tayiwa Ummah complain tace ai saboda bataji ne shiyasa Shima ya sauya mata, Kuma mema take aika tawa dazaibi ya tsaneta? ๐Ÿ˜โ˜น๏ธIdan akan samari ne tayaya za'a Hanasu kula samari Bayan sun kusa yin candy, idan suka gama makaranta babu saurayi qarshan zancen ace za'a hadasu da samarin dangi, ayi musu auren zumunci, Kuma a wannan zamanin waye zaizo auren cushe, auren zumunci?

Tanajin alamun bude kofar toilet din tayi sauri ta daga hannun ta sama


Be kalli inda takeba, Kai tsaye gaban mirror ya wuce yana gogo lallausar sumar Kansa ta buzaye da wani Dan qaramin towel, saikuma wani dayake daure a qugunsa, nocking din Dakin akayi, ya dakata da abinda yake ya kalli kofar tareda fadin "shigo"

Sa'eed ne yashigo da wata leda ahannunsa me d'aukeda kudade Yan dubu dubu, ya rissina cikin ladabi yace "Bร bร รฑ Yaya an canzosu"

Turare yafara fesawa a jikinsa yace "kaje kaida Sa'ad ku rabasu dubu goma goma, a saka kowacce dubu goma cikin Envelope, anjima idan mun fita masallaci Sai arabawa mabuqata"

Waheeda tanajin zancen dubu goma tayi sauri tabude idonta, kudin ta kalla tagansu dayawa yanzu duk wannan mabuqata zai bawa?jitayi kamar taje ta qwace, Gata, gasu yanbiyu agida suma ai mabuqata ne ๐Ÿ˜ƒ

Sa'eed ya kalli Waheeda yadaka mata harara sannan yafice daga Dakin yaja musu qofa,tunda yaganta a Dakin yasan laifi tayi

Kallan Babban Yaya tayi taga ya Dauko wasu kayan zai saka, maimakon ta dauke idonta saita qura masa ido, yana Kallan yanda take kare masa kallo tagefen idonsa, ya tabbatar Waheeda raini takeji, tunda har zata Iya zuba masa ido har haka tana Kallan sa to yasan cewa Dan ance namiji yasha bakinta ba za'ayi qarya ba, da niyya yajuyo ya fuskanceta sannan yafara kokarin cire towel din guqunsa, idan wani abun take so tagani saita Gani da hujja๐Ÿ˜‚

Gaban Waheeda ya yanke yafadi, cikin sauri ta runtse idonta, cikin qasa qasa da murya yace "Ashe ke qaramar 'yar'iska ce"

Ita Kuma tayi tunanin magana yamata, tunda Dama haka yake magana qasa-qasa kamar baiso, gudun kartayi laifi yace yayi mata magana ta qyaleshi shiyasa ita Kuma ta daga murya tace "Na'am Babban Yaya Dani kake?"

Dawowa yayi ya zauna agefen gadon, Bayan yagama shirya wa tsaf ya kalleta yace "badake nakeba qaramar marar mutunci, kullum aka ganni a Nigeria ta dalilin ki ne nake zuwa, haka kawai Ina Kan har kokina saikin aikata abinda zaisa dole sainazo qasar Nan, ke wacce irin mahaukaciya cene? Kwata kwata bakida aji bakida Hankali irinna yanmata, anturaki makaranta ashe soyaiya kike harda su kiss, nakafa doka a gidan Nan kina take wa yafi a qirga, saboda ga sa'anki, to yau idan jikinki yagaya miki, ko ance ki kalli samari ma bazaki kallesu ba, dangane da makaranta Kuma nasan matakin dazan dauka a kanki"

Yana kaiwa Nan ya tashi yafice daga Dakin, Waheeda tafashe da Kuka, cikin kuka tace "Nashiga uku na, ashe yaji, shikkenan Aryan yacuceni, Allah ya'isana" haka taci gaba da kneel down tana kuka, babu damar tatashi yazo yaga tatashi nanma taqara wani laifin, tun yanzu ma jitake gwiwowinta harsun fara zafi


Yana futowa daga Dakin yatarar da Dady da Ummah a zaune, gaida su yayi cikin ladabi sannan yakoma gefen Ummah ya zauna tareda Dora Kansa akan kafadarta yace "Ummah"

Murmushi tayi tace "Yayansu ya hanya, maza tashi muje Kaci abinci, gashi can na shirya ma" babu musu ya tashi, saboda yayi missed girkin umman tasa, saboda aturai koda yaushe baida abinci saina gwangwani, Daddy ya kallesu itada Yaron yace "idan kin gama bashi abincin inason magana dashi"

Ummah tace "to Alhaji"

Ita da kanta ta dinga bashi abinci abaki, kowa ya kallesu yasan akwai tsantsar soyaiyar uwa a tsakanin su, Sai shagwaba yake mata abu kadan yace Ummah, ita Kuma Sai lalla6ashi take

Saida ta tabbatar ya qoshi sannan suka koma falon, wajan Alhaji Umar, Babban Yaya ya Kalle shi yace "Daddy nagama, meyafaru?"

Kallan sa yayi yace "menene zai faru banda maganar Aurenka?ai tunda Naga kazo yau nasan kun daidai tane kaida ita Habiban ko? Yaya kukai da'ita?" ๐Ÿ˜‚

Sunkuyar da Kansa yayi yana Sosa girarsa, yama kasa dagowa ya kallesu

Ummah tayi ajiyar zuciya tace "wacce Habiba Kuma Alhaji? Yarinyar da harma munyi magana da mahaifiyar ta awaya sunce sun janye batun auren, nabawa mahaifiyar yarinyar hakuri Amma Sai tace ai habiba tace bazata iya zama da mutumin da bazai bata kulawa ba, to tunda naji haka, kawai saina bata hakuri tunda bansan me suka Tattauna ita dashi a wayar ba, shi yasan meya qulla "tana fadar haka takawar dakanta Gefe tana girgiza qafa

Alhaji Umar ya Kalleshi yace"Naufal"

Ahankali yace "Na'am Daddy"

"bakada lafiya ne irinta maza?"

Maganar tayi masa nauyi, saiya kasa dago Kansa ya kalli mahaifin nasa, Ahankali ya girgiza Kansa yace "A a Daddy"

Daddy yace "okay, iskanci ne yake damunka kenan?"

Nanma yakasa bashi amsa ya girgiza Kansa yayi shiru

Daddy ya ajiye Jaridar hannun sa yace "kaiba 6oyaiyan mutum bane dakake tunanin mutane bazasu saka Maka ido akan aure ba, muna zaune lafiya bazaka ja mana zagi agari ba, zamusa qafar wando daya dakai tunda haka kaza6awa rayuwar ka, Kuma neman aure yanzu muka fara nema Maka, idan ma wani abun daban kake fadawa yaran mutane har suke gudunka kaika Jiyo, mude bazamu fasa nema Maka aure ba, har a wajan Allah muna neman fita haqqin ka ne a matsayin mu na iyayenka akan kayi aure gudun aikata Zina, mutumin banza mutumin wofi, katashi kabamu waje Kuma aure dolen dole Sai kayi "

Runste idonsa yayi, maganganun Daddy sun shige shi sosai, yaji zafin maganar Daddy sosai, tayaya ne zai futo fili yafada musu yarinyar dayake so Bayan tarin matsaloli dakuma qalubalan dazai fuskanta ? Tayaya? Ahankali ya tashi daga gabansu yanufi dakinsa, zuwa yanzu magrib har tayi

Yana shiga dakinsa yaga Waheeda yanda yabarta, gaba daya cinyoyin ta sun sage, Saitayi kamar zata fadi qasa, saita dawo baya taci gaba da abinda take, bacin ran dayake ciki ne yasa yanemi belt yanufeta gadan gadan, tana ganin haka tatashi tsaye tanaja baya, kuka take wiwi tana bashi hakuri Amma idonsa sun rufe saida ya lafta mata belt dinnan ajikinta, qara tasaki tana fadin "Dan Allah kayi hakuri, wallahi tallahi nadena Babban Yaya, Dan Allah kayi hakuri"

Cikin 6acin rai yace "kifadamin waye wannan Yaron dayake neman lalata ki?, harkinashan bakin wani saboda bakida mutunci ko? "

Belt din tariqe idanunta cikeda hawaye tace "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan sake ba, idan nasake Kamin komai ma nayarda"

Fizge belt dinsa yayi yasake zuba mata shi ajikinta, zafin dataji ne yasa batamasan lokacin data tashi ta rungume Shiba,yana jin yanda Albarkatun qirjinta suke tsikarinsa saboda bata saka bra ba, lokaci daya jijiyoyin jikinsa suka kar6i saqon, ๐Ÿ™ˆAmma tsananin 6acin ran dayake ciki yasa baza'a gane hakan ba
Fizgeta yayi daga jikinsa yasake Dora mata wani belt din, cikin kuka tace "Akofar fada yake, gidan Alhaji Hamza"

Tsaki yasaki tareda wullar da belt din qasa yace "Stupid"

Ummah tana Jiyo kukan Waheeda tata6e baki tace kanku akeji kunfi kusa, Daddy ne yake tambayar ta meta masa, anan ta fada masa komai ciki harda wayar Babban Yaya data daga batare data saniba

Futowa yayi daga Dakin yabarta anan, su Ummah suna zaune har lokacin, suna ganinsa yafuto fuskar sa a daure, yana shirin fita daga falon, anan yaci Karo da Yanbiyu harsun dawo daga islamiya kasancewar anfara Kiran sallar magrib, yanda sukaga fuskar sa sunsan ransa a6ace yake, cikin sauri suka bashi waje yafice daga falon

Suna qarasowa falo suka gaida Daddy, Shima ya tashi yayi shirin tafiya masallaci, Dakin Babban Yaya aka bude ahankali, kamar me koyon tafiya hake take takawa, idanunta sun kumbura sunyi jajir, Sai yarfe hannunta take, hawaye wani nabin Bayan wani, Ahaka tashige cikin dakinsu babu Wanda yace da'ita uffan daga Ummah har Yan biyu, tana zuwa daki wani irin zazza6i yafara kokarin rufeta, kawai zubewa tayi agadonsu taja Bargo tarufa.๐Ÿ˜‚

Da daddare duk suna zaune afalo gaba dayansu suna kallo, har wajan karfe takwas da rabi Waheeda bata futo falo ba
Babban Yaya yana zaune yana danne danne a wayarsa, Sa'eed da Sa'ad Kuma suna gefen sa suna bashi labarin 'yanmatan dasuka hadu dasu wasu yanbiyun suma, magana suke masa Amma hankalinsa yanakan wayar dake hannun sa, ahankali yake amsa musu, su yanbiyu suna zaune suma, suna Kallan film din da'akeyi, Ummah da Daddy suna can Gefe suna zance qasa qasa, Daddy ya kalli Babban Yaya yasake yin qasa da murya yace "ke baki lura da abinda nafada miki ba? Ki lura dashi sosai qarya yake mana bashida lafiya"๐Ÿคฃ

Itama Ummah Kallan sa tayi tace "Aina yarda Alhaji, kunyar fada mana kawai yake, Amma duba fa yanda 'yan' uwan suke bashi labarin yanmatan su Amma yayi mursisi, maza dason zancen yanmata Amma shi kaduba kagani fa suna masa magana kamar sunayi da dutsi"

Daddy ya girgiza Kansa yace "dole zan dauki mataki hajiya"

Shikuwa Babban Yaya baisan sunayi Bama ๐Ÿ˜‚Kallan intisar yayi yace "ke tashi ki kira wannan yarinyar tazo tayi kallo"

Intisar tasan da Waheeda yake, ita kadai ce bata futo falo ba, cikin sauri ta nufi dakinsu, tana shiga tahau kan gadon ta yaye bargon da Waheeda tarufa, bude idon ta tayi ta kalleta, duk yanda Waheeda take gane yanbiyu, take banbancesu dukda tsananin kamar dasuke, yau kasa ganesu tayi,๐Ÿคฃ intisar ce tazo kiranta Amma Waheeda tana qare mata kallo cikin wahala tace "Ihsan Dan Allah ki temaka ki taro ruwan zafi a toilet kizo ki gasa min cinyoyina, jikina yayi tsanani bazan iya tashi ba"

Dariya ta kama Intisar, saita danne gudun karsuzo suna fada, tace "Babban Yaya ne yace kifuto kiyi kallo kowa yana falo banda k....." kafin ta qarasa magana taga Waheeda ta duro daga kan gadon ๐Ÿ˜‚
Kokula sauran zancen batayi ba tafice daga Dakin, tana zuwa falon babu Wanda ta nufa Sai shi, har gefen qafarsa ta zauna, hawaye yazubo daga idanunta, a Hankali tace" Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri kaji.... "

Babu Wanda yasan metake fada masa, saboda ahankali tayi masa maganar, Shikuwa banza yayi yarabu da'ita, hawayen tasake gogewa tace"kaji" memakon yabata amsa saiya tashi daga falon yashige dakinsa, haka ta zauna a wajan tana Kallan dole, saida takusa minti talatin tana kallo Amma bata fahimtar komai, Dan haka tatashi Takoma dakinsu tafara gabatar da sallah


Karfe bakwai daidai afalo tayi masa,yayi kyau sosai cikin manyan Kaya, yanda yaqara cika da kamala zakace yanada aure, agogon hannun sa ya kalla yadubi Ummah yace "kice musu Idan sun gama Ina waje Ummah"

Ummah tayi dakin yaran tace "kuyi sauri kufita yayanku fa kuyake jira"

Yanbiyu ne suka futo sun shirya cikin uniform dinsu, suna zuwa compound din suka hangeshi yana Dukan tayar motar da qafarsa yana Kallan agogo, suna ganin haka suka qara sauri suka shige motar, shida Kansa yayi driving din, Kai tsaye yanufi makarantar su

Suna zuwa kuwa Kai tsaye yanemi iso zuwa office din director, teachers dinsu maza Wanda suke harkar ball suna ganinsa suka fara zuwa suna gaisawa dashi, yana gaisawa da director yanemi afwa akan yanbiyu, babu bata lokaci sukace komai ya wuce Yara sukoma aji, Amma waccan dayar de kar akawota bazasu karbeta ba

Duk da haka saida yaqara basu hakuri sannan yayi musu ihsani yafuto daga makarantar, daga Nan ma ba gida yakoma ba, kofar fada ya nufa, yana tambayar gidan Alhaji Hamza aka nuna masa, futowa yayi ya jingina da motar yace ayi masa sallama dashi, Alhaji Hamza yana futowa yaga farin buzu a kofar gidansa, qarasa wa yayi yabashi hannu suka gaisa, Babban Yaya yace "Alhaji sunana Naufal, da Alhaji Hamza nake magana ko?"

Alhaji Hamza yace "nine samari, ba kaine yaranmu suke cewa Big Brother ba?"

"nine Alhaji, dama nazo ne akan maganar qanwata dakuma Yaron wajanka Aryan"

Alhaji Hamza yace "to menene yafaru?"

"Alhaji, Yaron wajanka yana soyaiya ne da qanwata, shine nazo muyi magana akan yaturo iyayensa idan aure zaiyi yanzu"

Alhaji Hamza yace "Wai Aryan wannan Dana Sani Dan wajena kake magana akansa?"

"shide Alhaji"

Murmushi Alhaji Hamza yayi yace "samari Aryan fa shekararsa goma shatara ne Idan nayi lissafi daidai, tayaya za'ayi masa maganar aure yanzu?"

Babban Yaya yace "hakane, to ita yarinyar dayake nema aurenta zamuyi, saboda haka Dan Allah Alhaji ajawa yaro kunne yadena bibiyarta, jiya matsala ce tafaru a makarantar su har hakan yasa suka Koreta daga makaranta, so aja masa kunne please"

Alhaji Hamza yace "Subhanallah, ashe yar'uwarka ce yaro, to kuyi hakuri Dan Allah, insha Allah zanyi wa tufkar hanci"

Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi gida

Yana zuwa gida ya tarar da Hajiya Anty da Ummah afalo, can ya hangi Waheeda a dinning tana cin abinci
kwanciya yayi akan doguwar kujera ya Dora Kansa akan cinyar anty yasaki wani irin murmushi dimples dinsa suka lotsa duka biyun yace "Anty nah ta kaina"

Sumar Kansa ta shafa tace "yayansu nayi fishi, kazo Amma koka leqoni, yanzu ma sannu da zuwa nazo yima dakuma wani albishir"

Hannunta datake shafa sumarsa yariqe yayi kissing Bayan hannun sannan yace "Ina jinki Hajiya Anty"

Tace "wallahi wata yarinya ce take zuwa Asbiti Ina dubata lokaci zuwa lokaci, shine nayaba da Hankalinta, nace zan turo mata Dan yayata su daidai ta ko Allah zaisa ayi abun da'ita"

Cikin sauri ya tashi daga kan cinyarta yace "Anty me kikace?"

"abinda kaji nace"

Kansa ya shafa yace "Anty Kode neman Kai kuke Dani ne?"

Tace "mekake nufi yayansu?tayaya zamu nemi Kai dakai?"

Bata rai yayi cikin shagwaba yace "to Anty gashinan Kuma arasa da wadda za'a hadani Sai majinyaciya?"

Ummah ce tasa musu baki tace "tunda kaqi lafiyayyu ai sai kakoma kan majinyata" tajuya ta kalli hajiya Anty tace "ki fada masa komai, kidena wani Lalla bashi"

Hajiya tace "yayansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login