Showing 18001 words to 21000 words out of 77020 words
Chapter 7 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
tsufa? "
Baba yusha'u yace" eto, saide wata tsohuwar wayata data lalace idan aka kirani banaji Kuma ba'a Jina, Kuma murfin wayar baya zama da kyauro nasa nariqeta, kafin hajiya ta sauya min wannan "๐คฃ
Babban Yaya yace
"yawwa, Bani ita"
Baba yusha'u ya Dauko yabashi, yakar6i kayan yajuya yashiga motarsa sannan yabar gidan
Kai tsaye Gida yakoma, yabar kayan acikin motarsa, yanbiyu da Waheeda suna falo sunacin abinci, Ummah tayi masa sannu da zuwa tana Bawa yanbiyu magani, zama yayi a kujerar yace "Ummah wace ba lafiya Kuma?"
Yanbiyu ta nuna masa tace "gasunan, kasan halin jinyarsu ai, idan daya tafara dayar ma Saitayi, Wai cikin su ne yake ciwo"
"ok Allah yasawaqe"
Ya kalli Waheeda yace "ki gama nakai ki islamiya tunda su babu lafiya"
Ranta ne ya6aci cikin shagwa6a tace "to Babban Yaya subazasujeba saini kadai? Lafiyarsu kalau wallahi, tsabar sharri ne kawai"
Wani irin kallo yamata, Nan take tayi shiru ko qwaqwqwaran motsi bata sake yiba
Dinning ya nufa da Kansa, yazuba abincin yanaci yana Kallan TV sama sama, har Waheeda tagama taje daki tafuto cikin shirin islamiya, ta kalli Ummah tace "Ummah zan tafi, saimu dawo tareda Maya, tunda yanbiyu bazasuje ba yau"
Ummah tace "saikun dawo"
Tashi yayi zai fita, ya kalli Ummah yace "Ummah naje gidansu Nadiya"
Murmushi Ummah tayi tace "Aida kabari Sai gobe, yanzu Naga alamun Garin akwai hadari, Amma idan kaje gobe zakufi sakewa ku Tattauna"
Yace "no,Ummah zanyi sauri naje insha Allah"
Cikin farinciki tace "to a dawo lafiya, ka kula da kanka"
Waheeda tace "to Ummah karki damu Nima zan kula dashi"
Ummah tace "Allah ya shiryeki Waheeda"
Waheeda tashiga gidan gaba taja murfin motar tarufe, tajuyo taga Babban Yaya yana Kallan ta, idanunta tajuya tace "Babban Yaya lafiya?"
"meyasa kikasa Ribom a kanki?"
Dariya tayi tace "laaa Babban Yaya bafa Ribom bane"
Muryarsa ya rage kamar yana tsoron wani yaji sannan yace "qarya kike yi, to mugani"
Hannu tasa tajanye hijabin daga kanta, dogon gashinta Mai tsantsi ya baiyana, ta dago tana Kallan sa tace "kagani?"
Ahankali yakai hannunsa kan gashi Nata, ya gyara matashi, sannan yace "nagani, mayarda hijabin"
Kallansa tayi tace "Babban Yaya idan baka so nadinga acuci da gashina kabani kudin kitso"
Kafadarsa yadaga yace "no, karkiyi kitso, kibarshi haka yafi"
Babu musu tace masa "to, mutafi karna makara"
Gyara zama yayi yace "kinsan de Banason aure yanzu ko?"
Mamaki yakama Waheeda, takasa magana saita gyada masa Kai kawai, ajiyar zuciya ya sauke, yakai hannun sa Mai laushi yakamo Nata hannayen yace "su Baba Habu sun hadani da wata yarinya Nadiya, idan na saukeki a islamiya wajan ta zanje yanzu, inaso na gwada sa'a ta ko Allah zaisa narabu da'ita"
Waheeda ta kalli qwayar idonsa, tana so ta tambayeshi abinda yadade Yana yawo a ranta, Amma tana tsoro karya mata fada, dakewa tayi, tayi jarumtar cewa "to Babban Yaya meyasa baka son auren? Sune baka so kokuma auren ne duka baka so?"
Kai tsaye yace "sune banaso"
Cikin mamaki tace "towa kake so?"
Kallan manyan idanunta yayi yakasa bata amsa, Waheeda taga Sai Kallan ta yake tace "Babban Yaya kayi shiru kana kallona"
Hannunta yasake riqewa cikin nasa hannayen yace "Aike qanwata ce, damuke uwa daya uba daya hakane ko?"
Waheeda ta gyad'a masa kanta alamun hakane
Yaci gaba da fadin "tunda ke qanwata ce, ke jini nace, idan kika kalli qwayar idona, zakiga yarinyar danake so" (tofa)
Matsowa tayi kusa dashi haryana jin saukar nunfashin ta akan fuskar sa, tazuba masa ido tana so ta tabbatar da maganar sa, Sai can tadawo ta zauna yanda take da, tace "banga komai ba Babban Yaya banda baqi dayake cikin fari na idonka" ๐
Murmushi yayi dimple dinsa suka futo, yace "naji, wannan maganar tazama sirri tsakanin mu, banaso kowa yaji, sannan baqin gawayi nakeso kisamomin acikin gida yanzu"
๐ณZaro ido tayi tareda rufe bakinta da hannunta tace "nashiga uku Babban Yaya qona Nadiyar Zakayi idan kaje?"
"banason shirme Dan Allah, amfani zanyi dashi, guda daya nakeso kisamomin"
Tunani tafara saida tagama ta Kalle shi tace "Babban Yaya ai kasan Bama qona gawayi, Amma Naga Ummah tanada wani na leda Wanda take sakawa akan gas idan yayi zafi saita saka turaren wuta, saide inje in Dauko mashi, Amma idan kaji tana jaje karkace nice"
Yace "nida kika kawo min tayaya zan fada? Yi sauri kije ki dauko"
Cikin sauri tafice daga motar tashiga falon da gudu, taje Dakin Ummah Allah yaso tana toilet, tayi sauri ta dauko ledar gawayin guda daya, ta6oye acikin hijab,ta kawo tamiqa masa tace "gashi"
Cikin mamaki tasake Kallan sa tace "Laaaa Babban Yaya yanaga ka sauya Kaya kasaka wannan tsumman? Cemata zakayi Kai mahaukaci ne?" ๐๐
Kallan ta yayi yace "saide in kece mahaukaciya" ya dauki gawayin guda daya yarabashi abiyu, yafara shafawa a fuskar sa da hannun sa, ya dauki wani rawani ya nada a Kansa,yacire agogon hannun sa, yanda yayi baqi ba zakace shine ba, Waheeda tayi shiru tana Kallan ikon Allah, saida yagama 6oye kamar sa sannan yaja motar suka tafi, agaban islamiyar ya faka motar yaqi fita, saida ta Kalle shi tayi murmushi sannan tayi masa bye bye tafice daga motar
Gidansu Nadiya ya nufa
Kafin ya qarasa ya tsaya yafaka motarsa acan nesa da gidan, sannan yafuto yatare wani Dan adedeta yace "Aron Napep din nake nakeso"
Dan adedeta ya kalli adedetan sa Sabo fil dashi, sannan ya kalli Babban Yaya yace "kamarya aro?, malam bansan kaba tayaya zan dauki sabon adedeta na nabaka?"
Babban Yaya yace "kaga mota na Nan, ka tsaya anan kajirani yanzu zan dawo"
Dariya Dan sahun yayi yace "hauka nake zan yarda dakai? Tayaya zaka mallaki wannan motar? In hakane meyasa zaka nemi Aron abun Hawa?"
Kansa yadafe, ya nufi motar ya Dauko agogonsa yabashi yace "yanzu kaga shaida mota tace ai ko? Kariqe wannan agogon idan ban dawo ba kaje ka saida shi zai iya siya Maka sabon adedeta harda Yan canji"
Dan adedeta yayi shiru yana nazari, badan ransa ya soba yafuto yabawa Babban Yaya, Nan da Nan Babban Yaya yahau yatuqa da bissmillah aikuwa adedeta yafara tafiya, baiyi gudu ba ahankali yake tafiya harya qarasa gidan, yana zuwa yahango wata budurwa tana tsaye dawani saurayi me mota, motar ya kalla ya kalli wayar hannun sa, wayar hannun sa kadai zata Iya siyan motar gayen, cikin sauri yakashe ta, yasaka acikin aljihu, sannan yafuto daga adedetan nasa ya tsaya yana Kallan su yana daddanna wayar baba Yusha'u megadi wadda taji wahala harda kyauro ajikinta
Kallan sa budurwar tayi suka kwashe da dariya itada saurayin, Babban Yaya ya qarasa wajan su tareda Bawa saurayin hannu yace "Salamu Alaikum"
Saurayin ya Kalle shi daga sama har qasa yaga wani fatattakekken takalmi aqafarsa, yaga fuskar Nan tayi wani irin baqi, ya girgiza Kai tareda dauke Kansa, budurwar ta Kalli saurayin suka hada ido suka sake kwashewa da dariya
Babban Yaya yasosa girarsa guda daya da key din adedeta dayake hannun sa, abunda yariga ya zama dabi'arsa
Ya kalli Budurwar
Yace "Dan Allah Ina neman Nadiya ne"
Tace "nice Nadiya, ya akayi?"
Kai tsaye yace "Ina son magana dake"
Yatsina fuska tayi tace masa "me?"
Saurayin Nata yace "a a Beby, jeki kiji abinda yazo dashi, kika Sani ko neman sadaka yake?"
Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yakoma jikin adedetan sa,Nadiya ta biyo bayansa tana mamaki gashi talaka futuk daga Gani Amma yanayin tafiyarsa kamar ta manyan masu kudi, suna zuwa jikin adedetan ya kalleta yace"Nadiya inason ki, idan bazaki damu ba inaso mu qulla alaqa dake, alaqa ta har abada,Amma ni banida kudi, talaka ne ni idan har kina sona tsakanin ki da Allah, ni banida matsala, bazan 6oye miki komai ba, gidanmu munada yawa kusan mu talatin ne, sannan Mahaifiyata batada lafiya, Paralyze take yi, aikinsan Paralyze ko? "๐ณ๐๐ปโโ๏ธ๏ฟฝ?
Nadiya ta jinjina masa Kai tana jin wannan labari nasa,inbanda rainin Hankali meyake nufi da mahaifiyarsa babu lafiya? Tsayuwa ta gyara tace"kana nufin nice zanyi jinyar mahaifiyar ka kenan idan ka kaini gidanka? Sannan acikin mutum talatin din zanyi rayuwa?"
Babban Yaya yace "Allah yamiki Albarka, nasan tunda kinada Hankali Zaki kula da Mahaifiyata, sannan kinga wannan adedetan?" yafadi haka yana buga jikin adedetan๐
Nadiya ta daga masa Kai tace "Nagani"
Yaci gaba da fadin "to sojan hayane, banawa bane, kudin nake Tarawa idan suka cika dubu Dari shida saina Bawa meshi, kinga shikkenan daga Nan yazama nawa" ๐๐ฑ
Nadiya tasake jijjiga Kai tace "cigaba Ina jinka"
Babban Yaya yace "idan kika amince Dani, ba zakiyi DANA SANI ba
(My First Novel DANA SANI)
tun lokacin Dana fara ganinki naji duk duniya babu wadda nakeso saike, insha Allah namiki alqawari idan kika amince Dani, ba zakiyi nadama ba, saboda zan hada miki lefe nagani nafada, Sai Wanda yagani, sannan Kuma.... "
Kafin yaci gaba da magana Nadiya ta daga masa hannu โ๐ปtace" dakata malam, nayi ma kama da wadda zatayi jinyar mahaifiyar ka?,konayi ma kama da wadda zata auri Dan adedeta? Bari kaji, ni matar manya ce, akwai Wanda nakeso, Big Brother yana Nan zuwa, kar yazo yaganni dakai ya raina min Hankali, danhaka Sai anjima... "
tajuya tayi gaba, Babban Yaya yafara kiranta yana fadin "Nadiya! Nadiya!!"
Amma tayi banza dashi,Shima Dama Kiran Nata dayake qarfin Hali ne kawai, dama baya so tajuyo ๐
Babu musu yashiga cikin adedetan yatafi, yana zuwa wajan Dan adedetan ya futo yabashi key dinsa yace "nagode gashi"
Dan adedeta yace "Wai harka gama? Naga ko Minti talatin bakayi ba"
Motar sa yabude yashiga yace "nagode"
Cikin sauri Dan adedeta yace "toga agogon Naka"
Babban Yaya yace "Kabarshi kawai" yarufe motarsa yatafi,saboda hadari ne yake San tasowa, Kuma yanaso yaje ya Dauko su Waheeda a islamiya
*** ** ***
Tafiya suke ahankali suna zancen su gwanin sha'awa, Maya tace "Waheeda ki dinga sauri mana, ko bakya ganin hadari"
"ke barni inyi tafiya ta yanda nakeso, idan sauri nakema jikina ya dinga rawa kenan, nikuma banason wannan rawar"
Maya ta kwashe da dariya tace "su Waheeda manyan yanmata, zan so Naga mijinki Waheeda"
"Zaki Gani Maya, kijira munayin candy Sai aure nikam, banaso naci gaba da karatu, nafiso nayi aure na indinga kula da mijina, in shaga6ashi inyi masa abinda yakeso, kinga lokacin saina tafi makaranta, tun yanzu ma mata suna nemana, idan natafi University wakike tunanin zai nemeni? "
Kai tsaye Maya tace"Maza, Amma Kuma kinsan de Babban Yaya baya so ki dinga kula samari ko? Tayaya Zaki samu mijin? Bayan munkusa gama makaranta?"
" can ta matse muku keda Babban yayan, nikam daga Candy Sai aure insha Allah "
Maya tace"gaskiya yarinyar Nan wuyanki ya'isa yanka, nikam yanzu Ina Bayan Babban Yaya, tunda yabani kudin makaranta bazan taba mantawa da alkhairinsa agareni ba, Dan haka dole indinga tuna miki dokarsa a kanki "
Kafin Waheeda tace wani abu anfara yaiyafi, neman wajan 6uya suke Amma sun Rasa, abun Hawa suka fara tarewa Amma kowanne baya tsaya wa, ruwa yaqara karfi Nan da Nan mutane suka fara gudu musanman maza, ruwa yayiwa su Waheeda duka saboda babu mafaka, suna cikin wannan halin Babban Yaya yaqara so, yana zuwa yafuto daga cikin motar yanufesu, Waheeda taga ya sauya wannan kayan daya saka na dazu, murmushi tayi, cikin shagwa6a tace "Babban Yaya shine kaqi zuwa da wuri gashinan ruwa yamana duka nida Maya"
Bece da'ita komai ba, kawai gaban motar yabude mata, tareda fadin "I'm sorry, shiga"
Maya tana tsaye tana Kallan su, lalle Babban Yaya yana son Waheeda, wanne Yaya ne zai budewa qanwar sa mota saikace wata budurwar sa? Anya kuwa yayanta ne?
Saida Waheeda tashiga sannan yarufe, itama Maya tayi sauri tabude gidan baya tashiga, zagayawa yayi yashiga motar, yajuyo yana fuskantar Waheeda, cikin sigar lallashi yace "Sorry"
Bakinta ta turo gaba taqi magana, yasaka hannu yakamo kyakykyawar fuskarta yace "kinji"
Murmushi tasaki, dimple dinta suka futo, tace "shikkenan, Kuma alqawarin dazu, bazan fadawa kowa ba"
Murmushi yayi Shima yace "good girl"
Maya tayi gyaran murya, Dan taga alamun sun manta tana motar ๐
Tace "Babban Yaya Ina wuni"
Firgigit ya dawo haiyacinsa, shaf ya manta tana cikin motar, a taqaice yace "Lafiya"
Sannan yaja motar suka tafi, suna hanya Waheeda Sai zuba masa surutu take, Amma amsar dayake bata batada yawa, har suka qaraso gidansu Maya, suka ajiye ta sannan suka dauki hanyar gida, Bai wuce dasu gida ba saida yashiga tawani shago yasai mata waya qirar iPhone, ya ajiye agaban motar sannan yaja motar suka qarasa gida
Yana tsaida motar a compound din gidan nasu, Waheeda tafara kokarin fita, tana kama handle din kofar taji taqi buduwa, tajuyo tace "Babban Yaya bude"
Wayar daya siyo ya Dauko ya 'Dora mata akan cinyarta yace "Gashinan, nasan inda kinada waya Zaki kirani kicemin kun tashi, bazan Bari ruwa yamiki duka ba kamar yau"
Waheeda tafara kokarin budewa, tana Ganin wayar tasaki wani ihun murna ta rungume shi, yana jin yanda tudun qirjinta yake mintsininsa cikin ransa yace "yasalammmm!"
Daurewa kawai yayi, ahankali yazareta daga jikinsa yace "bansan yaushe zakiyi Hankali ba, kina ta6ani any how kamar wani muharraminki"
Kwata kwata Waheeda batama kalli inda yakeba bare tayi nazari akan kalamansa, cikin murna tace "Toda menene inba Shiba? Babban Yaya, nagode, Allah yasa kadinga cin ball a koda yaushe, Allah yaqara girma"
Saida ya hadiye wani irin yawu, sannan yace "Amin" yabude mata motar tafita dagudu tanaso ta nunawa yanbiyu itama tayi waya
Da daddare suna kallo gaba dayansu, Waheeda tana saka number Yan gidan tana saving dinsu cikin sabuwar wayarta, yanbiyu suna nuna mata wasu abubuwan da bata Sani ba, su Sa'ad da Sa'eed tareda Babban Yaya Sai labarin qwallo suke, Babban Yaya anta6o masa inda yakeso, wato zancen qwallo, Sai hira suke sunata dariya kamar bashi ba, Ummah ta Kalle shi tace "Yayansu Yaya kukai kaida Nadiya ne?"
Kallan ta yayi yace "Ummah naje tace bata sona"
Gaba dayansu Yan falon suka Juyo suna Kallan sa, wacce yarinya ce zatace bata son yayansu?
Ummah tace "kamarya?"
Juyowa yayi yasake Kallan Ummah yace "Ummah ki tambayeta kiji, naje nace mata Ina sonta, kifada mata nine naje da adedeta saboda motata tasamu matsala a hanya, Kuma tace koda na aureta bazata iya kula dakeba Ummah,sannan tare naganta dawani Gaye suna zance, kinga kenan itama tanada Wanda takeso,to menene amfanin auren ta? Ummah duk wadda bazata iya kulawa da mahaifiyata ba, bazan iya auren taba "
(Kai Babban Yaya irin wannan batu haka ๐คฃ๐)
Ummah tadauki wayarta takira wayar maman Nadiya, Bayan sun gaisa maman Nadiya tace
" Hajiya Baqon namu Kuma baizo ba, muna ta jira angama shirya masa abin motsa baki Amma Nadiya tacemin baizo ba Kuma bai kira wayarta ba"
Ummah tace" Yanzu nake tambayar sa yacemin yazo tace masa bata sonsa, Wai tace bazata iya kula daniba koda ya aure ta"
Maman Nadiya yace "Anya hajiya itace kuwa? Amma Bari inkirata"
Ummah tanaji maman Nadiya ta daga murya takira Nadiya, nadiya tana zuwa maman ta tace "Big Brother yazo kince masa bakya sonsa, kince kokin aure shi bazaki kula da umman saba, anyi haka ko ba'ayi ba?"
Nadiya tanajin wannan bayani tatuna mutumin dayazo wajan ta dazu a adedeta, ta d'ora hannunta aka ๐๐ปโโ๏ธtafashe da Kuka tace "wallahi mama bansan shibane, yaudara ta yayi, Allah Ina sonsa" cikin kuka tanufi dakinta da gudu
Maman Nadiya ta sassauta murya tacewa Ummah "Hajiya komai fa ya lalace, zamuyi magana daga baya" daga Nan ta kashe wayar
Babban Yaya ya kalli Ummah yace "Ummah kinji da kunnanki ai naje ko?"
Cikin bacin rai Ummah tafara girgiza kafarta tace "naji Naufal, ai banyi tunanin yarinyar zatace bazata kula daniba, bansan haka tarbiyar ta takeba"
Wani farin ciki ne ya mamaye shi, yaga Ummah ta yarda da komai, to tun kafin waccan Nadiyar tazo ta musu bayanin komai ta fada musu 6oye kamarsa yayi, Gara yagudu yabar qasar๐
Cikin ladabi yace "Ummah, muna shirye-shiryen fara World cup very soon, zan fara training Jibi, Insha Allah gobe da Asubar fari zan wuce" ๐๐
Ummah tace "Allah yakaimu Son"
Firar da ba'a qarasa dashi ba kenan, ya wuce dakinsa ransa fess๐๐ป
Sonake agano min iyayen wadannan taurarin guda biyu NAUFAL DA WAHEEDA
To Babban Yaya yatsira wannan lokacin, kome Waheeda zata aikata ya dawo dashi qasar?
Amnah El Yaqoub โ๏ฟฝ?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama๐: BABBAN YAYA
Writing By Amnah El Yaqoub
Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
11&12
Suna tashi da safe sukahau shirin school,awajan break fast Waheeda taga babu Babban Yaya, anan taji cewa yatafi tun asuba kamar yanda yafada jiya da daddare
Bataci wani abincin kirki ba, Sai tea me kauri, ta kalli 'yanbiyu taga Sai lokacin zasu fara cin abincin, tatashi tayi d'akinsu da gudu
Kowa yabita da kallo Amma babu Wanda ya tanka mata, wayarta tad'auko ta kunna ta sannan takira Babban Yaya, a lokacin suna cikin jirgi har anfara sanarwa a kashe waya jirgi zai tashi, yayi mamakin ganin number ta tana kira, already yanada number tun jiya yayi saving d'inta a wayarsa
Dauka yayi tareda cewa "Lafiya ko laifin kika sake yi?"
Dariya tayi tace "Babban Yaya,Aina Dena laifi yanzu, nayi Hankali Nima"
Yace "Allah yasa, kinga de wannan Karon munrabu lafiya dake, banaso wani abu yasake faruwa kisa in dawo qasar Nan kwana kusa, kinga yanda nasamu narabu da rigimar su Ummah akan yarinyar Nan Nadiya, to banaso kisake aikata wani abun dazaisa nadawo Nigeria ta dalilin ki "
Bakinta ta turo gaba kamar yana Kallan ta, sannan cikin shagwa6a tace" Babban Yaya to ai wannan dinma ba nice da laifi ba, Basaida na nuna ma abinda akamin ba?"
Runtse idonsa yayi, Waheeda zata kashe shi, yadade da mantawa Amma saida tasa ya hango cikakkun breast dinta a'idon zuciyar sa, cikin sauri yace"naji,naji, menene Kuma saikin tuna min?" ๐
Tace "to Babban Yaya kayi hakuri, yaushe zaka dawo?"
Kai tsaye yace "Babu rana, kuma nafada miki banaso kema kiyi sanadin zuwana Nigeria"
"Angama Babban Yaya, Allah yakiyaye hanya" daga haka ta kashe wayar Tata, Takoma falo,Ummah ta kalleta tace "lafiya?"
Tace "Da Babban Yaya nayi waya"
Sa'eed yace "um kaji masu waya"
Dariya tayi kawai, ta jira yanbiyu suka gama sannan suka fita compound driver ya daukesu suka tafi
Bayan uncle ya fita daga ajin nasu,Maya ta kalli Waheeda tace "Waheeda waiya kuke da Babban Yaya ne?"
Kallan Maya tayi tace "Kamarya ya muke? Mekike nufi?"
Maya tace "Ina nufin Wai Ummah ce ta haifeku dukanku?"
Kai tsaye tace "itace mana, me kikaga?"
"babu abinda nagani Waheeda, kawai de Naga kinshaqu dashi fiyeda yanbiyu, sannan Shima yana sonki sosai, shine nace koba Ummah ce ta haifeku ba"
Waheeda tayi mata wani banzan kallo tace "toba Ummah ce ta haifemu ba waye yakawo mu duniya Kenan? Nasan