Showing 48001 words to 50173 words out of 50173 words
gashi ba kullum sai ka dinga min ciki tun ban yaye yaro ba sai a ganni da wani cikin gashi yanzu ma an kuma."
Dariya ce ta kama shi duk da tsananin farin cikin da yake yi dan ya gane wani cikin ne dani bai hana shi tsokanata ba yace "toh laifina ne ni kadai? It takes two people ayi cikin nan ke d'in ce kullum buqatan ban ruwa kike da na dawo kike mak'ale ni ba dole kiyi ciki ba."
Haushi ne ya kamani ganin inda ya dosa juyawa nayi na fara tafiya ina cewa " toh wallahi ko a zubar da wannan ko kuna daga shi na gama haihuwa in ma zan k'ara haihuwar sai na gama makaranta."
A zuciyeya m'ike ya damk'oni juyo dani yayi ina fuskantarshi idanunshi sun yi ja saboda tsabagen b'acin rai nuna ni yayi da hannu kafin da kyar ya samu ya furta
"Wallahil azim kika yi min sanadin gudan jinina ko kika nemi yin tsarin iyali akan wani banzan karatunki sai na mugun sab'a miki kuma in datse d'an iskan karatun in ga yanda zaki yi"
Ya wurgar dani lokaci d'aya kuma ya taroni tunawa da yayi ina d'auke da ciki fita yayi a gidan gaba d'aya.
Ni kam wani tsoro ne ya kamani ganin ya koma min tsab yah rid d'in da na sani da lalubawa nayi na zauna ina dafe da kirjina,hawaye ma ya kafe a idanuna dan tun bayan shiryawan mu wannan shine karo na farko da yah rid yayi fushi dani haka har yake ja min layi.
Ranan bai shigo gidan ba sai da ya tabbata nayi bacci da ya fita sallahn asuba kuwa bai dawo ba har na tafi makaranta.
Fushi ya tsira sosai sai da na kwana uku ban sa shi a idona ba yammacin ranan ina zaune ya shigo ya wuceni ko kallo ban ishe shi ba.
Tashi nayi na bi bayanshi wani milk kalan yadi naga ya fito dashi mamaki ne ya kamani ko ina zashi da yamman nan.
Fitowanshi daga wankan ya katse min tunani na nufe da shagwaba na karb'i towel din hannunshi ina goge mishi ruwan jikinshi.
Zaunar dashi nayi na d'ane jikinshi na sak'ala hannaye na a wuyanshi cike da shagwab'a na fara magana" haayatee kasan wannan horon ya min tsauri pls kayi hak'uri ko mafarkin k'ara b'ata maka rai ba zan k'ara ba ka yafeni kaji mijina.
Ban bashi daman magana ba na had'e bakinmu ina mishi wani salon da na san ba zai iya resisting ba.
Ai kam tarkona ya kama dan dama na san 'yan kayana shi yasa yak'i yarda mu had'u ya san yanzu zan dawo dashi kan layi.
Ban barshi ranan ya taking lead ba ni na riding abina wanda hakan ya k'ara rikitar dashi.
Sai da muka nitsa ya samu daman yin magana "precious me yasa zaki nemi hana mu tara zuriya?"
Rufe bakinshi nayi da nawa sai da na tsotse shi na kusan mantar dashi maganan da muke yi na zare bakina nace " hayaatee ka daina tunaowa ranka na b'aci plsss na riga da na yi nadama baran k'ara wannan tunanin ba."
Ajiyan zuciya ya sauke tare da k'ara rungumoni da kyau ya matseni a jikinshi sai da na d'anyi k'ara yace " gobe ma ki k'ara" kiran sallan magrib ya sashi yin arghhhh precious kin hana ni zuwa zance har an kira magrib tashi zaune nayi nace " ayya ai ta makaro koma wacece ba magrib ba har isha ya kai mata"
Dariya yayi yace toh ai da naga kina k'in haihuwa ne shi yasa nayi tunanin in auro wanda zata zo tayi ta haihuwa amma Allah ya soki kin dawo sense dinki.
Dariya muka yi tare da tashi mu shiga bathroom.
_Jama'a ina labarin burin sadiq_ π€
SAWWAMA QAWWAMA.π
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: πBANI NAYI KAINA BAπ
By Sawwama A.
Page 49.
_Wannan shafin naki ne makwafin zakiyya sist maimunat(momy sultan) ke din zakiyya tayi gado wajen hali, you are a star daga ke ba dad'i_
Haihuwana yayi dai dai da samun promotion d'in yah rid murna a wajen mu ba a magana.
Takwara aka yiwa general yaro yaci suna Aliyu haidar inda me sunanshi ya mishi bajinta wajen bawa matar yaron former presdent wato *Tawakaltun salim* contract din tsara d'akin Aliyu da sauran yayunshi haka itama suka had'o nasu kayan barkan, *meenerl* d'in general kuwa gudunmawar had'in fulanin gembu ta kawo min dan in k'ara rikita oga sir kaman yanda tace.
Tunda nake haihuwata salma bata tab'a zuwa sai wannan karon kullum daga tace school sai tace extra lesson haka ko naje hwol ba yanda bana yi ta biyoni sai tace makaranta.
Wannan karon dai na taki sa'a tunda dai an gama makarantar ta zo.
Bayan suna da sati biyu ina zaune ina bawa hydar nono abubakar ne da farooq ke zaune suna shan cereal suma dawowansu kenan daga day care.
Salma ce ta shigo da gudu tana kuka ta wuce d'aki kafin inyi yunk'urin binta sai ga yah sadiq ma ya shigo yana k'wala kiran sunanta.
Hankali tashe ya juya ya fita ba tare da ya lura dani ba ko takwaranshi dake ta faman kiran uncle.
"ikon Allah" shine abin da nace kafin na tashi ina sab'e da hydar na nufi d'akin salman.
Tana kife a kan gado tana risgar kuka naje na zauna tare da dafata "k'anwata menene damuwanki, me ya had'aki da yah sadiq kike irin kukan nan?"
Tashi zaune tayi tana fuskantata tace " adda zakee yah sadiq ya kasa fahimtata nace mishi yayi hak'uri ba zan iya auranshi ba yak'i ganewa" ta k'ara rushewa da wani kukan tana fad'in nifa shi yasa ban k'aunan zuwa garin nan dan nan san takurani zai yi"
Ajiyar zuciya na sauke nace "wai tun dama kuna soyayya ne na tambayeki kika ce min ah ah?"
Girgiza kai tayi tace "ah ah ni bai tab'a cewa yana sona ba sai dai alamu da yake nuna min haka, ada nayi zaton haka sai da yazo yayi aure na cire wannan tunanin balle ma da naga bai kamata ace mun yi fadeela haka ba.
Gyad'a kai nayi nace ke dai ki dage da addua shine kawai mafita Allah shi ya san me yake nufi akan bayinsa.
Wasa wasa sadiq ya buwaye mu yazo ya tisa ni gaba ranan yana min magiyan in shawo mishi kan salma ya san tana son shi.
Ban b'oye mishi ba nace ni gaskiya ina jin kunyan fadeela wallahi.
Ranan na sha jarabar yah rid kaman ba gobe wai ina zuga k'anwata tak'i k'aninshi ni dai na bashi hak'uri na lallabashi amma kam ranan na ga jarfa me k'ani.
Washegari kuma sai ga fadeelan tazo rok'on mu wai ita dama can ta san da maganan tun kan ya aureta sai da ya gaya mata yana son salma kuma akwai lokacin da zai aureta in Allah yayi saboda haka ita ba komi wallahi in dan ita ne ba komi a ranta k'ila salman ce zata zo ta haihu musu tunda gata ita sai b'ari take.
Da kyar dai da sud'in goshi aka shawo kan salma ta yarda.
Wata biyu kawai aka saka ranansu muka sha biki bai ajiyeta a kano ba inda yake aiki ya kaita a abuja har cikin raina ban so hakan ba toh inda mijinta ya zab'an mata kenan na so ace gani ga k'anwata mu k'ara shakuwa da juna.
Ni kam dai sarkin haihuwa tare muka kuma haihuwa da salma wannan karon ma namij na haifa usman ana ce mishi nuraini salma ma namiji ta haifa aka samishi sunan yayah amma amir ake ce mishi.
Su fareeda sai mita suke su dai dan Allah in haifo musu mace me kama dani sai wani haifo maza nake masu kama da yah rid banda farina da suke d'aukowa.
Harara na b'alla musu nace tunda ga akuya ku me zai hana ku k'ara haihuwar? Ku barni da sojojina allah ya musu albarka suka ce amin.
Amma dai muna nan dawowa suna wani shekara cewar yusra da sauri nace sai dai a gidanki.
Dariya suka sa a tare suka ce bar cika baki kema ai kin san hakan ne.
Shiru na musu ban kulasu ba dan na k'ulu.
_
Saura final_
SAWWAMA QAWWAMAπ
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: πBANI NAYI KAINA BAπ
By Sawwama A.
Page 50 _final page_
_Wannan shafin naku ne_ _masoyana, masoyan_ *bani nayi kaina ba* _ina mik'a godiyata da jinjinata gareku_ _da kuka bini tun daga farkon littafin nan har izuwa k'arshen shi yau_.
_Ku d'in abin alfaharina ne kuma Ana mugun tare_.
Wannan karon Allah ya taimakeni sai da nuraini ya cika shekara na sami wani cikin.
Wanda ya mutuk'ar bani wahala ga zafin karatu ga na ciki har rok'on Allah nake ya tsayar min da haihuwar haka dan yarana akwai rashin ji musamman in mahaifinsu na nan.
Da cikin ya kai lokacin fitowarshi duniya doguwar nak'uda nayi sab'anin sauran haihuwata inda na haifi mace kyakyawa mai kama dani kamar dai nayi kaki.
Ranan yah rid murna yayi kaman ranan na fara haihuwa eto na bashi abinda yake muradine duk da ko sau d'aya bai tab'a nuna zak'uwarsa na son in haifi mace ba na san yana mutukar son in haifa mishi mace,toh amma dake mijina me ilimina yace shi ya san Allah ke bashi zaratan maza randa ya so zai bashi macen,in ma bai bashi macen ba alhamdulillah Allah ya albarkaci mazan dan wani neman namiji k'waya d'ayan ma yake bai samu ba.
Ni kam tunda na haihu nake aikin kuka tun ana tsamanin ko wani waje ke min ciwo,har aka faa sarewa da al-amarin tunda dai doctor tace lafiyata lau.
Yah rid ne zaune a bakin gadon da nake yana r'ike da jaririyar a hannunshi yayinda ya tsira min ido yana kalloj yanda nake kuka.
"Precious" ya kira sunana a hankali yayi d'an jim kafin ya cigaba "precious kiyiwa Allah ki fad'a min matsalarki, ko kyautar da Allah ya mana ne ba kya farin ciki da shi?"
Da sauri na girgiza kaina kafin nace "ah ah kawai ina tausayin d'iyata ce tunda ta kwaso kamannin kar ta tsinci kanta a halin da na tsinci kaina na k'iyayyar mijina"
Rintse ido yayi kafin ya bud'e su a kaina a take har sun canza kala sun koma ja.
A hankali ya furta "me yasa kika zab'i lokacin nan dan ki gaya min magana ko dan kinga nayi tsananin farin ciki da samun d'iya mace me kama dake ne zaki tuna min da na t'aba tsanan kamanninki eh na san akwai wannan lokacin da nayi wannan menene ribarki na rubbing min abinda na aikata to my face?"
"Kin manta ina da sani cewa dan adam bashi yayi kansa ba yanda na san *bani nayi kaina ba* haka nan kema ba ke kika yi kanki ba kuma itama ba ita tayi kanta ba dukkanmu d'an adam da wani halitta *Allah* shine wanda yayi mu."
Sauke ajiyan zuciya nayi nace " na gode Allah da ya ganar min da kai da dad'ewa Allah ya k'ara shiryar damu ya sa sauran mutane su daina kushe halittan d'an adam mumuna ko kyakyawa balle Allah baya halitan mumuna dole zaka ga akwai inda mutum yake da kyau,kyawun fuska ko jiki bashine kyau ba kaman kyan hali da zuciya suna kyan da ya kamata mu y'an adam mu gane."
"Haka ne precious Allah ya k'ara mana kyan zuciyoyi ya shiryi zuriyarmu ameen,"
ππππππππ
_Bayan shekara hudu_
Shigowata gidan kenan daga asibiti naje nayi round kasancewar yau lahadi.
Palour din nake karewa kallo yanda suka canza mishi tsari,kaina na girgiza cike da takaici.
Haka nan b'angaren dining anyi ciye ciyen su ice cream da chocolate ba bawon su nan an damalmala kan dining din.
Ko awa d'aya ban yi da fita ba sanin da nayi bazan dad'e bane yasa na barsu au kad'ai k'wafa nayi na wuce d'akin mazan inda nake da tabbacin suna can.
Abubakar na kwance kan gadonshi yana karatu yayinda sauran ke ta tsale tsalensu.
"Abubakar kai kam Allah yayi babban kawai ji yanda kuka min da gida to wallahi duk ku fito.
Wuri wuri suka fara yi da ido ban kulasu ba na fita suka biyoni rabawa kowa aikinshi nayi muka had'u muka gyara gidan.
Alawla na saka su suka d'auro nace to kowan nen su ya min sallah raka'a tamanin.
Abeer ce 'yar kimamin shekara 4 tabe baki kaman zata yi kukatace mimi nawa yayi yawa harara na b'alla mata nace lokacin da kika biye musu kuna wasan banza ai baki san yayi yawa ba.
Yammacin ranan ina kwance a kan grass carpet a backyard na saka bakin shade ina kallon sama.
.
Yayin da me gidan da yaran shi suke ta wasan su wai suna yaki da bindigar ruwa.
Ihunsu ne ya karad'e gidan gaba d'aya tashi zaune nayi ina kallon yanda suke dungure har da uban wai ana yak'i.
Sunkuyar da kai nayi ganin yanda abeer ke biye musu da ta fara k'ok'arin b'uya bayan daddynsu nuraini zai cabko jelan gashinta.
Yanzun ma abinda ya faru kenan daddy ya tsaya shari'a can kuma naga an had'a kai ana k'usk'us sai kuma aka nufo kaina a tare suka furta "mimi yunwa muke ji"
K'ok'arin mikewa na fara dan na san me suke shirin aikatawa.
Kafin in gudu sun fara jik'ani tuni na fara neman wajen b'uya suna bina suna jik'ani.
Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga All a (SWT) ya bani daman kammala wannan littafin fatana Allah yasa muyi amfanj da abinda muka karu da. Ameen.
Sai mun had'u a littafina na gaba *ribar biyayya*
SAWWAMA QAWWAMAπ