Showing 33001 words to 36000 words out of 50173 words

Chapter 12 - Bani Nayi Kaina Ba Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

346

da fuskata yana min sannu.

Yana rike dani muka koma mota ina mai da numfashi muna fara tafiya aka daga glass aka kunna ac sai naji kaina na juyawa.

Zuciyata na tashi nace mijin pls a kashe ac din a sauke glass kaina na juyawa da sauri ya bada umarni aka min yanda nake so.

A hankali bacci ya kuma daukata sai da muka tsaya sallah na farka sallah muka yi suka ci abinci dan ni gasashen masara naci na kora da coke.

Kallona yayi da mamaki yace precious me kike nufi wai abinda zaki ci kenen kawai.

Tura bakina nayi nace ni dai shi zan ci in ba haka ba kaina juyawa yake.

Kanki ke juyawa ya fada cike da mamaki we are seeing a doctor muna zuwa kano.

Nace yah fa ba ciwo yake min ba juyawa yake😇 na kwantata mishi da hannuna.

Shi dai bai ce komi ba muka kara daukan hanya ban kara bacci ba sai dai na sha coke kusan bottle biyar.

Da ya hanani kuka na dinga mishi sai da yaba ni ido kawai ya zuba min.

Can kuma nace yah in an ga mai masara dan Allah.

Gyada min kai yayi kawai yana kallona.

Sai la'asar muka iso cikin gida muka wuce ai ko ba karamin dadi naji ba dan na san gidana yayi kura.

Muna isa muka ga palon abba a bude nan muka fara bi hannuna cikin nashi.

Sallama muka yi suna tare da daddy dan dama su haka suke in suna free ko da yaushe suna tare.

Gaishesu muka yi sannan muka mike sosai suka yi farin cikin ganin mu tare tun ba da muka fita ya janyoni jikinshi ba.


Palon mama muka shiga taja ganina ta taso ta rumgumeni oyoyo diyata jana take amma yaki sakin hannuna.

Kai kaci gidanku sake min 'ya marairaice fuska yayi yace mama ta diyarki kike yi bani ba.

Dallah ban waje wani gototo da kai yaushe zanyi ta taka sake mata hannu.

Sannan ya sake min hannu ya zube a kujera mama ta zaunar dani kusa da ita.

Muka gaisa tana tambayata hanya gaba daya hankalinta na kaina.

Kur ya kura mana ido yana jin dadi har cikin ranshi yanda mama ke son zakiyya murmushi yayi da ya tuna lokacin da abin ke bashi haushi amma yanzu burgeshi yake.


Mikewa yayi yace na tafi inyi sallah toh tunda ba tani ake ba an daina yayina ko lafiyata ba aji ba.

Harara ta wurga mishi tace ba dole inji lafiyarta ba tunda na san halin rashin kirkinka.

Waro ido yayi yace toh gaki gata ai mama ban gutsire miki ita ba yana dariya yace precious bari inje sallah.

Yana fita nace mamah bari in dubo momy ina su yusra ma basa nan ne?

Tace suna nan hala basu ji zuwanku bane,momynku kuma tayi tafiya

Allah ya dawo da ita lafiya Mikewa nayi nace bari in dubo su


A kofan dakinmu muka ci karo tsalle suka yi suka rungumeni turesu nayi nace ba ruwana kaman baku san na iso ba.

Na wuce na zauna a bakin gadona biyoni suka yi.

Halima tace wallahi jarabar mijinki ne yasa bamu fito ba yanxu mu sha rankwashi.

Hararanta nayi nace mijina je jarababbe?

Kallon juna suka yi suka sa shewa lallai yarinya sai dai kema in yanzu ya daina miki jarabar.

Murguda baki nayi nace eh din ni dai a daina cewa mijina jarababe.

Halima tace munji ke me yaya ke baki ne kika wani kara kyau haka.

Nace madara mai gardi wanda ba a bawa yara.

Wani shewar suka saki halima tace ga alama kan shegiya ashe bakinki zai bude.

Nace gashi kuwa kai gwara ku bari inyi sallah.

Ina idar da sallah naji takunshi da sauri na haye gado nayi likimo.

Dan kwankwasa kofan dakin yayi kafin ya shigo.

Ina ji suna rige rigen gaishe shi as usual yand a ya saba haka ya ansa musu.

Karasowa bakin gadon yayi ya zauna a hankali Yace precious tashi na san ba bacci i kike ba.


Kallon juna su yusra suka yi irin huh😳

Ni kam Kara gyara kwanciyata nayi dan na san so yake mu tafu gidanmu ni kuma wallahi bana jin zuwa gidan.

Ban ankara ba sai ji nayi ya sunkuce ni kallon juna su yusra suka yi cike da mamaki.

Ni kam wuntsi wuntsil na fara ina fadin ka saukeni sai da muka kai bakin kofa ya saukeni ganin na fara hawaye.

Sa yatsanshi yayi ya dauke hawayen yana fadin meye na kukan toh.

Tura baki nayi tare da dan bugunshi a kirji nace ba kai bane.

Me nayi kawai fa so nake ki ci abinci muje kiga doctor kan wannan juyawan da kanki yake yi.

Turo baki na kuma yi nace toh ba ya daina ba kuma ni fa bana jin yunwa coke kawai zan sha.

Ah ah ban yarda ba muje gida sai in dafa miki wani abu kici in na gidan nan ne ba kya so.

Make kafada nayi nace ni dai mu kwana a nan gobe sai mu tafi gida tare da su yusra su tayani share gidan.

Lakuce min hanci yayi yace ai na sa sun gyara ba wani aiki a gidan precious yaushe kika fara gudun aiki ke da aiki kaman agogo.

Tura bakina kawai nayi.

Yatsansa ya sa yana zagaye bakin yace mmm wannan pink lips din na ta nemana da tsokana tun dazu i need to teach them a lesson.

Ya fadi hakan yana hade bakinmu kara mannewa nayi a jikinshi.

Tarin da aka yi ya tunatar damu inda muke sakeni yayi yana wani harare hararen borin kunya

Muje ki ci abinci noke kafada nayi nace ni dai coke.

Shima hade rai yayi yace nope you have had enough yau

Nace toh ni dai masara ina hade girata.

Yatsanshi yasa a tsakanin giran yace naji toh sake fuskan kin san bana son tattarewan goshin kin nan irin wannan hade gira.

Lemme get it for you just take care ok? Na gyada kai ya manna min kiss a goshi kafin ya fits.


Yana fita suka kwakumoni shegiyar zoki gaya mana abinda kika wa yayanmu duk ya sususce.

Daga kafada nayi nace me ko ma mishi ina dariya













SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖






By Sawwama A.






Page 38.











This page is dedicated to you aunt zuwairat Ene ufedo mi, uwe cene ke du kpayu mi kpayi edo omemele ku ke wu ki deyi uwe my star i so much cherish u and i adore your talent. Ufedo emi lailai









Ana yin sallan magrib ya shigo da masara lokacin muna dakin mamah.

Mama na uwar daka tana sallah dan mu mun yi cikin zumudi na tashi hannu na sa na karbi ledan hannunshi dan tuni kamshin gasashiyar masarar ta ziyarceni.

Ban bi ta kanshi ba na zauna jikina har rawa yake na bude na dau masara daya aiko da zafinta.

Fara ci nayi kaman wace ta wuni da yunwa gaba daya ido suka zuba min tun ba shi ba da ya san ba haka take abu ba.

Su yusra ma mamaki suke yi dan sun san ban wani damu da gasashen masara ba dama dama ma dafafe.

Dan ko zuwan mu hwol dasu haka zasu ta kwarainiyar gasa masara ina kallonsu amma yanzu ci nake kaman an aikoni.

Mama ce ta fito tana fadin zakiyya ai yanzu dai zaki ci abincin tunda kuka iso baki ci komi ba sai coke.

Ridwan ne ya amshe batun da fadin yauwa mama hala ke zaki sa ta ci abincin dan wunin yau gaba daya bata ci komi ba sai gasashen masara.

Mama ce ta juyo inda nake taga yanda nake cin masaran har na cinye daya ina kokarin cin na biyu tace ikon Allah dan tuni ta fara hasashen wani abun.

Dan tun shigowarsu ta zargi haka ganin irin kyau din da ta kara amma sai tayi la'akari da zaman waje daya tunda daman ita mai kyau ce.

Dan ta tabbatar sai tace to kici wani abu mana kafin masaran ko amai zai saki.

Da sauri nace eh wallahi mama dan ko tunanin abincin nayi sai naji zuciyata na tashi shi yasa ma bana bi ta kan abincin.

Masha Allah cewan mama to kuma ba kya sha'awan cin wani abun sai masara.

Shiru nayi ina tunani🤔 can nace yauwa mama sai popcorn.


Kallon juna su yusra suka yi cike da mamaki.

Shi kam dafe kanshi yayi🤦🏽‍♂ dan ganin yanzun ma ba wani abun kirki tace ba wai popcorn.

Yauwa mama da irin dry plantain din nan mama tace toh Ridwan samo mata.

Tsaki yayi yace mama ta tashi mu tafi dan na gaji na siya mata a hanya.

Gaskiya kam kuje ku huta ke zakiyya tashi ku tafi gidan gobe zan shigo ni da doctor Zainab.

Mikewa nayi ina neman gyalena nace mama waye ba lafiya.

Ba kowa zata zo ne ta muku barka da zuwa nace toh.




Sai da ya bi ya jido mun popcorn da dry plaintain muka kama hanyan gida duk a gajiye yake dan shi yake driving ya tura sojojinshi gida.

Muna isa wanka yayi nima da kyar ya dagani daga cin popcorn ya min wanka.

Kwanciya yayi yan kallon yanda nake cin popcorn din ina korawa da coke shi shan coke din ne baya so.

Bacci ya fara daukanshi na tabashi ina fadin mijina zanci plaintain kuma na barshi a parlor kazo ka rakani.

Bacci cike da idonshi ya tashi muka je muka dauko har zai kwanta nace ruwa zan sha kuma babu a fridge din dakin nan.

Nan ma ya mike yana layi dan bacci da gajiyane a tattare da shi ruwan na dauko.

Ya kalleni da lumshashen ido yace shikenan ko akwai wani abun.

Kai na girgiza tare da fadin babu jana yayi yace oya muje please ki kwanta precious dare yayi kuma duk mun gaji.

Kafada na makale nace ni bana jin bacci kai kawai ya gyada min ya kwanta.

Hira na fara mishi tun yana ansawa har yayi shiru bacci ya daukeshi.

Ni kuwa idona ya bushe kyamas ba alaman bacci sai buruntu nake kayanmu na fara jerawa a wardrobe.

Dago kai yayi jin buruntun yayi yawa ga haske da na kunna.

Precious what are you doing karfe biyu fa baki kwanta ba.

Baki na turo nace ni bana jin bacci tashi yayi ya janyoni ya kashe wutan sani yayi a jikinshi yace kwanta baccin zai zo.

Haka na dinga mutsu mutsu sai kusan uku na sami bacci.

Da asuba a daddafe nayi sallah ko doguwar addu a banyi ba na lallaba na kwanta.

Kallon yanda tana kwanciya bacci ya dauketa yayi yace atoh ba dolle ba rigima ya hanaki yin bacci jiya i wonder what is wrong with her.

Karatu ya dan taba shima ya koma gadon ya jawota jikinshi.


Basu suka farka ba sai wajen sha biyu lokacin ma wayarshi ce ta tashesu mama da dr zainab ne suka iso.

Hijab na zira na fito wajen mama kayan tea nayi kokarin kawo musu mama tace ah ah mu ai na rana muke jira yanxu kam dan mun tsufa da karyawa.

Dariya nayi na zauna na gaishesu.

Dr zainab ce ta min yan tambayoyi sannan ta bani wani kwalba naje nayi fitsari na kawo mata suka tafi.


Da yamma ta kaiwa mama test ina da cikin sati 5 murna kaman za tayi yaya...

Ba shiri ta kira ridwan tace yazo albishir ta mishi tare da bashi maganin da dr zainab ta prescribing wa zakiyyan.


Ina kwance bayan na gama cin masara bacci ya daukeni.

Banji shigowanshi ba sai kisses da naji yana showering dina da shi ido na bude ina kallonshi.

Murmushi yayi ya tashi tsaye tare da daga collar din riganshi sama yayi doro yana wani bubbudewa.

Tashi nayi zaune ina kallonshi da mamaki.

Gira ya daga min yace kin gane ko.

Ido na zaro ganin abinda yake yi.

Ya dan ja dogon hancinshi yace yawwa kina ji ni din fa ba na wasa bane na dage na zake dantse tare da baje kwanji nayi noma.

Noma kuma yayi albarka tunda tsirina har ya tsiro a gonata halak malak.

Gira na daga na zuba mishi ido da baki da hanci dan ban gane inda maganar tasa ta dosa ba duk da na san yana cewa ni gonarsa ce to me yake nufi.

Ganin ban fahimceshi ba yasa ya daukeni yana zagaye parlon dani yana fadin precious we are pregnant we are going to be a parent.

Toshe kunne nayi jin yanda yake ihu at the top of his voice ajiyeni yayi ya riko hannuna yana rawa dani irin na turawa.

Ni dai ido na zuba mishi wai ina da ciki ni zakiyya ce ke dauke da ciki kuma wai yah rid shine uban dan Allah buwaye gagara misali wa ya taba zata?🤔
















SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖






By Sawwama A.






Page 39.






AISHA KANYA INA KIKE TARE DA YAYUNA MAMAN SADIQ DA MAMAN MANAL BAN MANTAKI BA HASSANA DANLARABAWA KUNA RAINA ANA MUGUN TARE😘.






Kulawa na mussaman nake samu a wajen wannan zuriyar kowa nan nan yake dani su yusra mamakina suke yanda na shawo kan yah rid a cikin dan kankanin lokaci wai in gaya musu sirrin nace abin sirri ne.

A gaban kowa yah rid nuna min soyayya da kulawa yake wani sa'in har kunya nake ji.

Ranan da muka je gidan daddy motsi kadan zanyi zaice precious ya dai me kike so.

Sai da mami ta gaji tace ridwan yaushe son mace ya mai da kai mara kunya.

Murmushi yayi yana shafa kai yace mami ai ita dince ba lafiya ne ya isheta ba shi yasa.

Dariya tayi tace lallai kuwa manya za a zama uba ai ba zaman lafiya.

Shima dariyar yayi ya kwalawa fadeela kira dan fareeda taje yin online registration na post utme dinta dan bata yi tare da su fadeela ba ko meye dalili oho.

Zuwa tayi tana wani karairaye sai wani yatsina fuska take ni abin har mamaki yake bani dan dai ba haka fadeela take ba da.

Na san ita din mai son kai kanta ce kuma tana da dan rashin kunya amma yanzu abin yayi yawa.

Mussaman a gareni ta mai dani makiyarta ta gaske ban san dalilinta ba su yusra sunce bakin cikin kyau na take.

Abin bai ta'azara ba sai da aka fara maganan auran mu da yah rid ta kara kafa min kahon zuka maganan arziki baya hada mu sai dai harara da tsaki in ko ta min magana toh baka ce ta gaya min.


Kudi ya ciro a gaban aljuhunshi ya mika mata fuskar nan amurtuke dan shi bai son raini yaga alama kuma yarinyan na tashen balagan tsuntsaye yace kije ki siyowa precious masara na ga akwai mai gashi a farkon anguwan nan.

Karba tayi tana tura baki ta daukko gyalenta ta yafa ta fita.

Mami tace Allah ya shiryi fadeela ni dai ban san inda ta dauko mugun halin nan ba,saboda wannan halin ita da yar uwata ba wani shiri suke ba fa.

Kwafa yah rid yayi yace barni da ita ai tara ta nake randa zata shiga hannuna zata gane bata da wayo.


Muna nan zaune ta shigo da dafafen masara yana karba yaga dafafe


Dan ubanki dafafe nace ki siyo?

Yah ai baka fada min wanda zan siyo ba.

Ke kuma kin fi karfin ki tambaya ko toh maza ki mayr ki karbo gasashe.

A fusace ta fita ranta fal tsanan zakiyya wallahi sai ta dau mataki akanta.

Tana fita fareeda ta shigo ihu ta saka ta fado jikina tana murna.

Da hanzari yah rid ya tshi ya dagata yan masifa ke baki da hankalina sai kin ji mata ciwo.

Ido ta zaro tare da rufe bakinta mami tace su hankaline da su Allah dai ya shirya.

Gyada kai fareeda tayi tana dariya ta hade hannunta waje daya tace sorry kawata na missing dinki ne zo muje daki ta miko min hannu na kama ina dariya.

Muna shiga ta daka min duka tace shegiyas naga mutumin yayi ladab

Sosa bayana nayi nace shine zaki zage ki daka min duka ke da yah rid na juya kaman zan fita ta rikoni ke rufa min asiri kar kisa a lillisani a ce zan barar da ciki dan naga rawar kan da yake yi kenan.

Dariya nayi nace a ina kika ji ina da ciki su halima magulmata.

Ba ruwansu halima shi uban gayyan yayi ta kira yana fadawa mutane muna zaune da mami ya kirata.

Nace lallai kuwa ina zama a bakin gadon.

Kayan jikinta ta fara cirewa ni kuma na dau file din da ta shigo dashi.

Ido na zaro ina kallonta da mamaki nace fareeda wa ya aikeki applying LASU wa zai barki kiyi karatu a wani garin balle lagos.

Daura towel tayi ta zauna a kusa dani tace saboda a can zanyi aure bana so in apply BUK maganan aurena ya tashi a nemi hanani saboda karatu.

Nace aure? Wa zaki aura fahad ya koma aiki lagos ne?

Tsaki taja tace ban son rashin mutunci ni dama na taba ce miki ina son fahad ne ko zan aureshi?

Nace to waye wannan kuma fareeda da sanin su abba kika cike lasu?

Ajiyan zuciya ta sauke tace su daddy basu sani ba asalima wanda nayi dan shi bai san nan apply ba sai yau zan gaya mishi.

Innalillahi ni kam waye wannan da zakiyi abu gaba gadi ba tare da kin yi shawara da kowa ba akanshi?

YAH AUWAL ne zakiyya shine wanda zan iya yin komi saboda shi.

Ban gane yah auwal ba wani yah auwal din?

Yah auwal naki mana shine zakiyya nake soyayya dashi nake fatan ya zama abokin rayuwata.

Rungumeta nayi ina tsanin farin ciki nace amma naji dadi wallahi ke da yah Auwal abin yayi wallahi.

Ni da ina ce yusra ce fa budurwarsa.

Dariya tayi tana hararana tace ba haka bane toh,yusra ce kawai ta san yana sona wai injishi kama kafa yake da ita.

Dariya nayi sai kuma na kalleta nace toh ya zamuyi da su abba kin san dai sai anci ubanki.

Kafada ta daga tace sai me in dai zan kasance da hubbyna bani da case kuma ma yace yayiwa yaya magana yace zai zo cikin satin nan ya sami su abba.

Anya fareeda ba yah auwal ne ya saki cike lagos ba.

Da sauri tace wallahi bai sani ba...

Shiru muka yi da maganan ganin fadeela ta shigo.

Tana wani fisge fisge tace wai ki fito ku tafi ta juya ta fita.

Kallon juna mukayi da fareeda ta tabe baki muka mike muka fito.

Daga gidan ma gidan hajiya muka nufa mun samu tana zaune tana kwadon zogale tuni raina ya biya amma dai na dake.

Bayan mun gaisa ne ta kira mai aikinta tace saude dauko min plate in sawa wannan kishiyar tawa zogale.

Da sauri yah rid yace wata kishiyar taki baza taci ba ita fa ba komi take ci ba atoh.

Kankance idanu tayi tace wallahi rulwanu ka fita idona sai taci ai zogale magani ne zaka zo ka min fi'ili.

Na gaya miki ni ba sunana rulwanu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login