Showing 63001 words to 66000 words out of 81312 words
da qarfi cikin wani masifaffen tashin hankali sbd ganin qaramin ciki ajikinta.
Matsosa tayi cikin farin ciki tana Murmushi zatai masa magana yasake ja baya tareda ficewa da sauri.
Dayake safiya ce sosai sauran babu Wanda yatashi suna sassansu kowanne yazabi sashensa sunacan suna hutawa tuni suka samo masu hidima.
A cikin fadar ya shiga ya tsaya jikinsa na wani irin rawa zufa na karyo masa takoina
Ta bayyana a gabansa tareda riqo hannunsa ta 'dora akan cikin ahankali tace,
Cikine dani kuma........cak ta tsaya da maganarta jin sukar data sauka ajikinta daga bayanta
Cikin wani irin yanayin azaba ta juyo dan ganin waye taji wata sukar a gefen cikin duka biyun.
Jajayen idanuwanta ta 'dago cikin radadi da azaba takallesu amari ne da yonas,
Jinine ya fara fitowa daga hancinta ta 'damqe hannun Jamal da idanuwansa suke zubarda wata irin qwalla da kuka mara sauti,
kojo da ajani tareda haji suka tsaya gabanta tareda 'daga wuqaqensu suka soketa da qarfi aciki lokaci 'daya.
Tasake damqe hannun Jamal tareda fitarda wani nishi mai qarfi da wata irin azaba atake Jini ya balle mata mai matuqar yawanda basu taba ganin irinsaba hakama bakinta yafara fitarda jini ta yanke jiki ta zube bakin karagar mineelik tareda kallon Jamal daya fiddo wuqarsa yana hawaye ta lumshe ido cikin tsananin baqin ciki mai tsananin gaske sbd ta tabbatarda cin amanarta da yaudararta sukayi ahankali tabude baki daqyar ta furta,
Duk iya alqawari da soyayyar danake maka meyasa kazabi cuatatar dani.,
Karka kasheni kabarni na rayu kodan cikinka dake jikina nikuma zan maka alqawarin sabuwar rayuwa,
Haryanzu zuciyata nasonka ko ka kasheni bazan daina sonkaba.......
A hankali ya 'daga wuqar ya nufi qirjinta yana kuka yashigarda wuqar qirjinta da qarfi.
Atake tasaki wani irin azababen nishi mai qarfi daya amsa masarautar gabaki daya ta kallesa idanuwanta na fitarda wasu irin hawayen ahankali ta bude baki tace,
Meyasa????
Cikin izza ajani yace,
Sbd karagar mineelik.
Kallon Jamal tayi ya juya mata baya yana sake sakin sabon kuka ta kalli karagar tasaka hannu ta debi jininta dake zuba ta zubawa karagar ta lumshe ido sbd wata irin azaba dake ratsata cikin,
Hawayen azaba tace,
Ayau ni sarauniya mineelik 'yarda,soyayya dakuma amincewa yasa bawa mafi soyuwa a rayuwata ya kasheni ya zubar da jinin 'dana ko 'yata dan haka haqqin jinana bazai taba barin bibiyarku ba har qarnin qarshe harsai ranarda jini ya maida jini maimakon jini dan haka nayiwa mineelik baki zata zame muku masifa mara magani da ganewa,,,,daga yanxu jini ya ringa zuba kenan amaimakon jinin 'dana.
Kallon bayan Jamal tayi lokacinda taji ko maganar takasa sbd tsananin azaba ahankali ta furta nabar maka dukiyata sbd sarauniya bata alqawari ta 'daga saidai bazakaji dadinta ba......
Cikin rashin imani yonas ya daga wuqar ya soke mata maqogoro atake ta saki numfashi da ajiyar zuciya ahankali jikinta ya saki ta bace 6at.
Zubewa agurin Jamal yayi yana wani irin kuka mai sauti.
Cikin tsananin farin ciki da murna amari ya nufi karagar zai hau boka aqoob ya bayyana gabansa cikin wani irin murmushin mugunta yace,
Nine mai hawa wannan karagar duk Wanda ya........bai qarasaba sukaga kansa ya fille yafadi qasa.
Kojo sukaga yani a bayansa kenan shine ya fille masa kai
Cikin murna ajani ya nufi kojo zaiyi magana yonas ya sha gabansa cikin tsananin baqin ciki da zafin zuciyar ubansu da aka kashe yana 'daga wuqarsa zai cirewa ajani kai aka soke masa zuciya daga bayansa saida takobin ta fito ta qirjinsa.
Wanda amari ne yayi wannan aikin.
Haji na ganin haka ya juya da gudu ya fice yace,
Kusani wannan gabace da masifar dazata zo har zuriar zuriar bayanmu.
Cikin zaquwa amari ya juya zai hau karaga Jamal ya buge qafafunsa tareda miqewa ya isa karagar kai tsaye ya hau ya zauna tareda kallonsu da jajayen ido yace,
Nine magajin mineelik dan haka nine zanyi sarautar duk Wanda hakan baimasaba yana buqatar hada kwanji dani.
Kallon juna sukayi ga mamakinsa saiyaga sun nuna amincewarsu.
A ranar Jamal ya karbi sarautar mineelik kuma aranar aka dauki masu hidima 'Dari da hamsin atake masarauta ta cike da mutan gari ko sati ba'a rufa dukkaninsu sukayi auren mataye uku uku lokaci 'daya,
Mineelik cikin qanqanin lokaci tazama masarauta mafi girma da iko a wannan qarnin musamman data zama babban gari mafi girma
Kafin mulkin Jamal yaqare saida mineelik takoma itace a tsakiyar babban birnin Ethiopia sbd cika da garuwan qasar sukayi koina ya cike tazama babbar qasar cin kasuwar jiragen ruwan dake wajen gari.
Mulkin Jamal wani irin mulkine na daukar rayuka ba abakin komaiba,
Suna arziki da yawa da girma babu kamar mineelik a wannan qarnin sbd garin da masarautar take ko zakayi wata daya kana yawo bazaka zagayesaba.
Duk wani burinsu Jamal dasu kojo yacika saidai rashin haihuwar 'yaya maza daya addabesu daga qarshe har sultan jamal ya rasu bai samu 'da namijiba sai mata
Bayan saukarsa sultan kojo ya hau shima duk tsawon shekarunsa harya mutu bai haifi namiji ba dukkaninsu sunyi mulki ajani kawai yasamu namiji 'daya acikin 'yayansa Wanda bayan rasuwarsa shima dansa sultan amed yahau bayan sultan amed sai sultan nurin,dagashi sai sultan abaass da haka mulkin yayita zuwa qarni qarni so 'daya akayi assultana Wanda mulkinta karagar tafi ta6ata kasanewarta mace,
Alokacin mulkin assultana ankashe rayukane tamkar dabbobi sbd jini daya yawaita a mulkinta sbd iya zubar jini iya qarawa karagar qarfi qarshe abin taba kwaqwalwarta yayi ta samu tabin hankali ahaka ta rasu.
Da haka 'daruruwan shekaru suka shide musuluncin gske yashigo cikin qasar suka karbesa sosai inda a yanxu suna cikin qasashen dasukafi yawan musulmai duk da wasu haryanxu suna aladar bin bokaye.
A yanxu muna wani lokacine na waye da ilimin zamani tareda qarni mai dadi sbd rayuwar ilimin boko dana addini daya shiga koina ya wadata.
Sultan abdulshams sarkine mai tsananin son kansa fiyeda duk wani abu a duniya har yayansa har matansa shidai arayuwa kansa yasani shiyasa yadau alqawarin karya alkadarin mineelik domin yaci gaba da mulkinta shikadai sbd shikansa yaxubarda jinin alumma fiyeda qima dan haka yanason mulkin bazai barshiba shiyasa yayi bibiyar yanda zaiyi yagano ma'anar kalmar,
""""jini ne zai wanke jini domin jini"""" a cikin littafin tarihin masarautar mineelik.
Ma'ana soyayyace tamkar wadda takewa jamal mai hadeda jinin cikinta zata karya wannan masifar shiyasa azamansa da bawansa bulama ya fahimci wata irin qauna da soyayyarsa da matarsa yayi amfani da qarfin ikonsa yasa jakadiya ta ware musu wata 'daya suna kebantuwa da juna ranarda Jakadiya tagano asma'u ta samu wani cikin tasanarda sultan nan yafadawa sultana zaarah nufinsa bawai danta hanaba saidanta kawo masa asma'u gaban karagar da safe daidai irin lokacinda aka kashe sarauniya mineelik.
Badan sultana tasoba saidan tsananin iko da barazanar sultan agareta ranar wata laraba da safe tashirya tace Jakadiya tasa asma'u cikin 'yan rakata gurin sultan kai gaisuwa.
Koda suka isa tace asma'u tabita suna shiga suka rararda bulama tsaye yana jiran fitowar sultan nan sultana tashiga gurinsa tabarsu tsaye suka qurawa juna ido cikin qauna da soyayyar junansu ya kalleta cikin nutsuwa yace,
Idan kika haihu ko bananan kisawa yaron suna bilal idan mace ce kisaka mata asma'u.
Murmushi tayi zatai magana sultan da sultana suka fito sultan yakallesu kafin yayi magana Jakadiya tashigo daukeda qaton tray daukeda kofuna guda biyar takai gaban sultana da sultan suka dauka ta juyo ta miqawa bulama 'daya asma'u 'daya babu musu suka karba sultan yace,
Wannan taya murnace ga bawana bulama na 'yantasa daga yau.
Cikin tsananin farin ciki suka zube qasa suna godia sbd sunsan nesa tazo kusa sunkusa komawa qasarsu kenan.
Cikin tausayi Jakadiya tace,
Kusha kyautar sultan Ku godewa Allah.
Da sauri suka kwankwade lemon suna sake godiya suka miqe suka fice sultana ta sauke numfashin damuwa da tausayinsu tareda baqin ciki da dana sani Wanda take kallon kanta amatsayin wadda takashesu shiyasa take tsananin qaunar yarsu.
Acikin daren bulama ya rasu da ciwon ciki asma'u ma ta rasu da cikinta dabata haifeba Wanda babu Wanda yasan dashi saisu dasukai aikin saidai abinda basu saniba shine kozaku sadaukar da rayukan masoya 'Dari to masifar mineelik bazata karyeba sai masoyan dasuka kasance sunada jini da masarautar.
**
A matuqar gigice ta farka a firgice suka miqe tsaye amatuqar firgice suna watsa ruwan magani sbd basusan a yaya ta farko ba.
Maheer dake zaune hannunsa cikin na suhailat ya zare ya miqe ya nufi gadon yana kallon fuskarta dake bawa duniyarsa nutsuwa.
#mamuhgee.
[7/30, 7:38 PM] ummul aulad: _*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_
*37*
_Not edited_
_a gaggauce_
Haske writers association
Shiru tayi tana kallonshi cikin nutsuwa, ta rasa ta inda zata fara taimakonshi satar kallonta yayi cikin nutsuwa, sannan ya sauke numfashi yace.
Rayuwarsu a dajin wani irin rayuwa ce, mai ɗauke da soyayya da wani irin kulawa ba daga itaba har zuwa ita kanta. Mafi lokuta takan zauna tayita tunani anya ba wani kuskure bane yake shirin afkuwa na amincewa bil'adam, sai wani ɓangare na zuciyarta ya tuno mata tarin alkhairin da Jamal yake mata,
Wani lokaci suna zaune ta kalleshi, a nutse kafin tace,
"Menene silar barowarka daga gida ka shigo wannan dajin har kake tunanin kashe kanka da rayuwarka."
Kirjinshine ya bada wani irin sauti, kura mata ido yayi yana qoqarin qin barinta gano yanayin daya shiga cikin daidaita nutsuwa sai ya sunkuyar da kanshi cikin nuna baqin ciki yace,
Idan kika san abinda ya baroni da dangina sai kema kin gujeni, labarina ba labari bane sbd cike yake da bakin ciki.
Dafe goshinshi yayi yana dauke kai yana girgizawa cikin damuwa mai tsanani sannan ya cigaba da cewa,
"Idan kika san koni waye guduna zakiyi gwara mubar maganar haka dan babu alkhairi a ciki.
Wani irin qayataccen murmushi tasaki cikin qasaitar mulkinta dabatamasan tayiba tace,
Kayi min halacci zama tareda ni kana kula dani tamkar nauyina yana rataye akanka dan haka bazan gujekaba fadamin.
Girgiza kai ya cigaba dayi yana cewa,
Karki so jin waye ni, karki so jin waye ni, labarina cike yake da kayan haushi da bakin ciki.
"Ko baka yarda dani bane, dan idan ka yarda dani ai babu abin bakin ciki a jin kai waye saima karin amintaka a cikin zamanmu.
Gyara zama yayi zuciyarsa cike fal da farin ciki dan abinda zai fada mata shine matakin nasararsu.
"Kamar yanda na faɗa miki ni marayane bani da uwa bani da uba, amma akwai kawunaina, kasancewar iyayena sun mutu basu bar min ko 'dayaba koda kuwa kaza ce yasa na zama abin tsangwama a cikin mutane, sannu a hankali na fara niman nawa na kaina sai dai...
Kura mata ido yayi cike da jin ba daɗi da kuma hango yarda da Amana da tabashi sai ji yayi akaron farko bazai iya cika wani mugun kudiri a kanta ba, sunkuyar da kanshi yayi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki wanda bawai dan maganar da yake mata bane sai dan akaro na farko da zuciyarsa ta hango masa kuskure da suke shirin tafkawa ne Wanda zai iya bibiyarsu har jikokin jikokinsu na qarni mai zuwa.
Cikin nutsuwa tasake kiran sunansa tace,
Karka damu nimai riqe sirrinkace.
"A'a mineelik ina tsoron karki guje nine.
"Ina tare da kai nace ka yarda dani.
Gyaɗa kanshi yayi sannan yace,
"Nayi kokarin neman nakaina amma abu yaci tura daga nan kome na taɓa sai ya lalace kai ko kayan mutane na taɓa ya tashi aiki sbd baqin Jini da baqin qashin tsiya da'ake cewa inadashi daga nan mutane suka shiga jifana da mai kashin tsiya bani da albarka a rayuwa haka bai isheni ba sai na faɗa niman aure nanma mutane suka shiga korata a kofar gidajensu suna goranta min ynx waye zai yarda ya bani auren ɗiyar shi yanda tsiya da fatara ya kewaye rayuwata,
Qarshe ko qofar gidajen mutane sunhanani bi idan nabi qofar gidan mutum aranar saiya rafka babbar hasara tou tsangwama da qyama yasa nabar garin nashigo duniya shi yasa na shigo dajin nan sbd jin labarin ha'darinsa naso koma meyene aciki ya kasheni.
Abin tausayi abin dariya yar karamar dariya tayi wanda ya bayyanar da jerun kyawawan hakoranta farare.
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ɗan rufe bakinta cike da qaunarsa mai qarfi dake zuciyarta tace,
"Tabbas akwai abin dariya a rayuwar bil adama sbd kamar munfisu yarda da qaddarowar Allah ne.
Kallonta yayi da sauri cikin rawar murya yace,
Mekike nufi da bil adam ke kincire kankine daga bil adaman?
Kallonsa tayi cikin takaicin zancen datayi ta girgiza kai cikin son gyara zancen tace,
Dukanmu bil adama ne saidai wasunmu kamar basuda daukar qaddara sbd banga abin gudu da qyama ananba.
"Hmm kece kike ganin haka amma abin ba haka bane, aiku mata baku ɗauki kome da muhimmanci ba, tunda ba damunku abin yayi ba.
Girgiza kai tayi ni na amince zan aureka a duk yanda kake sile 'daya sun wadaci sadakin auren.
Mikewa yayi a razane tare da tsorata sbd baitaba kawo wata maganar aure atsakaniba yace,
Banda komai dazan inganta rayuwarki na kare martabarki amtsayin mijinki dan haka bazan iya lalata miki rayuwa ba.
Jikintane yayi matukar sanyi har tana dana sanin fada masa hakan sbd har cikin ranta takejin damuwarsa sbd tausayinsa mai qarfi da yayi wasi zuciyarta kamu tareda soyayyarsa mai qarfin gaske dan haka zata inganta masa rayuwa,
Zata basa kaf arzikinta saidai zata daukesa sunkoma duniyarta rayuwa acan zaifi musu dadi.
Ahankali ya furta idan har kin amince da aurena a yanda nake dinnan tabbas zan sadaukar da rayuwata gurin nema dan inganta miki rayuwa.
Yarda dashi yasa take kwanciya tayi baccinta batareda sakin dukkanin jintaba shikuma yana ganin tayi nisa a bacci
yasaci jiki ya nausa yamma da saurinsa da gudunsa sai tsakiyar dare sosai ya isa inda su Ajani suke tun daga nesa yake musu kukan wata tsuntsuwa dansu gane shine tafe dan karsu harbo masa hari daga nesan.
suna jiyosa cikin bacci duk suka mike
Suka fito rumfarsu yana isowa gabansu ya zube a wahalce yana fitarda numfashi tareda sakin ajiyar zuciya.
Amarine ya rungume shi cike da kewar kanin nashi yace,
"Da fatan anyi nasara?
Murmushi yayi ya nemi guri ya zauna, sannan yace,
Nasara tazo ne tareda matsala sbd tace na aureta.
Nan ya faɗa musu komai.
Shiru sukayi kafin Haji yace,
Toh ba zaiyu bane mu karɓi dukiyar da karfin cin tuwo basaika auretaba.
Wani mugun kallo amari yasakar masa zaiyi magana yonas dan boka yace,
Meya hana kai kaje gurinta sauka karbo da qarfin cin zaki bama na tuwo ba.
Zaburowa haji yayi tareda fisgo takobinsa mai tsananin kaifi ya nufi wuyan yonas Jamal yayi saurin tarewa yace,
Ba yanzu zakuyi wannan ba kubari mukarba daga baya kun kashe kanku,kafin ya kalli haji din cikin ido da Wani irin kallon banza dayayi masa cikin rashin jin daɗi abinda yace,
Lallai kusani koda barazana bazan karɓi dukiyarta ba sai da amincewarta.
Arazane suka hau kallon juna cikin wani irin mamaki da tabbarwa da maganar da boka yafada musu bayan tafiyar Jamal din da dayansu yaje.
ganin irin kallon da sukewa juna yasa shi shan jinin jikinshi sbd kuwa ya tabbatarda akwai wani abu dasuke boyewa.
Kuna qoqarin boye min wani abune akan mineelik?
Babu Wanda ya basa amsa sai kojo dayace masa,
Ko 'daya kashirya gobe zamuzo amatsayin nemanka muke daga nan zamu daura auren muyi abinda yakawo mu muje wata harkar sbd idan muka tsaya sanya zamu qarasa rayuwarmu ne a wannan dajin.
Juyawa yayi zuciyarshi bata aminta dasu ba ya fice yana tunane tunanen abinda suke boye masa dan kuwa yasan tabbas akwai abinda suke boyewa.
Bayan tafiyarshi Kojo ya kalli Ajani cikin bushewar zuciya da takaici yace,
Aqoob yayi gaskiya na cewar Jamal zai iya fara sonta na hango damuwa a cikin idanunshi ba jarumta ba kuma da zaran yasan da kudirinmu akan mataqin qarshe na mallakar dukiyar toh ba zai taɓa yarda damu ba kuma komai zai lalace.
Shiru sukayi dukkansu sbd bazasu taba bari banzar soyayyarsu ta kaisu ga rasa abinda suka sadaukar da rayuwarsu gurin nemaba.
Koda ya isa asuba tayi har haske ya'dan fara yayi saurin kwantawa yana wasi wasi akan mineelik da abinda suke boye masa,
hango wautarshi yayi da ya amince da bukatar ya yaudareta sbd yadaura ko a tsakaninsa da bil adama yar uwarsa ne haqqi baya barinka bare sarauniyar aljanu mafi hadari ko acikin sarakunan.
yana gurin har gari ya waye kafin tafito ya shiga daji nima musu abinda zasu ci.
Koda ya dawo taga rashin walwala akan fuskarshi tambayarshi tayi ko akwai wani matsala yace,
Babu kai tsaye yana juya mata baya sbd bayason kallon fuskarta yanzu jin yake zuciyarsa na karyewa da abinda suke shirin yi yanajin kamar bazai iyaba.
Shiru tayi ta cigaba da zama tana satar kallonshi da zaran sun haɗa idanu zata ɗauke kai tana murmushi haka shima yake qaqalo murmushin qarfin halin.
Kusan ita tayita janshi da hira, har ya sake da ita suka cigaba da hidimarsu can suna zaune sai suka jiyo sautin muryan mutane na doso inda suke mikewa tayi ta koma bayanshi tana leka inda take jin muryan mutanen.
Shikuwa dayasan da zuwansu bai wani nuna damuwaba saidai fargaba da wasi wasin abinda sukazo ayi wato auren.
Tabbas yanajin wani irin tsoro, fargaba shakku da wasi wasin aikatawa.
Cikin nutsuwa suka tunada gargadin boka aqoob dayace saisunyi matuqar taka tsantsan karta zargi wani abu ko taganosu dan kuwa rayukansu zasu rasa dukkansu idan aka samu matsala shiyasa
Su ajani ne suka iso har inda suke ja yayi da baya a tsorace su kuwa suka diro raqumansu da wani irin tsuma da far in ciki jikin na rawa suka qaraso gabansa cikin babbar murya kojo yace,
Jamal kasan abinda kayi da halinda kasamu ciki daka gudu aka rasaka?
Fiyeda kwana hudu muna yawo cikin dajin nan nemanka bayan mun share satittika muna yawon qauyuka nemanka mekakeyi wannan hadararen dajin....?
Kuka ajani ya saka cike da bakin ciki yace,
"Yau da ɗan uwanmu na raye ai kafi karfin wulakacin badan haji yace mu shigo ta daji ko kazo ka rataye