Showing 33001 words to 36000 words out of 77020 words
Chapter 12 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
a parking space yafuto, adede kofar shiga falon suka had'u da juna, cikin ladabi tace "Sannu da zuwa Babban Yaya"
Cikin 6acin rai yace "aikece za'ayi wa sannu,mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi, Kin tsaya yana miki hauka Amma ko ajikinki, kwata kwata bakya kishin kanki, idan kikai wasa naqara ganin qafar Yaron Nan a gidan Nan saina kakkarya qasusuwanki ...."
"Subhanallahi .... Naufal?"
Cewar Hajiya Anty da shigowarta kenan taga yana zazzaga wa Waheeda masifa
Kallan ta yayi, yayi qasa da Kansa, idanun Nan nasa sunyi jajir tsabar 6acin rai, Sai huci yake kamar zai Fashe, ita kanta hajiya Anty ta tsorata da yana yinsa, ta kalli Waheeda datake share hawaye tace "Ke wuce ciki"
Kallan sa tayi tace "Kayi hakuri" sannan ta wuce cikin falon nasu
Hajiya Anty ta kalli Babban Yaya tace "yanzu bakaji kunya ba? Kagama yimata fad'a Amma daga qarshe haquri take baka ko kallo bata isheka ba? Hakan dakayi daidai ne kenan?"
Yace "Anty kissing dinta fa yayi" yayi maganar kamar zai Fashe da Kuka
Hajiya Anty tace "to naji tayi laifi wannan fad'an dakake mata shine zaisa ta nutsu? Qanwarka cefa, jininka ce tayaya bazakaja yarinya a jikinka ba zakadinga mata fada irin haka,?to tun tana jin tsoron ka, watarana zata daina, kaja Qanwarka a jikinka kaji nafada ma, fad'a ko duka basa shiryar da yaro"
Qwalla ce take son futowa daga idanunsa yana dannewa, idan yatuna yanda Didat yake huro mata kiss, jiyake kamar yayi ihu, cikin 6acin rai yace "Anty niba qanwata bace, kidena cewa Qanwata"
Hajiya Anty tayi sakare tana Kallan sa, a fili tace "ikon Allah, to ba Qanwarka bace, karka jata a jikinka, gata Nan ka kashe ta"
Daga haka tajuya cikin gida tabarshi a wajan, Shima shigewa yayi ransa a6ace
Tunda yashigo 'Dakin yakasa sukuni, tunani yayi masa yawa, daga qarshe ma tashi yayi yafara had'a kayansa, gobe da safe zai koma England bakin aikinsa, kwata kwata bayajin zai iya zama yana ganinta tana mu'amula da wani namijin bashi ba
Cikin qanqanin lokaci yagama had'a komai,kawai jiran wayewar gari yake
Kamar wasa Waheeda tana kwanciya bacci ya dauketa marar dadi, sakamakon abinda yafaru tsakanin ta da Babban Yaya , haka Shima anasa bangaren, baiji dadin baccin ba, har yanzu wannan kiss d'in ya tsaya masa aqahon zuciyar sa,washe gari kalau tatashi babu wani alamun zazza6i atare da'ita, 'yanbiyu basa 'Dakin Sai ita kad'ai take juyinta akan gadon, doguwar Riga ce ajikinta ta bacci Amma me kauri, bata nuna shape dinta ba kwata kwata, saide kana iya ganin tsayayyun breast dinta yanda suka tsaya a tsaye cak tacikin rigar, brush taje tayi tadawo 'Dakin nasu taga Maya na kiranta awaya, d'auka tayi tace "uwar 'Yan Fassara ya akayi?"
Maya tace "ke dalla malama yau babu Fassara,Wai baqi mukai daga Abuja, shine wani daga cikin su yace yanaso na, ya tambayi mama yaushe zan gama karatu tace masa nanda wata shida, nikuma gaskiya Waheeda banason aure yanzu, nafison nayi karatu me zurfi, sannan baki ganshi ba Babba nefa, yakai Babban Yaya girma da shekaru, ko kunya babu waini yakeso, Dan Allah tayaya zan iya Zaman aure dashi Aida kunya"
Waheeda takwashe da dariya tace "lalle ma Maya, to miye abun kunya? Tab wallahi karkiji kunya, ba aurenki zaiyi ba? Aiba haramun bane"
Ummah ce tashigo 'Dakin zata fad'awa Waheeda taje gidan Hajiya Anty takira mata 'yanbiyu, Sai tajita tana waya, saboda haka saita dakata tagama wayar sannan ta fad'a mata Aiken, ita Kuma Waheeda kwata kwata bataji shigo war kowa Dakin ba
Daga d'ayan bangaren Maya tace "ke bazaki gane ba, novel damuke karantawa duk fa abinda akeyi a novel idan akayi aure Nima fa haka zanyi, wallahi bazan amince ba babu ruwana, ni kunyarsa nakeji, gashi qato"
Waheeda tasake fashewa da dariya tace "nikuma idan nice keko wallahi amincewa zanyi, tabdi to menene aciki ba mijina bane? Har wankansa zan dinga yi, keni har abar tasu zan kama na wanke, qarshe de kenan....." ππππ»ββοΏ½?
Hawaye ne ya silalo daga idanun Ummah, innalillahi wa inna ilaihirraji'un yanzu Waheedanta ce take wannan maganar?Har abar zata kama ta wanke? Cikin kuka Ummah tace"Waheeda?"
Gaban Waheeda ne yayi wata irin bugawa, kanta ya Sara, cikin sauri ta kashe wayar jikinta yana rawa,ko'ina na jikinta kyarma yake tama kasa yiwa Ummah magana Sai kanta datake girgizawa alamun Bahaka bane
Ummah tayi kukan kura ta kamata tafara dukanta, ihu take tana neman temako Amma babu kowa a gidan, cikin ikon Allah tasamu tafuto daga 'Dakin, Ummah ta zauna a wajan tana kuka.
tana zuwa compound adede lokacin shikuma yashiga motarsa kenan zai rufeta, ganinta yayi aguje ta nufoshi, kanta babu ko dankwali Sai dogon gashinta daya bazu agadon bayanta, kana ganinta kasan tana cikin mutuqar tashin Hankali,saboda fuskarta ma kadai gumi ne yake futowa ga hawaye sha6e-sha6e tanayi, duk ta rikice jikinta yana rawa kamar mazari, hakan yabawa cikakkun Breast dinta damar rawa kamar Wanda take kad'asu da niyya, tunawa da tayi jiya ransa ya6aci saboda ita, Sai taja ta tsaya cak a wajan tana waigen Bayan ta ko Ummah zata biyota, saboda tasan cewa Shima tana zuwa wajansa Dukan ta zaiyi.
tausayi ta bashi, lokaci d'aya jikinsa yayi Sanyi, duk yanda akai ba qaramin laifi tayi ba, shiyasa take neman mafaka, dama shine Mai taimaka matan, to Shima yanzu tsoron zuwa take, tana tsoron tunkararsa saboda tasan confirm zaiyi mata hukunci, tunowa yayi da fad'an Hajiya Anty, Kuma yasan idan Yabarta ma zataci gaba da haduwa da wannan Yaron ne, yanzu yana hura mata kiss, to gaba gaba kiss din zaiyi mata a aikace, Gara ma sutafi tare kowa ya huta, ahankali tamkar baya son magana yace mata "shigo mutafi"
Ai kamar jira Waheeda take , cikin sauri ta fad'a cikin motar, yayi mata key suka bar gidan
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandamaπ: BB
Har sukai Nisa da gidan jikinta bai daina rawa ba, yana Kallanta ta gefen Idonsa, Amma be tambayeta wanne irin laifi ta aikata hakaba, Kai tsaye boutique suka wuce, Yabarta a motar yashiga yasiyo mata doguwar Riga dakuma hijab, kawo mata yayi, yafita daga cikin motar yabata damar sauya kayan, dube dube tafara ganin motar me baqin glass ce saita sauya kayan cikin kwanciyar Hankali, saida tagama komai sannan ta qwanqwasa glass din motar, yashigo suka tafi, kwana kwata ko awa daya basu qara ba, jirginsu ya Lula qasar England, acikin jirgin ma tana kusa dashi, saide har yanzu baice da'ita komai ba, itama haka, saima fad'awa da tayi cikin duniyar tunani, haqiqa Babban Yaya yana kaunarta, laifi nede idan tayi masa tasan cewa babu fashi Sai Tasha duka, yau da ace bai dauketa ba ta tabbatar Sai tafi kwanaki bata iya had'a ido da Ummah ba, maganar tayi nauyi ace itace ta fad'a, Amma Kuma akwai abinda zaka iya magana akansa kaida qawarka, wannan tsakanin kune,babu kunya babu 6oye-6oye, ajiyar zuciya tayi, Tajuya ta kalli Babban Yaya taga Hankalinsa yanakan jarida yana karantawa, matsowa tayi jikinsa tariqe dantsan hannunsa na Dama sannan tad'ora kanta akafad'ar sa ta Lumshe idonta, yanajin yanda hannunsa yake taba gefen breast d'inta, Sai a lokacin yatuna bai sako mata da brezia ba, jaridar hannun nasa ya ajiye akan cinyarsa, yajingina Kansa jikin kujerar tareda Lumshe Idonsa, yanajin yanda numfashin ta ya sauya yasan cewa bacci take, duniyar tunani yafad'a,inama ace wannan tafiyar sunada aure Honeymoon zasu tafi? π€
Wani irin haushi yaji daya tuna Didat, dakuma Huzaifa da babansa yakira Daddy akan maganar Waheeda, jiyayi komai ya jagule masa, haka yayi shiru daga qarshe Shima baisan lokacin da bacci ya d'auke shi ba.
Da yamma suka sauka, hannunta yana cikin nashi suka shiga mota, sannan suka qarasa gidansa, yanayin tsarin gidan kad'ai Waheeda ta kalla tazama yar qauye, gidan yayi matuqar kyau sosai, an tsarashi yanda ya kamata kamar baza'a mutu ba, motoci Kala Kala kusan guda shida a ajiye a compound, ga wani waje da aka qawata shi da dutsina ruwa yana gudana daga jiki, tafiya suke Amma hankalin Waheeda yana can tana Kalle Kalle har suka qarasa cikin falon bata Kallan gabanta, suna zuwa ta qwace hannunta ta fad'a cikin kujerun falon masu matuqar kyau da tsari tace "gaskiya Babban Yaya gidannan yayi kyau sosai"
Zama yayi akusa da'ita Amma aqasan kafet, ita Kuma tana kan kujera, Kallan ta yayi yace "idan kinaso ai saiya zama mallakinki"
Kallan sa tayi tace "Dan Allah? To Bani shi zakayi?"
Murmushi yayi, dimple d'insa suka futo, yace "sosai ma, saiya zama mallakinki keda yaranki"
Cikin rashin fahimta tace "Babban Yaya, abar wannan maganar, nasan kawai fad'a kake,tab! wayaga Waheeda da Yara, hmm ni yanzu ma yunwa nakeji"
Babban Yaya ya kalleta yace "laifin me kikayi?"
Shiru tayi tafara wasa da yatsun hannunta, ita de bazata iya fad'a masa magana me nauyi irin wannan ba, tayaya zata kalli idon yayan Nata tabashi labarin komai? Aida kunya, qarshan ta shima idan yaji yasaka ta a jirgi yau d'innan ya maida ta gida
Kallan sa tayi tace "babu komai"
Kafad'a ya d'aga yace "shikkenan tunda haka kika so" daga Nan yatashi yafita daga falon yayi waje domin Nemo musu abinda zasuci
Tana ganin fitarsa tatashi ta dinga zagaye gidan tana santinsa, wayar Ummah datake hannunta ta kalla tasaki wani irin murmushi, ko Yaya suka qare agida? π€
*** *** ***
Ahaka Daddy yashigo yasamu Ummah ta zabga tagumi tana sharar hawaye, ga yanbiyu agefenta suna bata haquri, ganin shigo war Daddy yasa suka tashi suka nufi d'akinsu
Daddy ya kalleta yace "mekuma yafaru kike kuka Hajiya?, inata Kiran wayar ki Amma najita a kashe"
Hawayen ta share tace "wayar tana hannun Waheeda"
Cikin mamaki daddy yace "to Ina ita Waheedan take?"
Girgiza Kai tayi tace "bansan inda take ba, Amma megadi yace sun fita tareda yayansu, shikuma munyi sallama dashi zai koma England, bansani ba ko tare suka tafi"
Kafin yabata amsa hajiya Anty tayi sallama cikin falon tashigo, zama tayi Bayan sun gaisa da Daddy tace "Anga Waheedan?"
Ummah tace "ba'a ganta ba,tana tareda yayansu"
Hajiya Anty tafara kokarin Kiran Naufal, Amma wayar taqi shiga, haka ta haqura, bata dade da zama ba tatafi gida saboda Daddy yana Nan tace zata dinga try ko wayar zata shiga
Ummah naganin fitar Hajiya Anty ta kalli Daddy sannan ta zayyane masa komai babu abinda ta rage akan wayar dataji Waheeda tana yi.
Daddy yadafe Kansa yace "ita Waheedan ce tafad'i haka?"
Ummah ta 'Daga masa Kai alamun hakane, cikin damuwa yace "Hajiya, yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, tun kafin yarinyar Nan ta lalace Gara ayi mata aure, zaifi sauqi"
Ummah tace "Nima abinda nayi tunani kenan, amma muddin mukai ido hudu da Waheeda sainasa Sa'eed yayi mata Dukan tsiya, duk inda suka tafi ai zata dawo"
Daddy yace "matsalar yarinyar Nan bame qarewa bace, Allah yasa de yanda take fad'a a wayar bawani tata6a yiwa hakan ba" ππ
Cikin jimami Ummah tace "Amin"
*** *** ***
Anan falon ya dawo ya sameta, hannun sa d'aukeda ledoji, ajiye mata yayi yazube akan kujera, duba kayan tafarayi, leda d'aya ta abinci ne daya siyo musu, d'ayar Kuma kayane yasiyo mata nasaka wa, abincin ta zuba sannan Shima tazuba Masa nasa, saukowa yayi daga kan kujerar yaja Nata abinci yafara ci, Kallan sa tayi cikin mamakin abinda taga yayi tace "Babban Yaya ga Naka fa"
Wani irin kallo yayi mata Mai d'auke da ma'anoni, sannan yace "ni wannan nake son ci, kisa hannu muci"
Babu musu tasaka spoon din tafara cin abincin, wani abincin ya 'Debo a spoon me yawa, yaci 'Dan kadan, sannan ya nufi bakinta da sauran, yace "meyasa bakyaci dayawa ne?"
Murmushi tayi tace "Babban Yaya ai kaima haka, bakaci"
tafadi hakan tareda bud'e bakinta, babu musu yasaka mata,haka ya dinga yimata, Sai yaci kad'an saiya bata sauran, Waheeda bata d'auki hakan da wata manufa ba, zuciyar ta d'aya take cin abincin dayake bata, Kallan bakinta yake yanda take tauna abincin cikin nutsuwa, yanda lips dinta suka hadu da maiqon Mai suke wani irin shinning, Sai hankalin sa yafara tashi, yatuna ranar dayayi kissing d'inta
Jiyake inama ace ita d'in tazama mallakin sa? Da babu abinda zai hanashi kasacewa da'ita a wannan Daren, yamaidata cikakkiyar mace, ajiyar zuciya yasauke, ya kawarda wannan tunanin daga cikin ransa, tashi yayi yanufi d'akinsa ba tareda yace mata komai ba.
Yana zuwa 'Dakin shirin wanka yayi, ya wuce toilet ya watsa ruwa tareda d'auro alwala, 'Dakin tashigo hannunta d'aukeda ledar kayan daya siyo mata, ganin zaiyi sallah tayi saurin ajiye ledar tashiga toilet ta d'auro alwala tazo ta bishi, saida suka idar sannan tashiga wanka, shikuma yacire jallabiyar jikinsa ya kwanta akan gadon dagashi Sai gajeren wando, tareda 'Dauko wani diary yana rubutu aciki cikeda damuwa, daga shi har Waheeda babu Wanda yake tunanin Kiran Yan gidaπ
Futowa tayi daga wanka tana Sanye da rigarta ta bacci, turare kawai ta fesa tanufoshi ta zauna aqasan kafet din, shikuma yana kan gado ya rungume diary din a qirjinsa, Kallan ta yayi yaga tasa shi agaba tana aikin kallon sa kamar tasamu TV harda tagumi, yace "lafiya?"
Murmushi tayi tace "Babban Yaya wallahi kana birgeni, babu ruwanka da neman tsokana, Kai haka rayuwar ka take, inajin Kai ka haqura da duniya ma" π³
Kwata kwata baya cikin yanayin farinciki Amma jin wannan maganar Tata Sai dariya ta kamashi yace "na haqura da duniya Kuma?"
Fari tayi da idonta tace "Emana, gashinan to babu ruwanka da shiga harkar kowa, rayuwar ka cikin kwanciyar Hankali"
Juyowa yayi yana Kallan ta, har zuwa lokacin dairy din yana rungume a faffadan qirjinsa, yace "tayaya zan haqura da rayuwa Bayan bansamu abinda nake soba?"
Tace "zaka samu Babban Yaya,nasan saboda me kama da nine kace haka, Bari kaji ai dole ma ka sameta ko tana so ko bata so,nikam yanzu banida damuwar komai"
Yace "Serious?"
Wani iri farrrrrr tayi da Zara zaran gashin idonta, sannan ta 'Dora hannunta akan qirjinsa tana so taja littafin daya rungume, shikuma yahana, saima Qasan fillo daya turashi ciki
Bata d'auki hakan a matsayin komai ba, batasan cewa baya son taga dairy din bane, batayi tunanin wani abu na sirrinsa yake rubuta wa aciki ba, shiyasa Bata damu da saita ganiba, saita share, saima hannunta data d'ora akan faffad'an qirjinsa take shafa gashin da yayi kwance akan farar fatarsa, sannan tace "I'm serious Babban Yaya, banda damuwar komai, kana tsaya min akan komai,nasan cewa nafi kowa sa'ar samun Yaya me kula da qanwarsa, shiyasa bayansu Ummah da Daddy banida Wanda yafika"
Kwata kwata Babban Yaya baiji abinda Waheeda take fad'a masa baπ
idanunsa a Lumshe suke, shi Kansa ba zaice ga duniyar dayake ciki ba, wani irin dad'i yakeji yanda take shafa qirjinsa, Waheeda bata lura da yanayin data jefa yayan Nata aciki ba, kawai qirjinsa take shafawa tana wasa da gashin qirjinsa me mutuqar laushi, ahankali tace "Babban Yaya Wai meyasa bakasan aske gashin kirjinka? Yafara yawa fa...."
Babban Yaya baima bud'e Idonsa ba bare yabata amsa, baya so yayi magana ta daina abinda take masa, yafiso taci gaba, Kallan sa tayi taga Idonsa a Lumshe, tayi murmushi tad'auki wayar Ummah data gudo da'ita ta kunna, sannan ta kunna masa tasa wayar, kamar jira ake, tana kunna wayar Babban Yaya kira yashigo da wata number,tsabar nacin da me number take masa ne yasa ya rubuta wa ne number Ummi Nigeria , Waheeda ta janye hannunta daga kan qirjinsa tace "Babban Yaya Ummi Nigeria tana kira, wacece?"
Cikin takaici yabud'e Idonsa, yaji haushin shigo war Kiran wayar, gashinan ta katse masa jin dad'insa, Kansa tsaye yace "Ummi ce"
Cikin murna Waheeda tace "Bari in d'aga mugaisa"
Cikin sauri yatashi zaune yace "kice mata me? Karki d'aga, ni Bana d'aukan wayarta, me kikeso nace mata idan nad'auka?"
Waheeda takama dariya yanda taga ya rikice shi baza'a daga wayar Ummi ba,Sai hakan yasake bata dariya, tace "Toni kabarni in d'auka saimu gaisa"
Ganin zata d'auki wayar yasa yamatso kusa da'ita zai qwace wayarsa,ita Kuma tana ganin haka tahanashi, kokawa suka fara irinta masoya tana d'aga hannunta sama Dan karya qwace wayar shikuma yanaso ya qwace, saura qiris wayar ta katse Waheeda tayi nasarar picking ba tareda ta saniba
Daga d'ayan bangaren ummi tayi gyaran murya tareda lanqwasa harshe tace "Hello Dear"
Taji shiru, tasake cewa "Hello my Dear..." nanma taji shiru Sai alamun ma kokawa dataji anayi tacikin wayar, kasa kunne tayi taji Babban Yaya yana cewa "Kibani wayata nace...."
Waheeda ta hanashi Sai dariya take, tana tsaye akan gadon shikuma yana tsugunne bai tashi tsaye ba, cikin dabara yariqo Hips d'inta da duka hannayensa, cikin dariya tayi baya zata fad'i saiya tareta tafad'o qirjinsa, breast d'inta Wanda ko bra babu, yasauka akan fuskar sa, cikin ransa yace "Ya Salam.......wayyo Allah nah...."
jiyayi gaba d'aya jikinsa ya mutu, yaso ace yanada Dama da saide yasake rungume ta a qirjinsa,zaiso ace yasake cusa Kansa acikin nashanunta, lokaci d'aya yana yinsa yafara sauyawa
Daurewa yayi, yayi ta maza sannan ya qwace wayarsa, yasake ta tafad'a kan gadon tana dariya, wayar ya kalla yaga har anyi minti uku da d'auka.... Ba tareda yayi magana ba yakashe wayar
Daga d'ayan bangaren Ummi tasaki ajiyar zuciya cikin bacin rai tace "Kan ubancan!, da wacce shegiyar yake tare? Ni za'a nunawa bariki?" π€₯π
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandamaπ: WN
Sake Kiran wayar Ummi tayi, Amma Naufal yana Gani yayi mursisi yaqi dauka, saima wuta daya kashe, yayi shirin bacci, saboda gaba d'aya yanayinsa ba daidai yake jinsa ba
Waheeda ma fillo taja zata kwanta akan gadon, yana jin alamun kwanciyar ta kamar an tsikare shi yayi sauri yatashi zaune, yace "mezakiyi?"
Kallan sa tayi cikin duhu tace "Bacci mana Babban Yaya"
"ok" abinda yace kenan, sannan ya sauko daga kan gadon ya shimfid'a wani blanket Mai laushi, yaja fillo d'insa ya kwanta, yana d'auke fillon Waheeda taga wannan dairy din, batayi masa magana ba saida taji shiru alamun yayi bacci sannan ta d'auka tafara bud'ewa, 'Dakin yayi duhu bata ganin komai,saita janyo wayar Ummah ta haska tafara karantawa, shafin farko Zanan heart ne ajiki, yayi kyau sosai Zanan,har ya d'auki Hankalinta sosai, shafi na biyu ta bud'e tafara karantawa inda ya rubuta (Rayuwa Mai sauyi,a koda yaushe zata Iya sauya Maka, daga qaddara Mai kyau ko marar kyau,akoda yaushe qaddarar mutum tana iya sauyawa,banajin zan'iya rayuwa ba tareda itaba, Abaya kafin zuwanta komai nawa cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali nake yi, tunda tashigo cikin rayuwa ta, komai ya sauya, Abaya Ina rayuwa ne tareda 'yan'uwana cikin kwanciyar Hankali, haihuwar ta ne......