Showing 39001 words to 42000 words out of 77020 words
Chapter 14 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
musu basa son zuwa gidansu
Zama sukai a Dakin Sai hira suke, Amma Waheeda tayi shiru, Maya ce ta kalleta tace "qawata meyafaru ne?"
Waheeda tayi ajiyar zuciya tace "Daddy yasake min maganar auren Nan, na turawa Didat text yaturo iyayensa, Amma har yanzu banji yacemin komai ba"
Wani irin yatsina fuska Maya tayi tace "Didat Kuma? Ke a ganinki wannan sonki yake? Kawai be'iya komai ba Sai kishi, dama Huzaifa kika Bawa Dama"
Ihsan tace "ato fada mata de, danma bakiga yanda yake bane Maya, wallahi yahadu"
Intisar tace "kuka Sani ko Didat din tafuso?"
Waheeda ta murgud'awa intisar baki tace "waye yafada miki Ana mantawa da first lover?"
Inti tace "to karki min rashin kunya, inde Didat ne keda shi, Ina soyaiya abinda kusan sati kikai a kwance babu lafiya Koya leqo qi, gashinan Huzaifa yazo, kije ki qarata da Didat d'in"
Maya tace "Gaskiya Nima Ina ganin Gara Huzaifa, kawai ki share Didat d'innan kiza6o mana Huzy"
Waheeda ta d'aga musu hannu tace "tonaji,kawai zanyi shawara da Babban Yaya"
Ihsan tace "bakida Hankali Waheeda, kirasa dawa zakiyi maganar saurayin ki Sai Babban Yaya Dan raini?"
"Bazanyi maganar dashi ba? Yanda yake yayanki Nima Yaya nane, in'aka bibiyama yafi sona a kanki"
Ihsan tace "to kirashi, Wanda baiji Bari ba yaji hoho...."
Maya tayi shiru tana wani tunani a ranta,addu'ah take a ranta Allah yasa tasamu amsar tambayar tunanin datake, cikin sauri tace "eh wallahi, kira Babban Yaya muji, shawarar tasama itace daidai" Tajuya ta kalli yanbiyu tace musu "koba haka ba?"
Ihsan tace "hakane wallahi, Kuma a saka mana ita a hands-free"
Waheeda ta dauki wayarta takira Babban Yaya, yana zaune ad'akinsa a lokacin yana tunanin kiranta, tunda tatafi rabonsa da'ita, yayi missed dinta sosai, ya jira ya jira kozaiga kiranta Amma shiru bata kiraba, yasan cewa idan ta kirashi tayi kewarsa ne, yana duba wayar yaga kiranta yana shigo wa, cikin sauri Yad'aga yace "Sai yau kenan"
Yan biyu da Maya suka hada ido sukai murmushi kowa yayi shiru yana jira aji amsar Babban Yaya.
Waheeda tayi murmushi tace "Babban Yaya wallahi inason kiranka, kayi hakuri"
Yace "okay, Ina twice?"
Tace "suna Nan kalau, suna falo, yauwa Babban Yaya kasan me? Daddy ne yace zaimin aure, nabashi hakuri yaqi ji, tunde laifin danayi wa Ummah , to nayi wa Didat magana naji shiru, shine nakeso kabani shawara ko in yiwa huzaifa magana... Huzaifa de ai kasan huzaifa, zaka sanshi ma, Dan gidan minister ne maici a yanzu... "
Tunda tafara magana Babban Yaya ya runtse Idonsa, jiyake kamar ana watsa masa garwashi ajikinsa, ajiyar zuciya yayi yabude Idonsa, sannan yace"to Ina ruwana Kuma? Miye nawa aciki? Wato Waheeda na lura babu Wanda kika raina sama Dani duk cikin qanne na, nizaki kira kina fadamin hauka, saboda raini, wato ga sa'anki,ni karki sake kirana..... "
ya qarasa maganar tareda kashe wayarsa, dama bashi tayi niyyar gaidawa ba? Bakira tayi dantaji muryarsa ba? Wata zuciyar tace dashi saboda samarin ta takira ka, idanunsa ne sukai jajir baisan lokacin da yaji hawaye yazubo masa ba, yasaka hannu ya hargitsa sumar Kansa,ya kalli wayar sannan yayi jifa da'ita ta had'u da bango ta tarwatse
1/28/22, 20:50 - Ummi Tandamaπ: UD
Ihsan da intisar ne suka kwashe da wata irin dariya, dariya suke suna nuna Waheeda da hannu,Waheeda takasa cemusu komai Sai kanta datake jinjinawa alamun gaskiya ne.
Maya kuwa jijjiga kanta take ahankali tana sake gaskata tunanin ta akan Babban Yaya, haqiqa Dama ta dad'e tana wannan tunanin, Sai gashi yau ta tabbatar da abinda take zargi
** *** **
Hawayen Idonsa ya share, yayi shiru yafad'a duniyar tunani, Mutum d'aya ce tafad'o masa Arai,yasan idan ya kirata zaiji 'Dan Sanyi a ransa, babu 6ata lokaci ya d'auki wata wayar yayi Dialing number ta, bugu d'aya tad'auka muryarta can ciki, Shima cikin shagwa6a yace "Anty...."
Hajiya Anty tace "Na'am d'an Ummah ya akayi"
Cikin damuwa yace "banajin dad'i Anty , narasa meyake damuna..." ya qarasa maganar qwalla Nason taruwa a'idonsa
Tashi tayi daga kwanciyar da tayi, cikin yanayin rashin lafiya tace "meyake damunka?"
Cikin tashin Hankali yace "Anty ya naji muryarki haka? Lafiya kike kuwa?"
Runtse idonta tayi tace "wallahi zazzabi nakeji Naufal, Amma nayi allura ma, nasan anjima zanji sauqi insha Allah, Ina Ummi? Kuna waya deko?"
"Bama waya Anty, Amma zanyi mata magana yakamata tazo ta duba ki"
Murmushi tayi "a a karka damu, karabu da'ita tahuta"
"a a Anty dole zatazo taganki, please kikula da kanki, Sai anjima" yana fad'ar haka yakashe wayar tareda Dialing number ummi π
Tayi mamakin ganin Kiran Babban Yaya, har wayar takusa katsewa kasa d'auka tayi, saboda wani irin dad'i dataji Wai yau itace Big Brother yake kiranta, haqiqa tana d'aya daga cikin mata masu sa'a a duniya, cikin sauri ta d'auka tareda fad'in "Big Brother, My Husband to be ...."
Runtse Idonsa yayi, jiyake kamar ta watsa masa ruwan zafi a qirji, Wai husband to be.... π
Ajiyar zuciya yayi yace "Ummi... Anty nah batada lafiya, kisa lokaci kije kiganta"
Yatsina fuska tayi tace "mene? Wai Dama ba kirana kayi domin kaji muryarta Kuma mu Tattauna akan batun auren mu ba?"
Cikin 6acin rai yace "Duba lafiyar matar Nan yafimin komai ummi, idan kika d'auke mahaifiyata, duk duniya babu wadda nakeso sama da'ita"
Cikin haushi ummi tace "to ai Kai kace, wannan a kanka kake magana, kaine kake sonta Bayan mahaifiyar ka, tunda aka had'ani dakai maganar arziqi bata ta6a shiga tsakanin muba, kawai sai yau Ina murna kakirani,babu tambayar lafiya ta babu komai shine zakace inje Inga wata mata, gaskiya bazaka takuramin ba,Kai Bama lalle naje ba...."
ta qarasa maganar cikin rashin kunya
Cikin masifa yace
" muddin kikace bazaki mutunta iyayena ba,to bazan iya zama dake ba, ke ko wani daga cikin 'Yan gidan mu kikace bazaki mutunta ba, to babu dole, dama can banida ra'ayin auren yarinyar da banaso, inaso kisani dole akamin a kanki, danhaka bazaki samun ciwon Kai ba...."dif yakashe wayarsa
Ummi ta qulu iya quluwa, Sai huci take tana hura hanci, inbanda tana so duniya tasan ta'auri mutum mashahuri babu abinda zaisa ta tsaya wannan gayen yana fad'a mata baqar magana, badan taso ba, haka ta shirya ta nufi gidan Hajiya Anty.
Tunda suke unguwa d'aya bata ta6a shiga gidan ba, Sai yau, lokacin data qarasa megadi yatare ta yana tambayar ta wajan wa tazo, cikin Isa da gadara ta fad'a masa cewa itace matar da Naufal zai aura, cikin girmamawa megadi yabud'e mata gidan tashiga
Duk irin shigar da tayi ta alfarma tana ganin hajiya Anty a hakimce afalo duk Sai taji ta raina kanta, saida tagama qarewa hajiya Anty kallo taga mace har mace ga kyau ga kwalliya, ga Kuma irin daular datake ciki, saita yatsina fuska sannan tace "Sannu yajikin?"
Hajiya Anty tana kallon ta, duk taga abinda tamata,babu maganar gaisuwa kawai sai sannu π, Saita shareta ba tace mata komai ba Saima murmushi da tayi tace "A a kice yau amare ne a gidan namu, sannu da Zuwa Daughter"
Ummi ta kalli hajiya Anty asheqe, Wai Daughter, matarda ko haihuwa bata ta6a yiba itace zata kalleta qatuwar budurwa da'ita tace mata Daughter π
Saitayi yaqe ta kawar dakai, Hajiya Anty tatashi takawo mata ruwa da lemuka, sannan tayi kitchen takawo mata kaji cikin flet, babu musu ummi ta zage ta dinga cin kajin Nan saida taji tayi qat, sannan tayi mata sallama tatafi,Hajiya Anty tabita da kallo, babu Allah yasawaqe babu komai kawai cikinta yana cika taqara gaba, kwata kwata babu alamar Hankali a wajan yarinyar, babu kunya ko kara atare da'ita, ajiyar zuciya tayi a fili tace "Allah yabasu Zaman lafiya"
Sannan ta d'auki wayarta takira Babban Yaya, yana d'auka tace "Ummi tazo, kakirata kamata godia"
"ashe tazo" abinda yace kenan, domin beyi tunanin zatazo dinba
Tace "tazo wallahi, yanzu tatafi, nayi tunanin ma anan zata wuni, Amma duk da haka naji dad'i sosai, Allah yamuku Albarka Allah yahad'e kanku"
Memakon yace Amin, saiyace "Anty inada aiki yanzu, akwai horar war da'ake mana, zan kashe waya"
Murmushi tayi tace "yakamata kazo kaga lefen Nan, idan akwai abinda baiyi maba, Sai a sauya, sannan nace ka tambayeta size d'inta na pant da bra, Shima har yanzu bakace min komai ba"
Cikin shagwa6a yace "Anty zanzo... Shikkenan?"
Tace "eh, shikkenan" daga haka, sukai sallama
Wayar Ummah ce kange a kunnan ta, tana zaune afalo tana waya dashi cikin nutsuwa, tun Bayan da Babban Yaya yawatsa mata qasa a'ido yanbiyu suka mata dariya, bata sake bi takansa ba, ta nutsu ta ajiye Didat agefe, takama Huzaifa π
Huzaifa yasake lanqwashe muryarsa yace "Waheeda bazaki Bani Dama naturo iyayena gidanku ba? Kinsan kuwa yanda na matsu naganki a gidana?"
Murmushi tayi ta dauki cup din dake gabanta me cikeda fresh milk tayi sipping sannan tace "idan lokaci yayi ai zan baka damar, saurin me kake?"
Dariya yayi yace "Me kikeci?"
Tace "Madara ce, ko zaka Sha?"
Daga d'ayan bangaren Huzaifa yace "banashan madara, idan Nasha wahala take Bani da daddare, Saide inzaki Bani da hannunki saina sha..."
Kunya ce takama Waheeda, tasaka hannu tarufe fuskarta kamar yana ganin ta π
Uncle Usman ne yashigo falon yazo wajan Daddy, yaga yarinya Sai rufe fuska take ita kadai, ga Kuma waya a kunnan ta tanata murmushi
Qarasowa falon yayi cikin sigar tsokana yace "anata wayar ne Waheeda? Kode da sirikin nawa kike waya?"
Waheeda tayi sauri ta kashe wayar, sannan cikin kunya tace "Uncle Huzaifa ne..." tana fada masa haka, tashige dakinsu cikin kunya
Uncle Usman ya qarasa Dakin Daddy Bayan sun gama abinda zasuyi, Uncle Usman yace "Yaya yakamata fa Yaron Nan Huzaifa idan da gaske yake yaturo,inda zai iyu da anhada bikin Waheeda Dana Naufal"
Daddy yace "Eh da munji dadin hakan gaskiya, Bari zanyi magana da mahaifin sa, tunda Naga yanzu ta bashi Dama yana zuwa zance a koda yaushe nasan sun dedeta, zanyi magana da mahaifin sa, Saisuzo ayi magana kawai"
Kamar yanda suka yanke wannan shawarar kuwa, haka akayi, cikin satin iyayen Huzaifa suka zo neman aure, Daddy da Uncle Usman da baba Habu sukace sun basu π₯π€
Waheeda dataji wannan labarin bata damu ba, asali ma murna taitayi cikin ranta, saboda har aqasan ranta tanajin soyaiyar Huzaifa, tana sonsa sosai, idan ta zauna ta dinga tunanin sa kenan, shiyasa tadauki zuciyarta gaba daya ta damqa ta ahannunsa
** *** **
A kwatuna ne a shirye daya kan daya guda goma Sha biyu masu launin brown
Minister ne a tsaye yana kokarin Kiran waya, tsaki yayi ya zauna tare da fadin "inaga babu network ne, tun dazu nake gwadawa Amma taqi tafiya, ai Gara afada musu lefe yahadu, yaushe suke ganin yadace akawo musu?"
Hajiya Babba mahaifiyar Huzaifa, tajuya ta kalli huzaifa dayake Sanye cikin kayan shan iska, yana danna laptop din gabansa, tasake juyawa ta kalli minister tace" yanzu Alhaji baka ganin wannan kayan sunyi yawa? Ina laifin ma a kwatuna hudu ko biyar? "
Kallan ta yayi yace" kinsan me kike fada kuwa? Kinsan matsayina awannan jihar kuwa? A kwatuna shabiyu ai sunyi kadan hajiya, ko bakisan gidan da za'a Kai bane? "
Cikin 6acin rai tace" nasani mana Alhaji, ba gidan buzayen Nan bane? Ni kwata kwata yarinyar Nan bata minba, kana ganinta daga ita har yan'uwan Nata kasan irin sadaka yallar Nan ne..., duk abi a rabaka da danka ta hanyar asiri "βΉοΈπ
Huzaifa ya kalleta yace" Momy.... Ni inason Waheeda, Kuma gaskiya bazan iya barinta ba "
Minister yayi Dariya yace"to kinji, Kuma nikaina nasan idan Huzaifa ya auri yarinyar Nan zan samu jikoki kyawawa... Kisawa yaro Albarka kawai acikin auren sa"
Hajiya Babba takama jijjiga kafarta, ranta in yayi dubu ta ya6abaci.... Daga Dan har uban haka suka qyaleta, minister yaci gaba da neman number Daddy
** *** **
Washe gari karfe Tara nasafe, a Nigerian tayi masa,Kai tsaye wajan shopping yaje yasiyo panties da Bra, lokacin dazai za6a tunani yake wanne size zai d'auka mata? Shide bai ta6a ganinta azahiri ba,bare yayi hasashe ya d'auka mata Kuma pant da Brezia babu size din wadda yasani saina Waheeda, danhaka batare da tunanin komai ba ya 'Dauko mata daidai size din Waheeda ππ»ββοΏ½?
kasancewar sa mutum
na mutane bai samu zuwa gidan Hajiya Anty ba, Sai karfe goma Sha shad'aya, Kai tsaye gidan yashiga, kasancewar tana takura masa da waya yazo yaga lefe, yasan cewa idan ya wuce gidansu baizo yaga lefe ba, to zata dinga yimasa Mita ne, shiyasa Kai tsaye ya wuce gidan Nata, maigadi Sai washe masa haqora yake yana kwasar gaisuwa, saida yayi masa yayyafin kudi sannan yabarshi yasamu ganawa da Antyn nasa.
Gabansa tacika da kayan break fast, Sai Nan Nan take dashi kamar zata saka shi ajikinta, waya yake amsa wa cikin farinciki, yau yana jin wannan zuwan nasa na musanman ne, tunda har yazo Nigeria dan rad'in Kansa ba fitinar Waheeda ce ta kawo shi ba π
Yana ajiye waya, wata wayar tasake shigo wa, Kuma gaba d'ayansu masoyansa ne, tun yana amsawa harya fara gajiya, Amma duk da haka bai fasa d'aukar wayar masoyan nasa ba, saida Hajiya Anty taga abin nasa Bana qare bane, kawai saita kwashe wayoyin ta kashe su, sannan tafara bashi break fast din da kanta, saida yaci yaqoshi sannan tajashi zuwa wani d'aki, photunan Waheeda ne birjik acikin Dakin, saikuma na Babban Yaya dasu Sa'eed, saikuma na dukansu yaran gidan dasuka had'u suka d'auka tace "toga kayan lefenka..."
A kwatunan ya kalla guda ashirin da hud'u, ya kawarda da Kansa yace "nagani, sunyi"
Cikin mamaki ta Kalle shi tace "tayaya kasan sunyi Bayan ko bud'ewa bakayi ka Gani ba?"
Kallan inners d'in daya kawo tayi tace "sannan wannan kayan daka siyo sunyi wa ummi yawa, na ganta ai rannan, wannan bra din tamata yawa, bansan de pant d'inba, kaida nace ka tambayeta size dinta meyasa zaka siyo?"
"ai itace tace haka ne size din Nata" ya qarasa maganar cikin d'aure fuska
Hajiya Anty tace "to shikkenan, zanyi magana da ummanku, Sai muji ranar daza'a saka akai musu kayan"
Yana jin ta d'auko hanyar maganar auren sa, ransa yaqara 6aci, babu shiri yayi mata sallama yabar gidan yanufi gidansu.
Tun abakin get mutane suka masa cincirundo, Sa'ad da Sa'eed suka tar6eshi suka qaraso gidan, Ummah bakinta Qin rufuwa yayi, babu Wanda yayi tunanin zuwansa, Sai gashi ya basu mamaki yazo, Ummah ta Kalle shi duk farinciki ya cikata, ganin yanda yasaki ransa tasan cewa may be ya yarda da auran ne tace " 'Dana,me zakaci? Me kakeso nayi ma?"
Kallan ta yayi,yayi murmushi dimple d'insa ya lotsa, su yanbiyu da Waheeda Sai dariya suke musu shida Ummah, ganin yanda duk ta rikice ganin Babban Yaya kamar sudin ba sauran yaranta bane, kafin Babban Yaya yayi magana Daddy ya kalleta yace"haba Hajiya,Naga alama yakamata nadinga tuna miki cewa Naufal bashine auta ba "
Waheeda ta turo Dan qaramin bakinta gaba tace"Bayan Ummah tafi sonshi Dani"
Ummah ta kalli Waheeda ta kalli Babban Yaya tace "rabu dasu Dana, me zakaci nadafa ma dakaina? Karka damu da surutun su Dama can kishi suke dakai"
Fuskarta yakama yariqe yace "Ummah tah ta kaina, inason ki Ummah, naci abinci a gidan Anty, can nafara zuwa Naga Kaya, karki damu kanki, banajin yunwa, anjima de keda kanki Zaki Bani abinci da wannan hannun naki" ya qarasa maganar yana kissing hannunta, Ummah ta kalli Daddy alamun bata gamsu da maganar da Babban Yaya yafad'a mata ba, Daddy yace "yace miki ya qoshi hajiya,ai yana Nan a gidan babu inda zaije, anjima saiki bashi abincin"
Sai a sannan Hankalinta ya kwanta, ta kalli Naufal dayake Kallan ta cikin murmushi tace "to shikkenan, kaje daki ka kwanta ka huta, Kuma ka kashe wayoyinka kajiko"
Yace "to Ummah nah" daga Nan yatashi yayi dakinsa, Waheeda ta kalli brief case dinsa daya manta bai tafi da'ita ba, tasan Kuma kudi ne aciki, idanuwanta Tajuya, tana fatan ace yabata ko 50k ne, cikin sauri ta dauki jakar tabi bayansa
Tana shiga 'Dakin ta ganshi yana kokarin cire Kambos d'in kafarsa, Kallan ta yayi ba tare daya Dena abinda yake ba, cikin murna dajin dadin ganinsa tayi saurin qarasa wa wajan sa ta ajiye Brief case din akusa dashi tace "Babban Yaya ga kud'in ka" π
Murmushi yayi, ya kalleta yace "kud'i na kuma? Waya fad'a miki kud'i ne aciki?"
Hannun sa takama tacire daga kan takalmin nasa dayake so yacire, ta qarasa cire masa takalmin kamar wani mijinta, sannan tacire masa safar tana cusata cikin takalmin, takama dogayen yatsun kafarsa masu laushi tanaja ahankali sannan tace "ai nasan kudi ne aciki, Dan Allah Babban Yaya ka temaka kabani kudi ko dubu hamsin ne"
Ba tareda tunanin komai ba yace "bude ki d'auka"
Kafarsa tasaki tabud'e jakar, da daloli tayi tozali, cikin mamaki ta d'ago ta Kalle shi tace "Kai kai Babban Yaya ashe kudin ne aciki? Allah jinake ba kudi bane, kawai fad'a nayi"
tafad'i hakan tana rufe jakar, sannan tatashi Takoma kan gadon ta zauna kusa dashi
Babban Yaya ya kalleta yace "ki d'auka duka nabaki"
Cikin mamaki tace "me? Wai kudin?"
Yace "Emana, kid'auka nabaki"
Kanta ne ya d'aure tace "Babban Yaya, daloli ne fa aciki, me zanyi dasu?"
Juyowa yayi yana fuskantar ta, yace "tome kike so? Idan kud'in kike so kitafi dashi, saiki saka cikin account dinki"
Murmushi tayi, dimple dinta yafuto kamar nasa tace "Babban Yaya kana magana kamar ranka a6ace, please kasaki ranka mana"
Murmushi ne ya qwace masa ba tareda shirya ba, yace "naji, tashi kibani waje, Ummah nah tace na kwanta nahuta"
Bakinta ta turo gaba, cikin shagwa6a tace "Babban Yaya Dan Allah mu 'Dauko anko? Wallahi Dama kud'in danace inaso d'in sonake naje kasuwa mu 'Dauko anko"
Dariya ce ta kamashi yace "kuma anko da dubu Hamsin?Bari kiji, babu wani anko da zakuyi, tunda bason auren nake ba, Kuma ta shafeku"
Tace "Dan Allah Babban Yaya kaji, wallahi muna so, Dan Allah muyi? To wai Kai meyasa baka son auren?"
Cikin damuwa yace "nafad'a miki Bana burin zama da wadda banaso, karki sake min wannan tambayar, Sai me Kuma kike so Bayan wannan?"
Lallausan Hannun sa takama tariqe cikin Nata, Kallan ta yayi cikeda mamaki ya kasa magana haka Kuma ya kasa qwace hannun sa, cikin nutsuwa tafara yimasa magana tace"nikam ai nagama samun abinda nakeso a rayuwa Babban Yaya, iyayena suna sona, Babban Yayanmu yana sona, sannan Huzaifa yana sona, Bana tunanin komai akansa, nasan ko Bayan munyi aure zai riqeni Amana kamar Babban Yayanah, saide Kuma naso ace nasamu