Showing 42001 words to 45000 words out of 77020 words
Chapter 15 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
me kama dakai Babban Yaya"
Gabansa ne yake Dukan Tara Tara, tunda tafara yimasa wannan maganar, kwata kwata yafita haiyacinsa, zuciyar sa ce take zigashi akan yafad'a mata komai, karyayi wasa da damar sa, karya Bari abinda yadad'e yanaso yakufce masa
Cikin sauri kamar Wanda aka mintsineshi yace "koda nine....?"
Kallan idanunsa tayi, cikin rashin fahimta tace "kamarya?"
Shima Kallan qwayar idonnata yayi yace "Zaki iya auren me kama Dani, meyasa ni bazaki aure niba....?"
Kuyi hakuri Dan Allah ππ»ππ»
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandamaπ: SM
BB
Cikin sauri ta d'ago ta Kalle shi, tsananin mamakin abinda yayan Nata yafad'a ne yasa takasa rufe bakinta, gabanta yafara fad'uwa ganin yanda fuskarsa ta nuna kamar da gaske yake, wata zuciyar tace da ita ke mahaukaciya ce? Tayaya hakan zata faru tsakanin ku?yayanki uwa d'aya uba d'aya tayaya?
Dariya ta kwashe da'ita tace "Babban Yaya aure Kuma? Tayaya? Tayaya zan aure ka? Please Mekake so kace? Nasan inajin sonka acikin raina fiyeda yanda nake jin huzaifa acikin zuciyata, saboda Babban Yaya ubane, Kuma ba'a sauya uba,shi kuwa Miji Ana sauya shi"
Kansane yasara har saida yariqe goshinsa, lokaci d'aya ya dawo cikin haiyacinsa, yatuna irin kato6arar da yayi, cikin sauri yace "lokaci ya quremin, Sorry....kuje kuyi ankon tunda Kuna so, tashi kije"
Cikin murna Waheeda ta rungume shi tareda manna masa kiss agoshi, tafice daga d'akin
Tana fita yazube akan gadon nasa, duk yanda yake jin dad'i idan jikinsu yahad'u yau baiji komai ba kasancewar yasan cewa akwai Babban aiki a gabansa, idan yarinyar ta amince da auren sama Tofa bata sonsa, soyaiyar jini take masa,ba soyaiya ta masoyi da masoyiya ba
wani irin huci yayi yafitar da iska daga bakinsa,kwanciyar da baiyi ba kenan, ya wuce toilet duk da safiya ce, ya d'auro alwala yafara kaiwa ubangiji kukansa.
Washe gari da safe Bayan sun gama break fast, compound suka fita buga ball, kowa yana Nan banda Waheeda data tafi makaranta
Sun dad'e sunayi sannan suka koma ciki, abinci sukaci kowa yakama harkar gabansa, Babban Yaya kuwa shirya wa yayi zaije wajan abokinsa mashkur, Wanda Dama can shine de abokinsa guda daya, sun dad'e tare, hatta 6angaren sana'ah ma Shima mashkur ball yake bugawa, saide kowa da Club d'insa, Amma duk a England suke rayuwar su, yana barin d'akinsa anan falo yaga baqi maqota suna shigowa gidan nasu, Sai a lokacin Ummah take fad'a masa kayan lefen Waheeda ne za'a kawo, ba qaramin kokari yayi ba wajan saita Kansa, daga qarshe yafice yabar gidan, domin kuwa abubuwan qara ta6ar6are masa suke π
Baidawo gidan ba saida yamma, a lokacin baqi Wanda sukazo aka kar6i Kaya dasu suntafi, daga Sa'ad da Sa'eed Sai 'yanbiyu da Hajiya Anty da Ummah ne a falon, ga akwatunan Nan agefe hajiya Anty tana duba kayan da aka zuba aciki, Sai kuma uwar gayya wato Waheeda tana zaune kusa da Hajiya Anty tana shan tea da waya a hannun ta tana karanta saqon Huzaifa Sai murmushi take, gabansa ne yafad'i, ganin da gaske de ankawo kayan lefen Nata, lokaci d'aya ransa yayi baqiqqirin
Shigowa falon yayi duk da yanda yake ganin duhu-duhu kamar Idonsa yana son rufewa ππ»ββοΏ½?
Adede lokacin daya qaraso tsakiyar falon yaji hajiya Anty tana cewa "Hajiya yaushe zamu saka rana akai na Naufal ne? Tunda sunbar mana komai a hannun mu ai yakamata mukai musu kokuwa?"
Cikin sauri yayi hanyar d'akinsa, Babu Wanda ya lura da yanayin sa Sai hajiya Anty, ta Kalleshi cikin tsananin mamaki, yashigo falo babu Wanda yayiwa magana Kuma ya wuce cikin d'akinsa da wannan sauri haka,tasake juyawa ta kalli Waheeda, kanta ta jijjiga tareda cizon lips d'inta, yau d'aya de yakamata ace tayi wani abu akan wad'anan 'ya'yan nata a matsayin ta na uwa π³(tofa)
Kallan Waheeda tasake yi, tana jin qaunarta acikin zuciyarta, koda wasa bata son abinda zai ta6a lafiyarta balle yasaka ta cikin wani Hali, Amma Yaya zatayi.....?
Ahankali tatashi tabi Bayan Naufal, tana tura kofar 'Dakin tana shiga ta ganshi a tsaye yana Kallan p.o.p din d'akin, Kansa ne yaji yasara lokaci d'aya jiri ya d'ebeshi zai fad'i, cikin sauri hajiya Anty ta qarasa tatareshi yafad'o kanta
"subhanallah....Naufal lafiyarka kuwa?"
Idonsa ya runtse, yasaka hannu yadafe goshinsa, but kwata kwata yakasa magana, janyo shi tayi ta kwantar dashi akan gadon, itama ta zauna sannan tad'ora Kansa akan cinyarta
Lallausar sumar Kansa take shafawa, saida taji yad'an nutsu sannan tasake tambayar sa
"meyake damunka?"
Hawaye ne yafuto daga idanunsa, mamaki yakama hajiya Anty, Naufal ne da Kuka yau? π€
Tun yana hawaye harya dawo yana kuka harda shashsheka,bata hanashi ba, rabuwa tayi dashi bata hanashi ba, saida yayi me isarsa, sannan yayi shiru Sai Jan zuciya yake, ajiyar zuciya tayi akaro na biyu tace "meyake damunka?"
Cikin rawar murya tamkar ba Babban Yaya ba, yace "Allah idan na rasata mutuwa zanyi....."
Gaban Hajiya Anty yayi wata irin fad'uwa, cikin sauri ta Kalleshi tace "what....? Wacece?"
Sai a lokacin Babban Yaya yatuna abinda yafad'a, hawaye ne yazubo masa, Sannan yace "Anty ni bazan iya rayuwa da wadda banaso ba, bazan iya Zaman aure da'ita ba...."
Ajiyar zuciya tayi, Amma maganar sa ta farko Sai yawo take mata acikin qwaqwalwarta, karfa tunaninta ya zama gaskiya.....idan hakan ta tabbata Yaya zasuyi da wannan tsohon al'amarin da wannan Yaron yake son tado musu shi?
Kallan sa tayi tace "shine damuwar?"
Kasa magana yayi, Sai Kansa daya d'aga mata kawai
Tace "to shikkenan, zan samu ummanku muyi magana da'ita, ka kwantar da hankalin ka banason wannan kukan"
Sake d'aga mata Kai yayi, Ajiyar zuciya tayi, sannan ta rungume shi sosai ajikinta, ta sunkuya tayi kissing goshinsa, sannan tad'ora masa Kansa akan Fillo tafita daga d'akin
Tana futowa daga d'akin taga yaran basa Nan,Sai Ummah kad'ai tana kallo, godia tayi wa Allah cikin ranta, sannan ta qarasa wajan ta tace "Yaya a Kwai matsala fa, nasamu yayansu yanzu, maganar gaskiya baya son auren Nan har yanzu"
Cikin tsananin damuwa Ummah tadafe kanta π€¦π»ββοΏ½?"nashiga ukuna,Yaya zanyi da wannan Yaron ne, banaso Naga Naufal cikin damuwa, Bari inje in sameshi...." tafad'i haka tana kokarin tashi
Cikin sauri hajiya Anty tace "Zauna Yaya, Wai meyasa bazaku zaunar da Yaron Nan yafad'a muku wadda yake so ba?"
Ummah ta kalleta cikin damuwa tace "to inda zai fad'i wadda yakeso d'in ai zanji dad'i Nima...., idan an tambayeshi fa cewa yake shi har yanzu babu wadda yakeso, ayi namiji baligi Amma ace kullum babu wadda yakeso?"
Anty tace "to yanzu ya za'ayi?"
Cikin damuwa Ummah tace "tunda ke yafara sakewa dake har yana fad'a miki damuwar sa, kifad'a masa zai iya qarawa da yarinyar dayake so d'in, yanzu su Alhaji sun Riga sunyi magana tayaya zamu ce a banje wannan auren mu maida su qananan mutane?"
Hajiya Anty tace "Eh hakane Kuma, tunda yanada damar dazai iya qara auren shikkenan, Allah ya tabbatar musu da Alkhairi, Allah ya basu Zaman lafiya Kuma"
Ummah ta jijjiga kanta kad'an, ba tareda tace komai ba.
Bayan kwana biyu aka shirya aka Kai lefen Babban Yaya,su Daddy sunyi magana da iyayen kowa daga cikin su, Ummi dakuma Huzaifa, danhaka aka tsaida date din 'Daurin aure sati hud'u masu zuwaπ’
Su kuma su Sa'ad da Sa'eed aka tsaida nasu bikin Bayan shekara d'aya ππ»
Yau duk suna zaune afalo gaba d'ayansu,yana jin yanda intisar take cewa "akai musu wannan uban kayan Amma abada tukwicin dubu ashirin?"π€
Ihsan tace "ai sai kiyi tayi, kanki akeji, tunda sude bazasu qara komai ba, ni dazu danahau Instagram ma kayan nagani anata turawa, mutane Sai cewa suke anyi almubazzaranci dayawa, Kuma nasan Yan gidan sune suka saka kayan a internet"
Babban Yaya Ko Kallan su baiyi ba,bare ya tanka, yasan suna magana ne akan 'Yan gidansu ummi, wayarsa ce ahannunsa yana Kallan pictures din Waheeda, wasu tun tana zama, wani Kuma ahannunsa take yana bata fida tana Sha, wani Kuma tana cikin baho yana mata wanka, wani Kuma yad'agata sama yana kissing Kumatunta, a lokacin tafuto daga d'akinsu wayar Ummah tana hannunta, Kai tsaye wajan sa ta nufa ta zauna, yana ganin ta yayi saurin rufe wayarsa kartaga abinda yake Gani, wayar Ummah ce tasake qara, cikin 6acin rai ta dauka tace "Wai Dan Allah Didat mekake so nama? Nafad'ama gaskiya kadena kirana anriga ankawo kayan aure na"
Daga d'ayan bangaren Didat yace "wallahi Waheeda idan kika kuskura kika auri wani baniba wallahi saikin kashe auren kin futo kin aure ni...."
Cikin 6acin rai tace "au haka kace?"
"eh haka nace, Dan renin hankali kince min Inturo iyayena baki tsaya kinji abinda zan fad'a miki ba kawai saiki cemin yanzu ankawo miki kayan aure.... A a, sadaki aka kawo miki ba Kaya ba, wallahi idan kika yarda aka miki aure da wanina dagani harke Sai ran kowa ya6abaci "
Dif... Yakashe wayarsa
Waheeda tasaki tsaki ba tareda tace komai ba, tajuya ta kalli Babban Yaya har zata masa magana saitaga ya daure fuska, dolenta taja bakinta tayi shiru π¬
Da daddare abokinsa mashkur yazo,zaune suke akan had'ad'd'iyar motar Mashkur din, wadda yayi parking dinta a compound din gidan, mashkur 'Dan Gayu ne na gaske, akwai d'aukar wanka tamkar Babban Yaya, Ihsan ce ta kawo musu lemuka ta ajiye akan 'Dan qaramin wani dinning table dake gabansu,ta gaida mashkur sannan tajuya, har tayi Nisa Idonsa yana kanta, bata dad'e da tafiya ba intisar takawo musu cups, cikin mamaki ya kalleta yace "kaiii, Wai daga shigar ki har kika sauya Kaya kika futo?"π€
Murmushi tayi tace "a a, Bani bace, Ihsan ce dazun"
Murmushi yayi tareda shafa qeyarsa,intisar tajuya tatafi, mashkur ya dubi Babban Yaya yace "tsakani da Allah kunada wannan kyawawan yanmatan Amma kabarni Ina shan wahalar neman matar Aure? Gaskiya Allah yamuku kyau Abokina, Wannan kyanta ace zan'iya had'asu duk su biyun, da lokaci d'aya zanyi wuf dasu"
Babban Yaya ya Kalle shi yace "banason is'kanci mashkur...."
Mashkur ya d'auki lemo guda d'aya ya tsiyaya acikin cup sannan yace "to na tambaye ka meyakamata mu tsara na bikin kaqi cewa komai, to bagara inyi abinda ya shafeni ba, Kai kasamu matar ne shiyasa kake mana is'kanci, nikuwa Sai yanzu nagani, Dan Allah Bro wannan ta farkon datazo, Ina ciki...."
Babban Yaya yayi ajiyar zuciya, cikin ransa yafara godewa Allah daba Waheeda ce takawo musu lemon ba π€£
Yatsani yaji wani namijin yana cewa yana sonta
Ya kalli mashkur yace"ni bazaka Jamin raini awajansu ba, kamusu magana da kanka, sannan babu abinda zamu tsara, ayi bikin haka, mashkur inaji araina matsawar narasa yarinyar danake so, to wallahi mutuwa zanyi...."
Mashkur dayakai cup din lemo bakinsa cikin sauri yafasa Sha ya ajiye, sannan ya Kalle shi da mamaki yace"kasan mekake fad'a kuwa Naufal?"
"yes, bazan iya daina sonta ba"
Mashkur yace "wacce me sa'ar ce wannan? Why not kafad'a mata? Mekake jira?"
Babban Yaya yace "lokaci yaqure min mashkur, bazan iya fad'a mata ba, Amma wani bangaren inaji ajikina ita d'in tawa ce"
Cikin sanyin jiki mashkur ya bubbuga kafad'arsa, yace "kayi hakuri Abokina, yanzu meka yanke akan hakan? Wanne irin mataki ka d'auka?"
Cikin damuwa yace "band'auki kowanne mataki ba, kawai Ina addu'ah de..."
"no, hakan ai yayi kad'an Friend, saura sati hud'u bikinka fa, kamata yayi mushirya muje Saudia, Nima zan tayaka da addu'ah Allah yabaka za6inka, idan har zai kasance alkhairi agareka, idan Kuma ba alkhairi bane Allah yabaka haquri da juriya akan rashinta "
Ransa duk adagule ya kalli mashkur yace "mashkur lokaci yariga yaquremin.... Itama aure zatayi, tayaya za'a fasa dawani ayi Dani? Tayaya zan rabu da wannan nacacciyar yarinyar ummi? Wallahi haushin ta nakeji, idan ta kuskura ta aure ni ko.... Wallahi saina mata filla-filla aranar da aka kawota kuma da niyya"
Mashkur ya kwashe da wata irin dariya sannan yace "Abokina bakada Dama wallahi, kadena wannan tunanin, kasa aranka zaka yarda da qaddara mekyau ko marar kyau, sannan karka manta komai yayi zafi maganin sa Allah, a lokacin daka shiga cikin matsala kadinga tunawa cewa akwai Allah.... Saboda haka yanzu ma shi zamu kaiwa kukan mu, me muke yanzu a qasar? Mushirya gobe mutafi Saudia, daga Nan kawai muwuce England.... "
Sai a lokacin Babban Yaya yasaki wata irin ajiyar zuciya, yace
" nagode Friend"
cikin farinciki suka rungume juna
Washe gari karfe goma a compound tayiwa Babban Yaya, sunyi waya da mashkur zasu had'u a Airport, Waheeda da Yanbiyu ne suka rakoshi har wajan motar dazai shiga, wayar Ummah tana hannun Waheeda, Huzaifa ne ya kirata cikin murna ta d'auka tafara masa magana Sai wani kashe murya take.... Babban Yaya yabude motar zai shiga ya kalleta yace "mahaukaciya..." π€£
Yanbiyu sunji abinda yace, sunsan cewa akusa yake, danhaka sukai murmushi suka juya ciki
Waheeda ta katse wayar sannan ta Kalle shi tace "Babban Yaya mekace?"
Cikin 6acin rai yace "bansani ba"
Jikinta ne yayi Sanyi, ta qarasa wajan sa tace "nayi laifi ne Babban Yaya? Kayi hakuri...."
Fasa shiga motar yayi, yafuto tareda d'ora hannun sa akan murfin motar, cikin masifa yace "au tambaya tama kike me kikayi? Kullum kina liqewa mutum saikace kaska, kwata kwata baki iya Jan aji ba, to Bari kiji, namiji tsanar mace me naci yake, marar aikin yi kawai..."
Kukane yakama Waheeda, ita tarasa meta masa tun ranar da aka kawo lefen ta yake daure mata fuska,komai tayi saiya dinga Jin haushinta, bata iya haqura ba saida ta rushe da Kuka Sannan tayi cikin gidan da gudu
Tsaki yasaki yanajin haushin zuciyar sa Kuma, Dan me zaisa Waheeda kuka? π€£Yanzu haka kukan ma ya haddasa mata ciwon Kai, wani tsakin yasake saki, yarufe motar zaibi Bayan ta, domin yabata haquri
"Salamu Alaikum"
Juyawa yayi yaga meyi masa sallama, budurwa ce Babba, wankan tarwad'a, tanada tsayi had'eda jiki, saide babu alamun kyau atare da'ita, hannunta d'aukeda wani flask d'in abinci,Kallan rashin Sani yayi mata, beyi mata magana ba yajuya zaiyi cikin gida
Cikin sauri Tariqo rigarsa tace "Husband baka ganni bane?"
Cak! Yaja ya tsaya a'inda yake, sannan ya Juyo cikin nutsuwa yacire hannunta data riqe masa Riga, ya kalli idonta yace "Dama kece?"
Ummi tayi farrrr da idonta, cikin yanga tace "nice, meyafaru ne Naga kamar kana cikin 6acin rai? To kayi hakuri ga girkina nakawo ma da hannu na nayishi, idan Kaci zakaji dadi"
Cikin tsananin 6acin rai yanunata da hannu yace "Ummi!!!, kidena damuna, kidena shiga cikin rayuwa ta, waike Ana so dole ne? Sau nawa zan fad'a miki Bana ra'ayin ki? Ba girki ba, ko kanki Zaki Bani bazanyi ra'ayin ki ba"
Cikin rashin kunya tace "qarya kake wallahi, Kai d'in wa? Dazaka dinga fadamin baqar magana, cemaka akai ni dinma sonka nake? Inaso na aure ka ne saboda duniya tasan cewa eh Nima na auri mashahurin mutum, Naga alama bakasan darajar mace ba, Amma duk lokacin daka aureni saina koyama yanda ake...... "
Cikin 6acin rai yakai hannu zai wanketa da Mari tareda wata irin tsawa yace"Ummi!!!"
Tsananin tsoro ummi ta tsorata da yana yinsa,jikinta ya d'auki rawa batasan lokacin da flask din hannunta yafad'i qasa ba, jallop rice din ciki ta zubeπ
Idanunsa harsun sauya Kala sun koma ja saboda 6acin rai, cikin sauri Hajiya Anty taqaraso wajan su tariqe hannunsa, shigowarta kenan gidan, ta tarar da wannan drama, cikin 6acin rai ta Kalle shi tace "Duka Kuma Naufal....?"
Yanda yaji tafad'i kalmar duka d'in kamar zatayi kuka duk Sai jikinsa yayi Sanyi, Amma sai huci yake, tunda yake ba'a ta6a yimasa rashin kunya kamar yanda ummi tamasa ba yau, Hajiya Anty ta maida Kallan ta wajan Ummi tace "kiyi hakuri, d'auki flask d'inki kitafi"
Ummi ta tsugunna ta d'auka, sannan ta d'ago ta kalli Hajiya Anty sannan tasakar mata tsaki, ta wuce tabar gidan
Babban Yaya yana ganin abinda Ummi tayiwa Hajiya Anty yabi Bayan ta zai damqo ta, Hajiya Anty ganin yabi Bayan ummi tasan tsaf zai lakad'a mata duka, Dan haka cikin sauri ta ruqoshi, tace "karabu da'ita nace"
"Amma Anty... Kina.... Kina ganin abinda tamiki fa..."
Yafad'i maganar a rarrabe cikeda qunan rai
Murmushi tayi tace "naji, karabu da'ita"
Jijjiga Kansa yayi, sannan yashiga motar sa yamata key yabar gidan,wajan Waheedan ma fasa zuwa yayi π€
πππ
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandamaπ: QN
Kwanan su uku a Saudia suna gudanar da addu'ah shida mashkur, gaba d'aya kashe wayoyinsu sukayi, ibada kawai suka sa agaba,Sai akwana na hudun ne sannan suka koma England.
Kwanansu hud'u da komawa England yakira wayar Hajiya Anty, Bayan sun gaisa yace "Anty kiyi hakuri akan abinda yarinyar Nan tamiki, na lura kwata kwata batada kunya...... Sannan duk laifin ku ne dakuka liqa min ita"
Murmushi tayi "son rigima, to kayi hakuri mana watarana zata dena, karka damu babu komai, baka fita wajan aiki bane Naga kiranka da wannan safiyar?"
"Ina gida Anty, yau babu inda zanje, zan zauna agida inyi shara, inyi mopping, inyi wanke wanke, Anty Allah nagaji...." ya qarasa maganar cikin shagwa6a
Murmushi tayi tace "yau Kuma shagwa6ar ce tatashi?, ko Inturo ma Waheeda?" tafad'i hakan tana so Tasha cikinsa ko zataji wata maganar
Murmushi yayi, yasan Sarai da biyu tayi masa wannan maganar, yaganota, cikin dakiya yace "tazo tamin me? Anty wannan yarinyar ai damuwa ce... Nayafe tayi zamanta"
Murmushi tayi tace "to shikkenan, yaushe zaka dawo?"
Yatsina fuska yayi sannan yace "ai kinsan zuwan nawa yana hannun Waheeda.... Idan tayi wani abun to zaku ganni, but nide ara'ayina bazan dawo ba Sai biki"
Dariya tayi tace "Haka Waheedan tazama? Karka yimata sharri" π
Sun dad'e suna zance, daga baya sukai sallama.
** *** **
Cikin hawaye yake yiwa Baban nasa bayanin komai, Alhaji Attahir ya Jinjina Kansa cike da 6acin rai, duk abinda d'ansa yakeso Tofa Shima yanaso, wacce irin yarinya ce wannan da zata rusa farincikin d'ansa? Kallan sa yayi yace "ita yarinyar bazata iya hakuri harna dawo daga tafiya ba, insamu iyayenta muyi magana dasu? Yar gidan wacece ne?"
Cikin kuka Didat yace "yarinyar Alhaji Umar Arabo ce"
Alhaji Attahir yace "Nasan Alhaji Umar, ka kwantar hankalinka, zamuje dakai ayi magana, dole a warware wannan maganar auren datace anyi dawani, dakai za'ayi wannan auren, ka kwantar da hankalinka kaji?"
Kakar Didat dake zaune agefe tayi murmushi, ganin mahaifin nasa zai samo masa abinda yake so, haqiqa tana tsananin son Didat, bata son abinda zai shiga tsakanin sa da farincikin sa, tun Bayan rasuwar mahaifiyar sa, itace taci gaba da Kula dashi, shiyasa take jinsa har cikin zuciyar ta
** *** **
Tafiya suke ahankali agefen titi suna hirarsu ta qawaye, Maya ta kalli qawar tata, "gaskiya qawata na gode da ziyara, naji dad'in zuwanki gidanmu"
Waheeda tace "Dama rashin dama ne yasa Bana zuwa ai"
Maya ta kalleta tace "yanaga yanayin ki kamar kina cikin damuwa?"
Ajiyar zuciya tayi "wallahi Maya, Babban