Showing 21001 words to 24000 words out of 77020 words
Chapter 8 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
nashaqu dashi yanda bakya zato, saboda tun Ina qarama nasaba dashi, sannan dakika ce yanaso na wannan Kam Ina tantama, saboda idan yana sona ma, to wannan soyaiyar dayakemin bata hanashi yamin hukunci, idan nayi laifi zaneni yakeyi wallahi, kinbani mamaki Maya, ashe zarginmu kike "
Maya tace" innalillahi.... Waheeda zargi Kuma? Meyasa zan zargeku Bayan yayanki ne uwa d'aya uba d'aya? Kawai de kun birgeni ne jiya danaga yanda yake baki kulawa, harfa mota yabude miki, shine nayi tunani idan ku masoya ne abun zaifi dadin Gani, yana miki soyaiya kina maida masa martani "
Cikin masifa Waheeda tace" A'uzubillahi.... Maya kamar wata marar Hankali Zaki dinga dangantani da yayana?"
Maya ta kamo hannunta tace" yi hakuri qawata, nabata miki rai, kiyi hakuri Dan Allah "
Waheeda tayi banza ta qyaleta, har wani uncle din yashigo ajin yafita, bata sake kula Maya ba, Sai tsaki take saki ita kad'ai
Bayan sun koma tana duba wayar ta taga missed call dayawa da wata number, cikin mamaki tace "to waye wannan ya kirani har 5 missed call da number daya?"
Kiran number tayi, cikin zazzaqar muryarta tace "Naga kirane waye?"
Cikin salon yaudara akace "kira Kuma? Da wannan number?, Kai may be mistek ne"
Ba tace komai ba ta kashe wayarta
Bayan kusan minti biyar wannan number tasake kiranta, harta d'aura towel tana shirin shiga wanka, tadawo ta d'auki wayar, "Amincin Allah ya tabbata agareki sarauniyar kyawawa"
"Amin, Lafiya?"
abinda tace masa kenan
Yace "bekamata mace kamar ki, tayimin wannan tambayar ba kyakykyawa, ai kinsan ta tsuniyar gizo bata wuce ta qoqi, wallahi tunda kika amsa wayata dazu, naji hankalina ya kwanta dake, nasan aduk inda kike, ke mace ce Mai nutsuwa, me tarin Hankali da cikar haiba, uwa uba tare da kyau "
Kalamansa sun ratsa Waheeda, da atsaye take, Amma yanda taji yana zubo Nata kalamai, saita nemi bakin gado ta zauna
Yanbiyu suka shigo Dakin kowacce tana ajiye Jakarta, Ihsan tayi toilet da gudu saboda fitsarin daya matseta, inti Kuma ta kwanta agadon
Waheeda tajuya idanuwanta tace "nagode, naji dadin yabonka agareni, kafadamin meyafaru?"
Intisar tadago daga kwanciyar da tayi, ta kalli Waheeda, taji tawani sauya murya tana waya da alama da wanine
Daga nasa bangaren yace "zan so kibani Dama indinga jin wannan zazzaqar muryar Taki koda sau daya ne a rana"
Kai tsaye tace "inde Dama ce nabaka, menene acikin muryar tawa?"
Yace "bakisan menene acikin muryarki ba? Muryarki tana d'aukeda wani sinadari, duk Wanda yajita, dole ne tatafi da Imaninsa"
Dadi yakama Waheeda, ashe muryarta tanada dadi shiyasa Babban Yaya yahanasu kula Samari, ashe Dan karsu hadu da samari su dinga yabon baiwar murya me dadi irin tasu shiyasa yaqi dadi yahanasu kula samarin
Cikin jin dadi tace "Nagode sosai, baka fadamin sunan ka ba"
Yace "Af... Aina manta ban fada miki sunana ba, gaba daya nagama shagaltuwa dajin wannan daddad'ar muryar Taki ne, sunana Hassan, Ana kirana Sas, ni soja ne, iyayena da kowa da kowa nawa suna zaune a kaduna, iyayena suna damuna inyi aure, nikuma har yanzu ban hadu da wadda nake soba, tun Bayan rabuwa ta da budurwata ta farko "
Waheeda tace" Allah sarki, Allah yabaka mace tagari, nikuma sunana Waheeda, Ina Garin kano, Ina zaune a unguwar, Amma inaso kabani labari menene yahada ka da budurwarka har kuka rabu? "
Yace" Waheeda sunanki nada dadi kamar yanda muryarki Takeda dadi, zan baki labari anjima idan kin Bani damar sake kiranki Akaro na biyu, saboda alfarmar Dana nema shine indinga kiranki sau daya a rana "
Waheeda tace"nabaka Dama ka kira"
Cikin farin ciki yace "yanzu kin amince indinga kiranki sau biyu kenan a rana?"
Kai tsaye batare da tunanin komai ba tace "Na'amince"
Yace "nagode Yar'uwata, gaskiya kinada hali Mai kyau, please ki kula da kanki karki Bari ko quda yata6a ki"
Cikin farin ciki tace "to shikkenan" sannan ta kashe wayar
Ihsan da Intisar da tun dazu suke Kallan ta sukace "dawa kike waya Waheeda?"
Harararsu tayi tace "miye naku? To da saurayi nake waya, soja ne, Kuma ni tundaga yanzu ya kwanta min araina, so kuke naqi kula samari kamar ku daga qarshe a hadani da wani a dangi? To banason auren had'i, danhaka samari na zan kula"
Intisar tace "aikuwa wallahi baki isaba, bazakija Babban Yaya yazo ya qwace mana wayoyin muba, tunda yahanamu, kega me kunnan qashi ko?"
Waheeda tace "kunnan qarfe Bana qashi ba,nide saina kula samari, ku Kuma dakuka tsaya Babban Yaya yamuku hud'uba, to saikuje kuyi tayi, bakusan halin Babban Yaya bane, kaiku zaiyi yabaro"
Ihsan tace "Waheeda idan kika kuskura kika sake fadar wata magana dangane d Babban Yaya na rantse da Allah Sai munyi miki duka a Dakin Nan, qarqari kice Ummah zatazo cetonki, to wallahi kulle kofar zamuyi saimun nuna miki jiki, banza marar kunya" tafadi haka tareda kokarin cire uniform dinta.
Waheeda tace "ku kasheni ku kaiwa uwata gawata, qarshe kenan" tafadi haka, tareda shigewa toilet domin watsa ruwa
Sas soja bai sake Kiran Waheeda ba Sai dare, a lokacin harta matsu ya kirata, a zaune suke afalo yakira, tana dagawa tayi cikin dakinsu da gudu, kowa yabita da kallo gaba dayansu sunyi tunanin Babban Yaya ne ya kirata, yan biyu ne kawai suka San abinda take 6oyewa, kwanciya tayi akan gado,tana yi masa sallama, Bayan sun gaisa tace "Ina jinka, tun dazu nake jiran kiranka, Amma baka kiraba"
"kiyi hakuri sarauniyar kyawawa, oganmu ne ya kirani, kinsan sojoji babu zama"
Murmushi tayi tace "Ina jinka, kabani labarin abinda yarabaka da budurwarka"
Yace "Mun dad'e tareda yarinyar,kinga nide soja ne, Amma bantaba yin kuka ba Sai akan yarinyar Nan, nayi kuka kamar zanyi hauka, Waheeda muna cikin soyaiya da yarinyar Nan har ankai kudin gaisuwa da komai, mamanta tace ai akwai Wanda ta yiwa alqawarin auren ta, waje daya suke aiki dashi, haka aka bamu hakuri, akwai gida na bakiga yanda na tsara Shiba, Sai hakura nayi dashi nabawa qanina shi, gashi nine Babba a gidanmu, kowa so yake nayi aure, yanzu haka lefen Dana hadawa yarinyar suna Nan, kawai wasu qananun abubuwan ne ba'a saka ba, yanzu gashi narabu da'ita komai ya zama tarihi, saide in nemi alfarma awani waje ko za'a Bani Dama "
Waheeda ta Lumshe idonta tace" wacce irin alfarma kenan?"
Yace" Alfarma mana, nasamu Dama nashiga cikin zuciyar ki, kibani key dinta na kulleta, ta yanda babu wani d'a namiji dazan iya bud'ewa bare yasamu damar shiga "
Tace"to inde wannna ne, nabaka Dama, Allah ya tabbatar mana da alkhairi "
Farinciki yakama Sas, yace"amma inaso namiki wata tambaya guda daya"
Tace "Ina jinka"
Yace "gashi bamu taba ganin junaba har mun qulla alaqa, meyasa kike sona?"
Ajiyar zuciya tayi tace "gaskiya nayaba da Hankalinka, dakuma tarin nutsuwarka, wannan kawai shine"
Murmushi yayi yace "zakici gaba da sona Waheeda idan kikai tozali Dani? Karnaje dadin baki kikemin, saboda nide baqi ne, banida d'iqon fari kod'aya ajikina, ni baqi ne"
Waheeda tayi shiru tatafi tunani, tatuna wata hira dasuka ta6ayi dasu Neenah aboarding, sunce mata maza baqaqe sunfi lafiya ko a wajan aure, sunfi fararen mazaje bada himmaπ
Sas yace "kinyi shiru Waheeda"
Cikin sauri tace "ai nafison irinsu, Allah yabarmu tare"
Yace "Amin, yaushe zanzo naganki kiganni? Banaso ki ganni awaya kiji bakya sona Waheeda, Gara nazo ki ganni a zahiri, sannan inyi magana da babanku cewa Ina sonki, inaso na aureki idan kin kammala makaranta"
Waheeda tasake yin qasa da murya tace "Allah yakawo ka lafiya"
Yace "to shikkenan, ki kulamin da kanki, karki manta kiyi alwala sannan kiyi addu'ah kafin ki kwanta"
Waheeda tayi hamdala cikin ranta, ta San cewa tabbas tayi dace da samun Miji na gari
Duk abinda take 'yanbiyu suna ganin ta, basuce mata komai ba saboda idan sunyi mata magana ma rashin kunya zata musu, kawai de sunsa aransu duk lokacin da taja Babban Yaya yahanasu riqe waya Sai sunyi mata dukan mutuwa π
Tsawon sati biyu Waheeda ta d'auka tana waya da soja, ba tareda kowa nagaidan yasani ba, daga ita Sai yanbiyu ne kawai suka sani, zuwa wannan lokacin Hankalin Babban Yaya ya kwanta, yanayin ball d'insa cikin nutsuwa bashida damuwar komai, tunda yaga yayi sati d'aya, yayi biyu, har uku, ba'a kirashi agida akan matsalar Waheeda ba yasan cewa taqara Hankali, idan yaga Kiran Ummah har d'auka yake cikin nishadi, yasan cewa kawai gaisawa zasuyi.
Cikin sati na hud'un ne Sas yace mata zaizo yaganta ranar asabat, ranar kuwa tun safe takasa zaune takasa tsaye, yanbiyu tun kafin su tashi daga bacci tafara tashinsu, cikin ladabi tace "Inti yau Soja zaizo, mezan shirya masa?"
Intisar tace "waida gaske zuwan zaiyi? Bakya tsorone Waheeda?"
Bakinta ta turo gaba tace "Toni Ina sonsa, Dan Allah Kuna 'yan'uwana mata idan Baku Bani goyon baya nafita kunyar sa ba, wakuke so yabani?"
Tausayin ta yakama Intisar, tajuya ta kalli Ihsan, Ihsan tace "kinga Inti babu ruwana, idan Babban Yaya yaji, mezamu ce masa?"
Waheeda tace "Kai Ihsan Dan Allah, idan Ummah ta tambaye ku karkuce saurayina ne, kawai kuce mata Dan makarantar mu ne, ba shikkenan ba?"
Nan take,Waheeda ta kalallame zuciyar 'yan'uwan Nata, suka d'auki shawarar data basu,Waheeda ta wuce kitchen tafara hadawa soja kayan makulashe
Karfe hudu na yamma, soja yazo, d'an sahu ne yakawo shi har unguwar ya ajiyeshi, yakira wayar Waheeda yasanar da'ita yazo
Rabonta da saka mayafi harta manta,saboda Babban Yaya yahanasu, Amma yau haka taci kwalliya cikin Riga da siket, kayan ya kar6i jikinta sosai, tayi kyau nesa ba kusa ba, fuska taci kwalliya, tadauki mayafi Dan qarami ta yafa, sannan tadauki kayan data had'a masa tafita dashi compound din gidan, Ummah tana daki ba tasan Wainar dasuke toyawa ba.
Kamar yanda yafada dinne kuwa, domin kuwa Waheeda tana zuwa ta ganshi baqiqqirin dashi, gashi gajere, Amma duk da haka Saitayi murmushi ta qarasa wajan sa tace "qaraso gidan mana"
Babu musu yabiyo Bayan ta Sai qarewa tsarin gidan nasu kallo yake yana jijjiga Kai, komai da komai na tsarin gidan yamasa kamar tsarin ginin turawa, daga Gani yarinyar 'Yan manyan mutane ce
Gidan suka shiga, baba maigadi dayasan cewa basa saka mayafi Kuma basa kawo samari, Sai mamaki ya kamashi, Dan haka yanufi cikin gidan zai fadawa Ummah abinda yake faruwa yaji koda sanin ta haka zata tafaru
Sas yana ganin shigar maigadi ya kalleta yace "ashe da gaske banyi qarya ba Dana saka miki suna sarauniyar kyawawa"
Waheeda tayi murmushi ta rufe fuskarta da tafukan hannunta cikin kunya, sannan tace "tun dazu nake jiran zuwanka, ashe saukar yamma zakayi"
Yace "eh wallahi,Ina hanya ma wayata ta dauke babu charge, yanzu ma kunna ta nayi na kiraki,kinga harta sake mutuwa, gashi ban kira mama na nace mata na'iso wajanki lafiya ba, kinsan me ma? Jiya fa dazan taho wajanki saida tace idan nazo na kula dake sosai, sannan tamin lissafin abubuwan da babu acikin kayan lefen Dana had'awa budurwa ta tada, Wai babu takalmi da jaka, yakamata aqara guda uku uku akan nada, da ansaka dozin d'aya, idan aka qara uku akai, kinga ya zama Sha biyar kenan, yakamata ace nakira ta nasanar da'ita nazo wajan Mai kyau,gashi wayar tawa tamutu,Bani Aron taki wayar nakirata"
Waheeda tanajin wannan dogon bayanin nasa taji dad'i, gashi de bashida wani kyau na azo agani,Amma ita a haukan ta bataga laifin sa ba, babu tunanin komai ta bashi wannan sabuwar waya tata, tace"gashi kakirata to"
Sas ya kar6i wayar yabata wata leda a hannun sa yace"ga kyautar Dana kawo miki, nayi niyyar kawo miki Riga irintamu ta sojoji, sainace idan zan sake dawowa saina kawo miki rigar, Amma yanzu ga wannan"
Waheeda ta kar6a tace"nagode"
Yace "Bari inkira mama"
yamatsa jikin get din gidan zaiyi wayar, Hankalin Waheeda yanakan kyautar daya bata, taji de abu yana yawo aciki, Amma bata San menene ba, saboda anyi wrapping din abun da wata leda me kyau, tana d'ago kanta, taga wayam! Babu Sas babu dalilin sa ππ»ββοΏ½?
Gabanta ne yafad'i, cikin ranta tace"wannan mutumin fa ba saninsa nayi ba, kar naje yagudu da wayata, ba kowa ne ya fado mata araiba Sai Babban Yayaπ
Ledar da Sas yabata ce tasulale tafadi daga hannunta, cikin sauri ta bude get din gidan tafita, mayafin data yafa yafad'i qasa Amma batabi ta Kansa ba, haka tafuto titi tana waige waige, Amma abu kamar wasa, babu soja babu dalilin sa, awajan ta tsugunna ta Dora hannunta aka ππ»ββοΈtace "nashiga uku na, namutu na lalace!, wallahi Babban Yaya saiya kasheni" π
Baba megadi yazo da gudu shida Ummah, Ummah ta dakata daga bakin get din, baba megadi ya qarasa wajanta yariqo hannunta yana fadin "Waheeda lafiya? Me yayi miki? Ina baqon naki yake?"
Waheeda bata Bawa baba me gadi amsa ba, saboda kuka dayaci qarfin ta, cikin kuka tace "innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, shikkenan namutu, nakade har ganye na, Wallahi barin garin Nan zanyi tun kafin Babban Yaya ya dawo"
Baba megadi haka yakamota suka shigo gidan, suna zuwa compound din gidan tazube awajen tana ihun kuka, yanbiyu suka qaraso da gudu suna tambayar ta menene, Ummah ta riqeta tace "kimin bayani mana, Wai menene?megadi yacemin kinyi baqo, Wanne irin baqo kika kawo gidan? Kuma me yayi miki?"
Waheeda de takasa magana, Dan Gani take idan ta fad'awa Ummah to zata kira Babban Yaya ta fad'amasa
Yanbiyu suka dauki Ledar da Waheeda ta yar, Ihsan tabude Ledar da'aka yi wrapping dinta, tana budewa saiga chesee ya bayyana, 'Yan hamsin hamsin guda biyu, hada baki sukai sukace "Laaaa Cizi ne"
Kallan Waheeda sukayi, intisar tace "meya miki ne?"
Cikin kuka tace "Yagudu da wayata, naduba ko'ina baya Nan, wallahi gidan Nan zan Bari" tana fadar haka ta kwasa da gudu tayi cikin gida
Anan Ummah ta fahimci komai, Kai tsaye tabi Bayan Waheeda har d'akinsu, tana zuwa ta rufeta da duka, daqyar yanbiyu suka ceceta, Ummah taja kofar Dakin ta kulle Waheeda aciki, Dan tayi alqawari wannan Karon Waheeda tadena fita bare taja mata wata masifar
Har dare Waheeda tana d'akinsu akulle, Ummah tahana kowa yabudeta, Daddy ne ya dawo daga wajan aiki Sai masifa yake, ta inda yake shiga batanan yake fita ba
Duk sunyi shiru babu Wanda ya tanka masa, ita kanta Ummah ba tasan me zatace ba
Kallan 'yanbiyu yayi yace "kuje ku budeta tazo Nan Ina nemanta"
Inti taje ta bude Waheeda, akan gadon su taganta har lokacin kuka take, ta kifa kanta akan cinyoyin ta,dogon gashin kanta yazubo gadon Bayan ta, wani Kuma yarufe mata fuska kamar de mace me aljannu, kanta har ciwo yake saboda kuka, yanzu shikkenan wayarta tatafi, wayar ko wata daya Babban Yaya baiyi da siya mata itaba, ta Ina zata Iya Kallan idonsa tace takawo saurayi gida shikuma ya sace mata wayar? Intisar tace "kije Daddy yana kiranki"
Ahankali tataso, suna zuwa falon kowa yabita da kallo, su Sa'ad jisuke kamar Su make ta, Daddy ya kalleta yace "Dan wanne gidane Yaron? A wacce unguwa yake?"
Cikin kuka tace "Dadday bansan gidansu ba, ni bansan shi ba, yau nata6a ganinsa, Dan girman Allah Daddy karka fadawa Babban Yaya, Allah kasheni zaiyi"
Cikin fishi Daddy yace "yau kika fara ganinsa har kika d'auki waya kika bashi saboda ga yayanku me kudin banza yasiya miki waya ko?"
Ihsan tace "Daddy kayi hakuri, insha Allah bazata sake ba"
Sa'eed yakalli Ummah yace "Ummah kikira Babban Yaya kifada masa Dan Allah, sonake ya dawo ya kakkarya yarinyar Nan, Danni idan nakamaki saina miki Dukan mutuwa, inyaso nakawo gawarki, tunda haka kike so Dama"
Waheeda de tayi shiru, takasa cewa komai, Sai Jan zuciya take, fuskar Nan tayi jajir saboda kuka
Ummah tace "bazan kirashi ba Sa'eed, kullum Waheeda cikin janyo mana masifa take, kullum ninake kiransa nafada masa, yanzu Kam, bazan kirashi ba, idan kullum zan dinga kiransa Ina fada masa matsala ai Kuma idan yaga kirana gabansa faduwa zai dinga yi,sannan Kuma bance kufada masa ba, kubarshi yayi aikinsa, Daddynku zai dauki mataki akan haka"
Haka suka zauna a falon kowa yayi jugum, anrasa takamaimai Wanda zai kira Babban Yaya yafada masa abinda yake faruwa π
Washe gari Waheeda bataje school ba, haka ta zauna tayi shiru adaki kamar marar lafiya, ko sunan Babban Yaya taji an ambata gabanta faduwa yake,yanda ta nutsu awaje daya, Sai gidan yayi shiru, idan ka kalli Waheeda saita baka sha'awa yanda tazama wata kamila, saide kowa taciki na ciki
Tsawon kwana biyu kenan da 6atan wayar Waheeda, har yanzu babu Wanda ya fad'awa Babban Yaya, sannan daddy bai d'auki wani qwaqwaqwaran mataki ba, asalima fishi yake da'ita, Kuma a kwana biyun Nan Waheeda bataje makaranta ba, tana zaune agida abun duniya yataru yayi mata yawa, yau da yamma suna zaune, Anty Maryam tashigo gidan cikin tashi Hankali, tana zuwa ta nufi Ummah tace "Ummah yajikin Waheeda? Ashe batada lafiya Amma Ummah kukasa fadamin? Awanne asbitin aka kwantar da'ita?"
Kafin Ummah tasake magana, Maya tayi sallama cikin falon nasu tana sharar hawaye, ta qarasa wajan Ummah tace "Ummah ashe Waheeda batada lafiya? Shiyasa Bata shiga makaranta kwana biyu? Na tambayi 'yanbiyu sunce min lafiyarta kalau ashe 6oyemin sukayi"
Kan Ummah ya d'aure, ta kalli Maryam dinta dakuma Maya tace "Wai wacce Waheeda kuke magana a kaine?"
Wayar Ummah ce tayi qara, ta d'auka tare fadin "sa'ad ya akayi?"
Yace" Ummah, wannan gayen daya sace wayar Waheeda fa inaga Dan damfara ne, ba'iya wayar yakeso ba, harda damfara a tsarin nasa, yanzu Ina zaune yaturo min saqo Wai me wannan wayar batada lafiya, tana kwance agadon Asbiti, Ana buqatar tallafin kudi, Sai kuma account number aqasan saqon"
Ummah tace "innalillah.... Sa'ad shiyasa na kulleta Adaki fa, saboda muna Zaman zamanmu wata Rana zatasa azo har gida a sacemu"
Sa'eed ne yake Kiran wayar, Ummah tace "Sa'ad kashe, ga dan'uwanka Nan Shima yana kira"
Tana daukar wayar Sa'eed din, Shima abinda yafada mata kenan, Ummah ta kashe wayar ta kalli su Maryam "wallahi lafiyar Waheeda kalau......" anan Ummah ta basu labarin abinda yake faruwa, Maya tace "Kai Amma wannan anyi tsinanne, yazo har gida yasace mata waya sannan ya dinga turawa mutane cewa batada lafiya aturo Masa kudi?, Ummah Ina Waheedan?"
Ummah ta nunawa Maya d'akinsu Waheeda, tatashi ta nufi Dakin, anan taga Waheeda ta zauna tayi shiru tana tunani
Maya ta dafata tace" Alhamdulillah, har hankali na ya kwanta wallahi qawata, text fa akamin bakida lafiya, kina gadon Asbiti a kwance, Wai Ana buqatar tallafin kudi ta wani account Number dayake Qasan saqon "
Waheeda tayi shiru takasa Bawa Maya amsa, Maya tace" Waheeda kalau kike kuwa? Inata magana kinyi shiru? Yanzu Waheeda shawarar Dana baki ashe baki d'auka ba saida kika kula saurayi?"
Waheeda tacire hannunta daga tagumin da tayi tace"Maya Babban Yaya"π
*** ** ***
Motsa jiki yake cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali, wayarsa dake ajiye