Showing 6001 words to 9000 words out of 50173 words
daga tsugunan da nake.
Uban me kika tsaya yi kuma wai ke baki san yanda na tsani ganin fuskanki bane wallahi har mafarki nake yi kuma ni tsoro kike bani ki tashi ki fitar min a daki mayya kawai mai suffan aljanu.
Tafiya nayi ina tunanin ya suffan aljannun yake ko ya taba ganine oho shi dai bashi da kalman dangantani da aljanu da mayu dan tsaki naja na shige dakinmu.
Sai magrib duk yan gidan suka dawo da masu suna da masu islamiya.
SAWWAMAN QAWWAMAN😘😎
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 7.
Ridwan zaune gaban iyayenshi maza da hajiya kakarshi kasancewar kakansu namiji ya rasu.
Gyara murya daddy yayi yace Ridwan a matsayinmu na iyayenka baza mu danne maka hakkinka ba muna so ka gaya mana ko kana da wacce kake so dan ka san mun daga maka kafa ba dan kadan ba.
Yanzu shekarunka 34 zuwa da biyar ba aure a matsayinka na lafiyayen namiji ko baka da lafiya ne bamu sani ba?
Ya dan sunkuyar da kai yana murmushi yace ni daddy lafiyata kalau asalima ina da yarinyan da nake so tana karatu ne a Europe shekaran can ta fara dama ina so in muku magana kuje a sami iyayenta duk da babanta yace sai ta gama tukun za ayi auran a cewarta.
Tunda ya fara magana duk suka kura mishi ido ba kaman hajiya da take ji kaman ta tashi ta mangareshi wai tana kasar turai kuma ma sai ta gama.
Tace kai rilwanu wai kai kam yarone da shekara ishirin ko kuwa mtsw ta ja tsaki tayi shiru dan ta san tana iya ci mishi uwa yanzu.
Abba ne yace toh nan da shekara nawa zata gama makarantan?
Kara lankwashe kafa yayi cike da kwarin guiwa ganin abba da kanshi ne ya mishi wannan tambayan yace eh toh nan da shekaru biyu dan ta sami mtsala a shekarar farko.
Abba ya gyada kai yace zuwa lokacin kuma an nada ka shugaban gauraye ko to ba zai yuwu ba ba a zuriyarmu ba.
Hajiya aka gyada kai aka ce tabbas kam ba a zuriyan nan ba rulwanu ba kai bane shugabanmu.
Daddy yace ba zamu hanaka auran zabinka ba amma kam muna da sharadi...... Ya zuba mishi ido.
Shi kam ridwan hadiye wani yawu mai kauri yayi wanda yasa adams apple dinshi yin sama da kasa yana tunanin menene kuma.
Daddy ya cigaba da cewa sharadinmu ba wani mai wuya bane wanda dama ko da ace ita yarinyan da make so din a shirye suke toh muma sai ka bi namu ra'ayin ka auri yarinyan da muka tanada maka tun da dadewa.
Wani gumi ne ya keto mishi aure kuma? Wata yarinya kuma innalillahi.
Abba yace saboda haka tunda su wadan can ba a shirye suke ba sai a fara wannan in yaso ran da suka shirya ka aurota dan ko bamu da wannan nufin baza mu zuba maka ido kana zaune ba aure ba,in ba dai ba wata ta'asar kake aikatawa ba.
Saboda haka ka shirya nan da wata uku kana da mata dan mun riga munje mun sami mahaifinta an tsai da magana suna rubuta jarabawan gama secondary za a yi bikin ku.
Kaje ka kaiwa rabee kudi ta hada maka kayan akwati dan ba mai yi maka auran gata kana da kudinka ba zai yuwu mu baka mata mu hada ma da kaya ba haka kasa ayi gyara a gidanka kasa komi tunda dai an dade ana neman kudin nan sai a fito dasu a kashe. Cewan abba.
Shi dai gyada kai kawai yake kaman kadangare wai shi of all people za ayi wa aure wai da karamar yarinya ma yar secondary.
Hajiya ce tace tunda abin ma yar gida ce sai ka shirya yau kaje dakin uwarka hira.
Dammm a gida kuma wa kenan fadeela ko fareeda dan dai sune yam mata kuma yan secondary a zuriyarsu waro ido yayi da ya tuno abba yace sun gama magana da mahaifin yarinyan innalillahi Allah yasa ba aljanar can bane.
Daddy ne ya dawo da shi daga tunanin da yake yana fadin kai dai Allah ya maka albarka ai kai kayi dace da mata sai aduan zama lafiya kawai.
Hajiya tace ai zakiyya kam akwai hankali ga kyau ga kyan hali.
La haula wala quwata shine abinda ya fada a cikin ranshi dan bai iya wargi gaban iyayenshi.
Sallaman shi suka yi inda suka zauna da mahaifiyarsu suna shawara kaman yanda suka saba.
Bai so hakan ba so yayi da sun tafi ya fara saukewa wannan tsohuwar kwandon masifarshi.
Motarsa ya fisga yayi can bayan gari cikin awa biyu yasha kwalin taba daya da rabi, shi kadai sai huci yake lallai suna son daukan gawar yar su.
Wayarsa ce tayi ringing ganin mai kiran yayi dan tsaki shi kwata kwata ma ya manta da batun wai itama zata shiga tashin hankali in taji labarin nan.
Kin dauka yayi dan baya normal zai iya hucewa kanta.
Bai koma gidan ba sai taran dare ni kam a lokacin ina kwance ina hawaye dan dawowata daga Palon abba inda ya shaida min abinda suka yanke akan mu ni da ya Ridwan tare da shaida min da yaddan yayah suka yanke hakan.
Ni ba kukan kin auran nake ba kukan tausayin kaina nake su abba basu san irin tsanan da ya rid ya min bane da basu hada wannan abin ba.
Su yusra sun min tambayan duniya na kasa basu ansa toh me ma zance musu su abba zasu min aure bana so ai ko da na cika butulu.
Da suka lura bazan basu ansa ba sai suka kama lallashina sanin halina na zurfin ciki.
Gam aka banko kofar dakin mu ya ridwan ne ya shigo idon nan nashi yayi ja tuni jikinmu ya kama karkarwa ba ma kaman ni da na san mai ya kawoshi.
Wani kallo ya watsawa su haleema ba shiri suka mike suka fita nima nayi kokarin mikewa wani uban tsawa da ya daka min ne ya sa naji marata ta kulle da fitsari tuni na zauna tare da matsa kafata.
Kallona yayi sosai yace good da alama ke da kanki kin fara kukan makokinki daga yanzu kam ki fara irga kwanakin jin dadinki dan sun kusa karewa muddin kika kuskura kika amincewa auran nan.
Ke da kanki kin san irin tsanar da nayiwa fuskarki dama ke kanki gaba daya banda su abba yar ficiciya dake suke shirin aura min for what suna ganin zaki iya daukan buqatuna ne.
Yarinya bar ganin kina da nonuwa da duwaiwaka ba anan abin yake ba mtsw matsalar kenan ke din yarinyace i dont knw how to explain to u.
Ni dai ina shawartarki da kije ki gaya musu ba kyasona ba kya son aurena na tabbata ba zasu miki dole ba.
Baki kawai na sake ina tunanin irin wannan rashin kunyan shi ya dage sai zaro zance ya ke.
Ke dan ubanki ni tsaranki ne da zaki tsareni da shegun idanuwanki mai kama da na mayu Allah ya sawwake ni in hada zuriya da ke ki haifa min nasu siffofin aljanu shegiya mayya gwara ki sakarwa iyayena kurwa in ba haka ba wallahi inci ubanki ya kafa min rankwashi ya fice kaman kububuwa dan ko lura da su yusra dake tsaye a gefen kofanmu bai yi ba.
Da sauri suka shigo dakin haleema tace yanzu dama kukan da kike yi kenan tun dazu? Lallai dole kiyi kuka duk wanda aka hada da auran yaya ridwan ko da yana son mutum ya banu balle ke da ya tsana.
Yusra tace ni na rasa mai zakiya tayiwa yah rid da yake mata tsanan nan duk wacce ya sami mace irin zakiyya ya more.
Na share hawayen da ya zubo min da bayan hannuna nace toh ai inda matsalar take kenan siffata ce baya so yace na fiye kyau da yawa kyauna yayi yawan da baya burge mutane wai kaman aljanu dama haka aljanu suke na karasa fadan hkan tare da rushewa da wani kukan.
Yusra ta goge min hawaye tace kiyi hakuri duk tsanani na tare da sauki Allah zai kawo miki dauki mu dage da addua kawai..
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 8.
ASSALAM NAJI KORAFINKU A KAN TYPING ZA A DUBA INSHAA ALLAH.
Ranan kam bacci bai ga ido na ba kwana nayi sallah ina neman zabin Allah washegari da zazzabi na tashi Allah ya sa weekend ne
Mama ne ta zaunar dani bayan ta ban tea na sha tace zakiyya ki gaya min tsakani da Allah kina son auran nan ko ba kya so.
Na dan sunkuyar da kaina ina matsa hannuna nace mama ba wai auran ne bana so ba.......
Yayanku ne ba kya so kenan na girgiza kai nace ah ah mama ni tsoro nake ji
Mama tayi murmushi tace ki daina tsoro na fahimci abinda kike ma tsoron yayanku kam.tabbas wani irin murdadan mutum ne amma ai ke ya macece wacce ta mallaki komai da duk wata ya mace ke buri.
Kina da kyau kina da ilimi both arabi da boko kina da hali mai nagarta.
Wallahi ina mai tabbatar miki in kika yi amfani da wadannan qualities din naki sai kin juya Ridwan a nan din nan ta nuna tsakiyan hannunta amma fa sai kin dage da addua .
Nace toh mama na gode tace yauwa yata yi maza ki shanye shayin kafin yazo ku tafi asibiti.
Na dago a razane mama ta dan harare ni tace zaki fara haljn naki na tsoro ko ta fadi hakan tana danna nombobinshi .
Assalamu alaika lafiya maza ka zo yanzu zan aike ka.
Ta kashe wayar ba ayi minti goma ba ya shigo cikin bakin wandon jeans da navy blue din shirt.
Tsugunawa yayi ya kara gaisheta nima na gaisheshi ya amsa yana hararata kasa kasa.
Mama na lura da shi tayi kaman bata gani ba tace zakiyya ce ba lafiya ka dauketa ka kaita a duba ta.
Mama ni kuma duk yawan yaran gidan nan nine zan kaita asibiti? Haba mama dan Allah.
Gidan ku nace kaci gidanku ni ban san da yawan yaran gidan bane ko duk yawansu sune zasu aureta ba kai ba dole ka fara sauke hakkokinta dake kanka.
Yace toh mama ni nace ina sonta ko ni nace a mana aure ni dai gaskiya mama za a takurani me zanyi da wannan abar.
Innalillahi Rid ni kake gayawa baka son zabin mu toh kaje ka samu ubanka ka fada mishi bani marainiyar wayonka ba.
Kuma dolenka da gidanku ka kaita asibiti ba asibiti ba har makaranta kai zaka dinga kaita da duk inda za taje in ba dai so kake ka nunawa duniya ban isa da kai bane.
Zube guiwowinshi yayi a kasa yace mama na tuba kin isa da ni har kin yi yawa zan yi yanda kuka ce fushinki masifa ce a gareni.
Ni ban yi fushi da kai ba amma muddin ka nemi ketara maganarmu ina dab da yin fushi da kai.
Mama hakan ma ba zai faru ba in dai daga gare ni ne ke ki sameni a mota,mama ki samin albarka.
Allah ya muku albarka gaba daya tare da iyalin naka.
Runtse ido yayi yana mai jin zafin kiran zakiyya da iyalinshi da tayi amin yace a takaice ya tashi ya fita.
Ta juyo gareni tace yi maza kije ki dan gyara fuskarki kadan ki daina zama ba kwalliya ai in kana da kyau ka kara da wanka.
Tashi nayi na nufi dakin mu dan kintsewa kaman yanda mama tace a lokaci daya kuma zuciyata na lugude.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 9.
A daki na samu yusra na waya da fadeela kan maganan hadinmu da yah Rid.
Powder kawai na shafa na sa mai a baki na fita ina ta nanata la' illah ha'illah anta subhanaka inni kuntum minal zalimin.
A cikin mota na same shi a parking space kafarsa daya a waje daya a ciki sai cika yake yana batsewa tsayuwa nayi jikin motan na rasa yanda zanyi.
Wani uban tsawa ya daka min malam in baza ki shiga ba ki kama hanyarki kiyi wucewan ki yara sai shegen raini ni wallahi babbala mutum zanyi ya fadi hakan yana kwatantawa da hannunshi.
Da sauri na bude gidan gaba na shiga wani harara ya balla min kafin ya kafa min wani azababben rankwashi.
S
Dafe kaina nayi cike da azaba yayinda ruwan hawaye ya cika min ido da alama in aka kaiwa yah rid ni zai burma min kai da rankwashi.
Uban me kike kallo da shegun idanunkin nan wallahi kurwata kur gwara ma ki sake min iyaye kuma kije kice musu ke ba kya sona baza ki aure ni ba ina ba haka ba sai kin gwammaci mutuwarki shegiya.
Kuma wallahi bari kiji yanda kika sa uwata tace sai na dinga miki hidima haka kema sai kin min danni ba jakkin gidanku bane ba za kuma ki hadani da uwata ba.
Daga yau din nan gyaran part dina da girkin abincin da zan ci ke zaki min kuma wallahi kika min mara dadi inci ubanki aljana kawai
Sunkuyar da kai nayi hawaye na sauka a kumatu na yana diga a cinyata.
Kawai sai naji an dago habata cike da kulawa ya sa wani hanky mai kamshi yana goge min hawaye yana min wani rikitatan kallo.
Kadan mamaki bai kasheni ba me ke damun kwakwalwan yah Rid? Abba na hango zai shiga motarsa nan na gano dalilin kulawar.
Har abban zai shiga motarsa sai ya fito ya dan kwankwasa glass din side din ya rid.
Bala'i nan naga munafurcin namiji sai ya wani nuna alamun firgita da sauri ya sake habana yayi saurin sauke glass din.
Abba ne yace ridwan mai ke faruwa ne naga zakiyya na kuka ba dai wani abu ka mata ba?
Dan sosa kanshi yayi yace abba wallahi wai ba ta da lafiya ne shine zan kaita hospital shine fa take kuka wai ita bata son allura.
Ashsha sannu zakiyya ai gwara kuje asibitin ai zama da ciwo ba dadi kuyi maza ku tafi, Allah ya sauwake ameen.
Ya ja motar muka kama hanyan hospital ina mamakin shu'umancin yah rid Allah ka fitar dani.
Mun danyi nisa kadan duk inda muka wuce ana kallonmu gefen titi yayi parking yace fitar min a mota.
Dammm gabana ya ba da nace ki fitar min a mota ko malama ki koma baya danni bazan dinga tafiya dake ana bina da kallo ba haba kowa sai ya jinjina min daukan aljana a motata.
A hankali na sauka na koma baya(abin dariya in bai dauki aljana ba ai ya zama driver din aljana🤣🤣)
A haka muka isa asibitin aka min test aka ban magani dan mugunta sai cewa yayi a min allura,duk tsoron allura na haka na daure aka min hawayene kawai yake zubo min.
Haka muka kara dawowa ina bayan mota sai da muka kusan isa gida yasa na dawo gaba.
Lokacin da muka shiga gate yana waya da sauri na fita a motar da naga hankalinshi ba ya kaina nayi cikin gida da sauri.
Ina shiga na sami su fadeela sun zo wani mugun kallo na ga tana bina da shi ni dai bance wa kowa komi ba naje na hau gadona na kwanta.
Fareeda ce tace hmm hajiya zakiyya ko aunty zakiyya zance ya jikin
Da sauki na fada a takaice.
Banko kofarmu aka yi ya shigo ya wula min ledan magunguna na yace ba dai kin mai dani sa'anki ba zanci ubanki ne.
Ya fice wani shewa naji fadeela ta sa tace ah dadinta ba isa a mana fi'ili ba duk kyaun mutum bashi da farin jini a wani wajen.
Dukkanmu bawanda ya kulata,haka ta gama hargaginta ta fice ko meye hujjanta oho.
Haka yah rid ya gama hutunshi kullum shi yake kaini makarantan boko ya kaini islamiya kuma ba ranan Allahn da ba zai ci ubana ba.
Ni kuma gyaran part dinshi da girkinsa ni nake yi haka zai lissafo min abinci kala kala kuma yace sai nayi.
Su mama sai murna suke ya sakko ya rumgumi zabinsu,su yusra ma har an canza min suna daga matan yah rid ko auntynmu.
Ni kadai na san azabtuwar da nake a hannunshi tun ma wai ba a daura mana aure an barni daga ni sai shi ba kenan.
Dan mugunta haka zai labta min under wear dinshi yace in wanke a toilet wani sa'in har da kayansa ga washing machine ga komi amma haka zai sani wanki in dauraye in ajiye a toilet din.
Da zai koma mamah tace sam sai dai ya kira daya daga cikin sojojinshi ya ajiye 407 din shi a dinga kaini school a ciki.
Sunkuyar da kai yayi yace haba mama kina son bata yarinyan nan ta cigaba da bin motan gida mana in ina nan ba sai in kai ta ba.
Ah ah sam ni ban yarda ba sojojin nan dai an baka su a wajen aikinka ka dau daya ka bata yana mata hidima kuma ka sa a bude mata acct kasa mata kudi dan ka san yanzu bambancinta da matarka kadan ne.
Haka yana ji yana gani ya mata dukkan abin da mama ta zayyano yana kudurta irin ci mata uwa da zai yi dan yayi alqawarin mutuqar aka bata mishi akanta sai ya mata ninkinsa.......
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 10.
Nan da nan na dawo big gal duk inda zani da driver na ga kudi da mama ke sani kashewa ta canza min mai da su turare.
Tuni kyauna ya kara fitowa da haskena gashina kam har wani sulbi ya kara yi.
Wajen koyan kwalliya mama ta min register tasa aka kawo min make up kit na 50,000 haba ai sai su yusra suka ce suma sai an musu register.
Tasa aka musu make up kit kuma tace su tambayi yayansu ai ba wacce ta iya sai yah sadiq suka tambaya yace zai sayawa mutum biyu na 20 20 thousand in yaso ya ibrahim ya sayawa sauran biyun haka ko akayi.
Sai kumbure kumbure suke yi wai nawa yafi girma da kaya momy tace toh ai ni amarya ce.
Fadila kam ai kaman ta hadiyeni sai habaice habaice take jefana da shi wai na zo zan mallake musu dangi da asirin mu na fulani.
In banda rashin hankali na bafulatanin kauye ina ke ina yah rid yar kauyan kayayau da ke.
Halima tace wai ke fadila meye matsalarki ne meye naki dan ta auri yah rid iyayenmu sun ga dacewan hakane amma duk in bi dagawa mutane hankali.
Dalla banza mara kishin dan uwa tsakani da Allah in auran hadi ake so ayi da wa yafi dacewa a hada yaya gani ga farida amma a rasa da wanda aka yi tunanin hada shi da ita sai BARE yar