Showing 45001 words to 48000 words out of 77020 words
Chapter 16 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
Yaya ne, fishi yake Dani, narasa yanda zan masa, ya cika rigima wallahi"😔
Maya tayi wani murmushi Mai d'auke da ma'anoni tace "inyee saikace wani Babynki Babban yayan kike cewa yacika rigima? Meya miki to?"
"tunda akai maganar auren Nan, narasa gane Kansa, kwata kwata baya sakarmin fuska kamar baya, sannan Bahaka yakewa 'yanbiyu ba"
Maya ta riqe hannunta tace "qawata ki kirashi kibashi hakuri, nasan yana jin maganar ki, sannan ki marairaice masa kamar Zaki masa kuka, aikin gane dai, shagwa6a Zaki masa duk ki haukata shi"
Zare hannunta tayi daga cikin na Maya tace "me kike nufi? Waike Dan Allah meyake damunki ne? Saurayina ne dazan dinga masa wannan abun? Maya Babban Yaya fa nace Miki ba Huzaifa ba"
Maya ta yatsina fuska ganin plan d'in Nata bai samu kar6uwa ba tace "toki rabu dashi kawai, ai zai huce ne, yaushe Zaki fara gyaran jiki ne? Biki Sai matsowa yake, Gara fa tun yanzu kifara shan abubuwa Wanda zasu sa kifara tsiyaya, sonake kisa Huzaifa kuka a Daren farkon ku"
Ajiyar zuciya tayi tace "Anty tace gobe zan fara zuwa, kitaho da safe ki sameni a gidan Hajiya Antyn, saina yiwa Huzaifa magana yazo yakaimu gidan, namanta ma ban fada miki ba, Su Daddy sunce muje Asbiti ayi mana text, na jini, kinsan yanzu yanayin rayuwar ya sauya komai Sai ahankali "
Maya ta Jinjina kanta, tafara wani tunani, ta kalli Waheeda tace"hakane Kam, saikaje ka auri me sikila ma baka Sani ba, Gara kuje din Kam, wanne Asbiti zakuje? "
Zuciya d'aya Waheeda tace"na fad'awa Huzaifan de, yacemin tunda gobe zamuje wajan gyaran jiki,jibi Sai muje asbitin, akwai asbitin da ake duba 'Yan gidansu, (Al'islah Hospital) private ne, can nake tunanin zamuje"
Maya tace "to shikkenan, Allah yakaimu goben, saina shigo"
Daga Nan sukai sallama, kowa yatafi gida
** *** **
Washe gari da safe Maya a gidan Hajiya Anty tasamu Waheeda, anan sukayi breakfast sannan Waheeda takira Huzaifa yazo yad'aukesu suka tafi
Maya tana gidan baya, Waheeda da huzaifa suna gaba, Sai kashe mata murya yake suna soyaiya, hankalin Maya yana kan wayarta tana daddannawa, a gidan da Hajiya Anty ta fad'a musu yasauke su, sannan yatafi, gidan suka shiga aka fara yimata gyaran jikin yanda ya kamata, tsawon lokaci suka d'auka ana mata abu d'aya,Bayan angama gyaran jiki matar tabata wasu magungunan na mata, ta zaunar da'ita a gabanta, saida taga ta Shanye sannan,wani irin qyalli Waheeda tafara, gyaran yau ma kenan, ita kanta Maya Kallan ta take tana mamakin yanda tayi kyau, to rana d'aya ma kenan idan kuma aka gama gyaran gaba d'aya Yaya Waheeda zata kasance? 🤔
basu gama da wuri ba Sai wajan yamma, sukayi mata sallama saikuma gobe idan sun dawo
Allah ne kawai yakawo su gida lafiya, domin kuwa Huzaifa yana ganin irin gyaran da akayi Waheeda saiya susuce bashida aiki saide yajuya ya kalleta, yana driving yana Kallan ta, Maya ta godewa Allah data ganta a kofar gidansu sunzo lafiya, tana futowa daga motar ta leqasu ta window tace "to wallahi ango kakula da qawata sosai, nide na godewa Allah tunda ankawoni gida lafiya"
Dariya huzaifa yayi ya shafa sumar Kansa, yasan Sarai taga halin daya shiga ne shiyasa tayi masa wannan maganar, Waheeda ma tayi mata murmushi tace "to Sai munyi waya qawata, gobe karki shirya da wuri, saida yamma zamuje, saboda da safe, Asbiti zamuje"
Maya tace "to shikkenan qawata, Allah yakaimu, kikula mana da angon namu"
Ta qarasa maganar cikin tsokana
Huzaifa yaja motar suka tafi, har zuwa lokacin Maya tana tsaye a'inda suka sauketa, saida taga sunbar layin gaba daya,memakon tashiga gidansu sai ta tare adedeta tashiga,tayi masa kwatance sukad'au wata hanyar
** *** **
Tafiya suke cikeda nishadi, kana ganinsu kasan suna cikin tsantsar farinciki, qamshin turaren sa yahad'u da Nata ga Kuma sanyin esi Sai abun yaqara bada armashi
Kallan sa tayi "Bae kadinga sauri muje mana, kana driving kamar baka so"
Kallan ta yayi "so kike nayi sauri Dan muje asbitin mugama da wuri kitafi kibarni ko?"
Murmushi tayi batare da tace komai ba, yasake Kallan ta yace "inason murmushinki Waheeda, yana birgeni, musanman idan Naga wannan dimple din...."
Kallan sa tayi "da gaske? Aikuwa koda yaushe zan dinga yima ka shi, saboda inci gaba da birgeka a koda yaushe, Dan banasan wata Rana kaga wata yarinyar itama ta birgeka"
Kafad'a ya d'aga yace "ai Bana tunanin akwai yarinyar dazata birgeni Bayan ke Waheeda, nifa banga amfanin zuwa wannan text din namu ba, saboda nasan kede lafiyarki kalau, Kuma Nima haka,idan kinada wata cuta ma ai saide in nine nasaka miki, tunda nine nabaki jini batare da angwada jinin nawa ba "
Cikin rashin damuwa tace"dansu Daddy sun matsa ne ai, Amma yanda nake jin ka acikin zuciyata ko wacce irin cuta ce dakai, zan iya zama dakai Bae"
Murmushi yayi ba tareda yace mata komai ba, suna qarasa wa asbitin sukayi wa nurse bayani,dayake tasan Huzaifa tun tuni, Nan asbitin suke zuwa duka family d'insu, cikin qanqanin lokaci aka d'auki jininsu aka basu wajan zama
Basuyi awa d'aya ba, doctor yakirasu zuwa office d'insa, zama sukai ya Kalle su yayi murmushi yace "Huzaifa kace ankusa angoncewa"
Murmushi Huzaifa yayi, "Eh wallahi Doctor, ga madam Nan"
Yace "To Allah yasanya alkhairi, Allah yabaku zuri'ah Dayyiba"
Ahankali Waheeda dake wasa da yatsun hannunta tace "Amin"
Takarda ya miqawa Huzaifa yace "toga result d'inka, Congratulations, baka d'aukeda kowacce irin cuta...."😃
Huzaifa ya kar6a yana fadin "to Alhamdulillah"
Kallan ta Doctor yayi yace "Waheeda"
'Dagowa tayi ta Kalle shi sannan tace "Na'am"
Yayi ajiyar zuciya yace "Waheeda duk abinda kikaga yasamu Bawa, to anaso ya yarda da qaddarar sa, ita cuta ba mutuwa bace, sannan idan kin yarda da shawarwarin dazan baki Zaki zauna lafiya, sannan Zaki rayu kamar kowa idan nad'oraki akan magani,kuma....."
"dan Allah dakata Doctor Mahmud, mekakeso kace ne?"
Cewar huzaifa daya dakatar da doctor
Doctor ya kalli idon Waheeda da yayi tsilli-tsilli tana Kallan su duka su biyun, sannan yace "Waheeda kiyi hakuri, Amma abunda bincikenmu ya nuna shine kina d'aukeda qwayar cuta me karya garkuwar jiki"
Lokaci d'aya, Waheeda da Huzaifa suka miqe tsaye
Huzaifa yace "What...? HIV fa doctor, tayaya?"
Gaban Waheeda yayanke yafad'i, tasaka hannu tadafe qirjinta, kanta take girgizawa kwata kwata takasa magana, lokaci d'aya jiri yad'ebeta tazube qasa sumanmiya "
Cikin sauri Huzaifa yabita, jijjigata yafara yi, yana fad'in" Waheeda!! Waheeda kitashi Dan Allah!! "
Office d'in aka turo, wata matashiyar budurwa tashigo, taci Gayu iya Gayu, tana ganin Huzaifa tace"Yaya Huzaifa lafiya Kuma? Meyasame ta?"
Huzaifa ya kalleta baice mata komai ba yasaka hannu ya d'auki Waheeda cancak, yafice daga office d'in
Yana fita matashiyar budurwar ta kalli doctor tace"meyake faruwa ne doctor?"
Kai tsaye yace "ta tsorata ne sakamakon gwajin da muka mata, muka Gano tana d'aukeda cutar qanjamau,but ni banga abun suma ba, kowanne Bawa da irin qaddararsa,Kuma ba lalle saika yi iskanci ne zaka sameta ba, akwai hanyo yi dayawa, wasu a wajan mahaifiyar su suke dauka, wasu ta hanyar hada jini Dame irin cutar, kokuma ayima allura da sirinjin Wanda yake d'aukeda cutar, kokuma sex, ko amfani da wani qarfe kamar su kibiya, to gashi ita tun kafin ma nafada mata magungunan daya kamata ta dinga Sha harta sume"
Cikin razani budurwar tace "mene? Wallahi saina fad'awa Hajiya, Kuma akan me qanjamau din yake wannan rawar jikin?Huzaifa d'an'uwana ne, cousin d'inane, bazamu Bari ya auri me wannan cutar ba, ta shafa masa masifa, ita tasan inda tasamu cutar ta"
Tana fad'ar haka, tafice daga office d'in, Doctor yayi murmushi sannan yabud'e wani file yaci gaba da rubuce-rubuce
Motar ya bud'e yasaka ta aciki,har zuwa lokacin Waheeda bata farfad'o ba, Shima yashiga, dube dube yafara anan yaga wayarta cikin hand bag dinta , Kai tsaye contact d'in wayar ya duba, mutum d'aya ne yafad'o masa, dayake wayar Ummah ce yana ganin Ansa Naufal Son,yakira wayar, Babban Yaya yana gida yana motsa jiki, yaga Kiran Ummah, dayake ringing d'inta daban ne, saiya daina abinda yake ya d'auki wayar
Cikin damuwa Huzaifa ya zayyane masa komai, Babban Yaya yadafe Kansa da hannun sa🤦🏻♂️yakasa cewa komai,banda innalillah wa inna ilaihirraji'un babu abinda yake maimaita wa a ransa, lokaci d'aya yarasa a'ina yake, a zaune yake ko a tsaye, gabansa banda Dukan uku uku babu abinda yake,Hiv Kuma? Hasbunallah..... yana jin Yanda Huzaifa yake fad'in "hallo hello, baka jinane?"
'Dif yakashe wayar, cikin tashin Hankali yazura kayansa yanufi Airport, ko wanka bai tsaya yiba
** *** **
Suna zuwa gida yad'aukota a hannun sa yafuto da'ita daga cikin motar, yanbiyu dasuke daukan photo a compound sukaga Huzaifa ya 'Dauko Waheeda, cikin sauri suka nufesu, Adede lokacin Didat da kakarsa da babansa suka shigo gidan, ta window din motar ya hango Wani ya dauki Waheeda a hannun sa, tun kafin babansa ya qarasa tsayawa da motar, yabud'e yafuto ya nufesu, yana zuwa ya cakumi wuyan Huzaifa "ubanwa yace ka d'auki wannan yarinyar...?"
Huzaifa ya kalli gaban rigarsa, yaga yanda Didat ya riqeshi cikin 6acin rai yasaki Waheeda tayi qasa, 'yanbiyu suna ganin haka sukai kan yar qanwar su suka cacimeta Sai jijjiga ta suke, Ihsan tayi gudu cikin gida ta fad'awa Ummah abinda yake faruwa, intisar Kuma tayi wajan fomfon da'ake bayin fulawa ta 'Debo ruwa ta watsa mata, lokaci d'aya ta farka tareda sakin wani irin kuka
Huzaifa yakama Didat, suka fara dambe 🙆🏻♀�?
Baban Didat ya kamashi yace "wuce mutafi gida, banason tashin Hankali son"
Ummah ta qaraso wajan itada Ihsan cikin tashin Hankali take tambaya ''menene yafaru?"Didat dayake ta haki da kumfan baki yace "Ummah saboda me wannan banzan zai dinga d'aukar Waheeda? saboda me Ina son yarinya wani qato zai dinga riqeta"
Cikin 6acin rai Huzaifa yace "nafi karfin a kirani qato, tunda nine Nan zan aure ta"
Didat yanuna shi da hannu yace "Dan zaka aure ta shine hakan yabaka damar ta6a jikinta? Aibaka aure taba"
Hajiya Anty tashigo gidan ta shirya tsaf zata wuce Asbiti, tabiyo wa Ummah zasu gaisa,kamar yanda tasaba, tana zuwa batabi takan kowa ba tanufi Waheeda, datake kuka kamar ranta zai fita, tambayar ta take "meyake faruwa?"
Amma Waheeda tayi shiru tama kasa magana.
kakar Didat ce ta matso ta kama hannun sa tace "muje" ta sake Kallan Ummah tace "Hajiya zamu dawo daga baya"tana fad'ar haka tajuya tashiga motar su, shikuma Didat babansa yakama hannun sa, yayinda Huzaifa yake sake gyara gaban rigar sa da Didat ya cukwikwiye masa, mutuqar tashin Hankali Hajiya Anty tashiga, jikinta Sai rawa yake tana kallon Waheeda, bata taba ganinta tana irin wannan kukan ba, gashi taqi yimata magana, Cikin 6acin rai ta make Waheeda da duka,tace"Dan ubanki bazaki fadamin abinda yake faruwa ba? "
Cikin kuka tace" Wai... Waii.... Ninn nice nake da qanjamau... "ta qarasa maganar tana rushewa da Kuka
Yanbiyu suka zaro ido😳 suna fad'in"qanjamau Kuma?"
Didat da babansa suka juyo da sauri, kowa Idonsa akan Waheeda sunaso suji ta amsa abinda yanbiyu suke tambaya, ahankali ta daga musu kanta alamun hakane
Didat ya kalli Waheeda ya jijjiga Kansa, sannan yayi gaba, babansa ma yabi bayansa suka tafi
Yanbiyu ne suka ja Waheeda sukayi ciki da'ita, gaban hijab dinta duk ya jiqe da hawaye, hannunta ta dora aka, tana rusa uban kuka, Hajiya Anty tabiyo bayansu cikin wani irin yanayi, kwata kwata bata sanin inda take jefa kafarta, kawai tafiya take, Ummah kuwa jitayi kamar tana tafiya akan is'ka, kalmar qanjamau d'innan Sai yawo take acikin zuciyar ta,Huzaifa yashiga motarsa yaja yabar gidan
ihun da Waheeda take ne yafuto da Daddy daga cikin daki cikin sauri, Nan yafara tambayar ba'asi, Amma kowa yakasa bashi amsa, da Yanbiyu da Waheeda kowa Sai kuka yake, su Sa'ad da Sa'eed ma suka futo daga daki kowa yana tambayar ba'asi
Hajiya Anty tadauko wayarta ajaka takira Uncle Usman tace "Alhaji gidannan fa babu lafiya, katashi daga baccin Nan kazo" tana fada masa haka muryarta na rawa alamun kuka zata fara, daga Nan ta kashe wayar ta
Ko minti biyar ba'ayi ba saiga uncle Usman yashigo dagashi Sai jallabiya, Daddy yace "Hajiya, mu duk munzo Nan mun zauna, muna tambayar ku meyake faruwa kunyi mana shiru, Yara suna kuka kunbarsu babu Wanda yake lallashin su"
Ummah ta Kalle shi "Alhaji Wai Waheeda ce me qanjamau..." tana fad'a masa haka hawaye yazubo daga idonta
Daddy da Uncle Usman suka nemi waje suka zauna suna fadin "innalillahi wa inna ilaihirraji'un...."
Hajiya Anty tadafe kanta daya ke ciwo kamar zai fado,Waheeda tanajin furucin Ummah tafara girgiza kanta,cikin kuka tace "wallahi ni banida komai, Allah sharri akamin" yanda take kukan abin tausayi shine yasake karya zuciyar yan'uwan Nata ma, Nan da Nan falon nasu ya kaure da koke-koke,
Ahankali Hajiya Anty tatashi ta janyo ta jikinta ta rungume ta, idanun Waheeda yayi jajir, fuskarta ma haka, Sai ajiyar zuciya take, Hajiya Anty ta kwantar da kanta a qirjinta tana bubbuga Bayan ta, Amma kwata kwata takasa cemata komai, ita kadai tasan metake ji acikin zuciyar ta
Maya ce takira wayar yanbiyu, cikin kuka intisar ta d'auka, Maya tace "Inti nakira wayar Ummah zanyi magana da Waheeda to ba'a d'auka ba, Dan Allah ki had'ani da'ita"
Cikin kuka intisar tace "Maya Waheeda babu lafiya"
Maya tace "innalillahi.... Kinga Bari kawai Gani Nan zuwa, tunda naji kina kuka nasan ba lafiya ba"
Ko awa daya Maya bata qaraba tazo gidan, yanda taga qawar Tata ta haukace tasan babu lafiya, haka sukaci gaba da zama sun kasa ta6uka komai, Uncle Usman yayi ajiyar zuciya ya kalli Daddy "yanzu Alhaji menene abin yi?"
"Salam Alaikum" yayi sallama ciki-ciki tareda shigowa falon
Gaba d'ayansu suka d'aga Kai suka Kalle shi, Waheeda tana ganin Babban Yaya tatashi da gudu ta fad'a jikinsa tareda sakin wani irin sabon kuka,ahankali ya Lumshe Idonsa sannan yabud'e su,yaso ace su kad'ai ne daya sake rungume ta ya lallasheta, ahankali yad'ora hannun sa abayanta yana bugguga Bayan ta kad'an kad'an , but duk da hakan yana jin yanda nonuwan ta suke bugar qirjinsa
Maya ta Kalle su, itade wad'annan mutanan suna birgeta, cikin sigar rad'a yaace "kiyi hakuri, is ok, kukan ya'isa haka"
Cikin kuka tace "Babban Yaya Allah banida komai"
Zareta yayi daga jikinsa
Yaruqo hannunta suka zauna a falon, Kallan Daddy yayi yace "Daddy ni Hankali na bai kwanta da wannan asbitin da suka jeba, why not Akira family doctor yazo gida ya dauki jinin Nata agaban mu saiya kawo mana result d'in mugani"
Daddy yace "to Son.... Tun dazu ma mu bamuyi wannan tunanin ba, munkasa aikata komai, hakan ma yayi"
Maya ta dauki wayarta tayi kira, ahankali tatashi ta kalli yanbiyu tace "Ina zuwa, zanyi waya"
Yanbiyu suka d'aga mata kai, ita Kuma tafita cikin sauri
Babban Yaya yakira family Doctor d'insu, yayi masa bayanin komai ta waya, cikin qanqani lokaci doctor khamis yazo gidan, yanda yaga family din duk sun had'u waje daya, yasan cewa haqiqa akwai abinda yake faruwa, Babban Yaya ya nuna masa Waheeda, doctor khamis ya qarasa ya dauki jininta, sannan ya musu sallama cewa zaije ya dawo
Har doctor khamis yatafi, banda addu'ah babu abinda mutanan Nan suke yi, kowa yayi shiru Sai zancen zuci, Waheeda kuwa Hankalinta ne ya kwanta, tasan cewa yanzu ne gaskiya zatayi halinta, zasu yarda da abinda take fad'a musu, kusan awa biyu suka d'auka suna jiransa, Sai gashi yashigo falon fuskarsa Sai had'a gumi take, suna ganinsa kowa ya miqe tsaye kamar Wanda suke jiran me naquda
Babban Yaya ya qaraso wajan sa, yariqe hannun sa yace "doctor ya ake ciki?"
Doctor khamis ya kalli Babban Yaya yace "kuyi hakuri yalla6ai, Bahaka naso fad'a ba, Amma tabbas akwai wannan cutar"
Babban Yaya yasake shi tareda dafe Kansa🤦🏻♂�? yace "Oh my God"
Sai hawaye
nanfa hankalin su yasake tashi, falon ya kaure da Kuka, musanman da basu ta6a ganin tashin hankalin dayasa Babban Yaya kuka ba Amma yau sunganshi da idonsu yana kuka, Babban Yaya yayi kan Waheeda yana cewa "Daddy zan kaita wani asbitin, ni qanwata batada komai"
Jin shiru Waheeda bata tashi ba yasa ya kalleta, Sai a lokacin ya lura ta suma 🙆🏻♀�?
Gabansa ne yafad'i, cikin tashin Hankali yafara jijjiga jikinta "ke.... Ki Tashi.... Please kitashi ninasan bakida komai Waheeda"
Yajuya ya kalli Ummah yace "Ummah kice mata batada komai...."
Magana yake yana kuka da Idonsa, kwata kwata kamar ma baya cikin hayyacinsa
Hajiya Anty ta share Hawayen idonta tatashi tadauko ruwa a fridge ta shafa mata, da Kuka tafarka, muryarta harta fara dashewa
Babban Yaya ya zauna, yadafe Kansa da hannayensa biyu tareda rufe Idonsa, Daddy ya kalli Waheeda yace "ke zonan"
Ahankali tatashi taje gabansa ta tsugunna tana sharar hawaye, Daddy ya kalleta yace "nasan bakya ji Waheeda, kifadamin a gidan ubanwa kika Dauko mana wannan masifar?"
Wani irin kuka ne yataso mata, hawaye masu zafi suka zubo daga cikin idonta, kanta tafara girgizawa tace "wallahi tallahi Daddy bansani ba.... Ni bansan zan dauki cuta ba"
Gaba d'ayansu Sai suka maida Kallan su wajan Waheeda, Daddy yace "ni nasan akwai abinda kika aikata, kifadamin kokuma yanzu yanzun Nan namiki illa a wajannan...." ya qarasa maganar cikin tsawa
Cikin kuka tace "anta6a yimin allura da sirinjin da akayiwa Didat dashi, sannan d'azu muna hanya Huzaifa yace min Wai jinin daya Bani a Asbiti ba'ayi masa text ba, haka aka Sakamin ba tareda an gwada jinin ba"
Wani irin kishi ne yakama Babban Yaya,shi yana can yana hauka akanta ashe ita tana Nan soyaiyar ta takeyi da samarin ta.
Cikin 6acin rai yatashi tsaye yace "What....?, ashe bakida Hankali bakisan mutum ba kawai saboda wata banzar soyaiyar ku Zaki yarda ayi miki amfani da sirinjin da aka masa allura?, sannan anfad'a miki ansaka miki jini batare da text ba so yarufe miki ido kikasa daukan qwaqwaqwaran mataki akai? Kifadamin ke wacce irin mahaukaciya ce? "
Kallan sa tayi tafara girgiza masa Kai tahad'e hannunta biyu waje d'aya 🙏🏻alamun yayi haquri
Babban Yaya bai saurareta ba ya d'aga hannu ya wanke tada mari, zai qara mata wani Marin cikin sauri Uncle Usman yace"Naufal"
Cak yaja ya tsaya yafasa dukanta, Uncle Usman yace "kayi Hakuri"
Sannan yajuya ya kalli Sa'eed da Sa'ad, yace "kuje kuzo mana da Huzaifa dakuma Didat, ga doctor khamis Nan bai tafi ba, saiya dauki jininsu aga waye yasaka mata cutar acikinsu"
❤️❤️❤️
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandama😇: GG
Daga Huzaifa har Didat, babu Wanda ya sauya Kaya daga cikin kayan da sukai fad'a d'azu 🤣
Dama kowa kamar jira yake, shiyasa su Sa'eed suna zuwa suka biyo bayansu, suka taho gaba d'aya
Uncle Usman ya kalli doctor khamis yace "dauki