Showing 45001 words to 48000 words out of 50173 words

Chapter 16 - Bani Nayi Kaina Ba Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

347

nishad'antar kasancewan duk wanda ya santa macece mai barkwanci.

Sosai malama zuwaira tayi magana akan hakokin aure da irin fushin ubangiji kan mace mai k'auracewa mijinta.

Tayi magana kan ha'inci, da yanda hassada ke cinye kyawawan aiki, tayi magana ta fadakar sosai wanda sai da jikin kowa yayi sanyi.

Duk da yanda malama zuwairan tayi k'ok'arin sako barkwanci hakan bai hana zuciyoyin mutane cika da tsoro ba.


Ba kaman zakiyya da take cikin zarin da na sani na hana mijinta hakkinsa kuka take tuk'kuru gudun kar ta janyo hankalin mutane kanta yasa ta mikewa ta shiga part din yah rid tana rusan kukan nadama.

A dai dai wannan lokacin yah rid din ya shigo bangare dan yana da tabbacin 'yammatan na wajen walima kuma akwai abinda zai d'auka a bangaren.


Sai dai me? Precious dinshi ke rizgan kuka ita k'adai tsayawa yayi yana kallonta dan bata san ya shigo ba ya san ba komi ke damunta ba illa kishi da yana da yanda zaiyi ya k'auracewa auran nan da yayi amma ina bakin alkalami ya bushe fadeela ta yi nasaran wargaza mishi farin cikin sa.

A hankali ya k'arasa shiga dakin ya rungumota ta baya yana fad'in "precious ki yafe min bani da wani wayo ko dabaran k'auracewa auran nan fadeela tayi nasara akaina."


Da sauri na juyo na rufe bakinshi da tafin hannuna nace "haba mijina ya kake irin maganan nan bazan tab'a goya maka baya kak'i bin maganan abba in nayi haka na zama butulu tunda nima haka aka had'a ni da kai ba tare da kana so ba kuma ka aure saboda biyayyarka a garesu dan me kuma yanzu dan abin ya zagayo kan fadeela in mata bak'in ciki alhalin annabi yace" _imanin d'ayanku baya cika face ya soma d'an uwanshi abinda ya sowa kanshi__eh na san da zafi akwai kishi but i have to fight dan in samu in k'arfafa maka guiwa kayiwa abba biyayya, amma sai me sai na kasance na k'aurace maka ina horar da kai da abinda baka da laifi ko d'aya akai. Mijina ka yafe min na maka alqawarin zan so fadeela in k'aunaceta zan gujewa duk wata fitina da zai wanzu a tsakaninmi kaima ka min alqawarin riketa a matsayin mata kar ka bari shed'an la'annane yayi nasara akanka wannan karon kar ka bari kuyi irin zaman da muka yi daga farkon auranmu"kuka ne yaci karfina na fad'a jikinshi ina wani irin kuka mai cin rai.

Tsam ya rungumeta ya kasa magana sai ja da idonshi yayi kaman wanda aka yiwa turare barkono ina ma zai samu ya zubar da hawayen nan shima da yaji dad'i ya jawa fadeela Allaj ya isa yafi shurin masaki.


Fadeela ce ta juya a guje tana wani irin kuka dan tun da zakiyya ta fara magana tana tsaye tana jinsu saboda itama gudowa tayi daga wajen waliman saboda tsoro da fargaba da ya cikata.

Sai kuma tazo ta tarar da su a haka wani irin nadama ne ya shigeta mai ta aikata haka? Saboda zunzurutun _hassada_ya Allah kasa mufi karfin zuqatan mu.

Da yah sadiq suka ci karo rik'ota yayi yana tambayanta lafiya?

Fadawa tayi jikinshi tana kuka wanda saida tsigar jikinshi ya tashi jin lallausan nonuwanta da suka mannu da kirjinshi.


Cikin kuka take furta" kaicona yah sadiq kaico da irin halina na son zuciya na biye zuciyata na cutar da baiwar Allahn da bata tab'a nufina da wani mugun abu ba, bata tab'a min ko da kallon banza bane."

"Tir da rayuwata yah sadiq tunda har zanyi k'ok'arin shiga tsakanin farin cikin masoya biyu yah sadiq ka taimakeni ka samowa rayuwata mafita ina tunanin nayi nadama a k'uraren lokaci ban isa in tunkari su abba da batun fasa auran yah rid ba dan ko kad'an yah sadiq bana sha'awar auran yah rid bana sha'awar shiga tsakanin zakiyya da farin cikinta yah sadiq ina so in samarwa zakiyya farin ciki kaman yanda take kokarin samar mi yah sadiq ya zanyi?"

Rabata yayi da jikinshi yana tunanin ya taimaka mata ya taimaki zakiyya da BB d'inshi ne ko ya? Toh shi kuma nashi burin ya kai ina kuma? Rintse ido yayi yana tunanjn mafita.(masu karatu ku bawa sadiq mafita)
















SAWWAMA QAWWAMA😘
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: 💖BANI NAYI KAINA BA💖






By Sawwama A.







Page 46.






D'an m'ikewa nayi daga jikinshi ya kuma kamoni yana tura fuskanshi cikin kirjina.

Tun jiya da muka dawo daga gidan abba ya bi ya kanainayeni duk wani bashi da yake bina sai da ya fansheshi tsakanin jiya zuwa yau.

Wayarsa na janyo dan duba lokaci sha biyu har ta gota na tabbata amaren na can suna nemana wayata kuma na palo sauk'inta daya mun baro salma a can.


D'ago kanshi nayi na sakar mishi murmushi tare da fad'in " haayatee lokaci ya tafi fa ka tashi mu samu mu shirya kafin lokacin d'aurin auran"

Had'e rai yayi yace" ai ko ba na nan zasu iya d'aurawa ba lallai sai na halarta ba."

Girgiza kai na ja dogon hancin shi nace" ko kana nan ko ba ka nan za a d'aura so is better kaje d'in su abba su k'ara tabbatar da kayi na'am da auran rashin zuwan zai sa su acikin fargaban zaka rik'e amanar da aka baka ko kuwa"

Shiru yayi idon shi a rufe ni kuma na k'ura kyakyawar fuskarsa ido.


Mirgino ni yayi tare da cafkar bakina da wani urgency da kyar ya zare bakinshi sannan yace "i guess i will have to have my way first"

Sannan ya cigaba da abinda yake yi wajen biyawa kanshi buqata so ba adadi.


Sai da aka kira azahar ya kyaleni wanka muka yi a gurguje na shirya shi cikin farar shadda like any other ango har da malin malin.


Kallona yake da mamaki dan shi bai ma tanadi kayan da zai sa ba wannan din ni na siya mishi.


Kau da kaina nayi dan bana son wani dogon magana nima shiryawa nayi cikin wani swiss less dak green mai adon orange colour flower nayi das dani.


Indian gold na saka sannan na sa orange takalmi na dauko gyale orange zan yafa.

Rik'e hannuna yayi na d'ago ina kallonsh ya wani sha kunu nima sai na aro nawa na had'e rai.

D'an sassauta fuskanshi yayi ya marairaice yace " kin dai son ban son kina fita da gyale ana kalle min ke"

Dan turo baki nayi nace " naga dai tare zamu fita kuma ni da zan shiga cikin gida me zai fito dani in ba tafiya ba"

Gyad'a kai yayi ya riko hannuna muka fita yaje ya ajiye ni gidan abba.

Nan ma sai da ya javwagwala ni wai yana sallama da babyn shi sannan ya kyaleni.


Ina shiga gidan aka min caaaa akai wai ban zo da wuri ba sai yanzu ni dai bani da bakin magana.

Wajen amaren na wuce duk ba wanda ya kulani wai suna fushi dani abin mamaki sai fadeela ce take kareni wajensu kowa a wajen yayi mamaki kuma yaji dad'i ko ba komai zamu yi zaman lafiya.

Wayata na sa a charge dan ta mutu toh tun jiya ban bi ta kanta ba tambayan inda salma tayi nayi.

Fareeda tace " tana can wajen y'an uwanku da suka zo d'aukan amarya tun goma suka iso an nemiki a waya an rasa."


Da hanzari na mik'e ina fadin" hande mi bone a ina aka saukesu?"

Dariya duk suka yi ganin yanda duk na tsure fadeela tace " rabu dasu sis suna b'angaren momy"

Wajensu na euce da saurina ina murna da fargaban yanda na manta zasu zo ina can ina soyewa.

Sunyi murnan ganina sosai Allah ya soni salma ta wankeni tace naje mu duba gidan sauran amaren.


Hira muka yi sosai muna nan zaune har akayi d'aurin aure.


Fareeda ce ta shigo da gudu ta rik'o hannuna tana jana ta manta shap wai surukanta nake tare dasu.


Hankalina a tashe nake binta sai da ta sada ni da yah rid dake tsaye cikin 'yammatan amare da amaren kansu yana jiran isowarmu.

Ya cire babbar rigar da na sa mishi muna isowa bai yi wata wata ba ya raba ni da kasa yana juyi dani.

Mamaki ne ya kara kamani menene hakan tsananin farin cikin an mallaka mishi fadeela ne ko ne? namiji munafiki ne.


Sai da ya direni ya rike fuskata yana kallom cikin idona murmushi kwance a fuskanshi wanda yake nuna tsananin farin cikin da yake ciki.

A hankali ya furta " precious i am yours alone."

Wani haushine ya taso min ganin yana son raina min hankali ya gama murnan d'aurin auranshi yazo yana wanj ce min shi nawa ne ni kadai.

K'ok'arin zame hannunshi nayi yayi saurin hade goshinmu tare da k'ok'arin kai bakinshi nawa.

Kau da kai nayi a hankali nace "haayatee look around you bamu kad'ai bane.

Sai a lokacin ya tuno inda suke juyawa yayi yaga yanda k'annen nashi suka zubo mana ido cike da mamaki banda fadeela da ta san murnan meye kunya ce ta kama shi amma sai ya maze ya fara harare harare ya ja hannuna muka fita.

Sai lokacin magana ya fara tashi a d'akin me je faruwa haka? Wannan wani irin so yakewa matarshi ? Ba shine wanda ya auri fadeela ba amma ko ta kan amarya bai bi ba yana ta uwar gida.


Fadeela ce ta lumshe ido tana tunanin lallai da ta tafka babban kuskurw shiga gidan irin masoyan nan ko ana sonka sai ka kai zuciyarka nesa balle ba a sonka.

Tuno yanda suka yi da yah sadeeq tayi.


"Zaki aureni?" Shine kalaman da suka fito daga bakinshi lokacin da take fad'a mishi damuwarta.

A lokacin kukanta tsayawa yayi cak da jin abinda ya fito daga bakinshi.

K'ara maimaita kalman yayi "zaki aureni? Domin mu hana faruwar aurenki da yah rid?"

Hannuwansa biyu yasa ya shafi fuskarsa yace " kina da kyau da halin da mutum zai so kasancewa dake kafin kika zo kika sauya naji dad'i da kika dawo da halinki na da hakan ya kwad'aita min auranki"


Murmushi tayi tana kare mishi kallo yah sadiq namiji ne ta ko'ina yana da halin nagarta ga tausayi da son samawa mutum farin ciki mutuk'ar zai iya wajen kyau ma ba a magana dam kusan duk familyn su shine fari amma duk su bak'ak'e ne shi kadai ya d'auko hasken kakansu duk da shima d'in ba wai fari bane sol.

A hankali ta gyad'a kai tana murmushi lokaci daya hawaye na zubo mata.

Shima gyad'a kan yayi yana murmushi yace" amma da sharad'i" kallonshi tayi gabanta na fad'uwa sharad'in me kuma.

Murmushi tayi da jin sharad'in ba komi ta yarda.

Yace" toh muje mu gayawa iyayenmu dan na san sun dawo daga sallar magrib gashi ni kin hananj samun jam'i."

Daddy na ganinta ya had'e rai amma jin me ke tafe dasu ya sashi farin ciki sosai take suka tsai da magana kan washegari da sadeeq za a d'aura aure.


Ina gama jin wannan batun na rungumr mijina ina mai tsananin farin ciki yah sadeeq yah sadeeq nawa bawan Allahn nan ba abinda bai min ba a rayuwa ya ceci rayuwata a karo na biyu.











SAWWAMA QAWWAMA😘
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: 💖BANI NAYI KAINA BA💖






By Sawwama A.






Page 47.

_
_Queen Ayush, __ our lil princess,_ billyn Abdul and every member of baiwa writers this page is for you. _You guys _a genius___ 😊





Cigaba akayi da shagalin biki k'ara sakin jiki nayi aka cigaba da harkoki da ni daman haka Allah ke abin shi da yanzu na d'aga hankalina nayiwa mijina tijara ko danginshi da yanzu na ji kunya.


Anzo tafiya da fareeda nace zan bi sam yah rid ya hana nayi ta kuka amma sai ya fita ma ya barni gaba d'aya ma.


Nima ko na tubure salma ba zata bisu ba dan naga take takenta in ta samu ta tafi ba dawo zata yi ba.

Haka aka gama biki aka kai ko wace amarya gidanta fareeda k'auyan mu aka kaita inda zata yi sati kafin su wuce lagos

Sauran kuma duk nan cikin kano suke zaune muna tare.
***** ***** *******
Cikina ya shiga wata bakwai wanda yayi dai dai da watan salma biyu a kano kasancewan tana hutun GSCE ne.

Yau saura kwana biyu ta tafi sai shirye shirye muke,yanzu ma muna zaune muna shirya kayan da tela ya kawo wanda na bayar a d'inka mata.

Kallonta nayi nace" yanzu salma maimakon kiyi zaman ko anan sai yah rid ya sama miki makarantan cikin anguwan nan ko wace muka gama amma kin ki ko?"

Tab'e baki tayi tace "nifa na gaya miki ba zan iya zaman kano ba gwara min kusa da dadana ke baki zauna a gida ba nima ba zauna a gida ba munta barin dadan kenan? Kuma ma ni ko sha'awan zama garin nan baya bani yanzu ma ji nake kaman in janyo ranan tafiyar"

Harara na balla mata nace kin dad'e baki jawo ba,da ki jawo da karki jawo ranan yana zuwa in kin ga dama ki fi ruwa gudu."

Dariya ta kyalkyale da dan ta san na riga da na k'ulu ne.


Doorbell muka ji hakan yasa duk muka mik'e dan ganin waye.

Yah sadeeq ne had'e rai salma tayi ta gaishe shi kafin ta wuce kitchen abinta.

Zama nayi ina gaisheshi yace " zakiyya irin wannan kumatu da kika ajiye sai ina haka?"

Dai dai lokacin da salma ke ajiye mishi ruwa nace "ai da ban kai matarka kumatu ba"

Dariya yayi kafin ya ban amsa yaga salma na shirin shigewa da sauri yace salamatu zo.

Dawowa tayi ta zauna ido yake so su had'a amma sam tak'i ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah.

Ajiyar zuciya ya sauke yace " jiya BB ke gaya min zata tafi jibi wai"

Nace "eh wallahi bata gaya maka ba kenan?"

"Hmm bata gaya min ba ni sam ban san me nayiwa salma kwana biyu ba take wani shashare ni"

Juyowa nayi na kalleta nace ke kuma ta hannun daman yah sadiq me ya had'a ku?"

D'aga kafad'u tayi tace "ni nace ya min wani abu ne ba fa komi"

Da sauri yace " toh ki bari sai wani sati ni in mai dake da kaina kinga yanzu abuja na nufa"

"Ah ah zanje in fara shirin school ka bari kawai driver ya maidani"

To kawai yace amma da ka gani ba haka ya so ba bandir d'in 200 naira ya ajiye mata wai tayi tsaraba sannan ya mana sallama ya tafi.

Kallonta nayi nace "salma akwai wani abu tsakanin ki da yah sadiq ne?"

A firgice ta d'ago tace ah ah me kika gani?"

"Ba komi kawai dai naga yanda yake ji dake ne tun da"

Yamutsa fuska tayi tace "kema ai kin san haka yake shi dai k'ok'arin shi ya ga ya samarwa mutum farin cikinshi duba da yanda kema ya dinga k'ok'akarin sama miki naki farin cikin.tun daga samun makarantar ki har izuwa hana ayi miki kishiya"

Ajiyan zuciya na sauke nace haka ne naji dad'i da ya kasance babu wani abu a tsakaninku kar ya zama na shiga tsakanin farin cikin ku in kuma yace zai had'aku banwa fadeela adalci ba ta guji zama kishiyata ni in had'ata kishi da k'anwata?"

Tab'e baki tayi wanda na lura haka ya zaman mata jiki kwana biyu tace" toh kima kwantar da hankalinki ba wannan batun,ni d'in ma gaba d'aya guda nawa nake da kike wannan maganan?"

Shiru nayi ina kallonta dan ban isa in d'orar da wani abu akan halayen salma ba tunda ba wani rayuwa muka yi ba duk da take y'ar shekaru sha biyar tana da wayo sosai.


**** ******* *****

Na riga na shiga watan haihuwa na cikin yayi k'ato kaman mai d'auke da y'an biyu.

Wata ranan juma@ muna kwance da yah rid bayan ya dawo sallah muna hira.

Shiru nayi da maganan da nake yi ganin ciwon da nake ji tun safe ya tsananta.

Ankara yayi da halin da nake ciki ba shiri ya kinkimeni sai hospital.

Banyi wani dogon nak'uda ba amma kam naji azaba ba,dan kasa kuka nayi wani ciwon yafi gaban kuka sai ido da nake zarewa ina had'a zufa.

D'ana namiji na santalo me kama da ubanshi sak sai haskena da ya d'auko.

Murna a wajen familyn nan ba a magana yah rid tisa ni yayi a gaba yana kallona tare da babynshi ko k'iftawa bayayi.

Ranan suna nace sunan yah sadiq nake so asa dariya kawai yah rid yayi yace saboda ya hana a miki kishiya ko nace "ba wannan ba kad'ai amma yana d'aya daga ciki"

Yaro yaci Abubakar sadiq taron suna yayi goshi dan manya motoci biyu daga hwol ga su fareeda mutanen lagos salma ce kawai bata zo ba wai makaranta.

Y'an uwana sun so tafiya dani mamah ta hana tace abarni wajenta tunda nima na kusan komawa makaranta haka kuwa akayi wajen mama na zauna nayi wanka na.












SAWWAMA QAWWAMA😘
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: 💖BANI NAYI KAINA BA💖






By Sawwama A.







Page 48.





Zauran biebie this page is for una, u gals dey try una dey encourage person make una keep it up







Abubakar bai cika shekara ba na samu wani cikin murna a wajen yah rid ba a magana yace dama yanda ya dad'e bai yi auran nan ba dole y'ay'ansa suyi rushing din zuwa duniya.

Amaren mu duk sun haihu banda fadeela da tayi b'ari.

Fareeda 'yan biyu ta haifa dukka mata intisar da ibtihal Yusra kuma ta haifi me sunan dady ana ce mishi waleed sai halima kuma ta haifo me sunan abba ana mishi inkiya da abulkhair.

Abubakar na da shekara daya da wata bakwai na haifi umar farooq,shima umar bai cika shekara ba na samu wani cikn.


Kuka na saka bayan naga test din da nayi ba zai yuwu ba haihuwa yasa ni a gaba ya hana min karatu cikin kwanciyar hankali in bana da ciki toh ina da goyo bari inje in sami yah rid gaskiya.


Zaune yake yana aiki a laptop kasancewar promotion dinshi ya kusa karkashin jagoranci *GENARAL* *ALIYU* *MUHD* *RUMOH* wanda yake abokinshi kuma me gidanshi inda shi genaral din ke k'ok'arin ganin brigadia general Ridwan ya samu promotion zuwa major general.

D'auke laptop d'in nayi daga gabanshi na had'e rai, kallona yake da mamaki kafin yace " precious ya akayi ne?"

Hawaye ne ya fara zubo min shar shar tuni hankalinshi ya tashi ya kamo ni yana son jin matsalata.

Cike da shagwab'a nace"hayatee gaskiya ni wallahi kana hana min karatu" sai na kuma fashewa da kuka

K'walo ido yayi yana kallona yace "precious ya za ayi in hana miki karatu bayan kin san nafi kowa son kiyi karatun nan duk da takura min da karatun yake yi."

Volume din kukana na k'ara nace " eh mana ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login