Showing 12001 words to 15000 words out of 50173 words

Chapter 5 - Bani Nayi Kaina Ba Book 1 Hausa Novel Complete

11 Dec 2024

337

mutane irin su fadila su sami daman ci miki fuska.

Na sauke ajiyan zuciya nace Allah ya sa in iya daurewa dan ni kaina bam san me zuciyata ke shirin dauko min ba,zuciyata na son kaini inda yafi karfina.


Ba abinda yafi karfin Allah just keep on praying cewan fareeda.


Washegari parade akayi da yamma hade da dinner ya hade fuskar shi tamau sai ya kara kyau da kwarjini.

Abin ya kayatar gwanin kyau fulaninmu sai tsorata suke idan aka harba bindiga🤣🤣🤣

A Daren ranan aka sada ni da gidana ba wanda ya kwana na sha kuka har na gode Allah.

A haka har bacci ya daukeni ba duriyar ango daman ban saka aka ba inji mai satar hula.

Na sani sashin da nake ba zai kalla ba. Da na tashi wankana nayi na yi kwalliyata mai kyau na fito a amarya ta.

Wajen goma su yusra suka kawo mana break fast ko minti sha biyar ba su yi ba duk yanda na so su zauna sam suka ki.

Abinci naci na koma dakina ina zaune bakin gado ina karewa akwatina guda bakwai da suke jere kallo ina tunanin ta inda zan fara saukewa in kalli kayan dan na san ba karamin nauyine dasu ba.

Dan bana manta ranan da mamah ta tisashi a gaba ya bawa aunty rabi kudin lefen.

Tana zaune a gabanta yayiwa aunty rabi transfer 1.7 million a hado yana ta kunkuno tace taji kuma ya bada dubu dari uku kudin fitar biki.

Sai da yayi ta million biyu dai ranan.


Burum naji an shigo min daki a fusace yana sanye da 3 kwata da vest na kamu ya hada fuskan nan tamau.

Tsaye na mike sai kuma na zube kasa ina gaishe shi.

Malama ba wannan ya kawoni ba tashi zaki yi ki min break uban wa kika ajiye da zai min abin karyawa?


Cikin rawa murya nace yah an kawo abinci daga cikin gida.


Ko a gidan abincin uban wa nake ci oh kina ce kinzo zaman hutu ne to bari kiji ba aiki daya da na dauke miki acikin ayukan da kike min da sai ma wanda ya karu..

Shegiya ji yanda take wani piki piki da shegun mayun idontan nan toh kurwata kur mayya kawai kin tashi kinje kin sama min abin da zanci ne ko kuwa.


Da gudu na fita daga dakin na shiga kitchen na soya mishi dankali da plantain da kwai.

A palour na sameshi yana kallon ball naje na dan tsuguna nesa kadan nace yah na shirya table din sai da ya gama shan kamshin shi ya juya yace min and so? Get out of my sight my frnd.

Cikin rawar jiki na mike har na kai kofan passage yace ke zo nan me ma kika dafa min.

Na juyo cikin faduwar gaba nace chips and plantain.

Bashi nake da ra'ayin ci ba kije ki dafa min indomie da kayan lambu sai boiled eggs.

Nace toh na nufi kitchen din ina tsaka da aikin ya kwala min kira na ajiye naje.

Ki saka min serdine sannan ki dama min oat nace toh na koma ina aikin ina tunanin irin rayuwan da zanyi da bawan Allahn nan.

Naci alwashin zan mishi duk wani irin bauta da zai sa ni tunda dai na san ibada nake yi.

Ai kuwa yah rid made sure he made my life miserable dan cikin kwanankin nan kullum sai an kawo mana abinci daga gida amma hakan baya hanawa yah ridwan ya saka ni dafa mishi abinci kala kala.

Kuma ya hana kowa zuwa wajena ranan da muka yi kwana shida yah samir da yah ibrahim suka zo.

Ina kitchen ina girki naji yah ridwan na fada musu irin fushin da shraihat tayi.

Yah sameer yace toh sai me ka kyaleta kawai.

Hararanshi yayi yace in kyaleta fa kace toh wallahi ba don kar su abba su ci min mutunci ba da na tsufa a Europe amma gobe karfe 4 ne flight dina

A tare suka cewa zuwa Europe din?

Ya hada rai yace eh ai gwara inje in rarasheta ta san ni ba wai son auran nake ba me zanyi da wancan aljanar yarinyan.

Yah Ibrahim yace Allah ya kyauta amin.

Haka kawai na tsinci kaina da yin hawaye wannan wani irin wulakanci ne.




SAWWAMA QAWWAMA

💖BANI NAYI KAINA BA💖


By Sawwama A.



Page 14.

TAQABAL MINNA WA MINKUM.

GORON SALLAH

THIS PAGE IS HIGHLY DEDICATED TO U MY LOVELY FANS ALLAH YA BAR KAUNA




Dogon numfashi na ajiye lokacin da na dawo daga dogon tunanina.


Na yankewa kaina ko yah rid ya dawo na gama shiga harkarshi ai BANI NAYI KAINA BA da zai sani a gaba.

Allahn da yayi ni shi yaso ya ganni haka.

Ban kuma san yana son wata shuraiha ha sai naga ya dawo gidan nan tare da ita a matsayin matarsa.


***********

Karan sigari ne a hannun shi yana zagaye dakin shi na sovi barrack da yake garin ilori.

Yau kwanan shi uku da dawowa image din abin da ya gani ya kasa barin kwakwalwanshi.

Wani zuka yayiwa sigarin sai da ya kare tas ya kashe a ash tray tare da kara kunna wani.

Runtse ido yayi ya kuma budewa da sauri dan da ya rufe ido babu wanda yake gani sai shuraiha akan wani katon bature tana riding dinshi.


Yayi kwana da yini a jirgi zuwa Europe dan ya ganta amma me da yaje sai idon shi ya mishi mugun gani.

Lokacin da isa Europe har ya dau waya zai kirata ya ga zai ruining surprise din gwara ya karasa kawai.

Apartment dinta ya nufa ya hau lifter zuwa samanta.

Har ya daura hannu ya knocking kofan sau daya ba a ansa ba har zai kuma sai ya tuna inda take ajiye spare key dinta.

Tuni ya lalubo ya bude tun daga sa kafanshi a palon ihun nishinsu da surutansu ya sanar da shi abin da ake aikatawa.

Zuciyarshi taki yardan mishi wai shuraihan shi ke aikata masha'a the innocent shuraihat he knew.

Cikin bedroom din ya nufa inda ya tarar da shuraiha na sukuwa akan bature tana surutan dadi na dirty talk.

Shi kuma saurayin nata yana rike mazaunanta yana fadin come on baby ride the shit out of me come on oh yeahhhhh🙊🙈

Bai san lokacin da ya kwala kiran sunanta ba a firgice ta dirka akan baturen tana zazzare ido.

Gadan gadan ya nufeta har ya sa hannu zai shako wuyanta sai ya fasa yayi wani shegen murmushi.


You what alhamdulillah na godewa Allah da ban debi sauran turawa na kai gidana ba.

Wallahi ban kasance mazinaci ba na sani Allah ba zai hadani da mazinaciya ba.

Ba abinda zan miki kije Allah kika yiwa laifi bani ba dan dai da da aurena na kamaki haka wallahil azim ba abinda zai hanani bindigeku.

Ki manta kin taba sanin wani Ridwan a rayuwar,ina nan ina kokarin Ganin na mallakeki ashe ke kina nan kina mallakawa wasu jikinki toh ba dani ba.

Ya juyo ya fita ya barta kaman an dasata a wajen.

Kwananshi biyu a garin ya kamo hanya ya dawo direct wajen aiki ya wuce.

Shi kam sha'anin mata ya tsorata shi shuraihat kenan da ba wani kyaun kirki ne da ita ba tana bin maza.

Ina ga wancan aljanar yarinya na tabbata ko bata bisu ba su zasu bita.

Da kuwa na ci ubansu ya fada a fili.

Shi yanzu ya zai ne ma lokaci kara tafiya yake buqatata kara qaruwa yake.

Shuraihat din da nake tunanin zan aura ko bata tare ba zan dinga sauke buqatata akanta ga yanda ya kasance.

Wata zuciyar tace mishi ba ga mata an aura maka ba.


No no no no haba ta ina zan fara tunkarar aljanar nan da buqatata salon ta rainani.

Hade giranshi yayi yana tunanin mafita.


Fans sai ku sama mishi mafita😝😜





SAWWAMA QAWWAMA

💖BANI NAYI KAINA BA💖



By Sawwama A.



Page 15.

Yau kam na tashi zuciyata wasai saboda na riki al Qur'ani da sallahn dare harkokina kawai nake yi har wata yar kiba nayi.


Yau su yusra ne suka zo min yini aiko munsha hira sai sakalcinmu muke yi.


Mu dafa wannan mu kwaba wancan mu jika wancan mu dai sha'anin mu kawai muke yi ba mai kwaban mu.

Fareeda ce tana kwaba iloka tace kai gidan kai akwai dadi anya nima ba auran nan zanyi ba.

Duk muka sa dariya Halima tace kayi son ranka ba mai hanaka in ka dama ka kwana da yunwa ba ruwan wani.

Mussaman ma in mijin matafiyi ne irin su yah rid,ai ba karamin haushin hanamu tayaki kwana da yah rid da momy suka yi ba ta fadi hakan tana kallona.

Farida tace toh ai sanin halinmu in mun hadu ya sa aka hanamu.

Yusra tace yau kuma sai mun fanshe ba muka sa dariya ni dai binsu kawai nake da ido ina murmushi dan wani dadi nake ji ina tare da yan uwana.

Karan bude gate da shigowan motoci muka ji dukkanmu zaro ido muka yi a tare muka furta Allah yasa ba yah Rid bane..

Da gudu muka nufi window din palo ai kuwa shine da sojoji sun kai takwas.

Da sauri muka fara tattare palon muna jera pillows din kujerun sai dibi dibi muke yi.

Murda kofan da akayi aka shigo ne ya samu tsayawa da abinda muke yi.

Duk munyi cirko cirko da kaganmu ka ga rashin gaskiya.

Kallon mu yayi daya bayan daya ya hade rai ya kalli yusra yace ku dan ubanku bana ce kar kuzo min gida ba uwar kuka zo yi??

Duk muka yi tsuru tsuru dan ubanku ba da ku nake yi ba ya daka mana wani uban tsawa.

Da sauri Halima tace mamah ce fa tace muzo mu duba zakiyya ya take.

Da kuka zo kunga an yanyankata? Shegu munafukai kawai.

Ke kuma.mayya uwar me kika gaya musu ya juyo kaina yana tambayata.

Cikin in ina da rawar murya kaina na kasa nace ba komi.

Yace atoh dan ni dai iya sanina ba abinda na miki a gidan nan in ma suna tunanin yanka ki nake yi.

Ni ba a zo dubani ko ba da aka hadani da aljana sai ke yahi kwafa ya wuce daki.

Muna cikin sauke ajiyan zuciya ya kwala min kira abin dariya duk sai muka firgice.

Da sauri na isa dakinshi ina adduan Allah yasa ba wani abu ya gani ba dai dai ba dan ko da safen nan na karkade dakin.

Ina shiga ya wurga min harara kasa kasa naji yace mayya kawai gyaran murya yayi yace malama abinci zaki dafa min yanzu.

Sannan ki dafa na kimanin mutun goma kuma dan tare nake da mutane.

Nace toh har na tashi zan fita yace zo nan na sallameki ne rankwashi ya kafa min me shegen zafi.

Yace nace miki na gama ne ko na gaya miki abincin da zaki dafa min.

Nayi shiru idona na kawo ruwa.

Yarinya ai baki yi hawaye ba tunda kika sake kika auri Ridwan.

Ni tuwon alkama zaki min su kuma sauran sakwara kina jina SAKWARA nace ya fadi haka yana zare ido shi kanshi ya san ya hada ni da aiki.

Nace toh sannan ya sallameni na fita a kitchen na sami su farida suna tattare shirmenmu.

Ni wallahi har na manta wai sunzo da sauri suka karaso wurina.

Halima ce ta cire hannuna dake bisa kaina dan har lokacin ina dafe da inda ya rankwasheni.

Yusra tace hala ya rankwasheki? Hawayena ne suka basu ansa.

Lallashina suka yi sannan na basu labarin yanda muka yi.

Kut yah kasheki yake so yayi ya tsufar dake da wuri wadancan kartin yake so ya saki yi musu girki da dare ya mukurkusheki da rana ya saki bauta tab.
Cewar yusra

Hararenta nayi nace ya mukurkushe wa?

Dukkansu suka dauka laaaaaahhhh haba biri yayi kama da mutum.


Ni dai ban ce musu komi na fara aikina su ma suka hannu nan da nan muka gama sakwaran ma na leda muka tuka suka tayani muka gyara gidan tsaf.


Dakina muka shiga muka zube a gado farida ce ta dan dago tace zakiyya kin san me duk abin da yah Rid yake miki kina da laifi.

Tashi nayi zaune ina kallonta da mamaki laifin me kuwa?

Tace good tana mikewa zaune suma sauran suka mike dan sun san halinta akwai lecture

Laifinki shine baki dauki shawara ko daya da muka baki ba na tabbata kin cigaba da yawo a cikin hijabi kaman yanda kika saba.

Ina ji su auntu shema da aunty rabi suka baki shawarwari bana jin kinyi amfani da ko daya.

Ke bari kiji so nake ki fighting abu biyu ki kwato yancinki a cikin gidan nan su abba basu muku aure danku rabu wata rana ba.

So kiyi kokarin dai daita gidan auranki.

Numfashi na sauke na ce me zan fighting hajiya farida murmushi tayi tana karkada ido.

Halima ta daka mata duka tace shegiya uwar mata zata fara manyancen.

Hmmm so nake ki fighting TSORO da KUNYA bance ki zama mara kunya ba kunya ai ado ne akwai inda zai miki amfani amma ba yanzu ba.

Na san ba yanda za ayi tashi daya ki cire tsoron yahRid a ranki nuna mishi kawai zaki yi ba tsoron amma bai san yana nan cike pal a ranki ba.

Kunya kuma ajiyeshi zaki yi ki daina yawo da hijabi ko manyan kaya a gidanki ga dinkuna an miki fitinannu ga uban english wears da aunty rabi ta jibga miki.

Rikitashi da halittun da Allah ya miki yake kushewa show him what he is missing out ki dinga fishar hankalinshi ki kuma dinga nunawa kaman ba danshi kika yi ba kina yi ne on ur own.


Daura towel dai dai cinya ki fito wanka ki nufi kitchen a guje kaman kin daura abu kina tsoron kar ya kone in kin tabbatar yana palo.

Saka riga mai budadden kirji kije bashi ruwa ko wani abu..........

Haka suka hadu suka ta ban shawara suka sassaka ni groups na whatsapp.


Suna shirin tafiya ya leko dakin ya korashi wai sun cika mishi kunne da hayaniya shi hutu yazo ba jin hayaniyarsu ba.

Ajiyan zuciya na sauke tare da kudurta niyyan zanyi amfani da shawarwarin da suka bani in gani.









SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖



By Sawwama A.




Page 16





Bayan tafiyansu farida yah Rid ya kirani ya fada min ga nan sojoji ya kawo biyu zasuyi gadin gate in zan fita zan fita da biyu sannan biyu masu tsabtace compound din gidan da zuwa aika.


Shi duk a tashi hikimar in ya kewayeni da yaranshi bazan bi maza ba ya manta yaran nashi maza ne yazo ya cika gida da maza a hikimarsa ta hana yaduwar zina bai san in mazinaciyarce ba a cikin yaranshi ma sai ta ci amanarsa.


Washegari da safe bayan na gama gyare gyare na da girke girke dan yace har suma ni zan dinga musu girki dan bakin mugunta.


Na fito wanka ina daure da towel ya banko kofar ya shigo naga alaman rashin sallama a inda nake al adarsa ce dan baya sona da zaman lafiya balle ya nema min.

Dan kura min ido yayi sai kuma ya kau da kai yana hadiye yawu😜 na gane hakan ne ganin yanda Adams apple dinshi ke sama yana kasa.

Dakewa yayi ya min magana cikin sarkewan murya duk yanda ya so ya kaurara murya abin ya faskara muryarshi sai da ta nuna halin da yake ciki.

Ki shirya zamuje cikin gida abinda ya furta kenan yayi hanyan waje karo na farko kenan da ya min magana ba da tsawa muna mu biyun mu.


Da gangan nayi kaman santsin tiles zai ka dani na dan sake towel dina yayi kasa na tallafe rabin nonona suka bayyana


Wayyo shine abinda na furta a kidime, da sauri ya juyo a lokacin na dafe dressing mirror gesture din da nayi ya sa towel din kaina kuncewa gashina ya zubo ya rufe idona.

Rintse ido yayi tare da dan kama gabanshi saboda yanda yaji ya harba tashi daya.

Cikin sassarfa ya bar dakin tun kafin zuciyarshi ta sashi aikata abinda zai zo yaji kunya.

Bai taba tunanin yarinyan ta mallaki diri haka ba dan shi yawancin lokuta a cikin zumbula zumbulan riguna yake ganinta ga shegen sa hijab.


Shegiyar yarinya ga kyan fuska ga na jiki a fili ya furta ALJANA kawai wallahi bazan bari ta rikita min lisafi ba.

Duk laifinane da ban knocking kofan ba kafin in shiga da ban ga abinda zai dameni ba.

Haka ya ta sambatunshi shi kadai yana shiryawa, manyan kaya ya saka light blue shada anyi mata karamin dinki ya dauko navy blue din hula ya kafa tare da sa navy blue din takalmi ya daura agogon fata shima navy blue sosai yayi kyau ya haska abinshi.


Yana fitowa ya sameni a zaune a palo ina jiranshi dan ko sukunin yin breakfast ban samu ba saboda doki.

Kura min ido yayi a zuciyarshi yake fadin wai wannan wata irin aljanar yarinya ne wai bata san tana da kyau bane zata wani sha wannan adon.


Sanye take da jan gown yar dubai me fararen stones a jere a gaban rigar da hannun rigar sai ta rollong farin veil ta saka farin heel ga jakarta fara.


Kun san jan abu da daukan ido balle an hadashi da fari kuma a jikin farar mace ai ba a magana ga fuskarta ta sha light make up.

Ajiyan zuciya ya sauke ya nufi table ya zauna da sauri na karasa na serving mishi abinci na hada mishi tea.

Na koma palo na zauna yana daga dining area yana cin abinci idonshi na kaina.

Tsakuran abincin yake duk dadinshi amma zuciyarsa daci take mishi dan ya san duk inda suka gifta sai an kuma kallonta.

Tsaki ya dan ja zuciyarshi na mishi zafi shi yasa fa shi baya son mace mai kyau dan Allah ya gani yana da tsananin kishi.

Wani tsakin ya kuma ja a ranshi yace toh ai ita wannan ba sonta nake ba balle inyi kishinta kawai ona kishin aurane dake kanta ne.


Ke jeki kiyi shigar da kika saba baki da aure ma hijab kike sakawa balle yanzu da aurena dan kin rainani ko kin tashi ko yaya.


Ina zumbure zumbure na mike nayi hanyan danki
Kut ni kike turawa baki da sauri na girgiza kai.

Kwafa yayi yace kar ki wuce wallahi kika bata min lokaci tafiya zanyi abuna.


Da sauri na shige naje na saka riga da skirt din atamfa na daura hijab dai dai guiwa a kai.

Da na fito kallona yayi ya kau da kai yace shegiya ko ya tayi sai tayi kyau.

Dan zaro idona nayi dan naji abin da yace sai ma ya ban dariya.

Ko da muka je bakin mota tsayuwa nayi dan ban san ina zan shiga ba ko bayan da ya saba sani in shiga zan shiga ko yaya oho.

Ganin ya shige yayi shiru ni yake jira ya sa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login