Showing 39001 words to 42000 words out of 50173 words
zan aure mata miji naga dai dan uwana ne ita bare ma ta sameshi balle ni.
Girgiza kai fareeda tayi kawai ta furta Allah ya shiryeki a hankali ta fita.
Cikin daga sauti tace ameen in har zuci ne.
Bangarena ganin har 11:30 ba alamun yah rid ba wayarsa hankalina yayi mugun tashi sai lokacin na fara jin tsoron kiran da abban ya mishi.
Allah dai yasa lafiya dan nayi ta gwada number dinshi a kashe.
Tashi daya hadari ya hadu ruwa ya kece hankalina ya kuma tashi wayar mama na kira nace mata yah bai dawo ba har yanzu itama hankalinta a tashe ta nufi side din abba duk da ba ita bace da shi
Hango motanshi tayi hakan ya tabbatar mata yana gidan dakinshi ta nufa nan ta sameshi.
Tace haba sojana ba a san soja da ragwantaka ba kabi ka tadawa kanka hankali tare da matarka ka manta yanayin da take cikine.
A firgice ya mike yana duba lokaci ya kalli maman a sanyaye yace mama ban san me zance mata ba.
Kar kace mata komi gobe ka kawo min ita ni zan fahimtar da ita ai zakiyya yar albarka ce zaka sha mamakinta kai dai kayi kokarin danna damuwarka tashi ka tafi gidanka dare yayi hankalinta ya tashi.
A sukwane ya mike ya mata sallama ya fita.
SAWWAMA QAWWAMA
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
42.
KU GAFARCENI NAJI NA SHIRU JIYA I WAS CARRIED AWAY BAN TASHI FARGAWA BA SAI WAJEN 12am.
Gudu yake ba kakkautawa ga ruwa da ake tsulawa titi yayi tsantsi hakan ya bawa tayoyin motan daman gogar titin kaman ana ja.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida saboda irin gudun fitar hankalin da yake yi.
Horn yake dannawa kaman wanda aka koro a gigice sojojin suka bude mishi gate suna al-ajabin me ya fusata uban gidan nasu.
Yana karasowa bakin kofan palon na bude kofa a jike yake jagab dan fitowan da yayi daga car park zuwa kofar palon ne ya jike saboda ruwan da ake tsulawa.
Taranshi nayi ina tunanin me ke damun mijina haka.
Da karfi ya hade jikin mu ya min wani irin matsa da yasa ni zaro idanuna waje.
Dan patting bayanshi nayi duk da ban san meke damunshi ba hakan bai hanani lallashinshi ba.
Shhshh is okey cire kayan nan kar sanyi ya kama min kai na fadi hakan ina zamewa tare da balle botin din rigarsa.
A nan na cire mishi kayan ya rage i sai boxers janshi nayi zuwa dakinshi muka wuce toilet.
Taimaka mishi nayi yayi wanka na dakko abinci na feeding dinshi kaman yaro.
Shi kam ba abinda yake in ba kallonta ba,suna zamansu cikin aminci ana neman kawo musu fitina.
Bathroom na kuma kaishi muka yi brush ban matsa mishi da son jin meke damunshi ba tunda dai na san mahaifinshi ya kirashi kuma ba zai cutar dashi ba beside tsakanin da da mahaifi sai Allah ni yar kallo ce duk lokacin da yaso in san matsalar shi zai fada min.
Precious....
Dago kai nayi ina kallonshi da murmushi a fuskata nace na'am mijin precious.
Shima murmushin yayi yace na gode.
Gira daya na daga nace da akayi me.
Na gode da kulawarki a gareni Allah ya miki albarka.
Amin na ansa.
Precious, nace hummm.
Ki yafe min zan miki babban laifi wanda ko a mafarki ban taba tunanin zan aikata miki haka ba.
Da sauri na dago kaina nace me kake fada yah rid wani irin laifi kuma.
Rintse ido yayi yace ba zan iya yi miki shiru in barki a duhu ba har sai gobe precious abba na so in auri fadeela nan da sati uku.
Ido na kura mishi ba tare da ina gane me nake kallo ba dan Wani duhu duhu na fara gani kaina na wani jujjuyawa me nake ji ko dai mafarki nake yi.
Dan jijigata yayi yace babe dawo hankalin ki wallahi bana sonta ban son auranta ban san me zanyi ba ina cikin tashin hankali.
Hannu yasa ya riko fuskata ban san lokacin da na buge hannun ba idona yayi ja dan wani irin tukuki zuciyata yake yi.
Ya Allahu pls kar ki min haka ki fahimceni ke kadai zuciyata ke so da ke kadai nake burin kammala rayuwata ya kara kokarin kai hannu jikina.
Wani karfine ya zo min na dira daga kan gadon nace kar ka kara gigin tabani hmmm nayi murmushi nace zaka auri yar uwarka kake fada min ko na girgiza kai kwalla na cika idona dan na rasa da wata kalma zanyi amfani dan ina iya fadan mara kyau.
A hankali na furta me yasa suka aura maka ni tunda ga farko sun san zasu aura maka yar uwarka.
Me yasa basu bari na auri wani cikin dimbin masoya na ba suka aura maka ni alhalin sun san zasu baka yarsu girgiza kai na kuma yi hawayen dake mamale a idona ya zubo.
Right ni banda gata bani da zabi saboda mu ba wasu bane tallafawa rayuwata aka yi.
Da farko an daurawa wanda baya sona aure dani na ci wuyarsa sai yanzu da na samu soyayyarsa nake ganin zan samu kulawarsa nafi ko wace mace sa'a a dai dai wannan gaban ne za a aura masa wata.
Kallonta kawai yake dan bai taba ganinta a cikin wannan yanayin ba katse mishi tunani tayi da fadin wai kai baka da zabi ne a rayuwarka especially rayuwarka ta aure sai yanda aka tsara maka?
Biyota yace zakiyya kar kishi da bacin rai ya saki furta abinda zakiyi da na sani ki fahimceni ki fahimci iyayyenmu basu taba kinki ba asalima sun san da fadeelan suka yi kwadayin hadamu aure fadila ce kawai da fitina ta taso da wannan maganan a yanzu.
Right fadeela ta sha cewan ban dace da rayuwarka ba ko mai yasa oho kaima ka san ban dace da rayuwarka ba ko.
Tausayi ta bashi sosai ganin yanda take kaman sabuwar kamu duk maganganun da take a nutse take yi sai da yayi kokarin kusanto kanshi da ita a lokacin ne ta bude murya tana fadin nace kar ka matso kusa dani.
Ture bedside lamp din nayi lokaci daya na dire guiwowina akasa ina wani irin kuka me cin rai dan tabbas an gama da rayuwata.
Matsowa yayi ahankali ya rumgumeni tun ina turje turje har na hakura saboda irin rikon da ya min.
Kuka nake sosai ina surututai da ni kaina ban san mai nake fada ba a takaice daren ranan ba wanda ya runtsa a cikinmu.
Da safe ko kallo bai isheni ba dan gani nake shima munafuki ne ai bai nuna kin auran kaman yanda ya nuna kin aurena ba ko dan ita yar uwarshi ce oho.
A daddare yace mata ta shirya mama tace tana nemanta dan shi wani shakkanta yake ji dan bai taba ganin ta hada rai haka ba.
Ba wanda ya karya cikin mu dan ko kitchen din ban leka ba muka nufi cikin gida.
Ko a mota ba mai kula wani shi tsoron yi mata magana yake ita kuma dama a sama taje jiran kadan take.
Zaune nake gaban momy tana fahimtar dani makasudin auran tare da min nasiha kuka nake tukuru amma zuciyata ta dan sanyaya dan tabbas alamu sun nuna ba kowa ke son auran ba dan kam ko da mama bata furta ba fuskan ya nuna baro baro bata son auran.
Ita taje gaya min irin tashin hankalin da yah rid ya shiga da akayi mishi maganan auran take nadama da tausayin mijina suka shigeni.
Kunyarshi ce ta kamani yanda na rufe ido nayi ta mishi rashin kunya jiya Allah sarki yah rid zan tayaka yiwa iyayyenmu biyayya and i will support you in every aspect.
KUYI HAKURI DA WANNAN ZUWA DARE.
.
SAWWAMA QAWWAM
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 43.
Lekowa dakin yayi jikinshi duk a sanyaye ganin tana bacci a kan gadon mamah ya sa shi sakin ajiyar zuciya.
Tun da ya kawota ya fita wajen sameer yanzu ma ya zo ya mata sallama ne dan jirgin karfe shida zai bi.
A hankali ya karaso ya zauna a bakin gadon innocent face dinta ya kurawa ido yanda bakin zara zaran eye lashes dinta ke kwance.
Bakinta ya kalla dan tsut dashi a cune murmushi ya saki ba tare da ya shiryawa hakan ba babban yatsarsa yasa yana shafan leban.
Da sauri ya janye hannunshi ganin ta motsa the last thing je want shine fada da precious dinshi kafin ya tafi ya gwamace ya tafi bai mata sallama ba.
Allah ka huci zuciyar baiwarkan nan bai daddara ba ya kai hannunshi kan fuskanta yana shafawa a hankali.
Murmushi tayi a cikin barcin shima murmushin yayi ya sunkuyo a sumbaci bakinta kafin ya furta i love you dearly my flying squirrel.
Hannu yasa ya daga rigarta ya dora hannusa a flat tommy dinta kaman bata da komi lokaci daya ya tuna da fadeela yar lukuta ko makaho ba zai comparing matarsa da wannan kundumar yarinyan ba🤣
Sumbatar cibiyarta yayi ya mike dan ganin lokaci na tafiya.
Yana fitowa daga bedroom din mama na shigowa dan kallonta yayi yace mamah ni zan wuce anjima mustapha ya mayar da ita gida.
Tace bara ta kwana ba girgiza kai ya dan yi yace tana da makaranta gobe ko da shike ba da safe take da lectures ba ta kwana kawai sai goben ni bari in wuce lokaci na kurewa.
Toh Allah ya kiyayye ya tsare sai nan da sati biyun kenan?
Yace sai in Allah ya kaimu ni na wuce.
Toh Allah ya tsare yayi albarka ya bada abinda aka je nema.
Amin ya furta kafin ya fita mustapha ya kai shi airport.
Ban farka ba sai da ana kiran sallar magrib da ciwon kai na farka alawla nayi na gabatar da la'asar da magrib.
Mama ce ta shigo dauke da tray da sauri na tashi na karba tace kin dai samu kin yi sallah gyada kai nayi nace eh ina wasa da yatsuna.
Hannun ta kamo tace diyata ki kwantar da hankalinki kinji kinga condition din da kike duk da dama ni na san baza ki ban kunya ba.
Gyada kai nayi nace inshaa Allahu mama zan kiyayye ba zan dinga daga hankalina ba.
Yauwa yar albarka Allah ya miki Albarka ridwan din ya wuce ai kina bacci kici abinci kije wajen yan uwanki kuyi hira.
Toh nace mata kawai ina mamakin yah rid wato tafiya yayi bai min sallama ba.
Wayata na dauka bayan mama ta fita na danna number dinshi.
Bugu daya biyu yayi ya picking amma sai yayi shiru.
Danna zuciyata nayi na saki murmushi mai sauti nace ba dai fushi mijina keyi dani ba? Dan Allah ya rufa min asiri ya daina fushi dani kar Allah ya kamani.
Ajiyan zuciya ya saki lokaci da ya furta zakiiiiiyyyyyaaaaa i really miss you.
A hankali nima nace i miss you more my hub dan Allah ka yafe min bazan kara ba.
No no no baby ni zaki yafewa ke akayiwa laifi ai ni bana fushi dake.
Cikin shagwaba nace kayi mana bayan ka tafi ko sallama har ma da wani ce min zakiyya ba precious ba.
Dariyan jin dadi yayi ganin zakiyyarsa ta saki ranta.
Hiran soyayyan mu muka sha yana kara kwantar min da hankali nima ina kara mishi kwarin guiwar yiwa abba biyayya ko ba komai daddy ya wuci a kyamaci yarsa.
Shi dai sai dai yace anya zan iya precious.
Zaka iya in Allah ya yarda you are doing it for daddy not her.
Haka dai muka yi sallama yana ta wani turturjewa.
Sallahn isha nayi na tafi dakinmu na da su yusra na zaune ko wacce da waya a makale.
Lokaci daya duk suka yi sallama da samarin nasu suka zubo min ido cike da tausayawa.
Hararansu nayi nace meye haka kallon kuma na meye.
Halima ce ta rikoni ta zaunar dani tace zakiyya kwata kwata bamu san me zamu ce miki duk bamu da masaniya kan abinda fadeela ke shiryawa.
Murmushi nayi me ciwo nace toh meye kuma na damuwa ba dai ya rid bane gata ga shi ai.
Ba tare da na shirya ba na fashe da kuka tare da rufe fuskata da tafukan hannuna.
Kuka nayi me isata suna lallashina fuskata cike da hawaye nace me nayiwa fadila haka duk mazan duniyan nan ta rasa wamda zata so sai mijina.
Yusra a lokacin da nake murnan na samo kan yah rid a lokacin ne tayi sha'awar tarwatsa farin cikina? Duk akan me? Wannan kyaun da nake dashi fa BANI NAYI KAINA BA fa Allah ne yayi ni haka da zata dau kahon zuka ta kafa min.
Rungumeni suka yi suna tayani hawayen yusra tace saukin abin daya yah ba son auran yake ba bata sani ba kanta take shirin muzgunawa dan tabbas yah rid sai yaci mata uwa.
Girgiza kai nayi nace kun manta ne nima da haka muka fara kun manta yah rid ya kini ya nuna min tsana ne daga baya yazo ya soni???
Toh haka itama zai so ta watakila ma fiye da yanda yake sona tunda ita yar uwarshi ce na karasa maganan gwanin tausayi.
Tsaki halima taja tace ki daina irin maganan kema din yar uwarmu ce ai yanda fadeela take takaman ita kanwarshi ce kema haka kike kanwarshi tunda iyayyenmu basu bambanta mu.
Kai kawai na gyada na zame na kwanta dan ni kadai na san yanda nake ji.
Washegari na shirya muka tafi gidana na dauka abubuwan makaranta na muka wuce.
Bayan na fito daga lectures ina zaune karkashin wata bishiya ina cin popcorn sai ga fadeela da wasu kawaye da ta samu a nan makaranta.
Tsayuwa suka yi a kaina tare da kwashewa da dariya daya daga cikjnsu tace fadeela kishiyar taki fa ba laifi.
Hade rai tayi tace eh kam ba laifi amma kyaun nata bai kare ta da komi ba tunda gashi ina kokarin shiga gidan mijinta.
Kwashewa suka yi da dariya dayar tace kai amma an yi kyaun asara ashe dai akwai inda kyau baya amfani.
Mikewa nayi zan wucesu fadeela ta rikoni tace ina kike shorin zuwa zakiyya ai ban gama ba ki shirya karbata a gidan mijinki nan da kwanaki kadan.
Kuma kisa a ranki ni da yah rid auran mu mutu ka raba ne babu rabuwa domin rabuwar mu na dai dai dai da rabuwar zumuncin mu kefa?
Kuna iya rabuwa a ko da yaushe tunda ba uwar da kika hada dashi.
Hannunta na kabe daga jikina nace da alama zuwan da muke yi islamiya raka mu kawai kike yi tunda kika iya mantawa musulmi dan uwan musulmi ne toh in baki sani ba yau ki sani yah rid dan uwana ne kuma mijina.
And da kike maganan zaki shiga gidan mijina toh bismillah gaki ga gidan zuciyar mijina ne sau dai hange daga nesa ke ko hangen ma baza kiyi ba dan yafi karfin ganin ki balle ki shiga.
Hannu ta daga zata mareni runtse idona nayi ina jiran inji saukan mari sai dai shiru.
Bude ido nayi naga an rike hannunta gam..........
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖BANI NAYI KAINA BA💖
By Sawwama A.
Page 44.
Dago ido nayi dan inga wanda ya rike mata hannu Halima ce rik'e da hannun fadeela.
Cike da bacin rai Halima tace "da alama wad'annan kucakan k'awayen naki sun koya miki shaye shaye"
"Dan kam in ba shaye shaye ta fara ba, ba yanda za'ayi tayi gangancin kai hannu jikin wacce take so precious to yah rid"
Cewar yusra.
"Wallahi kinji kunya fadeela an fadi ba nauyi baki da girma sai na jiki banda rashin girma meye naki na sako wad'annan sokayen a cikin hurumin gidan mu?"
Yusra tace" to ma me zakiyyan tayi mata banda neman magana ? Ita da zaki aure mata miji bata tsokane ki ba sai ke gwana mai d'an uwa"
Cike da rashin gaskiya fadeela ta fara borin kunya " to karya nayi ba d'an uwana bane? Karya ne ita din ba bare bace a cikin mu?"
Cikin daga murya Halima tace " karya kike zakiyya ta wuce bare a wajenmu ko da bata auran yah rid ,ita y'ar uwarmu ce balle tana auran shi har da rabo. To wallahi ki kiyayi kanki in kina son zaman lafiyanki da yah rid gwara kin nutsu kin girmama mishi precious"
Cikin k'araji tace wallahi abinda ba zai yuwu ba kenan wacece wata zakiyya ku take y'ar uwa a gareku bani ba banzaye marasa aikin yi marasa kishin d'an uwa.
Ta ja hannun k'awayenta suka tafi.
Tsaki yusra taja tace " Allah ya sawwake ya shirya"
"Ameen" muka amsa a tare.
Hakuri suka ban nace "hakurin name fadeela y'ar uwata ce ba komai ke damunta ba illa kishi so muyi mata uzuri"
Halima tace "kishi? Wani irin kishi ke da ita wa ya kamata ya nuna kishinshi a zahiri"
Yusra tace " toh ita hankali gareta ko zakiyyan ai baki ga ta biye mata ba" kwafa tayi tace tab wallahi da ta mari zakiyya yau a yau din nan ba gobe ba zan kira yah rid in gaya mishi"
"Da ko taci ubanta karshe ma ya tubure watakila yaki auran dan Allah zakiyya ki daga mishi hankali yaki auran nan ni yau da fadeela son Allah da annabi take yiwa yah rid kuma kuna shiri baza mu kyamaci auran ba tunda itama y'ar uwarmu ce amma ita ba Allah a ranta fitina ce kawai take son tayarwa." Cewan halima.
Ajiyan zuciya na sauke nace "ni kuma bazan kulata ba,ba zan kuma dagawa mijina hankali ba tazo ta zauna Allah ya bamu zaman lafiya ai kowa ya iya allonsa."
"Haka ne Allah ya mana zabi gaba daya ameen".
***** ****** ****
Bayan na koma gida shiru har dare banga fareeda ta dawo ba waya na d'auka na kirata dan jin me ya hanata dawowa tunda na san ta san yah rid ya tafi ko duk shirye shiryen ne.
A lokacin tana zaune da labtop gabanta tana duba lectures d'inta dan ta nan take karatun kafin ta tare a lagos din.
Fadeela kuma na kwance tana chart,wayar fareeda yayi ringing.
Sai da gabanta ya fad'i dan har ga Allah tana tsananin jin kunyar zakiyya wai ace y'ar uwarta ce ta sako ta gaba.
D'aukan wayar tayi had'e da sallama bayan mun gaisa ne nace"ke kuma lafiya ban ganki ba har anyi magrib?"
Inda inda ta fara can sai tace "bari in sa a kawoni" ta katse kiran ba tare da ta jira ansanta ba.
Mtswww wani dogon tsaki fadeela taja kannan ta d'aura da fadin "shegiyar yarinya mara zuciya meye nata na kiranki kuma kije mata gida?"
"Ina ruwanki cewar fareeda ko ke ta kira kuma ma wa ya sako ki a maganan mu ke da ita waye mara zuciya kina neman kai kanki inda ba'a sonki zaki wulak'anta."
Kwafa tayi tace "