Showing 1 words to 3000 words out of 81312 words
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_haske writers association_💡
*5*
Saida gari yayi haske sosai yayi tsit su kutti sukaji tsit suka fito daga ma6oyarsu cikeda tsoro da tashin hankalin rashin ganin mamani dasu bulama.
Dakatarda sauran yayi ya ringa bin cikin hakukuwa batareda yana dogon motsiba yaje ya leqo qauyen.
Tsit sai koke koken dake tashi gawarwaki kuwa gasunan kwance
Jini kuwa tuni yake gudana a qauyen dabbobinsuma ba'a bariba shiyasa gawarwakin bana mutumba bana dabba ba.
Saki jikinsa yayi sosai zuciyarsa tayi nauyi yasan tunda su bulama basa taredasu to kuwa sun mutu ko antafi dasu tafiyarda bar abada ba dawowa,
Tafiyarda gwara mutuwa da ita sbd a qasqantaccen bawa zaka qare wasuma kafin akai wahala da azaba tareda yunwa takashesu.
Komawa yayi yana daga qafa da qyar jiri na dibarsa yakirawo sauran suka shigo qauyen babu Mai nutsuwa nansuka fara tsallake gawarwaki suna birkito wainda ke kife suna duba sauran iyalan gidan dabaa ganiba.
Tuni suma wasu daga cikinsu suka fara ihun kuka sbd ganin mazansu wasu kuwa sauran matansu Dan duka iyalan gidan baabah din mazansu da matansu tareda 'yayansu su talatin da takwas ne amma su ashirin da 'daya suka tsira ankashe sha hudu antafi da uku.
Lokacinda suka arba da gawar baabah nan suka qara saddaqarwa nandai akayi kukan daza'ayi aka dangana
Mazan dasuka saura haka aka hada gawarwakin sukaje nesa da qauyen suka rufesu suka dawo kowa yacigaba da rayuwarsa amma kullum cikin fargaba duk da sunsan mutanen bazasu dawo yanxuba sai zuwa nanda shekaru masu Dan tsawo sun kwatanci qauyen yasake cika sosai an hayayyafa yara sungirma sunxama samari da yanmata saisu sake dawowa su kwashe.
Tunda dai suna tsoro haka suka sake sakewa suka cigaba da rayuwa aka nada kutti amatsayin sabon shigaba Wanda wannan karon shi akan hada mugayen makamai na itace da dafin macizai da kunamu yamaida hankali sbd yadauki alqawarin angama satarsu ana siyardasu amatsayin bayi yaqi zasu shirya daga yanxu har ranarda mutanen zasu dawo.
*
Abincin dake cikin jirgin nasu ne iya sukadai suci su qoshi su kama wainda suka kamo suyita duka ba ruwansu da namiji ba ruwansu da mace ga yunwa sunbarsu da ita ga qishirwa tuni wasu daga cikinsu suka fara macewa sbd muguwar tafiyace mai nisa dazata kaisu nahiyar da
MENEELIK PALACE take
Duk Wanda ya mutu ruwa kawai suke jefasa ahaka mutanen suka rage da damansu.
Kwanansu goma sha bakwai ajirgin ruwar kafin suka isa da sassafe.
Cikin mutane sittin da 'yan kai dasuka kamo mutane arba'in kawai suka iso dasu daga qauyensu bulama sauran duk sun mutu ahanya.
Bayan 'yan qauyensu bulama dama sunsato wasu daga gurare da dama.
Kamar kayan wanki haka aka gargadosu dukkaninsu hannuwansu a 'daure kusan da igiya 'daya sbd ajere suke.
Babu Wanda zaka kalla kaga kamar baikusa mutuwaba sbd babu Wanda yake iya tsayuwa daidai sbd wahala da yunwa ga dau'da data canza musu kamanni mamani tuni kuka ya qare zuciya ta qafe banda tsanarsu asma'u ba abinda takeji sbd ganin sune sanadin zuwanta nan ga cikin jikinta haryafi na asma'u fitowa.
Bulama duk wuya da azaba asma'u yakeji itada mamani sbd ganin dukkaninsu juna biyune dasu gasu mata.
Kukansa da fargabarsa karsu mutu kafin a iso
Basu mutuba amma dai suna kusa sbd babu mai iya jan qwaqwaran numfashi acikinsu.
A inda suke baza hajar siyarda bayinsu suka xubesu nansuka rarrabu cikin mutanen dake cikeda kasuwar Dan kar agansu da yawa dakuma kalar marasa imani agane satosu sukayi ba bayi bane babbansu tareda manyan yaransa uku suka isa gurin wani mai siyarda 'yayan itatuwa suka zauna sunacin abinci cikin farin ciki da nutsuwa.
Asma'u ce ta yanke jiki ta fadi da 'dayansu ya lura yamiqe da sauri tareda yiwa ogan nuni da sauri shima ya miqe suka isa gurinta
Bulama tuni yafashe da wani irin kuka sbd yasan mutuwa tayi.
Ta6ata sukayi arikice 'dayan cikin wani yare mara dadin ji yace,
Tanada rai yunwa da wahalace muyi saurin bata abinci karta mutu kasan dokace anan duk mai siyarwa da masarauta bayi yazo dasu suka mutu aka gano wahalace kashesa shima akeyi musamman mu da satosu mukayi idan sultan dinsu yaji yankamu za'ayi abawa zakunansa namanmu.
Yawun tsoro ogan ya hadiye sbd yasan atarihin sarkin fiyedama hakan zai iyayi musu ba abin suqarasa kashetaba basuda gurin 6oye gawarta ko yarwa batareda angansuba sbd tsantsar tsaro da qa'idojin da sultan din nahiyar yake bayarwa.
Da ido yayiwa yaran alama suka kwanceta tareda fakar idanun mutane suka koma can baya da ita suka siyo mata abinci da ruwa kafin suka kelaya mata ruwa ta bude ido daqyar tanajan numfashin wahala.
Miqa mata abincin sukayi hannu na rawa ta kar6a daqyar take saita hannunta yashiga bakinta
Nan take ta cinye abincin tanashan ruwa sai amai.
Amai tayi sosai wainda yasata matuqar galabaita nantake zazzabi mai qarfi yafarasa jikinta karkarwa.
Damqo gashinta ogan yayi 6acin rai da takaicin sbd ita rayuwarsu na cikin ha'dari ya bude jajayen idanuwansa sosai yace,
Idan baki saki jiki kin nuna lafiyarki kalauba zan yanka mijinki agabanki na qona namansa nazuba tokarsa a takarda Nayi sigari dashi.
Marinta yayi da qarfi saidata kifa cikin qasa qasa da murya yace,
Kingane?
Bakinta dake jini ta goge hannu na rawa ta 'daga kai idanuwanta na qara rinewa da Jan axaba.
Ingiza qeyarta yayi ta fadi ta lalaba ta miqe da qyar suka koma gurin sauran bayin.
Bulama na hangota gabansa yayi mummunan faduwa ya sunkuyar dakai tareda sakin sabbin hawayen baqin ciki sbd hango jini abakinta duk da tana gogewa
Tafiyarma sai ha'da hanya takeyi a wahalce amma haka take daurewa sbd bin umarninsu karsu kashe bulama.
Sai da rana ta fadi suna aje cikin rana baci hargwara ruwa yau anbasu ganin mutane akasuwar gashi suna tsoron akwai 'yan rahoton sultan
yamma tayi sosai suntabbatarda lokacin sultan ke shaqatawa tareda 'dansa namiji qwaya 'daya tal a gurin shan iskansa dake cikin masarautarsa kuma alokacin ake bada damar kai bayi sbd kullum masarautar bata gajiya da siyan bayi sbd girma da ikonta.
Isarsu masarautar yayi daidai da fitowar yarima MAHEER IBN ABDULSHAMS tareda abokinsa KHALEEFA ABDALLAH 'Dan wazirin sultan 'yan kimanin shekaru goma sha biyu biyu sun fito daga sassan hutawar sultan fadawan hudu na bayansu zasu gurin baturen malaminsu dayazo koyardasu karatu.
Kallo 'daya yarima yayiwa sashen daduke ana gargadasu zuwa sashen koyarda bayi aiki ya 'dauke kai
Khaleefa kuwa tsayawa yayi yana kallonsu yace,
Idan nagirma zansiyawa ummyna bayinda harsu mutu suna kularmin da ita.
Tsayawa yarima yayi cak tareda juyowa jin abinda khaleefa yace yasa yatuno da alqawarin dayayiwa ammynsa yauda safe cewar zai mata kyautarda mutuwace kawai zata rabata da ita sai kawai yace atsayar masa sa bayin.
Cikin hanxari aka tsayar dasu batareda ya kalli gefensuba yace abashi namijin qarshe da macen qarshe ya siya amafi tsadar farashi.
Jiki na rawa aka janyo bulama da asma'u dake baya aka kawosu gabansa amma daga nesa sbd warin dau'da.
Still basu yake kalloba sbd iko da mulki na jinin mahaifinsa dake yawo jikinsa yace,
Akaisu ke6antaccen guri a tsaftacesu abasu abinci da suturu kyautace zanyiwa mahaifina da ammynah akaro na farko.
Yana fada ta wuce khaleefa yabisa yana tunanin siyawa nasa iyayen amma zaibari sai ansake kawo wasu bayin.
Sukuwa dasuka kawo bayin maqudan kudaden qasar akabasu cikeda jaka suka karbe abinsu suka juya suna isa kasuwa suka siya guzurin abinci mai yawanda zai ishesu suyi wata qasar safaro wasu sudawo su sake siyarwa.
Lokacinda aka ke6esu bulama aka tsaftacesu tsaf aka basu watadaccen abinci mai kyau sukaci nantake suka 'Dan murmure sukai fasali aka fito dasu aka nufi Sashen da sultan da iyalensa kowa keda part.
Kallonta bulama yayi idanuwansa taf da halayen tausayin gararinda rayuwarsu da abinda zasu haifa sbd tasake shiga,
Tasu qaddarar ahaka take daga 'yaya masu gata da dukiya sunkoma wasu mutane masu wani yaren dabam agarinsu baabah yanxu kuwa zasu zamo wasu bayi masu bauta kuma iyayenda zasu haihu su haifarwa iyayen gidansu wani bawan ko wata baiwar.
Itama kallonsa take da ido jajir sbd sanin daganan rayuwarsu amatsayin ma'aurata ta tsaya takuma wargaje sbd ikon ganin junaba basudashi yanxu bare kebewa kosunga juna iyakarsu satar kallo ko ikon magana basudashi.
Ahankali aka jasa aka shige dashi babban palon sultan cikin tsananin biyayya 'Dan Aiken yarima ya zube yace,
Allah yaqarawa sultan yawan rai da lafiya tareda qarfin mulki,
Ga babbar kyauta ta musamman daga yarima.
Kallon bawan yayi tareda sakin wani kyakkyawan qasaitaccen murmushi kafin yakalli 'dan aiken yakalli saikin gida yace,
Sarkin gida gobe tundaga 6ullowar rana aje abudewa wanda yakawo saqonnan na yarima ma'ajiyar abincin masarautar meenelik yaringa dibar duk abinda yakeso yana kaiwa gidansa harsai rana ta fadi sanann yanxu yacire rigarsa ya shimfida acika masa itada sutura mai tsananin tsada kalolo ba iyaka wanda saiya 'dauka daqyar sbd wannan ce kyautar yarima ta farko agareni Dan haka wannan itace kyauta mafi soyuwa araina kyautarda mutuwace zata rabani da ita
Aje asanarda yarima kyautarsa ta faranta ran mahaifinsa ayimasa albishirda zuwa qasarda yakeson bin baturen malaminsa karatu.
Jin haka Dan aike ya zube jikinsa ba inda baya rawa sbd farin ciki yadinga rero kirari da godia kafin yafice daukeda kayanda sarki yace yana nishi daqyar sbd yawansu da nauyinsu.
Kallon bulama sarki yayi kafin yakalli su waziri cikin farin cikinsa dabai 6oyuba yace,
Wannan kyautace daga yarima bazaiyi bautaba bawan dazai riqa kula da hutawatane daga yau anadasa.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
*1*
BISMILLAHIR RAHMANIRRAHEEM
For you my ummu-khulthum.
Bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasu nsu kuma a qaqqame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar
Dukkaninsu kalar kayansu dayane mazansu da matansu kalar dark blue Wanda zaa iya kira da uniform.
Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana ra6ewa gefe tareda sunkuyarda kai qasa sbd takun tahowar sarauniya Wanda sautin anklets din zinarin dake qafarta shine yake sanarda isowarta ko tahowartar tundaga nesa wanda tunda ta tashi arayuwarta ta taso agidan sarauta tasaba duk inda take sautin sarqar ke sanarda tahowarta harzuwa yanxu data manyanta sbd mulki a jininta yake.
Tana qarasowa hanyar dazata shigarda ita 6angaren mai martaba sarki ta tsaya cak batareda tace qalaba tareda juyawa ahankali tadan kalli gefenta da dama.
jakadiyarta dake gefenta tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su shida kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suka tsaya tareda sunkuyarda kai.
Boyayyar ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda shiga qofarda aka jima da wangale mata jakadiya tabita abaya aka rufo qofar.
Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs red and golden kamar zinari sai qyalli suke sai komai daya qawata palon yazamto shima red and golden dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama palon takoina sbd wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a palon.

Babu kowa a palon sbd palon farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki
Ta sake tsayawa cak tareda sake sakin wata sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren jakadiyaba murya a karye tace,
Wannan saqon na sultan(sarki) yana matuqar girgixa zuciyata sbd saqone daya zamto na baqin ciki agaresa,
Duk wani bawa ko bafade yakai wannan saqon abakacin rayuwarsane shiyasa nazabi nazo na isardashi dakaina,
Ajiyar zuciya mai nauyi jakadiya ta sauke tareda kallon sarauniya zaarah din cikin tausayawa acikin aranta afili tace,
Allah yataimaki sultana yakuma sanyaya ranki badan kinyi rashiba yabaki ikon isarda saqon sarkin sarakuna....
Katseta sultana zaraah tayi da cewa,
Haihuwa tazamar mana abar fargaba maimakon farin ciki.
Uwargijiyata Allah ya sassauci fargabarki amma dakin sake kin nunawa yarima farin cikinki da qaruwar dayasamu tunda shi yanaso ahakan kuma yana godiyar Allah da arzikin qaruwa daya basa
Allah ya raya abinda aka Haifa din yasa ayi alfahari da hakan gaba.
Ajiyar zuciya sultana tasake tareda furta amin qasan maqoshinta kafin ta tattaro jarumta da qarfin gwiwa ta gyara zaman gyalen kanta daya rufo dogon gashinta dake kwance har bayanta Wanda shima gashin harzuwa goshinta adone na wata kyakkyawar sarkar zinari ta kai sai aka rufo gyalen doguwar rigarta dark purple dataji adon duwatsu masu shegen kyau da kyalli gyalen naja har qasa kadan.
Ratsa dogon palon tayi jakadiya na bayanta ta nufi qofarda zata kaita ainihin palonsa na musamman tana zuwa wanda ke tsaron qofar ya wangale mata qofar ahankali tashiga jakadiya takoma gefe ta toge itama tana jiran fitowar uwar dakin tata.
Wani palon ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali

Zaune yake cikin shiga ta alfarma
Dattijone sosai da Hutu da mulki na jinin sarauta daya ratsasa,
Kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa taso rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da qarfin hali.
Qarasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa murya na rawa tace,
Allah yataimakeka saqo daga GEORGIA.....
Idanuwan daya sake watso matane yasa taso daburcewa tayi saurin gyara murya cikin nutsuwa ta dauke idanuwanta daga kallonsa murya na rawa tace,
Yarima yabugo yasanarda saqon matarsa ta sauka ansamu 'YA MACE.
Sake dauke kai tayi sbd gudun ganin yanayinsa sbd kodagajin yanda ya dauke wuta tasan ran maza ya baci babu jin dadi ko alamar farin ciki dagajin saqonta.
Tsawon mintuna ashirin shiru
Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace,
Kin isarda saqon yarima Dan haka kisanardashi saqonsa ya iso
Ke kuma tukuicinki na sanarda saqonsa bazaki sakashi a idoba sai bayan shekara daya,
Karya dawo harsai matarsa tasake samun wani cikin wannan karon anan zata haihu
Zata haifi yariman da ubansa yaqi amsa.
Yana gama fadar haka ya miqe zai shige turakarsa
Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin kanta dabazataga 'dantaba ko awannan shekarar
Tsawon lokaci kenan tunda yayi aure matarsa tahaifi ya mace suka koma Georgia sarki yace karsu dawo saita sake samun wani cikin tasamu tasake haihuwar mace yasake korasu yarinyar ta rasu still yahanasu dawowa harsaita haifi namiji yanxuma gashi macen ta haifa kuma yanxunma saiwata shekara kenan kusan shekara biyar kenan rabonta da danta tana tsananin kewarsa dason ganinsa.
Cikin sanyin murya tace,
Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna
Na karbi hukuncina matuqar hakan zai faranta ran sarkina
Saqon yarima kuma kamar yagama isa a kunnensa ne
Nabarka lafiya.
Juyawa tayi ta nufi qofar tana isa aka bude mata ta fice
Jakadiya tayi saurin Mara mata baya kanta asunkuye sbd ganin yanayin uwar dakin nata.
Suna isa babbar qofa suka fice kuyanginta sukai saurin Mara musu baya
Bayi sai zubewa suke suna sunkuyar dakai yaukam ko kallonsu bata iyayi bare amsa gaisuwarsu dankuwa ranta amatuqar dagule yake.
Tana isa sashenta cikin tsananin sauri aka bude mata qofa tashiga
Tana shiga kai tsaye hanyar bedroom dinta tayi bayan tasake wuce palonta na musamman inda babu mashigowa duk fadin masarautar daga ita sai danta yarima sai amintacciyar kuyangarta datake kamar matsayin 'ya agareta saikuwa jakadiya ko matar yarima bata taba shigowa nan palonba iyakacinta na farko bedroom dinta kuwa ko yarima baitaba shigaba bare jakadiya kuyangarta mai gyara mata kawai keshiga.
Tana shiga bedroom din taganta a tsaye jikin wardrobe din lafiyyan dakin tana jera mata sabbin kayanta dasuka iso.
Daidaita nutsuwarta da fuskarta tayi tareda gyaran murya batareda takalletaba.
Juyowa tayi da sauri tana ganin sultana zaarah tasaki wani irin lafiyyan murmushin daya bayyanarda dimple dinta duka guda biyu cikin tsananin taushin murya da tsantsar ladabi tace,
Ammy barka da dawowa.
Daga mata kai ammyn tayi batareda sakin fuskaba kamar yanda suka sababa murya a dake tace,
Ina buqatar hutu.
Cikin nutsuwa tayi saurin aje kayan ta nufi qofa zata fice jiki asanyaye sbd ganin yaudai ammyn bata cikin kwanciyar hankali dankuwa tunda safe take lureda ita bata cikin kwanciyar hankali.
UMMU-RUMANA....cak ta tsaya jin ammyn takirata tareda juyawa cikin ladabi tace,
Allah yataimaki ammy.
Bana buqatar damuwa takomai da kowa ko dogon motsi banaso kowa yafice daga nan shashen zuwa anjima saiku dawo ina buqatar Hutu.
Ahuta lafiya ammy"""tace cikin sanyi tareda ficewa jiki ba dadi sbd damuwar ammy na matuqar ta6ata sbd akoyaushe idan takalleta cikin annushuwa ganin take tamkar mahaifiyartace cikin annashuwar kasancewar mahaifiyarta babbar amintacciyar baiwar ammyn kuma jakadiyarda kafin tarasu.
Tana fitowa bban palon ammyn duk ta sallami sauran kuyangi da bayin sashen itama ta fita masu tsaron qofar shiga sashen kawai aka bari tareda nufar hanyarda zata sadata da bangarensu na bayi inda kowa keda daki mutum uku daki daya.
#mamuhgeee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
*2*
Babban sashensu na bayi da bororin masarautar ta nufa tana isa kai tsaye dakinsu ta nufa tana ganin qofar abude tasan nuratu naciki tashiga bakinta daukeda siririyar sallama.
Zaune bakin katifa taga nuratun tana qoqarin zare wandon uniform dinta zata shiga wanka ta nufi bakin tata yar katifar ta zauna tana cewa,
Yau kingamo da wuri Nima nasamu dan qaramin hutu daga ammy yanxu kiyi sauri kiyi wankan sai kiyimin koda kalbane sbd inason zanyi wankan tsarki banasan nayi da kaina a tsefe zai dameni tunda ba iska zaishaba koyaushe muna cikin uniform.
Kallonta nuratu tayi jin yanayin data qarasa zancen dashi kamar koyaushe tun tasowarsu sun bude ido sun tsinci Kansu a bayi kuma yayan bayi Wanda har gwara ita tanada mahaifiya rumana din batada uwa batada uba.
Fasa shiga wankan tayi ta qarasa katifar rumana din ta zauna tareda zame mata dankwali tace zonayi miki daga baya nayi wankan sbd nima aikine dani matuqa zanje karbo sabbin furannin dazaa jera a kwalbar ruwan dake girke palon sarauniya adama na farko gakuma aikin chanxa
Gyara zama tayi cikin tausayawa rayuwarsu tace,
Mamani tasha saqe saqin maganinta kuwa kafin tafita aiki?
Girgiza kai nuratu tayi cikin tausayin mahaifiyarta dakuma na rumana din datake qaunar mamani da zuciya daya duk da kyararta datakeyi.
Kamar rumana tasan me take tunani cikin sanyin murya tace,
RUMANA INA MAI HORAR DAKE KI RIQE ALLAH AKO WANE HALI KO YANAYI KIKA TSINCI KANKI DA RAYUWARKI,
IDAN KIKA RIQESA KIKA ZAMA MAI HAKURI DA DANGANA DA DAUKAR QADDARAR DAYA DORA MIKI MAI KYAWU DA MARAR KYAWU TO KODA KIKE BAIWA RAYUWA BAZATAYI MIKI TSANANIBA HAKAMA IDAN KIKA ZAMO BAIWA MAI BIN UMARNIN UWAYEN GIDANKI TO HAKAMA RAYUWA BAZATAYI MIKI TSANANIBA...
Nuratu wainnan sune kalaman ummana da ako yaushe suke shawagi cikin zuciya da kunnuwana wainda sune nake kallo amatsayin wasiyyarta gareni,
Ni baiwa ce uwata da ubana bayine harsuka rasu,
Banida wani gata ko martabarda zan kalli kaina amatsayin wata mace ko 'ya mai qima sbd nima zanqarasa rayuwatane amatsayin baiwa kamar iyayena,
Tun lokacinda nayi wayo
cikakkiyar mai yanci ta hanyar 'yantawa
Allah yakarbi adduata amma adaidai lokacinda yantawar batada amfani sbd tana kwance ciwon ajali Wanda yasa na yanke rai daga samun ingantacciyar rayuwa.....
Katseta nuratu