Showing 9001 words to 12000 words out of 77020 words

Chapter 4 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete

harna yiwa uncle dinka maganar yarinyar shida Dadynka, Amma Kai Yaya kagani?"

Ummah tace "Yaya zai Gani kuwa? Yama amince kawai"

Tashi yayi daga wajan su yace "to Anty idan nasamu lokaci zanje naganta"

Ummah tace "yaushe zakaje?"

Kansa yadafe da hannun sa 🤦🏻‍♂️yace " wayyo Allah Ummah, zanje wallahi, anjima zanje"

Anty tace "to idan katashi zuwa ga wannan kayan kwalliyar kakai mata"

Uwar ledar data turo masa gabansa ya kalla, cikin ransa yace Dama de sun shirya komai
Yace "to"

Bai dauki ledar ba ya wuce ta gaban Waheeda yayi dakinsa,yanaaji yana cewa "good morning Babban Yaya" Amma ya shareta
wani qullutun taqaici ya to kare mata maqoshi, tasan yanzu Babban Yaya ya tsaneta, gashi ya maida yanbiyu makaranta Amma banda ita.

Hajiya Anty tana tafiya gida Waheeda taje wajan Ummah ta zauna, Ummah ta kalleta tace "Lafiya Waheeda?"

Girgiza kanta tayi tace "Ummah, Babban Yaya baya sona yanzu, ya tsaneni"

Ummah ta kalleta tace "yayanki uwa daya uba daya tayaya zakice baya sonki Waheeda? Halinki ne baya so, Waheeda bakya jin magana, saikin masa laifi Kuma kizo abun ya dameki, yanzu ni me zanyi muku akan haka?"

Idanunta ne yayi qwalqwal hawaye yana shirin futowa tace "to Ummah kinajifa nagaidashi Amma ya share ni"

"bai gama hucewa bane, kibari zuwa anjima ai zai sauko"

Hawayen data riqe ne ya silalo daga idanunta, tasa hannu ta share, sannan tayi dakinsu domin ta watsa ruwa

Umma na ganin tafiyar ta ta nufi Dakin Babban Yaya, yana kwance agadon sa yayi mata shi da hannayensa, duniyar tunani yatafi ita wannan yarinyar ta wacce hanya zaibi yarabu da'ita?

Turo kofar tayi tashigo, yana ganin shigowarta ya tashi zaune, zama tayi akusa dashi tace "Yayansu, magana nakeso muyi"

Nutsuwa yayi yace "to Ummah"

Tace "akan Waheeda ne, yakamata kadinga Jan 'yan'uwanka ajiki, qannanka ne bakada kamar su, idan Bama Raye kaine zasu kalla a matsayin ubansu, yarinya qanqanuwa Waheeda har tana min magana akan rashin kula da'ita da bakayi, tacemin yanzu kadena sonta, hannunka fa baya ru6ewa ka yanke kayar, yakamata kadinga janta ajiki kanuna mata fari da baqi, tunda Dukan bazaisa ta sauya ba saika dinga yimata nasiha "

Kallan ta yayi yace"Ummah nasiha bazata shiga qwaqwalwar yarinyar nanba, batajin magana, kullum itace takemin sanadin zuwana Nigeria "

Ummah tatari numfashinsa tace" kaikuma gashi baka son zuwa Nigeria saboda kar muyi ma maganar aure ko? "
Qasa yayi da Kansa yace" Bahaka bane Ummah, insha Allah zan jasu ajikin kamar yanda kikace "

Tashi tayi tsaye tareda fadin" Allah yamaka Albarka "

Cikin jin dadi yace"Amin Ummah tah"

Dayamma suna kallo afalo, Amma dukansu su ukun suna saka kayan makarantar islamiya, jira suke kawai lokaci yayi sutafi, futowa yayi daga dakinsa yayi wankan qananun Kaya kamar ka saceshi kagudu, wandon Jeans yasaka baqi, Sai Riga me kama jiki ruwan toka, dakuma yar sama me ratsin baqi, yasaka kambos Shima baqi me ratsin brown, yayi kyau sosai sumar Nan tasa Sai sheqi take, Ummah ta Kalle shi tace "masha Allah, yayansu Sai ina?"

Kansa ya shafa yace "inda hajiya Anty tace naje"

Fara'ah ce ta wanzu a fuskar Ummah, tace "kace gidan surukar tawa zakaje, irin wannan wanka haka ai dole a dedeta, Bari in Dauko Maka kyautar Tata"

Baice komai ba, yanemi kujera ya zauna, tareda daukar remote ya maida tashar Kallan ball, Kallan Waheeda yayi, suna hada ido tayi qasa da kanta, yace "4 o'clock kuke tafiya islamiya ko?"

Atare suka amsa da "eh"

Yasake dubanta yace "tashi ki rakani"

Cikin murna tatashi tayi dakinsu, farinciki take yayan Nata da alama yahuce, uniform dinta tacire tasaka doguwar Riga, sannan ta dauki dogon hijab dinta tasaka, tana futowa Ummah ma tana futowa daga daki, ta bashi ledar kayan, ya nuna mata Waheeda ataqaice yace "bata"

Ummah tace "yanaga kincire uniform din ko tare zakuje zancen?"

Waheeda tasaki wani murmushin jindadi, tace "eh Ummah"

Kallan ta yayi sosai, sautari idan yarinyar tayi wani abu saiya ga Takoma photocopy dinsa sak, musanman idan tayi dariya ko murmushi duk dimples dinta suka bayyana kamar de nashi, kauda tunanin yayi daga ransa yafita daga falon ita Kuma ta Mara masa baya, saida tajuyo tayiwa yanbiyu gwalo 🤪Sannan tafita

Ummah ta girgiza kanta cikin ranta tace gaskiyar sane daya ce bazata sauya ba

Motar dasuka shiga glass din motar tint ne, ba zakaga naciki ba, mafi yawan lokaci irinta yake Hawa saboda shi mutum ne na mutane, ko Yaya yafuto awaje dole ne kasamu Wanda yasan shi
Suna cikin tafiya ya kalleta yace "Bani labari"

Kallan sa tayi tace "Babban Yaya wanne labari gashinan muna shirin zuwa Naga Anty"

"wacece Anty?"

"Babban Yaya wadda zamuje wajan ta, budurwarka, harna matsu naganta wallahi"

Haushi ne yakama shi, yace "to naji Dan Allah, ni labari nace kibani bawani shirme ba"

Kallan sa tayi, cikin ranta tace zancen budurwar tasa yake cewa shirme to in hakane komai ma ta fada bazai birgeshi ba, duk da haka saita Juyo tana fuskantar sa tace "Babban Yaya inaso Naga kana Ball, ka'iya ball sosai, wani lokacin idan ka saka qwallo araga Sai inji jikina yana tsuma kamar nice nasaka"

Dariya tabashi, saida yayi dariyar sa sannan yace "ke meyasa bazaki Koya ba?"

"Bayan wacce kake Koya mana agida?"

"yes, idan kinaso saina sake Koya muku"

"muna so wallahi Babban Yaya,nafiso nafi yanbiyu iya Ball"

Kallan ta yayi kawai yayi shiru, saboda qarasowa dasukai gidan yarinyar da Hajiya Anty tabashi address, a kofar gida suka tsaya yakira Hajiya Anty ya tambayeta sunan yarinyar tace masa naja'atu, daga Nan yakashe wayar yatura wani yaro Akira masa ita

Yaron ya dawo yace ance su shigo, har falo suka shiga suka zauna, babu laifi gidan sunada rufin asiri, kusan minti biyar da zamansu Sai gata tafuto tana Sanye cikin atamfa Riga da siket, Sai wani Dan qaramin mayafi data saka, da farko tsorata tayi data ganshi, saboda lokaci daya yadaki zuciyarta, gayen yahadu dayawa, fatanta daya Allah yasa Shima ta masa
Zama tayi tareda gaidashi, ya amsa cikin kulawa, acan Qasan ransa yaji dadi dabata ganeshi ba da alama bata ganin ball, Waheeda ce itama ta gaidata fuskar ta d'aukeda murmushi, ta amsa mata

Shiru Waheeda tayi tana jira taji irin kalaman soyayyar da Babban Yaya zai tsara mata kamar yanda Didat yake mata idan sun hadu a school, saitaji yace "Naja'atu Anty nace taturo ni wajanki, basai nayi Miki dogon bayani ba nasan kinsan dalilin zuwana wajanki"

Murmushi tayi tace "Hakane, nide daga wajena babu wata matsala, Ina fatan kaima haka?"

Babban Yaya yace "a a, banda wata matsala Nima, saide inaso namiki tambaya guda daya"

Kafadunta ta daga🤷🏻‍♀️tace "babu damuwa Ina jinka fadi duk maganar dakake so"

Yace "Kina school ne yanzu?"

Tace "a a, tunda nayi candy bankoma makaranta ba"

Yace "masha Allah, Nima banda burin yarinya tayi dogon karatu batare da aure ba, but meyasa ke kinyi candy Amma bakiyi aure ba har kika dade agida kina neman tsufa?

Waheeda ta zaro ido 😳ta Kalle shi da sauri

Itama naja'atu ta Kalle shi tace"me?, nice na tsufa babu aure? "

Batareda damuwa ba yace"idan bakiyi shekara ar'ba'in ba tokin kusa, tunda Naga idanunki na tabbatar kedin Nan sa'ata ce, bazan girmeki ba, nikuma gaskiya nafison na auri yarinya qarama, wadda zan Koya mata komai"

Haushi yakama naja'atu, ta jinjina kanta tace "ni Dama nasan babu wani namijin Arziqi daza'a dinga neman Kai dashi haka kawai, na tabbatar kaima kyan Dan maciji ne dakai tunda har ake neman Kai dakai duk wannan kyan Naka, tunda kana tareda P.A dinka ai shikkenan saikaje ka aure ta"taqarasa maganar tana Kallan Waheeda

Cikin sauri Waheeda tace "kaiiii Yaya nane fa"

Naja'atu ta miqe tsaye tace "Au...to Allah yasa gware kukai kuka futo" 😂
Waheeda ta kalli Babban Yaya ko zai dakatar da naja'atu daga tafiyar datake shirin yi, taji yayi shiru, ahankali tace "Haba Babban Yaya"

Kallan ta yayi ya daga murya yace "Naja'atu"

Cikin fishi naja'atu tajuyo tace "kutashi kubar mana gida tun kafin nakira Yara su tule ku da qasa"😂

Dafe Kansa yayi 🤦🏻‍♂�?, sannan yadago yace "Dama wannan ledar ce kika manta bakidauka ba, Inji Anty tace akawo miki"

Tsaki naja tasaki tace "kuje da tsiyarku" daga Nan tashige tabar su afalo, ita kanta Waheeda taji babu dadi, tayi tunanin haquri zai bata Wai ashe leda zai bata, wannan rashin mutuncin ko ita akayiwa Allah ne kadai zai rabata da saurayin ranar 😖

Haka suka futo daga gidan Waheeda jiki a sanyaye, shi kuwa ransa fes

Amota kasa magana Waheeda tayi, Shima bece da'ita uffan ba, cikin ranta tana so ta tambayeshi meyasa yake gudun aure? Amma tarasa ta'ina zata fara? Duk cikin iyayensu babu Wanda yataba zama dashi yaji menene dalilin sa naqin matan da'ake hadashi dasu, kawai sude iyayen burisu suga yayi aure kawai, tana so taji menene matsalar sa, meyake so? Amma tana tsoron abinda zai biyo baya, saboda zai iya cewa ta raina shi

Tunanin tane ya tsaya lokacin dataga sun tsaya awani super market, p-cap dinsa ya dauka yasaka me d'aukeda sunansa ajiki, sannan yashiga wajan, itade Waheeda tana binsa Abaya taga Sai provision yake yi, itama yace tayaya shi haka suka dauki , su suger, cornflakes, madara, Maggi, kayan zaqi dangin su biscuit da chocolate, saida yagama hada komai tsaf, har tana mamakin Ina zaikai wannan uban kayan,? Wasu yanmata ne suka ganshi su kazo sunaso yayi photo dasu, babu musu ya tsaya sukayi sannan suka nufi wajan biyan kudin, a lokacin wani saurayi Shima yana wajan zai biya nasa kudin, ganin Babban Yaya yasa farinciki yarufe shi, Yama Rasa inda zai Dora ransa, Sai magana yake masa, Babban yaya yayi murmushi Shima yasake da saurayin kamar ya sanshi, shida Kansa ya biya kudin saurayin danasu kayan sannan yamasa sallama suka tafi gida

Suna zuwa gida taga yabawa Sa'eed wannan kayan dasuka zo dashi, sannan suka wuce Dakin Ummah, tare suka gansu itada hajiya Anty Sai hira suke da shewa kamar ba facaloli ba😃
a lokacin biyar da rabi har tayi, Ummah ta kallesu cikin farinciki tace "harkun dawo? Jinake ai sai dare"

Hajiya Anty tace "yayansu nasan de Najaatu tayi hundred percent"

Zama sukai gaba dayansu babu Wanda yayi magana, Ummah ta kalli ledar kayan kwalliyar dasuka tafi dashi tace "yanaga kunyi shiru, meyafaru ko bakuje bane?"

Waheeda ta janye hannunta daga tagumin da tayi tace "hmm Ummah cewa tayi mutashi mutafi tun kafin tasa atule mu da qasa, gashi mayafi take sakawa, shikuma Babban Yaya baya son mayafi, shine ya tambayeta meyasa ta tsufa batayi aure ba, ranta ya6aci tace masa yaje ya aureni tunda ni p.a dinsa ce, Wai ai Dama neman Kai kuke dash.... "
Hajiya Anty ce ta katse Waheeda cikin tsawa" ke dallah can rufe mana baki shashasha kawai. Yen yen yen Sai magana kike Babban Yaya baya son kaza, Babban Yaya baya son kaza, kunhada Kai kunje kunci mata mutunci kun dawo toshknn Hankalinku saiya kwanta, ita yar'iskace dabaza tace yaje ya aureki ba? Ina aka taba tafiya zance , ganin farko adiba atafi da qanwa? Saikune zaku nuna mata ku yan'uwan jini ne, banji dadi ba dabatasa anmuku wanka da qasa ba, tashi kibawa mutane waje manya suna magana kin tsomo baki kamar maganar aurenki ake "
Sum sum Waheeda tatashi tabar Dakin, shi kuwa Babban Yaya kasa hada ido yayi dasu

Ummah tace"ashe abinda kake fadawa yaran mutane kenan shiyasa kowacce Sai tace bata sonka, Toda kake cewa ta tsufa batayi aure ba kaidin shekarar ka nawa?" 🤔

Shiru yayi yakasa Bawa Ummah amsa, Ummah tace" dakai nake, nace Kai shekararka nawa bakayi aure ba? "

Kansa aqasa yace" Ummah kuyi hakuri, Nima ba laifi na bane "

daga Nan ya tashi yafuto daga Dakin Shima

Yana fita hajiya Anty tace" Yaya kinji me yace kuwa? Ba laifin sa bane Anya kuwa Yaron Nan kalau yake ba Sanyi da basir ne sukai masa mugun kamu ba? "🤣

Ummah tace" to Hajiya Anty tayaya zan Sani? Kuma yaqi yayi auren balle mugani kalau yake koba kalau yake ba "😂

Hajiya Anty tace" kaiii ninama Rasa mezance wallahi, tunani na ya tsaya Hajiya, Bari inje gida, idan nasake wani tunanin saina dawo "

Washe gari da sassafe ya shirya cikin qananun Kaya, so yake yabar qasar saboda jibi sunada match a Qatar, sannan muddin yaci gaba da zama to bazasu daina hadashi da yanmata ba, suna gama bresk fast, ya kalli Ummah da Daddy yace" Ummah, Daddy, zan wuce England yanzu, jibi munada match a Qatar, kuyimin addu'ah "

Atare sukace" Allah yabada sa'a "

Ya Juya ya kalli Waheeda, yabata 10k yace" gashinan, kiyi amfani da wannan idan kinje makaranta, anjima su Sa'ad zasu kaiki Boarding school, nariga nayi magana da principal din ta waya, Shopping din da muka iyo jiya nasan komai yamiki tunda ke kika za6o da kanki, Tunda bakya jin magana Dan Allah kisake aikata wani laifin Wanda zakisa nasake dawowa Nigeria saboda ke kinji..... "

Spoon din hannunta ne yafadi qasa tace" nashiga uku Babban Yaya Boarding Kuma? "

Kallan qwayar idonta yayi yace"yes, nafiso a kaiki inda zasu kasheki su kawo mana gawarki"





Duk me buqatar Babban Yaya yakirani kokuma yamin magana ta whtsapp 08033300034


Share please 🙏🏻





Amnah El Yaqoub ✍�?
1/28/22, 20:49 - Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA


Writing By Amnah El Yaqoub


Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/


5&6


Tanajin abinda yace tayi dakinsu da gudu tana kuka, Shima yajuya yafita daga falon, wannan Karon driver ne yakai shi Airport, Bai dade da zuwa ba jirginsu ya tashi

A wannan safiya Waheeda breakfast din da batayi ba kenan, tana daki tana kuka, Sa'ad ne yashigo Dakin yace ta shirya kayanta karfe goma zasu tafi, tanajin abinda yace tasake rushewa da Kuka, harta Bawa yanbiyu tausayi suma suka fara share hawaye 😥, sune suka shirya mata kayanta tsaf, sannan Ummah tazo ta lalla6ata taci cake da madara, sannan suka tafi, tabawa kowa tausayi a gidan, Hajiya Anty Kam dataji labari kasa zuwa gidan tayi, zuciyarta bazata dauki hakan ba, gashi babu damar Hana tafiyar Tata tunda Babban Yaya ne ya yanke hukuncin, iyayen nasu sun bashi power sosai babu yanda za'ayi ya yanke hukunci aqetara shi.

Lokacin dasuka kaita,riqesu tayi tanata kuka, saida principal din yasa wata yar ss3 ta riqeta suka tafi hostel tareda kayaiyakinta.

Wunin ranar haka Waheeda take addu'ah cikin ranta Allah yasa karsu Babban Yaya suci match din dayace zasu buga😂

Wannan yar Ss3 din data kaita hostel, Mai suna Rabi'at itace ta dinga bata hakuri ranar, Sai lalla6a Waheeda take tana kwantar da'ita ajikinta, tun Waheeda tana daukar abun na Hankali Sai kuma taga abun yafara wuce Hankali, taga agida ko jinya take yanbiyu basa kwantar da'ita ajikinsu, bare yanzu da lafiyarta kalau, Kuma bawani girman ta tayi ba, Kuma ita a aji biyar din datake anan aka Barta, duka duka tsiran aji dayane a tsakanin su bare ta nuna mata wani abu.
Duk wani abu da tasan ba'a sakawa a makaranta doka ne, tahana Waheeda sakawa, su ribom, zobe, Dan kunne, dasu kwalliya, duk tayiwa Waheeda bayani Kuma ta hanata sakawa.


Washe gari karfe biyar da Minti goma na asuba aka tashe su, Bayan sallar asuba gari yana haske aka sakasu share share, wasu wankin toilet, tun a lokacin Waheeda tafara raina kanta, agida basa irin wannan aikin, Sai yanzu tasake tabbatar wa Babban Yaya yana mata tsana mafi muni, mutumin dazai kawoka wannan muhallin ba qaramin maqiyinka bane,😖😃
Daqyar tayi sati daya, kafin tafara sakewa da sauran dalibai, acikin sati dayan da tayi harta hada group na qawaye irinta marasa jin magana,Neenah da zuly.


Kansu ahade yake, kudin datazo dashi makarantar shi take sakar musu suke yin komai da komai yanda ransu yakeso, shiyasa tana basu umarni sukebi.

yau data tashi da safe Bayan tagama komai zobunan gold dinta da wannan yar Ss3 din tasata tacire ta6oyesu, suta Dauko tasaka tatafi aji

Malaminsu yana karatu yaga hannunta Sanye da zobe yace "ke ba'a fada miki ba'a zuwa da zobe ko Dan kunne aji ba?"

Tace "Malam hannu nane yayi wani iri sungul babu kyan Gani shiyasa nasaka"

Malamin yace "kwalliya kikazo yi kenan" daga fadar haka ya ajiye littafinsa yafita waje yanemi bulala, yana fita ta daga kanta ta kalli silin din ajin taga wani ya6ule, tatashi tataka kan bancin dasuke zaune tasaka zoben aciki, ta kalli Yan group dinta tace "duk Wanda yafada ku gane min shi, nadena bashi ko sisina"

Malam yana zuwa yace ta bashi zobe tace ita babu wani zobe awajanta, ya tambayi Yan ajin kowa yayi shiru, qarshe baqin ciki ne yasa malamin yahadasu yadakesu gaba daya, ya dauke littafinsa yafice daga ajin😟


Washe gari da abincin ta tafita class bataci a hostel ba saboda ta makara, Kuma an hanasu zuwa da abinci class, tana hango malama tayi sauri tajefa flas din abincin Bayan window, duk wani Salo na6oye abu idan aka zo qwacewa tasan yanda zatayi ta6oye

Saida yagama karatun sa yafita, sannan tasake haurawa ta window tadauko abincin ta taci, tana gama ci senior master dinsu yashigo da wata qawar Rabi'at Wadda Waheeda ta dauketa suka tafi hostel ranar da tazo, agaban allo ya zauna yace "duba minsu daya Bayan daya, principal yace akwai Wanda suke zuwa da waya acikinsu, jiya an tsinci sim card, Kuma zasu iya aikata wa, maza maza duba minsu"

Qawar Rabi'at tazo tafara dubawa, ko'ina saita laluba ajikinsu ko sun 6oye wayar, tana zuwa kan Waheeda taji wani farinciki ya kamata, dama tunda taga Rabi'at tazo da'ita taji tana son yarinyar, ta yiwa Rabi'at magana akan ta Amma taqi bata goyon baya, saboda itama so take takafa Tata gomnatin acikin zuciyar yarinyar, malamin yace "dubamin ita mana, me kike jira ne?"
Cikin sauri ta nufi Waheeda tafara shafa jikinta, hips dinta take shafawa har matsawa take cikin wani irin Salo, malamin yajuya yana amsa waya tafaki idon sauran dalibai tazura hannunta cikin hijabin Waheeda da sunan duba waya tafara matsa mata boobs dinta, Kallan Waheeda tayi takashe mata ido tana sake murza mata nashanunta, Waheeda ta taqarqare tabige mata hannu cikin tsawa tace "Dalla malama Niki Bari, kawai sai wani lalube min jiki kike"

Tsoro ne yakamata, malamin yakashe waya yajuyo ya kalleta cikin fada yace "kunji min marar kunyar yarinya, mezata laluba a jikin ki qwaila dake? Idan kinsaba yiwa sauran malamai rashin kunya to ni duka zakici"

Murmushi tayi tace "malam ai kasan yarinya ce qarama, saida lallama, babu wayar ma ajikinta"

Tsaki yasaki yace mata"muje"
fita sukai daga ajin suka shiga wani




Bayan sun koma hostel sunacin abinci da qawayenta ta Kalle su tace "nifa barin Dakin da Rabi'at dinnan take zanyi, saboda abinda take min yafara isata, saita dinga Jana ajikinta tana wani shafani, haka dazu ma qawarta ta dinga ta6amin Nono, nayi magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login