Showing 72001 words to 75000 words out of 77020 words
Chapter 25 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
saba, ita kanta tafara jin dadin abun kadan kadan
Daga Dubai England suka wuce wajan aikinsa, suna zuwa gidan, jikin Waheeda yayi Sanyi, ta tuna lokacin da sukazo da ita, yanda take santin gidan alokacin yace mata idan taso zai iya zama gidanta, ganin yanda take tafiya ahankali jiki a sanyaye yayi tunanin gajiya tayi, Dan haka yasaka hannu ya sureta sukai cikin gidan, nanma suna shiga falo tatuna da Didat, wancen zuwan da tayi dashi ta dinga waya tana bashi haquri dakuma fahimtar dashi akan Babban Yaya yayanta ne,suna zuwa daki suka zube akan gadon, Waheeda tasake tunawa yanda sukai ta birgima akan gadon ita dashi wancen zuwan, alokacin Gani take babu ya Huzaifa, rayuwa kenan Dama hakane, zakayi samari kalakala ma banbanta, Amma bakasan dawa zakayi rayuwar aure ba, Babban Yaya ne ya katse mata tunanin ta, yace "Baby nagaji dayawa, wanka zakimin, dama yau baki minba, baki wanke abarki ba yau"
ya qarasa maganar yana murmushi dimple dinsa na lotsawa
Cikin shagwa6a tace "Naga takaina ni Waheeda Wai Dan Allah Babban Yaya waye yafada ma wannan maganar ne? Nide nasan dagani Sai Maya, dakuma Ummah mukadai mukasan maganar, Kuma nasan sude bazasu fadama ba"
Murmushi yasake yi yace "Ina ruwanki da Wanda ya fadamin, Nima bazan fada ba, tunda alokacin ko gidan Nan zai zama shaida saida na tambaye ki laifin me ki kaiwa Ummah, Amma kikace min ba komai"
Cikin shagwa6a tace "to Naga alokacin Kai Yaya nane, tayaya zan fadama"
"yanzu Kuma fa? Ni menene?"
Shiru tayi taqi bashi amsa, Sai wani kallo datake watsa masa na soyaiya
Tashi yayi yacire kayansa, yashige toilet zaiyi wanka, yana shiga itama tacire kayanta ta daura wani Dan qaramin towel , taje wardrobe tasaka kayan, tana kokarin rufewa idonta ya sauka akan dairy din Babban Yaya, Wanda tafara karantawa kwanaki, dauka tayi, ta zauna abakin gadon tabude tafara karanta wa
Gaba daya shafin farko Dana Gaba, tarihin rayuwar gidansu ne tun kafin ahaifeta, Sai kuma lokacin da aka haifeta da yanda ta sauya komai na rayuwar sa, yanda yake fuskantar matsala idan ya ganta da wasu mazan, da yanda ya baiyana tsananin yanda yake sonta acikin zuciyar sa, tausayi yabata, lokaci daya hawaye ya wanke mata fuska, tana karatu Amma hawaye yana d'isa akan paper, batasan yafuto daga toilet dinba, saijin maganar sa tayi akanta "idan kin gama karatun nafuto"
Tana d'ago kanta data ganshi, tatashi da sauri ta rungume shi tareda fashewa da Kuka, Shima qwalla ce tafuto daga Idonsa, ahankali yace "menene abun kukan to?"
Dagowa tayi daga jikinsa takai masa duka a qirjinsa, sannan tasake rungume shi cikin kuka tace "meyasa bazaka fadamin ba?"
Murmushi yayi yace "idan nafada miki ma nasan bazaki Soni ba, lokacin danace zan aure ki cewa kikai bakya sona..."
Tausayi yasake bata, tasake rungume shi sosai a qirjinta, saboda ita duk ya fuskanci matsi dakuma takura a wajan iyayen sa saboda aure, hannunta daya tacusa cikin lallausar sumar Kansa, cikin hawaye tace "I love you so much Babban Yaya, I can't life without you.... Ina qaunarka, please karka Barni"
Wani irin dadi ne ya ratsashi, ahankali yace "I love you too Baby..., zakisa nasake wanka fa,Bayan Kuma bayimin zakiyi ba, qiri-qiri de kinqi ki wanke abarki"
yaqara sa maganar cikin sigar tsokana, dariya ce ta kamata, tasaka bakinta awuyansa ta sumbace shi
❤️
1/28/22, 20:52 - Ummi Tandama😇: XV
Wani irin dadi yaji, ya Lumshe Idonsa, ahankali yace mata "karki Dena Dan Allah..."
Murmushi tayi ta Kalle shi tareda dora harshanta akan lips dinsa tana lasa, daga qarshe tahade bakinsu tana nuna masa tsantsar yanda take sonsa, tsayuwar gagararsu tayi, suka fad'a kan gadon, yana kwance tana samansa itace ta dinga yin komai, babu bata lokaci yafara Hawayen dadi, Bai taba tunanin zata Iya masa irin wannan soyaiyar ba, Bayan komai yagama wakana kukan shagwa6a yasaka mata Sai tayi masa wanka, tunda yayi abinsa tazo ta 6ata masa, babu yanda ta'iya haka suka koma toilet din yau dai tayi masa wanka, haka yaqiyin komai Yabarta ta wanke shi tas, tana murmushi tana masa wanka Dan dolenta yau takama abarta ta wanke 🙈
Saida sukai kwana biyar a gidan, babu inda suke fita kullum suna gida suna manne da juna, Waheeda Kai yawaye, tadena kunyarsa ko kadan, ta haqura ta saduda ta riqeshi a matsayin mijinta, yanzu ko kwanciyar aure zasuyi baya yin komai, ita yabawa Dama ta dinga yimasa duk abinda takeso, kwanansu shida yakoma bakin aikinsa, wani lokacin agida yake barinta, wataran Kuma sufita tare, duk yanda takejin kishin mijin Nata, haka take kokarin danne zuciyar ta, ta tsani taga mata suna rububunsa, jitake kamar zuciyarta zata Fashe, Amma idan ta tuna dan'uwan Nata bamai yawan magana bane da biyebiyen mata Sai hankalin ta ya kwanta, shi Kansa miskilin Kansa ne, idan kikace Zaki soshi ma haushi ne zai kamaki, Amma Kuma suna dawowa gida saiyayi lallashi, Dan ta dinga kumburi kenan akan danme yanmata zasu dinga kulashi, shi Kansa babu yanda ya'iya saide yarage murya yabata hakuri kawai
Yau agida Yabarta, tunda tatashi takejin zuciyarta tana tashi, duk abinda taci Sai amai, tun abun baya damunta har tazo tana damuwa, kitchen tashiga zata soya qwai taji kasala ta rufeta ga zazza6i, babu shiri tadawo falo ta takure akan kujera, wayarsa ta dinga kira zata fada masa, shikuma a lokacin suna training, saboda suna shiryen shiryen buga world cup ne, wayarsa bata hannun sa, lokaci daya taji wani baqin ciki ya kamata, ita kanta tarasa meyasa yanzu ko Yaya yayi mata laifi 6acin rai takeji marar misali, abu kad'an saiya 6ata mata rai
Haka ta wuni a wajan sallah ce kawai take tashinta, yana dawowa ta daga Kai ta Kalle shi ta watsar😏
Zama yayi aqasan ta yazuba mata ido cikin murmushi yace "yau Kuma laifin menayi gimbiya? Babu oyoyo babu komai Sai fishi?"
Cikin 6acin rai tace "bakasan ma mekayi ba? Inata Kiran wayar ka kaqi dauka, Kuma dakuka tashi baka kirani ba"
Yanda yaga tana magana daqyar Kuma a hakan ita masifa take, Bai kulata ba yad'ora hannun sa akan wuyan ta yaji zafi zau, cikin damuwa yace "subhanallah.... Ai zazza6i nema ajikinki, Wallahi kinga wayar tana cikin jaka, a silent take, sannan damuka tashi sauri nake inaso nazo naganki, tashi muje Asbiti naji jikin naki da zafi"
Shareshi tayi, tajuya masa baya, wayarsa yadauko a jakar yaduba anan yaga harda missed call din Hajiya Anty, kiranta yayi Bayan sun gaisa tace "Ina Waheeda"
Tace "gatanan Anty, kinga fishi takema saboda takirani ban dauka ba, wallahi Anty training muke, nafada miki muna shirye shiryen buga world cup ne, Sai sauri nake nazo na ganta in mata albishir zamu tafi Nigeria, duk da yawan mu kowa qasar sa zai tafi, Nima Kuma wannan Karon Nigeria zan bugawa, to kinga tamaqi kulani ta juyamin baya, Kuma naji jikinta akwai zazza6i nace mata muje Asbiti tayi shiru, Allah Anty yanzu komai nayi mata saita dinga min fada"
ya qarasa maganar kamar zaiyi kuka
Anty tayi murmushi tace" bata wayar "
Wayar yamiqa mata Shima ya kawar dakai alamun yayi fishi yace" ga waya inzaki karba, inbazaki karba ba inkashe wayata"😂
Cikin haushi tace "kakashe"
"au haka kikace?"
Yamaida wayar kunnansa yace "Anty ai kinji ko? Kinji de da kunnan ki ko? To tace na kashe bazata karba ba"
Anty tayi murmushi tace "Naufal, banason shirme bata waya nace"
Wayar yad'ora mata akan kunnan ta yakoma Gefe ya zauna yana girgiza qafa, Waheeda najin muryar Anty tatashi ta zauna tace "Anty Ina wuni"
Hajiya Anty tace "Daughter, meyake damunki? Fadamin meyafaru?"
Ahankali tace "Anty shine nakirashi yaqi dauka,tunda safe nake amai duk abinda naci sainayi amai, Kuma nakirashi ne dama infada masa, Kuma kullum Sai mata su dinga binsa suna liqe masa, kowacce mace saida dinga binsa tana masa Iyayi, Allah ni nagaji...." ta qarasa maganar tana fashewa da Kuka
Babban Yaya ya Juyo da sauri ya kalleta, dama fishin duk saboda kishin sa ne? Wani irin dadi yaji, shida yake kuka saboda soyaiyar Waheeda itama gashi tana kuka saboda tasa soyaiyar, murmushi yake yana kallonta
Tajuyo ta daka masa harara ta kawarda Kai
Anty tace "Daughter kina Jina? Ki kwantar da hankalinki, na tabbatar Yayanku yana qaunarki, mata nawa yaqi saboda ke? Wanne irin 6acin raine bai sakamu aciki ba saboda ke? Kema da kanki cewa kikai mata ne suke bibiyarsa, ki godewa Allah tunda bashine yake bibiyarsu ba, ki watsar da wannan kishin naki ki ringumi mijinki, kar wasu mata su dameki, kanki kika Sani, ai yasan matan suna bibiyarsa Amma ya liqe miki, yaqi auren kowa saike, duk wadda kikaga tana son mijinki kitayata sonshi, kedai karki bashi kofar dazai dinga sauraransu, ki riqe mijinki dakyau ko kadan karkiyi sakaci, karki bada kofar da wata zata shigo, Nima kaina bazan Bari yayanku yakawo miki wata ba, Amma idan kin kwantar da hankalinki kinyi abinda nace "
Tashi tayi daga wajan, ta matsa Gefe tace" to Anty zanyi, Kuma magungunan dakika Bani duk sun qare "
"kiyi hakuri Daughter wasu suna Nan na ajiye miki, yacemin gida zaku taho, Kuna dawowa zan kawo miki, kinji dai abinda nafada miki, kidena wannan kishin kinutsu ki mallake mijinki"
Ahankali tace "to Anty"
"yawwa Daughter, bashi wayar ki shirya kuje asbitin"
Zuwa tayi tabashi wayar, sannan ta wuce daki ta sauya Kaya tafuto
Anty tace "Naufal, Ina tunanin yarinyar nanfa ciki gareta"
Cikin sauri yace "Allah Anty?"
Tace "qwarai kuwa, kadena damuwa da wannan 6acin ran Nata, ciki yana saka haka, Amma kuje asbitin aduba ta"
Cikin murna yace "to Anty, Alhamdulillah"
Yakashe wayar, ya kalleta yace "to madam Waheeda muje ko?"
Cikin fishi tace "saide ka goyeni"
Dariya ce ta qwace masa, yace "yarinyar Nan.... Kodan shikkenan zoki hau"
Ya tsugunna agaban ta, tahau bayansa suka fita, saida yasaka ta amota sannan yashiga suka tafi Asbiti
Suna zuwa kuwa, gwajin farko suka Gano tana d'aukeda ciki wata daya, tun a asbitin ya d'auketa yana juyi da'ita, mutane Sai dariya suke masa kasancewar sa sanannan mutum, wasu daga cikin doctor's har video suke musu, wasu Kuma picture
Suna dawowa gida yad'ora ta akan cinyarsa yana shafa cikin, cikin murna yace "kamar yanda nake jefa qwalla araga, yanzu ma nayi nasarar jefa wata qwallon acikin ragar mata ta, kinsan nidin jarumi ne"
Dariya tayi tace "Babban Yaya ai kaine kake yabon kanka da kanka, Kuma anfison ayabi mutum"
Kafin yabata amsa wayar intisar tashigo, dauka yayi yace "intisar"
Ummah tayi murmushi tace "ba intisar bace, nice, yanzu suka taho da gudu itada Ihsan suka nunamin photon ku a Asbiti Wai Waheeda tana da ciki, hakane?"
Kunya ce ta kamashi, ya sunkuyar da Kansa kamar tana ganinsa yace "hakane Ummah"
Tace "Alhamdulillah, to Allah yaraba lafiya"
daga Nan ta kashe wayar, danta lura yanzu Naufal kunyar ta yakeji
Waheeda ta zaro idonta tace "Wai har sunji?"😳
Hararar wasa yayi mata yace "mekika daukeni ne? Nafada miki ni jarumi ne, Sunana Naufal Umar Arabo a.k.a Big Brother, ni mashahurin mutum ne, inayin abu kad'an, zakijini ayanar gizo"
Murmushi tayi tace "nayarda...."
Fuskarta yakama da hannun sa yace "Ina sonki Waheeda, abinda nasani kenan, Bayan haka bazan iya fada miki komai ba saide kigani a aikace kawai, Allah yayi miki Albarka, Allah yarabaki da Baby na lafiya"
Tace "Amin" tareda shigewa cikin jikinsa
Cikin satin ya shirya musu tafiya Nigeria,dashi da mashkur da wasu Yan ball d'in Yan Nigeria suna sauka kuwa aka yanyamesu, daqyar yasamu suka qaraso gida, a gidan Ummah suka sauka, Ummah Sai Nan Nan take dasu kamar zata maida su ciki, Dafarko Babban Yaya kunya yakeji, daga baya Kuma yasake kamar kowa, Waheeda koda yaushe tana tareda yanbiyu, duk abinda takeso na kwadayi sune suke samo mata, bangare daya Kuma Ihsan tana shan soyaiya itada mashkur, intisar Kuma da Safwan yayan Maya
Kullum Sai Maya tazo gidan wajan Waheeda, wataran ayi fada wataran arabu lafiya 😂
Amma hakan baya hanata dawowa gobe, ko bata dawo ba Sai Waheeda ta kirata, haka zatazo ta zauna suna hira ayita musu kamar wasu Yara
Babban Yaya yana wajan harkar Ball dinsu, acan yake wuni tareda su mashkur, da daddare kuwa ya lalla6a wajan matarsa su raba dare suna shan soyaiya, kullum Sai yayi, ko gajiya ba yayi, Waheeda har mamakin sa takeyi yanda yake rawar qafa akan abin, kuka kuwa babu fashi saide idan yanayin kukan tarufe masa baki karsu Ummah su jisu, shi kuwa baisan ma yana yi ba, abinda yasani shine matarsa tunda tasamu ciki taqara dadi, yariga yasan cewa Waheeda itace komai nasa a yanzu, tariga tagama mallakeshi
Sun dade a Nigeria, ko hanyar gidansu basu nema ba, suna Nan a gidan Ummah, su Babban Yaya kuwa Bayan wani lokaci Kuwait suka wuce, inda acan ne Bana za'a buga gasar qwallon qafar tasu
Saida aka gama qarqare wasa sannan suka dawo gida cikeda dumbin nasara, a ranar bai dawo gida dawuri ba saboda Kai tsaye Dama fadar shugaban qasa suka wuce, saida aka gama karramasu sannan kowa yatafi Gida
A ranar Waheeda saida ta raina kanta, tun suna abu na marmari har tazo tana kuka tana bashi haquri, saida yayi sau uku ajere, sannan yarabu da'ita
Washe gari shirya wa tayi suka tafi Asbiti, da'ita dashi dasu yanbiyu, harda su Sa'ad da Sa'eed, tallafin kudi sukaje suka Kai asbitoci, suna rabawa kowanne majinyaci
Ba asbitin gwamnati kadai ba, harma da wasu daga cikin private hospital
Suna zuwa wani private Hospital a lokacin har magrib tayi, suna sauri zasu koma gida sukaga Ana fada aharabar hospital din, wata mata da Miji ne sunata fada Sai rabasu ake
Mijin yana cewa "kin cuceni, Allah ya'isa tsakanina dake Zuby, lafiya ta kalau na aureki, ashe yaudarata kikai kika Sakamin cutar qanjamau, bazan taba yafe miki ba kije nasake ki....."
Waheeda ta dora hannunta akan bakinta cikin tsananin mamaki tace "Huzaifa!!!"
Ihsan ta zumbura baki tace "Allah yaqara"
Babban Yaya baice komai ba, yaja hannun Waheeda suka shige mota, huzaifa ya biyo su da gudu yana fadin "Waheeda ki yafemin"
Hannu kawai ta daga masa, bata iya cewa komai ba, Dan taga gogan Nata akusa yake, ya daure fuska sosai babu alamar dariya, ya dawo mata Babban Yaya sak! 😎
Tanajin yanda su Sa'eed da Ihsan suke ta maganar huzaifa, itade bata tankaba, Amma har sukaje gida tana mamakin rayuwa, haqiqa Maya tamata gata data nuna mata mutumin dayake qaunarka tsakani da Allah, tabbas Maya Tawuce qawa awajanta, saide Yar'uwa
Harsuka koma gida Rasa gane kan Babban Yaya tayi, Sai wani shan qamshi yake, a dakinsa ma sun futo daga wanka taga Sai wani abu yake yana dauke Kai, kamar bayason magana yace mata "kishirya kayan ki gobe zamu koma"
Cikin sauri tace "gobe gobe Babban Yaya? Tafiya babu shiri? Mubari mana ko zuwa next week ne"
Cikin daure fuska yajuyo ya kalleta yace "idan kin zauna a gidan me zakiyi? Ok nagane, kinfiso nabarki agida kina kallon wasu mahauka ta kina bude murya kina Kiran sunan su, miye hadinki dashi, kawai daga ganinsa Zaki wani kira sunan sa, to dake yake fadan ma kome? Shida matarsa ne, miye naki na magana? "
Dariya ce ta kamata, Amma saita danne taqi yi, inda itace take kishin sa haka zai zauna yasa ta agaba yana mata murmushi, Amma shi kalla yanda ya sauya lokaci daya
Ahankali tatashi ta qarasa wajan sa, ta rungume shi tabaya, tadora hannunta akan nipples dinsa tana shafawa tace "shine dalilin fishin?"
Cikin 6acin rai yace "shine"
Towel din jikinta tacire yafadi qasa, tafara goga masa boobs dinta ajikinsa, ta dora hannunta akan mararsa tace "to kayi hakuri nadena kaji Baby na? Bazan sake ba, kayi hakuri kaji?"
Ajiyar zuciya yasauke yace "shikkenan"
Cikin shagwa6a tace "to kayi murmushi mana"
Yabude baki zai sake mata wani korafin
Tayi sauri tadawo gabansa tasaka masa nononta a bakinsa, Sai yayi dif kamar bashiba, yakama yafara Sha, Dan dolensa haka ya haqura, awannan Daren sun Raya Sunnah yanda yakamata, ita kanta bataso ya daina ba, taji dadin abun sosai
Kwanan su uku, suna shirin tafiya,daga baya sukai sallama da kowa, suka tafi, Bai Barta ta zauna haka ba a England, Addmissoin ya nema mata tafara karatu, inda Allah ya temaketa laulayin cikin Nata yazo mata da Dan sauqi, haka tafara karatu cikin kwanciyar Hankali, suna kula da Cikinta yanda ya kamata
Amnah El Yaqoub ✍�?
1/28/22, 20:53 - Ummi Tandama😇: MH
Da shawarar Hajiya Anty tayi amfani, Kuma taga amfanin ta, domin kuwa Hankalinta yana kwance, duk abinda take buqata yanayi mata, Kuma mata da maza basu daina nemansa ba haka take danne wa, daga qarshe ma itace take daukan wayar ta fadamusu bayanan idan yabar wayar agida, wasu daga cikin fans dinsa idan ta daga wayar haka zasu dinga girmama ta, abinda tasani shine koda niyyar soyaiya suka kira mijinta kokuma da niyar zumunci itakam tariqe mijinta yanda ya kamata, duk wani haqqin sa tana kokarin bashi
Watan cikinta shida Amma daqyar take wasu abubuwan, tabashi shawara su yanbiyu sutaho kodan su dinga rage mata wasu ayyukan, Amma qememe ya nuna bayaso saboda zasu takura masa idan sunzo, bazasu barshi yayi kukansa cikin dare yanda yakeso ba 🙈
Saide shine yake Hana Kansa wani aikin, ya zauna a gidan suyi komai tare, bikinsu Didat Sai qara matsowa yake,dama can shekara daya aka saka, yanzu Kuma saura wata biyu, Waheeda Kuma saura wata daya tagama second semester dinta,a lokacin Shima Babban Yaya wani club dinne suke shirin siyarsa, tana gama exam kuwa, suka dawo Nigeria, Anty tayi mamakin girman cikin Waheeda, wata bakwai Amma yarinya idan zata tashi saita runtse idonta
Idan ta zauna kuwa wuni take a zaune, babu kunya Babban Yaya zaizo yasa ta agaba su zauna, duk abinda take buqata kawai fada masa zatayi, haka zai kama hannunta su dinga zagaya gidan suna tafe suna zancen su na masoya
Ranar biki kuka kawai take, yanda taga yanbiyu sunyi shiga Mai kyau Kaya yayi musu cif cif ita kuwa Qin shigarta yayi, dole Sai Hajiya Anty ce tasa akayi mata sabon dinki a ranar, akayi mata doguwar Riga bubu, akasa Mai kwalliya itama tayi mata, duk wani party da aka shirya dasu walima Babban Yaya yana tare da ita, idan yaga tagaji Nan da Nan zai kawo hannu ya d'auketa, ko kadan bayason abinda zai taba lafiyar cikin Nan
Anyi biki lafiya, ankai amare gidajan mazajensu Wanda Babban Yaya ya gwangwaje su dashi, gida iri daya Kuma kusa da juna
Dayake yanbiyu ne matan nasu Nan da Nan Sai