Showing 3001 words to 6000 words out of 50173 words

Chapter 2 - Bani Nayi Kaina Ba Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

336

weekend wani sa'in in anyi hutu kuma kullum muna tare da yah sadeeq yana bani labarin yan gida.

Mun shiga Jss 3 lokacin shekarun mu 13 alamomin girma sun fara bayyana a jikin mu su fareeda sai rawan kai ya karu an fara zama yammata.

Muna zaune a dakinmu har dasu fadila muna shirya irin ankon da zamu yi tunda bikin yah ibrahim ya kusa ko ince suna shiryawa danni da ido nake bin su.

Fadeela ce tace wallahi kar mu yarda muyi anko da kowa gamu nan har biyar muyi ankon mu daban kawai mu fito a kannen ango abinmu.

Shewa suka yi dukka yusra tace daddy zamu je mu sama ya bamu kudi muje mu dirji swiss less a gidan aunty rabee kasancewar ita kasuwanci take daga dubai zuwa india.

Halima tace kin kawo idea ai ba karamin casu zamu sha ba wannan bikin dan ma wannan a takuran na nan dawowa.

Sai kuma duk jikinsu yayi sanyi suka hada rai yusra tace ni wallahi dama a ta turashi kasashen wajen ya daina zaman nigeria kwata kwata.

Fadeela tace hmmm yah RIDWAN ko masifa carab halima tace ko jaraba ba ni duk shekara ukun nan da yayi baya gida ko kadan ban yi missing dinshi ba.

Yusra tace missing dinshi ai sai yah sadeeq dan shi dama in kinga rahamarsa toh ya sadeeq na wajen ko yah ibrahim, ya ibrahim din ma ai dan bai mishi da wasa ne shi shegen son girmanshi ne yayi yawa.

Fareeda tace toh ba dai yaga shine babba dukka ba shi yasa yake mana mulki.

Su aunty Aisha dai sun huta da suka yi aure abinsu Allah nima ina gama secondry aure zanyi.

Dariya muka sa dukkanmu har dani ma da nake sauraronsu, fareeda tace Allah kuwa dan jarabar ya Ridwan sai shi.

Halima tace su aunty rabin ma ai da suka yi auran ba tsira suka yi ba ina da ya samu labarin aunty Aisha ba karatu take ba ba kuma sana'a ba har gidanta yaje ci mata.

Ajiyan zuciya nayi nace ayya kuna ta ragewa bawan Allah zunubai baya nan amma sai kare mishi tanadi kuke Allah ba kyau in yazo sai na gaya mishi.

Dariya suka yi dukka fareeda tace lallai baki san yah Ridwan ba in baiyi kwallo dake ba.

Yusra tace kuka sani ko kyaunta ya rude shi ya kasa aiwatar da komi,sai suka dauka eh kuwa eh Wallahi.

Harara na balla musu nace ku dai kun shiga uku da shegen magana tun baku tafasa ba zaku kone ni din wani kyaune da ni koma ina da kyai yaushe na gama zama cikakkiyar mace.


Ihu suka kuma sawa halima tace ahegiya ashe kina magana har da wani yaushe na gama zama cikakkiyar mace ba nono a kirjinki ba duk nan kin fimu nono.

Hade rai nayi fadila tace kyau kam kuma sai dai ki mana ba'a mu bakake kuma bamu kaiki kyau ba

Farida taja dankwalina ta ware doughnut din da yusra ta min gashina ya zuba bayana tace ga gashi na fulqnin usul ba relaxer ba komi just natural beauty.

Halima tace ki duba manyan idanunta shape din kwai ko ni ta kalla wani sa'in sai naji gabana ya fadi ji eye ball din baki sidik shegiya ko kura baya rinan mata da farin ido..


Yusra tace sai hawaye ba dan akwai arhan su, suka kwashe da dariya haka suka ta zolayana.har nayi fushi na tashi na tafi dakin mama.

Ana biki saura sati aunty asma'u autar haj ta iso daga boston a nan take aure kuma bata taba haihuwa ba.

Ranan ne kuma yah ridwan ya iso duk da cika bakinsu yusra ranan sai murna suke har damu a taya aikin girke girke.

Lokacin da ya iso ana ta ihun oyoyo ina kuryar mama ina mata gyara gabana sai dukan tara tara yake ko mai yasa oho ko dan irin labarin masifanshi muguntarshi da iya bada punishment dinshi da naji ne oho.

Dakin momy ya fara shiga ya gaisheta kafin ya shigo gefen mama lokacin mama ta shiga wanka.

Sallama yayi har bedroom.din ya shigo sanye yake da wandon khaki sai short sleeve na shirt din khaki ya daure booth a kafarsa.

Bakine amma ba wuluk ba yana da dogon hanci sosai idanunshi manya ne amma basu kai nawa ba asalima eye ball dinshi ke da girma.

Girarshi cikakkiya ce baki wuluk kaman dan gashin kanshi shape din bakinshi mai kyau, dogo ne shi ingarma wato gaint.

Ke! Wata shegiyar tsawa ya daka min meye haka kin wani zubowa mutum idanu kaman wata mujiya toh in ke mayyace kije can ki nemi wanda zaki lasha, shegun masu aiki sai shegen kauyanci ina mamana.

Fitowa tayi daga bathroom din tace gani sarkin yan masifa ka dawo ko hutawa baka yi ba zaka tsoratar da yar mutane toh ba yar aiki bace kanwarka ce haba mutum sai bakar jaraba ni dai wallahi ban san inda ka dauko bakar zuciya ba.

Sunkuyar da kai yayi yana hararata kasa kasa yace haba mamaaaaa daga dawowana ko zama ban yi ba kin fara korafi.

Harara ta balla moshi tace ai kai naga ba halin naka ka fara nunawa ba daga isowarka kaga yarinya baka san ta ba ka hau ta da fada.

Kama kunnuwanshi yayi yace toh sorry my sweet mom na sameku lafiya,

Tana bude wardrobe dinta tace lafiya kaje ka samu ka huta bari a kawo maka abinci ma gaisa a nitse.

Yace toh yana balla min harara ya wuce ya fita.

Mama ta juyo ta kalleni tace kuje ke da halima ku kwashi abincinshi ku kai mishi.

Dan zaro ido nayi ban ma sani ba sai mama tayi dariya tace matsoraciya ba abin da zai miki yayanku haka yake gwara ki saba da halinsh, ki rage tsorata.

Nace toh naje na sami haleema na gaya mata abin da mama tace.

Lallai ma mama maimakon tasa masu aiki ko su yah mustapha su kai sai ta aikemu salon ya casa mu ba gaira ba dalili dauki tray din can ki fara zuwa ni na biyoki daga baya.

Ido na.kwalo waje nace haba haleema ke ki fara zuwa ai ke kanwarshi ce nifa bai sanni ba.

Haleema tace ai shi yasa nace ke ki fara zuwa kila ya miki baqunta ba zai ce miki komi ba.

Na kalleta a raina nace baqunta indeed dan bata san me ya min bane bata san ni ya fara saukewa kwandon masifa ba tray din na sunkuta nayi side dinshi zuciyata na lugude............ Ko yanzu wani draman zamuyi oho🤷🏼‍♀

💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.

Page 4.



Sallama nayi wajen sau uku ba a ansa ba ajiyan zuciya na sauke na fara tafiya sadaf sadaf na shiga naje na ajiye kan dining motsin bude kofa naji a cikin bedroom dinshi da sauri nayo hanyan fita sai ji nayi yana ke dan ubanki zo nan ai sai na kara wuta.


Kwafa yayi ya koma bedroom din yana raya irin casata da zaiyi dan da alama bata sami labarin halinshi,haka yayi ta magana shi kadai yana shiryawa dan dama yana wanka ya dinga jiyo sallamanta.

Ni kam da sauri na shiga kitchen na sami halima na jirana harara na banka mata nace Allah yaso baya nan ma.

Sauke ajiyan zuciya tayi tare da juya idanunta ta dau nata tray din nace ai gwara kije kema ki hadu da shi nayi ficewata zuwa dakinmu.

Nan na samu su yusra ana ta hira nima na zauna sai ga halima an shigo ido jage jage da hawaye ta sha rankwashi.

****** ****** ******

Duk yanda muka ci alwashin bikin nan ya Ridwan ya hana mu rawan gaban mu ya bi ya takura mana duk yanda muka kashe kudi wajen dinkunan mu haka ya hana mu zuwa duk wani event da akayi da dare wai munyi yara.

Su fareeda ansha kuka ni dama ban sa aka ba taro baya cikin budget dina suna dama suka takura.

Haka aka gama taro suna cikin dacin rai aka kaiwa yaya ibrahim amaryarsa shema'u aka watse.

********* ***** ********

A halin yanzu muna first term SSS3 mun gama zama yam mata ko wani alamomi na budurta ya gama bayyana a jikinmu.

Ni kam al amarina har tsoro yake bani yanda mutane ke kururuta kyau na mama hanani fita take in ma zan fita sai dai insa zumbulelen hijab.

Su yusra ma sun ce kashe musu kasuwa nake in mun fita tare ba kaman fadeela da ta dau abin da girma bata taba yarda mu fita tare wai ba yanda za ayi tana da kyaunta da farin jininta dai dai ita in kashe mata kasuwa tun muna daukan abin da tsokanane har muka fahimci ita fa da gaske take.

Daddy da abba har sun gaji da bawa mutane masu neman izini akaina hakuri haka kawayensu mama wai suna so ma ya'yansu.

Hira ma kwata kwata ni ba nayi tunda wani dan kawar mama ya dage yana zuwa wajena wata rana yaso ya min ta'asa mama ta tsorata ta gayawa abba shi kuma yace duk wanda ya zo nemana ace an min miji zaije ya samu yayah suyi magana.

Ya auwal da yah sadiq sun dade da gama har masters dinsu sun kama aiki yah sadeeq na abuja inda yah auwal ya luluka lagos.

Zumunci tsakanin zuriyarmu da tasu yah sadeeq kam ba a magana har abba da daddy sunje sun sami yayah sun shawarta tsakaninsu.

Ya Ridwan kam tun bayan auran yah ibrahim aka turashi Syria sau daya ya dawo shima ban bari ko sau daya mun hadu ba har ya gama hutunshi ya koma.

Abba ne ya kirashi yace maza ya nemi a dawo da shi gida Nigeria ko ya ajiye aikin gaba daya yazo ya kama kasuwanci.

Ai ba shiri ya nemi transfer zuwa gida yana dawowa aka kara mishi girma zuwa colonel .

Innalillahi abinda naji halima na fada kenan lokacin da driver ya karyo kwanan gida mun dawo daga sch daga ido muka yi ni da yusra lokaci daya muna kallon inda take kallo.

Dam gabana ya bada a lokacin da na hangoshi a tsaye a bakin gate shi da yah ibrahim da wani hannunshi rike da taba nan take naji wani kyamarshi dan abin da nafi tsana kenan.

Baba driver tsaya mu gaisheshi kar ya fara cin uban mu tun daga nan cewar yusra.

Sakkowa muka yi dukkan mu muka dan rusuna muka ce barka da yamma yah Ridwan barka da yamma ya ibrahim


Yauwa yan makaranta cewar yah ibrahim shi ko gogan sai da ya
Yar da taban hannunshi yayi ya take kafin yace uhmm yana kallonmj daya bayan daya a fuskata ya sauke idonshi yace wannan me kama da aljanun fa daga ina?.......

💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.


Page 5.



Tsaki yah ibrahim ya ja yace kai fa ba karamin dan rainin wayo bane mai kyau dince baka sani ba yarinyan da kusan shekaranta 6 a gidan nan.


Kana nufin kace min wannan aljannar yarinya tana gidan nan for almost 6 years for what ? Me hadin mu da ita dan duk danginmu ba mai kalar aljannan nan.

Rai a bace yah ibrahim yace kai tashi ku shiga ciki da sauri muka mike dan dama kaman a kan allura muke.

Tafe nake ina goge hawaye su yusra na ban haquri dan suma sosai ransu ya baci da kalan rashin mutuncin ya rid.

Ni ba abinda yake bata rai irin danganta ni da aljanu da yake yi.

Ibrahim ne ya juyo ranshi a bace yace kai fa wani sa'in baka da girma me zakiyya tayi mata zaka mata irin wannan diban albarkan.

Sameer da tun da ya hango zakiyya hankalinshi ya tafi yace gaskiya colonel baka kyauta yarinya mai kyau da hankali haka.

Tsaki ya dan ja ya shafa kanshi yace ku bazu gane bane kwata kwata tun lokacin da na fara ganin yarinyan nan wallahi naji tsananta ni a lokacin ma na zata yan zuwa bikinka ne dan a lokacin bikin naka na ganta.

Ban kara ganinta ba shi yasa na manta ta toh amma mai take yi A gidan nan me hadinmu da ita??

Ibrahim ne ya kwashe zuwana gidan ya fada musu kasancewar sameer shima ku san dan gidan ne.

Sameer yace ayya gata da hankali yanzu ai ta kusan gamawa ma.

Ai gwara tayi ta gama ta bar mana gida dan wallahi haka kawai ban son ganinta bata burgeni tun bata kai haka ba kyau kaman wata aljana irinsu sai shegen fi'ili da girman kai da iyayi su ba kowa ba.

Yah ibarahim ya dan girgiza kau yace ba dai zakiyya ba yarinyan da bata taba iya hada ido da mutum magana ma bai dameta ba da wuya ka ganta a cikin mutane ni ba zan so yarinyan nan ta bar zuriyarmu ba.

Cikin kuluwa Ya Ridwan yace toh ai sai ka aureta kaje ka hadata da shema da kuwa na bar shiga gidanka har abada.

Dariya yah ibrahim da yah sameer suka yi kafin yah ibrahim yace ai dan dai na riga nayi auran ne da na aureta sai dai ga sadeeq ko da yake gaka nan ma babban gwaza kaki kayi aure ya fada hakan cike da zolaya.

Naushi ya kai mishi ya kauce yana dariya yace ah ah oga sir ba soja bane bazaka illatawa matata ni ba gwara kai babban gauro ne.

Sameer ma dariya yake yace ai ya kusa ya tashi daga gauron duk zamu fita gauron mu huta da shegen iyayinka da anyi magana kace matata to kowa ma dai zai yi matan nan.

Bar dan iska ya rasa wace zai hadani da ita sai mai idon mayun can bayan ni ina da mata first class me zanyi da kalan lalura ai ni mai iya daukan buqatuna sai shuhaira.

Rike baki yah ibrahim yayi yace oh su shuhaira manya wato har ka gama sanin zata iya daukan buqatunka ko dai har ka fara sauke mata buqatun ne.

Sameer dai dariya yake yace wallahi ni kam nayi nan bazaku kashe ni da dramanku ba ya shiga mota ya tafi.

Shi kuma yah Rid ya fuskanci ya ibrahim rannan a hade yace ai dai ka san ni ba dan iska bane tunda sanin kanka ni asali ma mace bata gabana balle in nemi inyi lalata da ita ba shuraihan.ma ganin kamun kanta da yanda take sona yasa nake sauraranta kuma na san dole za a zo a matsa min da batun aure.

Yah ibrahim yace dole mana za a matsa maka da batun aure tunda kai ba waliyi bane yanzu fa ka haura 35 ai gwara ka san me kake ciki.

Sauke ajiyan zuciya yayi yace kai dai bari kawai bro Allah kadai ya san dauriyan da nake yi shi yasa Na yanke shawaran in an kwana biyu zan sami daddy da maganan shuraihat din in shi bai fara min maganan ba.......

Nima sawwama nace da rabon ko zai yi maka shigar sauri😜

💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.


Page 6 .


Tunda ya rid ya dawo ya sani a gaba sai dai in hanya bai hada mu ba yanzu zai zageni ya hada min har da rankwashi dan gwanine wajen rankwashi.


Yau lahadi na tashi da wani matsanancin ciwon ciki kasancewar ina cikin period dina ko da yamma tayi su yusra sai tafiya islamiya suka yi suka barni dan dama in har na fara period zuwa school kuma sai Allah.

Ni kadaice a gidan duk antafi islamiya su mama ma sun tafi sunan amaryan matan abokin abba.

Ina kwance a dakin mama dan in dinga jin masu shigowa duk da akwai masu aiki murkususu nake tayi ni kadai.

Sallamanshi naji a palo da kamshin turarensa sai warin tabar tuni zuciyata ta fara tashi saboda jin warin abin da natsana ga kuma ciwo .

Da sauri na tashi dan in shiga bayan gida saboda wani amai da ya taso min shi kuma dai dai nan ya shigo.

Carab ya ruko hannuna yace ke dan ubanki dan kin gan ni ne zaki tashi ki gudu wato ga dodo ko? Ni da ke waye abin gudu ke masu kalar aljanu ma ba a gudu miki ba amma har kina iya gudun ma wasu.

Toshe bakina da hancina nayi a lokaci daya ina girgiza kai ina kuma kokarin warce hannu na dan at any moment na kan iya yin aman saboda tabar da ke daya hannunshi


Ke ni kike toshewa hanci? Kut amma kin rai..... Maganan shi ce ta yanke a lokacin da na wanke mishi ciki da amai.

Kam bura uba abin da ya furta kenan ya sake ni ya wanke ni da mari kafin in dawo hayyacina ya kara min wani ya sa kafa ya kwasheni na fadi kasa

Ban iya cewa komi ba sai wayyo yayah kayi hakuri bani da lafiyane ba gudunka nake ba dan Allah kayi hakuri na hada hannayena biyu ina hawaye.

Wallahi banda ina gudun kasheki wallahi yau da sai na lahira ya fiki jin dadi ina ruwana da rashin lafiyarki a kyamace ya cire rigarsa ya wurga min afuska yace kuma wallahi na baki 30 mins ki wanke min rigata ki goge kuma ba a washing machine ba dan ubanki shegiya mayya ya juya ya fita.

Da kyar na Mike tsaye ai sai tsantsin aman ya kuma kayar dani wani dan marayan kuka na saka ina tausayin kaina.

Haka na lalaba na tashi na gyara wajen na cire kayana na hada da rigarshi na wanke.

Ina jin ciwon cikin nan ina komi haka na fito nayi ta yarfe rigar nan sai da na tabbatar zata iya goguwa na je na fara gogewa ina yi ina duba agogo duk na hada zufa.

Cikin sassarfa da tsoro na shiga side dinshi waya yake yi da alama da budurwarsa ce dan sai wani zuba shagwaba yake yi ko kunya baiji ba katoto da shi yana ya wani abu kaman yaro.

Tabe baki nayi in raina yayi dubu ya baci kura mishi ido nayi yana sanye da 3kwata na kamu (khaki)a jikinshi sai farar riga mai dan guntun hannu ya kama mishi jiki dan kana ganin zanen abs dinshi yanda jikinshi yake amurde.

Shi din baki ne mai kyau dogon hancin shi na masifar burgeni balle bakinshi hmmm😋

Idona kan yatsunshi suka dira dogaye dasu gwanin kyau i can't imagine hannunshi working therr magic on me wani lumshe ido nayi ina raya hakan a raina.

Innalillahi astagafurillah na fada tare da saurin zaro idona mai nake yi haka na shiga uku yaushe na fara developing dirty mind ba akan kowa ba ma sai wanda ya fi kowa tsanata a duniyan nan.

Ke naji an daka min tsawa a tsakiyar kaina sai da na zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login