Showing 36001 words to 39000 words out of 50173 words
in ba zaki iya cewa ridwan ba kiyi shiru da bakinki.
Anki ayi shirun ance rulwanu rulwanu rulwanu kayi abinda zaka yi ta karasa tana zabga mishi harara.
Hade rai yayi yana ta kwafa ba kakkautawa ni kam mai zanyi banda dariya dan kullum draman su daya tana ce mishi rulwanu.
Zogalen ta zuba min tana ajiyewa gabana ya dauke yana fadin haka kawai ba za ki sa min mata amai ba.
Marairaice fuska nayi mace zanci
Kallona yayi da mamaki yace kin tabbata ba zai saki amai ba kuma ina yanzu kika gama cin masararki.
Na kara marairacewa nace ni dai zanci.
Hajiya ta cafe Allah ya miki albarka yar nan kin min maganin dan iyayi ko yaushe ka fara son nata ina ce a nan ka Dinga tijarar baka sonta.
Miko min plate din yayi yana fadin ungo kafin ta min tonan silili ni dai dariya kawai nake yi.
Ba karamin ci nayi ba dan har kari na nema hajiya sai tsiya take mishi bai kulata ba.
Kwance nake ina kallonshi yana ta hada kaya dan saura kwana 2 ya tafi ni kuma wata kasala nake ji shi yasa ban iya tashi na hada mishi ba.
Wayarshi ce tayi ringing ya dauka cike da ladabi dan daddy ne.
Ido na zuba mishi dan na ga wayar kaman na damuwa ne dan tuni ranshi ya baci ina ji yana fadin toh sai ta iso zata gaya min uban da ya aiketa.
Ajiye wayar yayi yana tsaki kallona yayi yace ki duba shegiyar yarinyan nan wai lagos state university ta cike ko gidan uwar wa zata zauna a lagos oho.
Gabana ne ya fadi dan na san yau in fareeda ta shiga hannunshi mai kwatanta sai ya shirya.
Tashi nayj zaune na dan dafa shi nace mijina calm down ba fa wani abu bane wai ita da yah auwal ne fa suje soyayya shine ta cike nan saboda kar tayi aure karatunta ya katse.
Soyayya kuma? Da auwal wani auwal? Auwal naku?
Na gyada kai ina murmushi toh shine baza su fada su bari manya su yanke hukunci ba zasu yi gaban kansu.
Nan dai na kwashe komi na fada mishi har da zuwan yaya.
Shiru yayi ya ciro waya ya kira daddy ya fada mishi.
Daddy yace ba komi tabbas yaya ya kirasu yana zuwa gobe Allah yayi zabin alheri kawai
Yah rid yace ameen daddy sauran ma duk su fito da miji haka nan baza su dinga sa mana ciwon kai ba.
Daddy yace hakan za ayi zanje in samu abbanku muyi magana.
Suka yi sallama rungumeshi nayi ina miahi godiya.
Yace da na miki me baza kayi wa fareeda komi ba ina
Girgiza kai yayi yace ai na rantse sai na taba lafiyarta.
Turo baki nayi nace ni dai ah ah wallahi ko kuma in tayi maka kuka.
Yace baza ayi haka ba ki bari ko rankwashinta inyi dafe kaina nayi dan tuna zafin rankwashinsh, amma gwara rankwashin da duka.
Nace toh shikenan da ta zo kuwa sai da ta sha rankwashi ya fita ya barmu tare.
Murna muka dinga yi.
A daren ranan ne kuma aka kira sauran aka ce kowacce ta fito da miji nan da wata biyu yan banza duk murna suka yi banda fadeela dan ta rasa ta ina zata faro.
Ta duba duk cikin masu sonta ba wanda ya kai yah rid kudi ko kyau da nagarta ba kuma zai yuwu zakiyya ta fita kyau sannan ta auri mijin da yafi nata ba dole sai dai ita ta fita ko su zama daya hakan na nufin sai dai ta auri yah rid kenan😱
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 40.
FADI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU.
Washegari yayah da wasu daga cikin baffaninmu suka zo nemawa yah auwal auran fareeda.
Bayan sun gama abinda ya kawosu yah rid ya kwasosu dan suzo suga gidana tunda yayah bai taba zuwa ba asalima tun baki ba wanda ya kara zuwa.
Sosai suka yi farin cikin ganin muhallina sun san kam Allah ya ban miji daya tamkar dubu.
Sauka na musu sosai suma basu gushe ba sai da suka kara min nasihohi kan zaman aure da hakurin zaman.
Suka nunar min ba a ko da yaushe mutum ke samun abinda yake so ba inyi hakuri da duk halin da zan tsinci kaina.
Allah baya taba barin bawa mumini face sai ya jarabeshi kana fita a wani jarabawan kana shiga wani ne fatan Allah ya bamu ikon cin dukkannin jarabawan da zai jarabce mu amin.
Siyayya sosai yah rid ya musu ya hadasu da mota da driver aka ma yar dasu.
Nima cikin kayan lefena na dibi zannuwa da kayan shafe shafe na bayar akaiwa salma.
Sun tafi sun barni da tunanin wani kalar jarabawa zan fada kuma yanzu tunda na kubuta daga na kin da mijina yake min.
Jikina ranan a mace na wuni har sai da yah rid ya zata wani abu ke damuna ban boye mishi ba na gaya mishi damuwata dan haka nan naji zuciyata na tsinkewa.
Kwantar da hankali yayi sosai yace Allah baya taba dorawa bawanshi abinda ba zai iya ba dan haka ki kwantar da hankalinki ki yawaita addua Allah zai saukaka mana koma menene dan ba abinda yafi karfin addua.
Gyada mishi kai nayi kawai ina sauke ajiyan zuciya.
Lokaci daya kaman wanda aka mintsina ya tashi tare da kamo hannuna yace i almost forget zo ki gani.
Car park muka nufa wata mota na gani a dunkule an rufeta.
Hannu ya yaye rufin me zan gani wata shegiyar middle picano ce army green baki na bude ina kallon motan dan kam ya tafi da imanina.
Na dade ina sha'awar motan saboda kankantar ta ba karamin kyau motan ke min ba.
Key din ya kada min a gaban fuskata kallonshi kawai nake yi kaman doluwa dan na rasa me ke faruwa a nan din.
Hannuna ya kamo ya damka min key din a hannuna murmushi kwance a fuskarshi.
Kallonshi nake da mamaki da kuma alaman tambaya.
Gira ya daga min tare da sa hannunshi ya zagayo kuguna ya hade jikinmu waje daya ya sunkuyo da kanshi ya dora goshinshi kan nawa numfashin mu na gauraya.
Cikin rada yace precious ban taba son wata irin yanda nake sonki ba ke din wata jigone na rayuwata bana jin zan iya hada sonki da na wata ko wani abunke din daban ce kina da matsayi mai girma a zuciyata da rayuwata zan iya karar da duk wani abu da na mallaka dan in samo miki farin ciki.
Kullum cikin godewa Allah nake da iyayena da suka min gata suka aura min ke.
Kyawawan halayenki da kyautatawanki a gareni ya dasa kaunarki a raina.
Duk da irin muzguna miki da nake yi dai dai da rana daya baki fasa hidimta min ba.
A lokacin da nake cikin tsananin buqata baki duba halina ba kika kawo min dauki baki barni na shiga halaka ba niko me zan miki in biyaki.
Babu sai dai in kyautata miki gorgodo in kuma faranta miki kaman yanda kike faranta min a ko da yaushe.
Ni Ridwan na miki alkawarin da sanina ina cikin hayacina bazan taba kuntata miki ko in bata miki rai ba sai dai ko cikin rashin sani which we cant escape amma zanyi kokarin kiyaye hakan ma.
Jan hanci nayi hawaye sun gagara tsayuwa a idona halshena ya min nauyi me nayi haka Allah ya azurta ni da miji me sona me son faranta min.
Ganin kalma daya ya gagara fitowa daga bakina kawai sai na sa hannu na rungumo shi tare da fashewa da wani matsanancin kuka.
Bubbuga bayana ya fara a hankali tare da fadin shshshhss is okey kukan na menene na fadi wani abu da ya bata miki raine.
Girgiza kaina nayi tare da dagowa daga kirjinshi hannu nasa na tallabo fuskarshi da kyar na samu na bude baki nace
Mijina ban san me zan ce maka ba godiya yayi kadan sai dai in kara ninka aduan da nake maka kullum.
Nima ina rokan Allah ya bani ikon faranta maka ya hanani saba maka nima na dau alqawarin bazan taba saba maka cikin sanina ba.
Yah ban san me zance ba kalamai sun kaura daga bakina alokacin da nake buqatansu amma inshaa Allah zaka gani a aikace.
Hannh yasa yana goge min fuska rungumenj yayi tsam a jikinshi mun dade a haka kafin a hankali yace ba zaki shiga motarki bane ko bata miki ba a canzo?
Tsalle na daka sai da ya rukoni nace a camzo me baka san yanda nake son motan nan bane baka ji nace maka kalamai sun min kaura bane
Dariya yayi yace toh shine zaki barar min da baby dan kina murnan mota.
Nima dariyan nayi ina shiga cikin motan.
******* *****- ******
Ko wata ba a rufe ba maneman yusra da halima suka fito sameer ke neman halima ita kuma yusra wani dan makocin mu ne adnan canji dan canji ne.
Duk an karbi kudinsu fadeela kawai ake jira a sa ranan amma an gaya musu in aka tashi sa ranan ba zai haura sati uku ba.
Duk mun fara zuwa school fareeda ce kawai bata fara ba ita take zaune da ni a gidana.
Allah ya taimakeni cikin ba me sa ciwo bane sai dan banzan sani cin abu busashe busashe ko doya zan soya ko dankali sai yayi kayayau nake iya ci.
Shirya shiryan biki muke tayi duk da ba a sa rana ba mun san ba za a dade ba.
Wata biyu da aka debarwa fadeela ya cika.
Zaune take a gaban su abba da hajiya.
Abba ne yayi gyaran murya yace fadeeela kina da sanin lokacin da muka deban muku ya cika har sauran yan uwanki sun turo da maneman su tun kafin lokacin amma ke shiru.
Bayan ba wai rasa maneman kika yi ba saboda haka muna son jin ta bakinki.
Shiru tayi tana saka ta ina zata fara.
Daddy ne ya daka mata tsawa ba dake ake yi ba kin yi wa mutane shiru ko akwai sa'an ki anan?
Da sauri ta girgiza kai hajiya tace toh muna sauraronki.
Wiki wiki ta fara yi da ido ta dubi abban dan ta san bata isa ta kalli dadday da maganar da ke bakinta ba.
A hankali tace abba ni dai ya ridwan nake so shi yasa na kasa fitar da kowa.
Salati daddy da hajiya suka sa abba yayi murmushi tare da fadin mashaa Allah abu yayi kyau.
Daddy yayi saurin cewa haba abba me kake fada mutum da matarsa duk yaushe ridwan din yayi aure da za a bijiro mishi da wani magana.
Hajiya tace ai kuwa dai fadeela baki kyautawa kawarki ba ki rasa wanda zaki ce kina so sai rulwanu.
Abba dai murmushi yake tayi a tausashe yace ni ban ga aibin wannan abun ba ridwan dai namiji ne mijin mace hudu kuma yana da halin da zai iya ajiye mata hudu sannan kuna maganan yaushe yayi aure ina wadanda suke auran mata biyu a rana daya su kuma ace me?
Daddy yace abba baka fahimceni ba da farko mun ba ridwan mata ba tare da yana so ba ya amsheta hannu bibbiyu yau ko da ridwan zai kara aure nan kusa a barshi ya zabi matarsa wannan yarinya munafurci ne kawai yasa ta fadin haka me yasa tun da bata taba fada ba ya wurga mata wata uwar harara.
Kau da kai tayi gabanta na faduwa wani bangaren kuma dadi ne fal ranta ko ba komi abba na bayanta ta san kaman anyi an gama zakiyya zata gane kuranta.
Abba ne yace tashi ki shiga bayan ta shigene.
Ya juyo ya duskancesu yace ridwan bashi ya haifemu ba ba kuma shi yake da iko damu ba yanda ya karbi wancan baya sonta ya zo ya kaunaceta daga baya haka zai so wannan din ma balle ga soyayyan yan uwantaka a ransu.
Hajiya kam ta kasa magana takaici ya kumeta sam bata son nuna kinta akan auren saboda yanda shi daddy yayi kawaici ya nuna kin auran.
Baza ta so ta fifita dan wani a cikin a ya'yanta ba Allah yayi zabi shine kalmar da tace
Abba ne ya dubi daddy yace ka kira maneman sauran yaran su kawo kayan sa rana nan da sati uku za ayi biki.
Yayi wa hajiya sallama ya tafi.
Ina kitchen ina soya wainar rogo naji an rungumeni ta baya kamshinshi ya sanr mjn shine.
Da sauri na jiyo tare da kankameshi ina mamakin yaushe ya dawo dan bamu dade da gama video call ba baice min yana hanya ba kuma banga alamun haka ba.
Shafa kanshi ya fara yana dariya ganin kallon tuhuman da nake mishi.
Dariya yayi yace wallahi nima ban san zan zo ba.
Hararanshi nayi da wasa na juya na cigaba da abinda nake yi
Juyo dani yayi ya wani langwabe cike da shagwaba yace Allah da gaske abba ne ya kirani wai yana nemana kuma daman ina kewar matata da babyna.
Ya tsuguna are dasa guiwowinshi a kasa ya rungumo cikina.
Kanshi na shafa ina murmushi dago kai yayi da damuwa a fuskanshi yace precious four months amma yaki ya fara showing ba kya son cin abinci ko.
Kwalo ido nayi nace baby baka ga abincin da nake ci bane shi yasa.
Mikewa tsaye yayi yace ba wani nan baga irin abincin da kike ci na ya fada yana yatsina fuska.
Murmushi nayi nace laifin wa? Babynka ke son irin abincin ai da baka ga ina yin irin wannan din ba.
Tabe baki yayi yace muje inyi wanka in je inji kiran da abba ke min dan gabana sai faduwa yake yi shi yasa na kasa hakuri na biyo flight.
Har mun kai kofa na juyo nace barin kashe gas ina zuwa karasa fita yayi ni kuma na koma farida ce ta fito daga store tana sauke ajiyan zuciya.
Ni na manta shal tare muke a kitchen din ta shiga dauko indomie ta dafawa kanta.
Kallonta nayi da mamaki nace ke kuma fa indomie din ne ya rikeki harara ta balla min tace eh yanxu ai da baya kusa dake kiniya tuno da naje dauko indomie.
Nace sorry kar kiga laifina dan in yah rid na nan mantawa nake da komi da kowa toh ke me ya hanaki fitowa.
Wani hararan na samu tace yah rid din na soyewa zan fito in sami rabin rankwashi wancan da ya min sai da nayi ciwon kai duk da ban damu ba tunda gashi zan auri hubbyna yar isakan yarinyan can ke bata mana lokaci.
Dariya nayi nace ina ruwan fadeela kika sani ko tsayawa tayi ta zaba ta dirje duk sai ta kawo wanda yafi ku.
Tabe baki tayi tace ita sani fita nayi na koma wajen mijina.
Sai da muka soye yayi wanka yaci indomie kafin in mishi girki kafin ya daeo daga kiran abba.
Allah jishe mu alkahiri😂😂🤣🤣🤣
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
by Sawwama A.
Page 41.
NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GA DUK WATA MAMALLAKIYAR SUNAN ZAINAB INA MUTUKAR KAUNARKU INA DARAJA MASU SUNA ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKU.
Bayan tafiyan yah rid fareeda ma ta tattara komatsan ta tace tayi gida kuma sai ya tafi.
Wajen mama ya fara shiga inda ya tarar da ita zaune tayi shiru kallonshi tayi cike da tausayawa dan ta san dan nata ya kamu da son matarshi yanzu ga wata sabuwar magana za a daga mishi hankali.
Tayi iya kokarinta dan fahimtar da abba sam ya gagara fahimta da ta matsa da maganan sai cewa yayi ta kaunaci bare amma tana kin yar dan uwanshi dole taja bakinta tayi shiru.
Kallonta yayi cike da kulawa ganin kaman tana cikin wani yanayi take faduwar gabanshi ta tsananta.
A kidime ya fara tambayanta mamah lafiya me yake faruwa??
Ajiyan zuciya ta sauke tace ba komi ridwan Allah maka albarka yanda kake jajircewa wajen yi mana biyayya kaima Allah yasa ya'yanka suyi maka fin haka.
Amin ya amsa amma zuciyarshi na gaya mishi wani babban al-amari na shirin faruwa da shi.
Kai dai yanda ka saba yi mana biyayya ka cigaba inshaa Allahu akwai ranan da zaka ci RIBAR BIYAYYA(littafina na gaba).
Haka tayi ta mishi nasihohi mai sanyaya jiki haka da ya shiga wajen momy ma duk sun daure mishi kai.
Tare da momy suka tafi wurin abba inda suka tarar da mamah a can
Nan ya gama yankewa kanshi tabbas wannan kiran akwai rudani sai dai yayi mamaki da bai ga daddy ba Allah dai yada lafiyarsa lau.
Bangaren daddy kin zuwa yayi dan yace baza a muzgunawa ridwan dashi ba sai cewa abba yayi yana da uzuri dariya kawai abban yayi dan ya san zuwa ne baya son yi.
Gyaran murya abba yayi kafin yace ridwan da farko ina mai yaba maka saboda kasancewarka da mai biyayya.
Na biyu ina mai neman alfarma a gareka.
Da sauri yace haba abba wani irin alfarma kai fa ka haifeni ce min zaka yi aikata ni kuma in aikata matsawar bai kaucewa shari'a ba.
Jinjina kai abba yayi yace ridwan auranka na farko umarni muka baka wannan na biyun alfarma nake nema ka auri yar uwarka fadeela.
Tunda abba ya fara magana komi nashi ya tsaya cak yawun bakinshi.ya kafe da kyar ya tattaro sauran ragowan hadiye.
Bai san lokacin da ya furta abba kayi hakuri ina son matata ban dauki fadila a komi ba face matsayinta na kanwa abba wallahi bana sonta.
Zaka sota kaman yanda kaso zakiyya ai itama baka sonta aka aura maka ita yanzu ba gashi kuna zamanku lafiya ba.
Abba..... Abba.... Abba dafa shi abban yayi yace yi shiru ridwan tashi kaje Allah yayi maka albarka ni zan dau dawainiyar komi tunda har ka amince na da yan sati uku ne bikin Allah ya muku albarka.
Mikewa yayi kanshi na wani irin sarawa da kyar ya kai kanshi side dinshi na gidan key din motanshi ya lalubo dan key din na jiki ya bude ya shiga.
Dakin duk yayi kura cikin kuran ya shiga ya hau gadon ya kwanta .
Meke shirin faruwa da rayuwansu shi da precious me yasa abba ke mishi haka sai kace shi kadai ne namiji a zuriyar innalillahi.
Ta ina zai fara fadawa precious wannan maganan gashi lokacin a kure the last thing he want shine daga mata hankali a condition din nan nata.
Bam ta banko kofar tare da juyo da yar uwarta me nake ji haka fadeela me kika aikata?
Wato ke baza ki taba barin rayuwar zakiyya ba ko me zakiyya ta miki ne haka ki rasa wanda zaki aura sai mijinta ta karasa tana hawaye.
Murmushin rainin hankali fadilan tayi tace lallai tambayata kike me zakiyya ta min ko yanda kike behaving kadai ya isa yasa in tsani zakiyya ke yar uwata ce ta haihuwa amma kin fifita zakiyya a kaina.
Yanzu akan zakiyya iyayena haushina suke ji duk saboda zakiyya.
Kina wani maganan