Showing 54001 words to 57000 words out of 77020 words
Chapter 19 - Babban Yaya Book 1 Hausa Novel Complete
nasaka ku cikin wani Hali, Amma ba komai ne yasa nayi hakan ba Sai saboda taimakon da Babban Yaya yata6a yimin lokacin da muka shiga cikin wani hali nida iyayena, yatemaka mana a lokacin da muke buqatar temakon,.... "
Jin wannan furucin Nata yasa hankalin kowa ya dawo kanta, Sai kowa yazuba mata ido yanaso yaji abinda zatace, Daddy yace"menene yafaru Maryam, fad'amana muji"
Kanta ta sunkuyar tace "Gaskiya Waheeda bata d'aukeda kowacce irin cuta, lafiyarta kalau, tun muna ss2 nafahimci cewa Babban Yaya yana sonta, tundaga lokacin naci d'amarar temaka masa akan Waheeda, Ina bata shawara sosai akansa duk Dan naja ra'ayin ta, to Amma Naga hakan bata samu ba, saboda koda yaushe abinda take fad'a min d'ayane shid'in yayanta ne, Ina tunanin mafita saina ji har ankawo mata kayan lefe, narasa yanda zanyi in rabata da Huzaifa, kawai rannan Sai take fad'amin zasuje Asbiti ayi musu text, da wannan damar nayi amfani nasamu family Doctor d'inku wato Doctor Khamis, na fad'a masa komai, anan Shima yabani goyon baya, ya tambaye ni Dame nakeso ya temaka min, Kai tsaye nafad'a masa tunda shi Babban likita ne nasan yanada alaqa da wasu hospital d'in dayawa, inaso duk asbitin da Waheeda taje a fad'a mata cewa tana d'aukeda cutar qanjamau, ta wannan hanyar ne kawai zan gane wannan Huzaifan datake rawar Kai akansa shin yana mata soyaiyar Gaskiya ne kokuma ta qarya? Idan soyaiyar gaskiya yake mata to zanji dad'i nasan koda qawata ta aure shi zaici gaba da sonta, idan Kuma duk qarya ce, to lokaci zai nuna, Doctor khamis yabani goyon baya sosai, Kuma Alhamdulillah yanzu gashi gaskiya tayi halint...... "
Kafin Maya ta qarasa magana Sai ganin Waheeda sukai tatashi tsaye tashaqe mata wuyaππππ»ββοΏ½?
Sosai suka kama dambe, Maya tana kokarin qwatar kanta Waheeda kuwa idonta yarufe takama Maya Sai dukanta take
Su Ummah ne suka tashi da Anty da Kuma yanbiyu suka fara rabiya, Amma Waheeda tayi wa Maya wani irin ruqo kamar ba qawa da qawa ba ππ
Cikin kuka Waheeda tace "daga yau babu ni babu ke, karki qara zuwa inda nake, dama can kema nasan bakya sona, tun tuni nagane take takenki..."
Wani irin murmushi Babban Yaya yayi,haqiqa dole ya kyautatawa Maya, tayi masa abinda bazai ta6a mantawa ba,dama ta dalilin tane Waheeda bataje Saudia ba saboda Ummah taji suna waya, yanzu kuwa yayi alqawarin had'ata da qawar Tata sutafi Saudia tare, saisuci gaba da damben acan π
Ummah ta kalleta tace "bazaki saketa ba?"
Cikin kuka Waheeda tace "to Ummah meyasa zatasa a aura min Wanda banaso? Ita uwata ce?"
Uncle Usman ya kalli Babban Yaya yace "Kai tashi kaja matarka kubar gidannan"
Ummah ma tace "eh wallahi, ni nagaji da fitinarki Waheeda, memakon ki godewa Allah bakida cutar komai, saide ki kama dambe? Wuce kibishi kutafi gidanku mun yafe zamanku a gidannan, Allah yabada Zaman lafiya"
Ahankali yatashi yanufeta, har zuwa lokacin hannunta yana jikin hijabin Maya Wanda taqi saki, yana zuwa yasaka hannu yacire mata Nata hannun, sannan yajata zasu bar falon, ihun kuka Waheeda tasa tana fad'in " Ummah dan Allah kuyi hakuri, ni wallahi Bana sonsa, daku zan zauna, Ummah!, Anty!!"
Ummah ta d'aga murya tace "Nayafe Waheeda, kuje can ku qarata"
Haka suka futo daga falon har zuwa wajan motar sa, yana zuwa yabud'e mata tashiga, sannan yarufe Shima yashiga, fita sukai daga gidan suka d'auki hanyar gidansa, tunda tashiga motar takifa kanta acinyar ta tana gunjin kuka, yanajinta bai hanata ba, sunyi Nisa da tafiya yayi tunanin zatayi shiru Amma yaji shiru yarinya Sai kuka take masa, mamaki ya kamashi, Wai shine yau Waheeda take gudu. π
jikinsa ne yayi Sanyi, ahankali yafaka motar agefen titi yakifa Kansa akan sitiyarin motar, Waheeda tana kuka taji sun tsaya, batareda ta d'ago kanta taga dalilin tsaiwar tasu ba taci gaba da Kuka, Ahankali takejin wata shashshekar kukan tana tashi acikin motar, cikin mamaki ta d'ago kanta tazuba masa jajayen idonta, mamaki yasake kamata ganin Babban Yaya yana kuka da Idonsa, abinda bata ta6a ganiba a tarihin rayuwarta, lokaci d'aya ta nemi Nata kukan tarasa, cikin zuciyarta tace "Kuka?"
πππ
1/28/22, 20:51 - Ummi Tandamaπ: WN
Rikicewa tayi tarasa Yaya zatayi? Babban Yaya da Kuka? Tome aka masa dazai kama yimata kuka? Ita yanzu Yaya yakeso tayi ne? Bata ta6a ganinsa yana kuka ba, Sai hakan yasake d'aga mata hankalin ta tasake fashewa da Kuka,cikin kuka ta kalleshi takasa bashi haquri, cikin taqaici ya d'ago Kansa, Idonsa duk hawaye yace "bazaki min shiru ba saina bige bakinki anan?..."
Itama cikin kuka tace "toba kaine kaqi yin shiru ba..."
Hannunsa duka biyun yasaka yarufe fuskarsa, saida yagama kukansa ma'ishi, sannan yaja motar suka qarasa gidan
Maigadi yazo ya gaishe su cikin ladabi, ganin yanayin uban gidan nasa ba daidai ba yasa yajuya yakoma mazauninsa
Suna shiga falon ya nuna mata d'aki yace "gashinan"
'Dakin tashiga Wanda yaji kayan komai na more rayuwa, fad'awa tayi kan gadon ta Fashe da Kuka, wanne irin aure ne wannan? Babu masu rakiya babu komai ko kayan sakawa Ummah bata bataba, tayaya zata rayu dashi awannan gidan a matsayin ma'aurata? Kuka take sosai saida taji kanta yafara ciwo sannan tayi shiru
Tunda sukazo gidan bai leqo d'akin datake ba, itama bataje inda yake ba, ko kitchen d'inma bata shiga ba bare yasaka ran zata dafa musu wani abun, damuwa tataru tayi masa yawa yarasa ta'ina ma zai fara lallashin ta? Ada yana lallashin tane a matsayin ta na qanwar sa wadda yakeso, yanzu Kuma zai bata kulawa da lallashi ne a matsayin ta na matarsa, to gashi tana cewa bata sonsa, Yaya zaiyi ne?
Da tunani yafara yimasa yawa saiya dauki waya zai kira Ummah ya fad'a mata a aiko musu da abinci, yana kira Ummah ta d'auka tace "Yayansu yagida"
"lafiya Ummah, Am... Ummah idan yaran Nan sungama abinci, sutaho mana dashi"
"to zasu kawo muku, zanzo Nima nasake ja mata kunne nasan Waheeda batajin magana, karka fita ko'ina ka zauna agida ka huta Sai anjima..."
Babban Yaya yariqe wayar yayi shiru, yanaso yace mata Kozai dawo da Waheeda gidane idan tagama hucewa Saisu kawo ta, to Amma yaji kwata kwata Ummah taqi bashi wannan damar ma bare yayi mata doguwar magana, kashe wayar zaiyi, saiyajiyo muryar Anty tana cewa "Amma Yaya da kun Bari yarinyar Nan tad'an sake dashi kafin sutafi, kwata kwata bamu yi mata shirin komai ba, kamar batada gata?"
Ummah tayi tunanin Naufal yakashe waya, shiyasa tana cewa Sai anjima kawai ta ajiye wayar, Babban Yaya kuwa fasa kashe wayar yayi, yayi shiru yana jiran amsar da Ummah zata bayar
Ummah ta kalli Hajiya Anty tace" wanne irin sakewa Kuma Antynsu? Yau tafara zama da Naufal d'in? Tafi kowa sanin halinsa acikinsu, taje tayi ta kukan idan tagaji zata daina, yanzu Hankali na ya kwanta tunda tana d'akin mijinta, kwanaki kamata nayi tana waya da Maya, bansan de kan zancen nasu ba, Amma saina ji ita Waheeda tana hurewa Maya kunne Wai wallahi ta yarda ayi mata auren, inda ace itace yarda zatayi, ai har wanka ma ita zata dinga yiwa mijin, har abar zata kama ta wanke.... "
Babban Yaya yazaro Idonsa π³, dariya ta kamashi cikin sauri yakashe wayar kar Ummah ta d'auka taga waya a kunne
Hajiya Anty tace"mun shiga uku Yaya, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, to ai yanzu saitaje ta wanke ta yayansu" π
Ummah tace "shiyasa na dage akan ayi mata auren, Hankali na zaifi kwanciya"
Babban Yaya yadinga dariya ad'aki shi kad'ai,yana mamaki Waheeda ce tafad'i irin wannan maganar? π€Shiyasa daya tambayeta laifin me tayiwa Ummah tayi shiru taqi fad'a masa?
Ummah bata Bawa yanbiyu abincin sun kawo ba, Sa'eed tabawa yakai musu,Bayan tafiyarsa Babban Yaya yaje yayi nocking d'akin tanajinsa taqi bud'e masa haka ya haqura yajuya
Abu kamar wasa kwata kwata Waheeda taqi bud'e d'akin, inde taji alamun yana gida saita rufe d'akin ta, babu abinda take a gidan, tanajin yafita, saita futo tayi harkokinta Takoma d'aki, abinda tasa aranta shine itade bazata iya wannan rashin kunyar da Babban Yaya ba, domin kuwa rayuwar aure daban, rayuwarsu kafin aure daban, Gara suci gaba da tafiya Ahaka
Babban Yaya tun yanabi takanta harya dawo ya share ta, yau tanajin qaran TV afalo tafuto daga d'akin, lemo ne a gabansa dakuma computer yana typing, d'agowa yayi ya kalleta sau d'aya yamaida Kansa ga rubutun dayake
Zama tayi aqasan kujerar dayake zaune, ta sunkuyar da kanta qasa, batare daya kalleta ba yatashi daga wajan zai wuce d'akinsa, cikin sauri tatashi tabi bayansa, d'akinsa yashiga zai rufe kofar saigata kamar an jefota, d'aure fuska yayi yace "menene Kuma? Inace gudu na kike?"
Wasa tafara da yatsun hannunta, idonta yaciko da qwalla tace "Dan Allah Babban Yaya ka temaka ka sakeni...."
Cikin sauri ya kalleta, Kansa ya Sara kamar an doka masa guduma, cikin sauri yace "meyasa?"
Hawaye ne yazubo mata, tace "haka Nan..."
Yace "hakanan? To kiyi hakuri, bazan iyaba, because.... I luv you, sannan karki kuskura kisake min wannan maganar"
Yafad'i hakan tareda juyawa zai shige d'akinsa, kuka tafashe dashi tace "Dan Allah Babban....." kafin ta qarasa maganar Tata yajuyo yahad'e bakinsu waje d'aya
Lumshe idonta tayi, hawaye masu zafi suka silalo daga idanuwanta, tanajin yanda yake tsotsar lips d'inta kamar yasamu sweet, daga baya yakama harshen ta yana musu wata irin tsotsa kamar ba Babban Yaya ba, bud'e Idonsa yayi yaga yanda take hawaye kamar anbud'e famfo, ahankali yasaka Hannunsa yakama kanta yariqe,ya Lumshe idonsa yacigaba da kissing d'inta, abunda yadad'e yana mafarkin samu Sai gashi yau yayi mata shi, tana cikin hayyacinta Kuma a matsayin matarsa
saida yasha bakinta sosai sannan yasake ta, yana sakinta Tajuya d'akin ta da gudu tana kuka, Shima jingina yayi da jikin kofar d'akin yana sauke numfashi, ga wata irin sha'awa datake taso masa, jiyake kamar yaje wajan Waheeda
Mararsa ce ta murd'a yasaka hannu yadafe, ahankali ya qarasa kan gadon, tareda d'aukan wayarsa, yarasa wazai kira Ummah kokuma Hajiya Anty? Wazai fad'wa matsalar sa? Ummah de da'ita yasaba, yasaba fad'a mata komai, Dan haka yanzun ma ita zai nema, Ahankali yayi Dialing number ta, tana d'auka ya Lumshe Idonsa yace "Ummah, Waheeda taqi hakura har yanzu, Ummah me zanyi mata tasoni?, Ina sonta Ummah, yanzu cemin tayi insaketa fa Ummah... "ya qarasa maganar cikin rawar murya
Ummah tayi murmushi tace "kashirya katafi England, zanyi maganin komai son"
Kai tsaye yace "to Ummah" sannan yakashe wayar
Waheeda ma anata 6angaren cikin kuka takira Hajiya Anty, saboda tasan Kota kira Ummah ba goyon baya zata samu ba π
Anty tace "Daughter lafiya?"
"Anty Allah nagaji...." abinda tace kenan, tafad'i maganar cikin kuka
Anty tace "subhanallah, meyafaru ne? Kimin bayani Waheeda duk Hankali na yatashi"
Hawayen tashare tace "Anty ni bazan iya zama dashi ba, haka kawai saiya dinga min wasu irin abubuwa, aishi Yaya nane, meyasa zaimin haka"
Anty ta dafe kantaπ€¦π»ββοΈtareda murmushi tace "to kiyi hakuri yadena, zanyi masa magana karya sake 6ata miki rai, kinji Daughter"
'Daga kanta tayi kamar ba waya take ba, sannan tace "to" tareda kashe wayar
Kamar yanda Ummah ta bashi shawara rabuwa yayi da Waheeda, washe gari da safe ya shirya zai koma bakin aikinsa
Driver ne yad'aukeshi, Kai tsaye yace "muje gidansu Maya"
Suna zuwa driver yafuto da sari yabud'e masa motar, yaro yatura Akira masa Maya, babu 6ata lokaci kuwa Sai gata tafuto, tana ganinsa ta qarasa wajansa tace "Babban Yaya Ina kwana"
Idanu yazuba mata yace "Lafiya Maya, zuwa nayi inyi miki godia"
Murmushi tayi tace "babu komai wallahi, Allah yabada Zaman lafiya"
Envelope yamiqa mata cikeda kud'i yace "ga wannan ki kaiwa mamanku, sannan ki shirya Bayan qawarki tagama fishi zaku tafi Saudia tare insha Allah"
Cikin murna Maya tace "Babban Yaya mungode, Allah yasaka da alkhairi"
Yace "Amin, idan kinsamu lokaci kije gidan ki lallasheta, kibata shawara" yafad'i hakan yana Sosa girarsa d'aya π
Tace "to insha Allah zanje"
Murmushi yayi yashiga motar, yana fatan ace ta fahimci shawarar dayake nufi abawa Waheeda, fatansa d'aya Allah yasa tabata shawara irin wadda Ummah taji suna fad'a awaya ππππ
Kafin su qarasa Airport yaga text yashigo wayarsa daga Ummi naban haquri, shareta yayi baiyi mata replay ba, ya goge number ta daga wayarsa, ya tabbatar taji labari ne cewa Waheeda lafiyarta kalau, shiyasa takeso ta lalla6o tadawo π
** *** **
Sai wajan azahar Maya takira wayar yanbiyu suka kwatanta mata gidan da Waheeda take, sannan ta shirya tatafi, tana zuwa megadi yatareta yana mata tambayoyi tayi masa bayani sannan Yabarta tashiga
A falon ta dinga doka sallama Waheeda tana kwance ad'aki tana jinta taqi futowa, Maya dataji shiru saita fara bud'e qofofin tana dubawa sannan tayi nasarar bud'e na Waheeda
Mamaki ya kamata ganin Waheeda idonta biyu, qarasawa tayi ta zauna akusa da'ita tace "qawata kiyi haquri, nayi tunanin kin huce shiyasa nazo, ashe har yanzu Ina Nan acikin ranki"
Ba tareda ta kalleta ba tace "aina fad'a miki NI DAKE har abada Maya"
Maya tace "subhanallah, Waheeda me yayi zafi haka?nad'auka namiki gata ne akan aurenki da Babban Yaya, ashe Bahaka bane Wai Waheeda harni kika shaqe duk qawancen mu"
Tashi tayi zaune, cikin masifa tace "eh na shaqe kin, kiyi abinda zakiyi, ai wallahi Maya Kin bani mamaki, banta6a tunanin dake za'a had'a baki a auramin Babban Yaya ba, kin cuceni kuma kin gama Dani"
Cikin sanyin jiki Maya tace "ban cuceki ba Waheeda, temakon d'an'uwanki nayi, Duk Wanda ya zauna daku zaisan cewa Babban Yaya yana sonki, Kuma nasan cewa bazaki ta6a samun masoyi kamar saba, Babban Yaya yana qaunarki Waheeda, Kuma kun dace da juna sosai"
"yanzu ke Maya idan kece akace ki auri yayanki Safwan zakiji dad'i?"
Maya tace "to menene aciki? Abu d'ayane zai dameni yanda zan sake inyi masa abubuwan soyaiya na aure, Kuma Shima lokaci ne ahankali zan saba, kema kuma idan wannan ce damuwar ki toki daina,Babban Yaya zaisa ki manta da cewa shi yayanki ne, sannan karki manta da qaddara, kowa da irin tasa,Kuma munyi alqawari zamu yarda da'ita me kyau ko marar kyau"
Waheeda tana jijjiga qafa cikin damuwa tace "shikkenan ya wuce, Amma karki sake min irin haka, ni banaso, Shima Kuma bazan iya zama dashi ba, saboda tsabar abun kunya rannan har kiss yamin, Ina zan Kai wannan rashin kunyar?"
Maya tasaki dariya tace "yakaiki rashin kunya ne? Keda kowa yasan halinki ne haka bakida kunya? To menene ma danya miki kiss? Haka zakiyi haquri ki yarda, kema kiyi masa, wannan shawarar dakika Bani de akan za'amin aure itace zata dawo kanki, haka Zaki kama abun mijinki ki wanke"
"Dan girman Allah Maya kidena min wannan maganar, kodan kinga na kulaki? Ni banason jin wannan abun kunyar,inrasa wazanyi wa hakan Sai Babban Yaya?"
Maya tace "aikuwa saiki maraba da kishiya"
Cikin rashin damuwa tace "kofa abud'e take, tazo ta zauna ban hanata ba"
Kafin Maya tace wani abu yanbiyu suka shigo d'akin, sunci kwalliya iri d'aya ko ganesu bakayi, abinci suka ajiye mata Ihsan tace "ke ga abincin ki Nan inji Ummah"
Kallan abincin tayi tace "wannan ai yayi mana kad'an, ko Babban Yaya zai iya cinyewa, yanda yake cin abinci idan yasamu waje to wallahi shi kad'ai ma zai cinye wannan"
Intisar tace "wanne Babban Yaya Kuma shida yatafi England? Ni jinake ma dake zai tafi, ashe shi kad'ai yatafi, ke yanzu Waheeda ba abun kunya bane wannan? Sabon aure Amma kibar ango yatafi shi kad'ai? Kyaje yakula wasu matan acan wallahi, tunda yanzu ya d'and'ana yaji dad'in mace "ππ
Cikin 6acin rai Waheeda tace" uwar me ya d'and'ana? Inti banason rashin mutunci wallahi, ba England ba, yatafi kafi England ma,dayau yafara huld'a da mata? Da idona na ganshi mata suna yanyameshi Sai yage musu baki yake, da idona nagani "
Ihsan tace" to babu so menene Kuma yakawo kishi? Keda kike cewa bakya sonsa miye dankinga mata suna yanyameshi? d'an ball nefa, ba mata ba mazama yanyameshi zasuyi, malama kinaso kina yiwa mutane ihu ke bakya so "
Tace" eh banaso, ba Kuma zan so ba, da yau yafara kula matan dazaku zo Kuna cewa nabarshi yatafi, inda ace nasan baya gidan ma da tuni Nima na kama gabana, Zaman me zanyi yanzun Ina masa gadin gida? Saikace wacce batada galihu, Nina tafi gida idan kun gama kwa taho "tafadi haka tana Jan hijabin ta tafice daga d'akin ππ
Babu yanda suka iya haka suka futo suka biyo bayanta, saida sukazo gida sannan Maya tamusu sallama tatafi gida, sukuma suka shige cikin gida, megadi Sai tsokanar Waheeda yake yana fad'in"Amarya kinsha qamshi"
Yau kwananta hud'u agida, Amma kamar bata gidan, Dafarko tayi tunanin zasu kulata, shiyasa take wuni ad'aki, dataga babu Wanda yake shiga harkar ta, saita fara futowa tana abin gabanta, daga Ummah har Daddy idan ta gaishe su daga sun amsa basa qara cemata komai, haka yanbiyu ma tun lokacin dasuka mata fad'a tamusu rashin kunya suka tattara ta suka watsar, Hajiya Anty tahad'o mata magungunan mata masu kyau, ta zaunar da'ita ta mata bayanin yanda zata dinga amfani dasu, sannan tabata haquri akan Takoma gidan mijinta, Amma Waheeda tayi mursisi taqi komawa, magungunan ma ta ajiye su taqi shan kod'aya aciki.
Yau satinta uku agida, Kuma har zuwa wannan lokacin bata kira Babban Yaya ba, Shima bai kirata ba, Kuma babu Wanda yace tattara kayan ki kikoma, kowa yazuba mata ido kawai.
Yau suna break fast afalo gaba d'ayansu, banda Daddy, Sa'eed ya kalli Waheeda sannan ya kalli Ummah yace "Wai wannan yarinyar Zaman me take a gidannan Ummah?"
Ummah ta Kalle shi tace "gatanan ka tambayeta"
Kallan Waheeda yayi yace "keme kikeyi har yanzu baki koma ba?"
Idonta ne yayi qwalqwal yakawo ruwa, tana juya spoon acikin cup d'in tea d'in dake gabanta tace "ni Bana sonshi...."
Sa'ad yayi sauri yace "to cemiki akai shid'in sonki yake? Banda qaddara ma me Babban Yaya zaiyi dake? Ga yanmata Nan had'ad'd'u suna bibiyarsa zai tsaya anan Ana Rena masa Hankali"
Sa'eed ma yace "okay bakya sonsa ko? To Alhamdulillah, Ummah kawai idan yazo kibashi shawara yasake ta kawai"
Ummah ta ajiye bread d'in hannunta tace "na fad'a masa tun shekaran jiya da mukai waya, idan yasamu lokaci Yazo ya rubuta mata takardar, saisu koma makaranta itadasu Ihsan"
Sa'eed yace "Hakan ma yafi, Dan wannan yarinyar Dama ba ajin auren sa bace, kawai de Dan Allah ya rubuta Sai anyi ne, ni Gara ma dayake shirya abinda yafi masa, abinda Yayanke d'in yayi daidai, yanzu ne yasan zaiyi aure"
Gaban Waheeda yayanke yafad'i, ahankali ta zaro idonta π³batare datace komai ba
Shima Sa'ad yace "eh gaskiya Kam ya kyauta"
Hajiya Anty ce tashigo falon zata yiwa Ummah sallama