Showing 9001 words to 12000 words out of 50173 words
karo.
Farida tace ah ah ni kam ba ruwana da yah rid ba iyawa zanyi da shi ba macece wacce ta kai mace ma ya rid na wulakantata balle ni.
Ji banza ke din ba mace bace duk wani halitta na ya' mace kina da shi toh meye ya rage yanzu dan Allah wannan facakar da take ti da kudi da ba daya daga cikinmu ce take yi ba.
Ohoooo sai yanzu na gane inda kika dosa fadeela cewar halima amma kin bani kunya kice hassada ce kawai kike yiwa zakiyya sai yanzu na gane tun farko me yasa kike jin haushin zakiyya ashe bakin cikin kyan da Allah yayi mata kike yi yanzu kuma da Allah ya bata namiji daya tamkar dubu nan ma baki kyaleta ba kina mata bakin ciki.
Wallahi kin bani mamaki da kunya ai iyayenmu sun san da ke suka ga zakiyyar ce tafi dacewa da su ba zakiyya zaki zo kiyiwa tijara ba iyayenmu zaki je ki sama ki gaya musu abinda ya dace dan su suka hada ba zakiyya ba yanda yah Ridwan yake ikrarin bai sonta itama ai ba soshi take ba ita da take da asset din da namijin aure sai ta zaba ko da kuwa shugaban kasa ne balle wani yah rid.
Mtsw taja tsaki ta fita ganin duk cikin yan uwanta ma ba wanda ya goya mata baya.
Farida ta juyo inda nake kwance ina kuka tace ke kuma mara aikin yi ki zauna kawai kina zubar da hawayanki a banza indai kika ce wannan halin naki zaki cigaba da yi fadila ta samu daman rainaki kenan koshi ya rid kamata yayi ki nuna mishi kema fa macece.
Yusra tace wallahi kuwa shi yana wani ikrarin bai son mace me kyau ba ayi auran bane yarinya ajiye kunyanki da sanyinki zaki yi ci mishi uwa sannan ki dauka ki mayar.
Kwashewa suka yi da dariya dukkansu halima tace wallahi yusra gaskiya ta fada tun yaushe zata saito shi kan hanya shi ba namiji bane lafiyayye sai dai inshi dutse ne.
Duk shegen girman kan nan zai ajiyeshi sai yanda kika yi da shi tayi kwafa tace Allah maza ba karamin bani haushi suke ba.
Farida tace wallahi kuwa raini ne dasu mussaman gamu teenagers ganinmu suke yara shatab wanda basu san komi ba.
Yusra tace nan ko in muka sa su a daki sai yanda muka yi dasu. Shewa suka yi suka tafa nace Allah ya shiryeku amin suka amsa da karfi.
Karatun jarabawa muke sosai bama samun zama tun safe in muka tafi school sai hudu da sauri muke shiryawa zuwa islamiya saboda hadda muke shida kuma mun wuce wajen kwalliya sai takwas kuma.
Duk zirga zirgan da muke yi ni a motar yah rid ake kaini su kuma a motar gida in tajin haushi su da yawa suna hirarsu ko ban samu su baki ba ai da dadi kana cikin mutane.
In na yi musu korafi sai su ce min ai ni matar manya ce wane su hada hanya da matar soja.
Ko a makaranta wani respect ake bani daga dalibai har malamai ganin me uniform ke dawainiya dani.
Su kam har sun fara dana sanin shiga make uo classes din da suka yi suka ce dama sun bari sai anyi final exams tunda su ba amare bane.
Momy da mamah suka ce basu isa ba ai gulmar da yasa suka ce sai sun shiga toh sai sun karasa.
Ana saura sati mu fara jarabawa mama tace min ya rid zai dawo tuni naji kaman in gudu wani abin mamaki kuma da al amarina sai na tsinci kaina da son ganin shi.
Lallai bani da hankali ganinshi na dai dai da gani bacin raina dan tabbas na san watan cin ubana ya kama.
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 11.
Ranan da zai dawo wayan mama ya kira yace ta bani dan bai taba kirana ba asalima bai da number na.
Cikin faduwar gaba na amshi wayan mama ta fita.
Sallama nayi cikin sanyina amin kawai yace sannan yace ke kina jina na san kin sami labarin zan dawo yau toh ki fara shiryawa kanki dan kam tabbas kin san ba zan miki da sauki yanda kika sa aka rabani da farin ciki da kwanciyar hankalina toh kema haka zan miki koma fiye da haka.
Tuni hawaye suka cika min ido ina kokarin mai da su.
Kina ji ko nace uhmmm yace good yanzu ina so kiyi min fried noodles,salad sai tuwon alkama da oha soup sai zobo and any other home made drink ki min shirme wallahi ki gani.
Da sauri cikin rawar murya nace yah ban iya oha soup din ba.
Cikin tsawa yace i dont bloody care kawai in ganshi in na dawo sannan a gyara min part dinna ko jikin mutum ya fada mishi ya katse wayar.
Rike wayar nayi kawai a kunnena ina tunanin wannan masifan da nake shirin shiga Allah ka shiga tsakanina da bawankan nan.
Karan ringing din wayan dake kunnena ya ankarar dani da sauri na fita na kaiwa mama sannan na wuce dakinmu ina tunanin ta inda zan fara.
Halima kadai na samu a dakin tana kan system zama nayi a gefen gadona na zuba uban tagumi.
Halima ta dan juyo ta kalleni tace ke kuma fa irin wannan uban tagumi ki cigaba da sa abu a ranki kina yar karamarki da ke sai wata cuta ta kamaki shi yah rid ba asara ne da shi ba tunda ba sonki yake ba mu dai masoyanki za a bari da matsala.
Hmmmmm kawai nace har zata juya ta cigaba da abinda take yi dan ta san zurfin cikina in ban yi niyyar fadan abu ba duk nacin mutum sai dai ya kyaleni.
Nace kiji yah wai wani oha soup zan mishi ni kuma ban taba ba asali ma ban san miyan ba.
Jarfa meye kuma wani oha soup yah rid fa ba shi da dama tsakani da Allah muna kano ba kudu ba ina zamu san wani oha soup.
Ko miyan wani yare ne sai Allah duk shiru muka yi muna nazarin ta inda zamu fara.
Halima tace yauwa yammata Allah ya taimakemu we are in the 21 century where technology exist.
Na mata kallon tambaya kafin kwakwalwata ta tafi inda nata yaje da sauri na tashi na rungumeta.
Tace toh ta ina zamu fara sunan miyan zamu sa ko kuwa.
Nace ah ah mu fara da saka yoruba tribal soup mu gani nan muka typing sai gasu sun jero mana su ewedu soup,gbiri soup da sauransu amma ba oha soup.
Muka koma muka typing igbo soup nan fa muka fara cin karo da su banga soup atama soup vegetable soup ogbono soup sai ga oha soup ai nan muka sa ihu.
Halima ta copying yanda ake yi ni kuma na fara shirin zuwa kasuwa har na shirya na karbi list din ingrediant din nacewa Halima yana ga kina zaune ki tashi mu tafi mana.
Tace ke nifa tsoron shiga motan nan nake nace hmm ai baki kaini ba amma haka nake shiga dan banda yanda na iya dan Allah tashi muje.
Ta tashi ta karyar da wuya tayi kalan tausayi wai toh yana iya abin ma abin dariya aiko muka yi dariyarmu.
Munje kasuwa mun sai duk abinda muke buqata nan da nan halima har da yusra ma suka tayani muka hada mishi abincin da juices dinshi su ka kuma tayani muka gyara side dinshi.
Muna dawowa dakinmu suka turani bathroom wai in yi wanka bayan na fito ne ina zaune ina shafa mai.
Yusra tace yasin ni ban yarda yah rid da zakiyya basa son auran nan ba ji tun kafin ayi auran suka koma mata da miji kwana ne kawai basa yi tare amma duk wani hidimanta shine.
Haka itama duk wani hidimanshi itace yanzu ki duba sai kace wanda mijinta zai dawo an mishi girke girke an gyara gida anzo anyi wanka za a cancada ado ta karasa fadan haka cikin zolaya.
Ai ko na hade rai nace wallahi ba kwalliyan da zanyi ya samu daman ce min aljan da kyau.
Hakuri suka bani ai fir naki yin kwalliya kayana kawai na saka doguwar rigace budada dan momy tace bai kamata in dinga sa abu da zai matseni ba saboda budaden hips dina saboda maza ne a gidan kuma ba muharramaina ba
Sai ya kasance yawancin kayana open gown ne sai ko buba nayi sallahn la'asar muka fito babban palo inda muka sami mama da momy zaune suna hira.
Momy ce tace ah ah zakiyya ya ban ganki da kwalliya ba duk irin zuwa make up classes din nan da kuke yi.
Carab yusra tace wallahi momy ba yanda ba muyi da ita tayi kwaliya ba taki.
Momy tace maxa ki wuce kije kiyi kwalliya haba na mene.
Haka na koma nayi light make up duk da haka sai da nayi ziza.
Muna nan zaune a palon ya iso gaba na sai dukan tara tara yake gaishe da su mama yayi sannan muma muka gaisheshi ya amsa yana shan kamshi.
Sai ya kara min kyau bakin kwayan idonshi har wani walkiya yake yi fuskan nan tas ba ko gashi.
Hmmm shima yah rid din nan mai kyau ne fa yake zagin mutum dan dai kawai shi ba fari bane.
Hararata yayi kasa kasa ganin na kure shi da ido yayi kwafa a hankali.
Mama tace kai kuka kai da wa kak kwafa ya dan shafa kai yana murmushi yace mantuwa nake tunanin nayi.
Momy tace ayya yanzu dai kaje ka samu ka huta ai ka sha hanya kai dai da son tuki kake maimakon ka biyo flight.
Mama tace son wahala dai da son kudi kin san sojoji da mako kuwa.
Duk muka yi dariya har da shima ya tashi ya nufi side dinshi.
Yana shiga ya lumshe ido cikin jin dadin kamshin turare da na abincin da aka shirya mishi akan dining.
Wanka yayi ya zauna yana cin abincin yana mamakin yanda miyar ta dau zaki bayan tace ba ta iya ba.
Shegiyar yarinya ba laifi akwai tsabta da iya girki ko dan wannan ma zai aureta tana gyara mishi gida da yi mishi girki.
In ya auro shuraihat kuma sai ya baje kolin soyayyarsa da ita aljana kuma ta zama maid dinsu dan ya tabbata shuraiha ko coffee bata iya dafawa ba.
Ni kam bayan nayi sallan magrib ne ina zaune ina lazimi yah musty ya shigo yace inje yah rid na kirana.
Tuni jikina ya fara zikiri adduan dai da na saba ita na kama a bakina na nufi side din ina nanata la'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntum minal zalimin............
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 12.
HAMEEDAN HAMMA BAN IYA SUNANKI NA GAYU BA😜 WANNAN SHAFIN NAKI NE KE KADAI KINA KOKARI KINA FARKAR DA MATA ALLAH YA BAR KAUNA DA FAHIMTAN JUNA TSAKANINKI DA HAMMANKI AMEEN.
***** ****** ******
Sallama nayi a hankali na tura kofar kaman wata mara gaskiya.
Tsaye na sameshi a tsakiyan palon hannunshi da cikin aljuhu dayan kuma rike da sigari.
Damnm gabana ya fadi jin warin abin da nafi tsana dauke tsayawa nayi a bakin kofan ina dan dauke numfashi amma duk da haka ina jin warin.
Ke dan ubanki nan zaki tsaya ko ni kike nufin inzo inda kike?
Da sauri na karasa na rufe hancina cikin dabara da hijab din jikina naje na zube a gabanshi nace barka da yamma yah.
Bai amsa ba sai cewa yayi uban me kike toshewa hanci?
Da sauri nace ba komi.
Ya kalleni kaman bai yarda ba sai yace toh bude hancin ko inci ubanki.
Da sauri na sauke hannuna Allah ya taimakeni zuka daya ya karayi wa tabanya kashe a ash tray.
Sannan ya kalleni yace shegiya ke bakya kallon kanki a mirror ne?
Nace ina kallo......
Toh meye na kara wani kwalliya banda shegen kyaun da kike da shi yarinya kaman aljana, Allah daga yau na kara ganin shegen fuskankin nan kaman na mayu da kwalliya sai na watsawa fuskar acid.
Uban me kike kallona da mayun idonkin nan kaman magnet haka dazu kika wani tsareni da shegun idanunki sai na kwakulesu ya fada yana rankwashi na.
Na dafe kaina ina zubar da kwalla kuma uban me kike yi da kudi naga kina cire kudi ba kakkautawa.
Tsuru tsuru nayi na rasa me zance.
Ba dake nake ba?
Mama ce fa take sani ina cirewa ina sayan kayan kwalliya.
Kayan kwalliyan ne aka cire mishi more than hundred thousands?
Nace ah ah an min register din make up classes an kuma sai min make up kit da kuma su cosmetic din amfanina.
Kan uba wai ke nake zuwa nemanwa kudin ne da za a barnatar min da kudi a banza,wallahi sai kij biyani a sannu.
Gabana ya fadi ni dame zan biyashi kaji shi sai wani ta da jijiyoyin wuya yake dama mama tace soja akwai mako.
Kuma gobe da safe ki min kunun gyada da kosai.
Dan zaro ido nayi nace yah.....
Pap ya buge min baki yace ni kike zarowa ido kaman zaki hadiyeni da shegun idanunkin nan.
Nace ah ah fa yah gobe muna da school kuma da sassafe muke tafiya bama dawo sai 4 ga islamiya.
Oho i dont bloody care gobe ni dai inga break fast kuma lunch kawai zan daga miki kafa amma dinner kam ba abin da ya dameni da gajiyanki ke da dare ma sinasir zanci.
Na bude baki zan yi magana yace kut wai ke yaushe na dawo sa'anki ne ina magana kina yi lallai kina so inci ubanki.
Wallahi kar ki bace min da shegen fuskan nan naki kaman na aljanu a nan ki ga in ban babbalaki ba.
Da gudu na bar dakin,a daren na wanke wake na ajiye ana sallan asuba na hau aikin break fast dinshi.
Allah ya taimakeni na gama da wuri har na shirya yusra tace wannan ai daukan hakkine ki gayawa mama wallahi.
Nace barshi shi da Allahn shi yanzu in na gayawa mama sai wani abin ya billo kyalleshi ni kam.
Haka da muka dawo sallah kawai muka yi na jika shinkafa na gayawa momy ta bada akai markade kafin in dawo tace zakiyya irin wannan wahala ki bari yaci abinci da kowa yake ci mana haba in ba zai ci wannan ba ki bari ladi ta mishi kafin ki dawo nace momy ba komi.
Ko da ya dawo momy tace mishi yace in bar wahalan da nake yi haka ga karatu ga dawainiyarsa.
Momy wallahi ba yanda ban yi da ita ta bari ba wai ah ah ita dai in barta wai lada ai take samu gwara ta saba tun yanzu.
Momy ta rike baki tace oh yaran zamani ita zakiyyan ma da ake ganin kunyan ta kenan.
Muna dawowa make up school na shiga ina tausayin kaina ban gama girkin ba sai past nine.
Ai ko na sha masifa da su rankwashi yace kuma in gyara mishi side din da daren ya fita ya barni.
Ban gama ba sai kusan goma da rabi a gajiye na shiga cikin gida ina tausayawa kaina.
Haka yah rid ya dinga wahalar dani saukinta ana fara jarabawa na dan samu sauki saboda ba sammako kuma wani sa'in ba mu da paper sai karatuna da ya nema shigawa hakki.
Haka ya gama hutunshi muna tsaka da exams ya tafi nan na samu sa'ida.
NIMA INA GA ZAN HUTA.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 13.
TAQABAL MINNA WA MIN KUM.
RUQAYYA ZUMA, AUNTY HALEE, MAMAN USUF, MAMAN GIMBIYA AND MOM ILHAM KAR KU WANI TAMBAYENI GORAN SALLAH WANNAN SHAFIN SERVES AS UR GORAN SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MANA.
******** ****** *****
Bayan mun kammala paper din mu na karshe a waec ne abba yace in shirya zan tafi hwol hutun tsakanin WAEC da NECO.
Tare da su yusra muka je nan aka sa nayi ta zaga dangi dan daga wannan zuwan baran kara zuwa ba sai aurena.
Har Bauchi sai da muka je sosai muka ji dadin tafiya ana saura kwana uku mu fara NECO muka dawo.
Sai da zamu dawo ne dada ta zaunar da ni ta min nasiha mai ratsa jiki sosai.
Ta nunar min da shi zaman aura dan hakuri ne duk zafin soyayyan da kuke yiwa juna sai kun yi haquri da juna zaku mori zaman ku.
Nayi matuqar farin ciki da nasihun dada na daura dammaran ko min rintsi zan zauna da yah rid in mishi biyayya ko domin in farantawa iyayyanmu dan naga ba karamin daukaka auranmu suka yi ba.
Mun dawo kano cike da kewa su Halima suna kewan yanayin garinmu da rayuwan kauye tare da mutuniyarsu salma.
Nawa bangaren kuma ina cike da kewa da alhini rashin ahalina a kusa dani.
Yusra kam na lura wani abu na so ya kullu tsakaninta da yah auwal dan shima yazo weekend ya samemu.
Tafiyan dadi muka yi kasancewan driver na ne yazo ya daukemu😜
Mun iso garin kano da wuri kowa sai murnan zuwanmu yake ba kaman mama dan ita ko kadan bata surkunta dani.
Mun fara exams gadan gadan Allah ya taimakeni ko sau daya yah rid bai zo ba dan dama ya kan dade bai zo ba.
Muna gama exams aka shiga shirye shiryen biki bridal shower muka fara yi in da na saka blue gown,ban sa goggoro ba.
Sai aka gyara min gashina ya zuba ta gefen fuskana aka yafa min wani yalolon yellow gyale.
Su yusra da sauran kawayenmu na sch kuma suka saka blue jeans da yellow din polo shirt.
Raguna biyu da kaji goma aka bankare mana sai su Drinks na yanka cake kasancewan mata kadai muka yi abin mu.
Da next day kuma akayi kamu washegari ranan laraba muka dai hanya tare da masu kai akwati zuwa hwol.
Ran alhamis muka yi fulani day da yan kauyenmu da kawayeemu da suka biyomu..
A daji muka yi sosai ya kayatar dan duk a cikin events din da muka yi yafi dadi.
Anyi chedde(rawan fulani) anyi dai shagali muka watse washegari friday dumbin jama'a suka zo suka sheda daurin auranmu.
A ranan ne kuma aka tafi dani kano inda aka cigaba da shagalgula sai a ranan na sa yah rid a idona da daddare da ya shigo dakin momy dan nan aka saukeni sai an gama biki akaini gidana.
Hade rai yayi dan baiyi tsamanin muna dakin ba ya juya ya fita.
Yayi kyau yayi haske,kasa dauke idona nayi akanshi har ya fita, zungurina Halima tayi tace dallah can meye na kallonshi sai ya rainaki ashe farida na jinmu tace eh mana kar ki nutsu ki kama kanki sai ya dinga dizgaki a cikin