Showing 1 words to 3000 words out of 50173 words

Chapter 1 - Bani Nayi Kaina Ba Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

335


Compiled by Umar Dalha.


Copied by Hafsat Abbas Sawwama.




💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.



Page 1.

Bismillahi rahmanir rahim.

****** ******* *******

Kwance take kan makeken royal bed dinta tana juyi. Ya illahi wannan wani irin rayuwa ce ashe wai mutum har ya kai ya isa ya kushe halittar Allah wannan zamani ya kai har mutum zai kalli dan uwanshi mutum yace kai wannan akwai muni subhanallah ko kaji ance kai wance ko wane kyanshi yayi yawa har baya burgeni innalillah dama ai rabbi baiyi hallici wani abu dan ya burge wata ko wani ba.

In kaga abinda bai maka ba barshi a zuciyanka tunda ba kai kayi ba wanda yayi kuma baiyi dan ya burgeka ba .

Sake wani juyin tayi cike da gundira tana tunanin yanda itama mijinta ya tsani halittanta.

Runtse idonta tayi a lokacin da take jin muryanshi na mata kuwwa a kunnenta shgiya mai kama da aljanu ni tsinanniyar yarinyan nan tsoro take ba duk ta bi ta lashe kurwan yan gidan nan toh wallahi ni dai in gaya miki kurwata kur dacine QAWWAMA😘ryarki ki lasheni bar kallo da mayun idonkin nan ko wallahi in tsokalesu sai sun zube.

Sake tuno ranan da wani abokinshi ya tambayeshi ko ita kanwarshi ce sai cewa yayi kaga idanun gidanmu na kama da na mayu ne wannan mayya ce kana ganinta baka ganinta da suffan aljanu?

Tsam ta mike ta nufi dogon miro tana karewa hallitanta kallo menene laifin halitanta? Hawayene suka zubo mata a lokacin da ta tuna this same halitta shi ya janyo mata tsana a wurin mijinta yaya BANI NAYI KAINA BA ta furta a hankali.

Murmushi ne ya subuce mata da ta tuno yayan da take magana akai tuni yayi mata nisa tun bayan kwana bakwai da auren su ya tsallake ya bar mata kasan gaba daya.

Abin haushin ma wai tafiya yayi yaje ya lallashi budurwarsa da take karatu a can Europe akan auren da akayi mishi a gida ba tare da yana so ba.

Surprise visit wai zai kai mata kaman yanda taji yana fadawa amininshi ana gobe zai tafi.

A hankali ta koma ta kwanta a bakin gadon ikon Allah kenan kab family din mijinta bata da wanda yake kinta sai shi mijin kwacankwam baya kaunan ya budi ido ya ganta babu halittan da ya tsana irin nata.

To wai meye laifin halittan nata ai yaci ya rungumi zabin iyayenshi ko da baya so.

Wani sashi na zuciyanta ne yace zaki ce haka mana tunda ke duk wannan tsana da tsangwama da yake nuna miki shine namiji kwaya daya jal da yake burgeki kika dau soyayyar duniyan nan kika daura mishi.

Yamutsa fuska tayi tare da fadin that is the annoying part son ma so wani not only that wanda ya tsaneka ya tsani ganinka saboda halittanka anya ya cancanci soyayyarka.

Gyara kwanciyarta tayi ta daga ido tana kallon saman dakin tana so ta tunato rayuwarta ta baya.....................................

****** ******* *******


Hwol buji wani ruga ne ko ince kauye da yake karkshin garin mista Ali na cikin garin Jos a jihar plateau.

Garine da ya kunshi fulanin Bauchi da Jos sannan akwai sauran yarurrukan plateau a garin kaman su jarawa angas birom da sauransu

Garine da ake a cakude wato da masu sallah da marasa sallah, kowa ya san garin Jos ya san akwai su (marasa sallah).

Kaman yanda nace akwai fulanin Bauchi a garin to haka ya kasance iyayena fulanin Bauchine kuma suna nan a wannan gari.

Ba kaman yayah (mahaifinmu) dan shi anan aka haifeshi nan ya girma dadarmu(mahaifiyarmu) yar asalin Tilden fulani ce na karamar hukumar toro a jihar Bauchi daga nan yayah ya aurota.

Sana'ar mutane hwol ba wata sana'a bace da ta wuce noman kayan gwari da kiwo, in nace noman kayan gwari ina nufin noma abinda ya shafi timatir albasa tarugu,tattasai ja da kore, sai su karas kabeji,koren wake,latas,yalo da dai sauran duk wani abu da ya shafi vegetables.

Malam yusuf shine sunan mahaifina sana'arsa kuma itace koyar da magidanta fannin addini sannan yana sana'ar noma da kiwo kaman dukka sauran yan garin.

Dada zakee kaman yanda ake kiran mamanmu a garin asalin sunanta Ruqayya itama tana koyar da yara da matan aure fannin addini hakan ya sa muka taso da karatun addini sosai.

Mu uku ne jal a wajen iyayanmu yah auwal ni ZAKKIYAH sai autarmu salma wanda taci sunan kakarmu da take zaune damu a gidanmu.

Duk da kasancewar garin hwol cike yake da fulani amma mu kyan yan gidanmu ya fita dabban dukkanmu har yah auwal da dada muke kama, kusan duk na fisu kama da dada dan ni hatta tafiyarmu iri daya haka maganarmu hatta halin dada ba abin da na bari na wajen haquri da rashin son magana.

Hwol buji kam kauyene sosai dan babu makarantar boko a garin har sai mun dangana da mista ali kullum muna hanya haka in an tashi zamu debo rana mu dawo a gajiye likis gashi a kafa muke tafiya har gara wasu lokutan ma yayah yana kaimu a mashin dinshi ko ya biya makocinmi ilah ya kaimu amma fah in an tashi a kafa zamu dabo.


Yah auwal na shekararshi ta farko a university if Jos inda a can yake karantar Agriculture yayin da ni kuma na kammala primaryna ina jiran sakamakon jarabawar da muka rubuta ta scholarship.

Kwata kwata ni na kasance mutum ce mara hayaniya ko a kauyenmu ban da kawa bana fita ko ina dan duk inda na fita sai an ta yabon kyauna hakan yasa bana fita ko ina kullum ina like da dadana dadan ma tafi son haka dan gudun bakin mutane.

Kakarmu inna ma sai dai tayi ta fada tana fadin kullum ni dai baki a rufe kaman mai ciwon baki ko dan hira bana zuwa mata,toh mai zai kai ni ta cika ni da surutu.


Kaman kullum da safe bayan yayah ya ciri amfanin gonanshi babban buhu guda zai kaima abokin harkarshi ziyara a nan cikin garin jos ya mana sallama ya tafi salma kam ta tsufa a school dama yah auwal zaman hostel yake yi duk da a dakin abokinshi yah sadeeq yake.

Mu uku ne a gida dani da inna da dada. Inna na cikin dakinta tana gyangyadawa yayinda inna ke ta zirga zirganta ni kuma ina zaune ina sanye lalle a yatsuna sai ga yayah yayi sallama har ya dawo.

Da mamaki muka kalleshi ni da dada sanin da muka yi in yaje wajen abokinshi sai yamma lis yake dawowa.

Zama yayi a kusa dani dada ta kawo mishi ruwa bayan ya sha sai ya kalli dada yace rakiya kin ganni na dawo ko?

Ta dan gyada kai yace wallahi bayan illah ya fita dani titin farin lamba ya dawo ina nan tsaye ina jiran motan jos.

Sai ga wani alh nan ya parka a can daya barin ya tsallako muka gaisa yake tambayata menene a cikin buhun dan shi a tunaninshi kasuwar farin gada zani.

Nace mishi alhaji bana sayarwa bane har ya juya zai tafi yana ta waigena sai ya dan dawo yace na ga kamansu karas da kabeji ne dan Allah in bazaka damu ba ka taimakeni ka sayar min wallahi gida kano na nufa da safen nan na zo na duba yarona ne amakaranta toh da da safen nan nake so mu je can gidan su abokinshi in sayawa mutanen gida dan sallahun da suka ban kenan sai aka min waya muna da meeting a can inda nake aiki ka taimaka ka sayar min ko nawa ne.

Sauke ajiyan zuciya nayi nace mishi gaskiya ni ban ciro kayan nan dan in siyar ba alheri na so yi da shi amma tun da abin haka ne ka dauke ai ba a zaban wanda za ayiwa alheri.

Yayi ta min godiya na taimaka mishi muka sa a mota yana kokarin sa hannu a aljuhu nace mishi ah ah alheri nayi niyya na juya na.dawo abuna.

Allah sarki shine abinda muka ce dan shi yayah haka halinshi yake.


MAFARIN ABIN.
💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.
Page 2.

Scholarship result dinmu ya fito inda na sami Attaquwa International school dake jihar kano abin haushin kuma ba boarding bace day ne.

Yaya yace ba inda zani in shiga makarantan gwamnati na mista ali tunda mu ba yan uwa bane da mu a kano.

Ina zaune a tsakar gida nayi jugum idanuna sunyi jazir tsabagen kukan da na sha gidan yayi tsit kaman ba mutane kowa na tayani jimami.

Yah auwal da yah sadeeq ne suka yi sallama suka shigo kwata kwata banji karar motar yah sadeeq din ba sai da suka zo kaina.

Harara yah auwal ya balla min yana fadin baki jin.sallama ne baza ki ansa ba ina sauran mutanen gidn.... Maganan shi ce ta katse sa'ilin da muka yi ido hudu yaga yanda idona ya rine.

Tsugunawa suka yi a gabana shi da yah sadeeq meke faruwa ke da waye kike kuka? Wasu hawayen ne suka zubo min na sa bayan hannuna na goge.

Kafin inyi magana inna da ta fito bakin kofanta tace maigidana ba dole tayi kuka ba makarantan nan da take ta jira ta samu sakamakon ya fito amma babanku ya hana.

Yace toh Allah ya kyauta jeki ki dauko min scholarship din in gani ya fadi hakan yana karasawa dakin dada gaisheta suka yi suka wuce can dakinshi da yake zaure.

Abinci dada ta zuba min na kai musu tare da ruwa,sannan ta koma dakinsu ta daga katifarsu ta dauko file din ta rungume tana jira su gama cin abincin.

Kwala mats kira yayi da sauri ta tashi taje ta kai mishi ya karba yana cewa toh wai me yasa yayah ya hanki ne?

Dan zaro ido waje yayi ya dan yi baya tare da cewa ahhhh dole yayah ya hana har garin kano ba kuma boarding ba.

Sadeeq ne ya taso daga kwancen da yake yace kano? In gani ya mika hannu ya karba.


Yace lahhhhh wallahi auwal makarantar da muke yi kenan a gidanmu tun daga nursery har mu gama yanxu haka kannena a nan suke.

Makaranta na da tsada sosai amma duk bayan shekara biyar suna bawa 36 state na Nigeria scholarship dai dai this time Zakiyya is the luckiest a plateau state.

Hawaye ne ya kara zubo min yanzu shikenan na rasa wannan daman sadeeq ne yace no no daina kuka zamu samu yayah sai kije ki zauna a gidanmu ki dinga zuwa tare da kannena.

Wani sanyi ne ya ratsani duk da bani da tabbacin yayah zai bari, illai kuwa yaya yace sam bai san wannan zancen ba yace taje ta shiga makaranta irin nasu na ya'yan talakawa.

Ba yanda basu yi da yayah ba amma sam yaki sadeeq baiwa kowa sallama ba ya dau mota sai kano.

Bai isa kano ba sai da akayi isha kasancewan bai taso da wuri wajen abban shi ya fara shiga aiko yayi sa'a yana tare da daddy kaninshi.

Bayan sun gaisa daddy ya kalleshi cike da mamaki yace babana me ya kawoka gida a wannan lokacin?

Ya sunkuyar da kai tare da sosa keya da mukullin.motan shi yace wallahi daddy wata yar matsala ce ta taso.

Abba yace tohhhh matsala dai bata wuce ta kudi me yasa baka yi waya an turo maka ba

Kara sunkuyar da kai yayi yace abba ba matsalan kudi bane ina wannan abokin nawa da nace muku yana taimaka min sosai daddy ai kai ka ganshi.

Dadyn ya gyada kai yace eh haka ne wani abu ne ya sameshi

Yace ah ah dama......... Ya kwashe komi ya gaya musu.

Abba yace toh yanzu kai me kake nufi so kake mu daukota mu kawota gidan mu kai ka tabbatar da halinsu ne.

Daddyn ne yace Alh tabbas naga yaron kuma na yaba da halinshi duk da ba a shaidan dan mutum amma the boy look innocent.

Abba yace toh shikenan tunda kace haka gobe tunda Saturday sai ka bishi ka lallabi mahaifinsu.

Yace toh shikenan Allah ya kaimu,suka amsa amin sadeeq ya runsuna yayi godiya kafin ya shiga cikin gida kowa sai murnan ganinshi yake ba kaman BB(big bro) dinshi da shima ya dawo weekend sai fadi yake lil bro naji dadin ganinka it has being quite long da na ganka hope kana karatu.

Shagwabe fuska yayi tare da rungume dan uwanshi yace i miss u too BB.

Dan patting dinshi yayi yace kar ka damu zan nemi transfer zuwa rukuba barrack na jos sai ka dawo wajena kawai da zama ya fadi haka yana jan hannunshi zuwa side din su.

Dariya sadeeq yayi yace ahhhhhh yayah sai dai ka dinga zuwa kana duba ni dan tsakanin rukuba barrak da main camp akwai shegen nisa.

Yace ok we will see about that muje mu samu mu huta nima dazun nan na iso.

******* ******* ********

Washegari ko daddy da sadeeq suka dau hanyan jos sammako suka yi saboda haka kafin azahar sun isa hwol.

Sun ko yi sa'an samun yayah a gida abin mamaki kuma ashe daddy shine mutumin da yayah ya taimaka ya bawa kyautan kayan lambu.

Gaisuwa suka yi sosai na mutunci kafin daddy ya fada mishi abin da ya kawoshi

Murmushi yayah yace alh banki ta naka ba amma ita zakiyyan wata irin yarinya ce me kawa zucin gida ba lallai ta yarda da zaman can ba.


Daddy yace ai malam annabi yace a nemi ilimi ko da a birnin sin ne kuma can kanon akwai yarana da yaran dan uwana sa'o'inta kuma suma duk Jss one zasu shiga....... Da kyar da sidin goshi suka shawo kan yayah ya yarda amma sai ana sauran sati a koma makarantan yayah da sadeeq zasu kawota.

Daddy sai godiya yake yi kaman shi aka yiwa abu, har abin ya bawa yayah mamaki har ya dinga jinjina irin karamcin bayin Allahn nan.

Kayan lambu ya shiga gona ya hadowa daddy sosai har da su timatir daddy yayi ta godiya har ya tafi akan sai sun kawo zakiyyan.




TAFIYAN DA YA ZAME MIN MAFARIN MATSALOLINA.

💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.


Page 3.

Yau ce ranan tafiyarmu duk murnan da nake yi da dokin zanje makarantar da nake so,sai na tsinci kaina da rashin son barin mahaifata.

Kuka nake yi sosai haka inna da salma kaman wacce aka ce bazan dawo ba in na tafi.

Dada dai kam baza ka iya gane yanayin da take ciki ba haka na barosu.

Ni,yayah da yah sadeeq da ya auwal ne muka yi tafiyan.

Tunda uwata ta haifeni ban taba zuwa wani gari ba banda cikin jos sai ko bauchi wajen babban yayarsu dada hajja da take aure a can.

Tafiyar tayi min nisa da rashin dadi saboda rashin kyan hanyan saminakan nan.

A galabaice nake lokacin da muka isa garin kano,sosai garin ya min kyau ya kayartar dani.

Manyan idanuwana na fito dasu sosai ina ta kalle kallena zuciyata sai tsinkewa take yanzu a wannan garin zan yi rayuwa?

Ban kuma tsinkewa da al amarin ba sai da muka zo wani tabkeken gida bani kadai ba hatta yayah da yah auwal sun kadu da ganin girman gidan da haduwarsa.

Tuni yayah ya fara dana sanin amincewa da zuwan wannan gidan gashi shi yanzu ba zai iya janyewa ba coz he is man of his word.

Yah auwal ma cike yake da mamaki duk da ya san su ya sadeeq masu kudi kama da yanda shi kwata kwata bashi da matsala irin ta dalibai tunda shi har motan hawa yake da ita kirar civic 2 door amma bai taba tunanin suna da kudi haka ba.

Sauka sosai aka musu a gidan guest room aka kaisu,suka cika cikinsu da abinci kala kala da aka tanadar musu.

Bayan sun kammala sunyi sallah daddy da abba suka shigo aka sake sabon gaisuwa kafin yayah ya damka musu amanata suma suka karba.

Yaya cewa yayi baza su kwana ba a yau zasu tafi ba yanda abba bai yi da shi ba cike da ladabi (kasancewar duk zasu girmeshi) yayi musu bayanin yana da harkokin da zai je ya duba ga dalibanshi bai ce musu zai kwana ba.

Haka suka fito musu da tsarabar da muka kawo musu na kayan gona da su daddawa kuka kubewa da sauransu.

Su yah sadeeq ma sunce ba zasu kwana ba dan suna da test ranan monday gwara suje suyi karatu.

Haka suka tafi suka barni ina sharan hawaye shiga dani cikin gidan suka yi tare da kirawo matan gidan.

Alh abdullahi shine asalin sunan abba yana da matan aure 2 haj Hauwa itace matarsa ta farko tayi haihuwa 3 basa dadewa suke rasuwa a na hudun ne Allah ya tsayar mata inda ta haifi danta namiji RIDWAN a lokacin safwan(daddy) shima yayi aure inda ya auri sadiqa ta haifa mishi Ibrahim tsakanin Ridwan da Ibrahim wata bakwai ne Ridwan ya girmi ibrahim.

Bayan Ridwan haj hawwa sai ta kuma haifan rabi bata dade da haihuwan rabi ba alh abdullahi ya dada aura ya auri haj maimuna shekarn rabi biyu haj maimuna ta haifi sadeeq sai mustapha sannan sannan ta haifi shafa shekarun shafa uku ta rasu.

Ita kuma haj hauwa tun bayan haihuwan rabi bata kuma haihuwa ba sai suka zo suka samu ciki a lokaci daya da ita da haj maimuna da haj sadiqa matan daddy itama lokacin ta haifi yara biyu bayan ibrahim Aisha da kasim.

Haj sadiqa ce ta fara haihuwa inda ta haifi yan biyu fareeda da fadila, satinsu biyu haj hauwa ta haifi yusra kwanan yusra talatin da hudu haj maimuna ta haifi halima wanda sune sa'o'ina.

Dakinsu yusra aka saukeni kowa sai yabon irin kyau na yake yi kowacce tana so in kwana a gadonta.

Mama ma(haj hauwa) sai nan nan take dani haka momy kowa burinshi ya faranta min dan in sake a gidan.

Washegari mama tasa muka shirya muka je gidan haj mahaifiyarsu abba ta ganni daga nan muka wuce gidan daddy

Su fareeda sai murna suke da zuwan mu da zamu tafi ma dagewa suka yi sai da suka biyomu.

Sosai na sake da yan gidan bani da matsalan komi har abba yasa yah mustapha ya cike min form din islamiya.

Ba aji daya aka sani da su yusra ba kasancewar na musu nisa su suna aji daya ni biyu.

An koma school daddy yaje ya daidaita min komi muka fara zuwa dukkanmu har su yah mustapha driver ke kaimu.


Haka rayuwa taci gaba da garawa bana zuwa gida hutu sai in anyi hutun 3rd term saboda islamiya yah sadeeq da yah auwal su kan zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login