Showing 66001 words to 69000 words out of 81312 words

Chapter 23 - Tarayya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

17 Dec 2024

248

kanka ba,
Gidanmu ya qone qurmus bayan barowarka shiyasa muka tabbatarda zamanka a gidanma kuma wata rahamace kayi hakuri mu koma musan yanda zamu dora itace muyi wani gidan bazamu sake bari a wulaqantakaba zamu samo maka mata mu daura maka auren dakakeso.

          "Babu inda zani dan ni na sami wacce zata aureni da zuciya ɗaya bata damu da dukiya ko arziki ba.

Cikin Sauri da 'doki yonas yace,

Zamu aura maka ita yanzu dai kazo muje gida idan munje a daura maka ita acan tunda yanzu idan anyi bakada gurin sakata.
        
    Shiru yayi alamar nazarin zancen kamar gaske.
Ita kuma cikin nutsuwa takallesa ganin yashiga tunani ta dafashi ahankali ya matsa mineelik ta bayyana daga bayanshi.
   
  A tsorace sukayi baya zuciyoyinsu na rawa saidai jaruman gaske ne bazasu bari kyawunta da kwarjininta ya rikitasu ba.

      Cikin sauri kojo yace wannan ba irin matarka bace bazata zauna dakaiba idan taga talauci zai illatata.
    
"Na rantse da abin bauta bazan barta ba ina sonta kuma zan aureta idan kuka ce bazaku barin na aureta ba zan kashe kaina na huta.

   Cikin fusata Amari yace.
"Ka daɗe baka mutu ba wannan matar tafi karfinka ka nemi wata mana kokuma mu munema maka wata.

      Ahankali ta matso kwarjininta da wata irin haiba dake fitowa daga gareta na girgiza zukatansu saidai buri da kwadayinsu yasa suke kannewa cikin jarumtarsu cikin wata irin murya mai dadi tace,

Ku auramin shi nikuma na muku alqawarin taskar arzikinda dar qarnin qarshe zuriarku bazatai talauciba,
Ina sonsa zan auresa ahaka kuma nayi alqawarin ko bayan mutuwa zan qaunace bazan barsaba wannan alqawarine daga sarauniya datafi kowace sarauniya mulki,
wannan son dayake min yafi min kome a duniya.

     Wani irin kallo sukayiwa junansu cikin gamsuwa da burinsu yazo a sauqin dabasu taba tsammaniba.

Kojo ne ya matso gabanta suna fuskantar juna cikin rashin tsoro yace,

      Mun amince zamu daura muku aure a yanxu basai anje koina ba saidai bawai dan kinada arzikin dazaki bamuba dan da alama kema nema kikeyi.

     Murmushi tasaki ahankali tareda kallonsa takalli sauran dakuma raqumansu tace.

Idan sarauniya tayi alqawari bata canxawa,
Alqawarinta kamar rubutu ne akan dutse har abada baya canxawa.

        Murmushi yonas yayi tareda kallonta cikin ido yace,

Mukuma alqawarinmu idan muka dauki burin abu kamar rubutu ne ajikin dutse baya goguwa sai muncimmasa.

Murmushi tayi tace,

Buri da alqawari basa haduwa sbd 'daya saiya danne 'daya yake tabbatuwa amma Ku sani zaku tuna hakan wata rana.

Kallonta sukayi a 'dage kafin amari ya kalli Jamal daya qura musu ido cikeda tunani kala kala aransa game dasu yace,

Yanxu za'a daura aurenka da sarauniyar ranka saidai kasani soyayya gubace mai kaifin gaske kafadawa 'yaya da jikokinka wannan.

Shigewa tayi tantinsu tana jin wani irin yanayi na farin cikinda bata taba jinsaba sbd tana yiwa Jamal wata irin soyayya da qauna mai qarfi dazata iya sadaukar da komai kansa ciki harda rayuwarta.

Atake suka rabu biyu suka wakilci ango da amarya aka daura auren da sadakin sile 'daya.

Bayan daura auren ne sukace zasu tafi su dawo sbd boka aqoob dayace idan andaura suzo yabasu matakin qarshe.

Bayan tafiyarsu da daddare yana zaune ya kafawa wutar daya kunna ido shikadai gabaki daya zuciyarsa cikin wata irin dana sani da qunci take sbd abinda yakeji gameda mineelik bazai iya cutatar da itaba saidai kuma bazai iya fada mata komaiba ko yayi gangancin bari tagane sbd rayuwar 'yan uwansa dan yasan shi tana masa so mai tsananinda bazata iya kashesaba ko illatasa.

Ahankali yakejin sautin qarar sarqar qafa da taku na nufosa tareda wani irin haske da niimtaccen qamshin mai tareda sanyi na shigarsa ya 'dago ahankali ya qurawa gurin ido baiga fuskartaba sbd wani irin kyallin zinari dake fita daga wuyanta da kanta tareda damtsen hannunwanta da qafafunta sbd adon sarqunan dake jikinta.

Saidatazo gaf dashi ta tsaya cikin ainihin suffarta tana sakar masa wani irin murmushi mai qayatarwa ta miqa masa hannunta cikin wata irin murya mai dadi tace,

Ina tayaka murnar zama attajirinda babu kamarsa a wannan qarnin,
Ina taya murnar zamtowa mijin sarauniyar da babu tamkarta a wannan qarnin,
Soyayyace farko kuma soyayyace qarshe,
Zan rayu dakai na bauta maka domin Kaine sarki a masarautata saidai cin amana,qarya da yaudara basa cikin soyayyata basa cikin abinda nake dubawa amatsayin kuskure koda ga abinda nafi so ne.

Murmushin takaicin rayuwarsa yasaki sbd yasan tunda ya bari zuciyarsa takamu da soyayyarta rayuwarsa na tsaka sbd bazai iya rabuwa da 'yayan uwansa ya 6ata musu buriba sannan bazai iya bari acutatar da itaba.

Cikin sanyin murya data nuna zallar damuwar dayake ciki yace,

Wacece ke?

Ahankali ta furta,

Sarauniya mineelik,aljanarda aljanu da mutane suka buri da fatar gani kuma matarka ta har mutuwa.

Rintse ido yayi akaro na farko yaji jarimtarsa ta 6ace ya sauke kai cikin rawar murya yace,

Meyasa kike sona har haka bayan bakida cikakken sani akan abinda yake zuciyata.

Ahankali ta 'daga hannuwanta sama tayi budesu idanuwanta akansa tace,

Barka da zuwa masarautar mineelik.

Miqewa yayi cikin wani irin mugun tsoro da firgici yake kallon koina yana jujuyawa kamar wuyansa zai cire sbd ganinsa Cikin wata irin masarauta mafi girma da kyawun dabai taba ganiba duk yawon duniyarsu.

Adon ne zaibar zinari da wani irin gini mafi kyau da tsari
Wasu irin kujeru ne a Jere na sarauta sunsha ado wani irin ni'imtaccen kamshi na tashi daga  yanayin jerin kujerun da tsarinsu yasa ya tabbatarda nan ne asalin fadar wato dakin taron sarauta.

Wani irin qyalli yaringa gani yana hasko bayansa yayi saurin Juyawa a kidime yaja da baya tareda zubewa qasa kan qafafunsa yana kallonta cikin wani irin tsoro da firgici..

Zaune take kan karagar mineelik tafito masa Zak amatsayin sarauniyarta atake wani irin tsoronta da firgicin dabai taba jiba yasashi sauke kai yana girgizawa.

Ta bayansa yaji andafasa a zabure ya juya yaga itace yayi saurin kallon karagar yaga bata kai ya juyo yasake kallonta ta sakar masa murmushi mai sanyi tace,

Banason sanin sirrin dake zuciyarka sbd idanuwanka sun tabbarmin da abinda nake nema daga gareka wato soyayya mai qarfi dan haka masarautar mineelik takace kaima daga yau dakazama mijin mineelik.

Murmushin baqin ciki yasaki tareda miqewa ya juya mata baya cikin tsananin damuwa yace,

Idan 'yan uwana sunzo basu ganmuba zasu.......

Masarautar mineelik ta bayyanane ga dukkanin Wanda ke wannan nahiyar sbd duk girman wannan dajin da mutum zaiyi tafiyar kwana bakwai bai gama fitaba acikinsaba ba daji bane duk girman masarautar mineelik ne dan haka ayanxu mutane na kusa da nesa suna hanyar zuwa kallon masarautar dabasu taba gani ba ta mineelik data bayyana ga kowa.

Zai sake magana taga duk cikin tashin hankali yake mai tsanani
Ahankali ta riqo hannunsa cikin nata tsananin laushi da ni'imar fatarta yasashi kasa magana yabita tamkar raqumi suka nufi turakarta datafi kowace kyawu.
#mamuhgee
[8/1, 7:44 PM] ummul aulad: _*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡



*39*
_not edited_
Kallonta yayi da idanuwansa dasukai laushi sbd damuwa
Ahankali ya qarasa bakin gadon
Negasi ya bude baki zai dakatarda dashi ya daga masa hannu ahankali cikin mulki da bada umarni ya bude baki yace,

Ina buqatar ganawa da ita.

Cikin girmamawa suka fara ficewa ammy dake kallon rumanah kamar idanuwanta zasu fado zuciyarta na bugawa da sauri gabaki daya bata cikin nutsuwa so take taji rumanah tayi magana tasan halinda take ciki saidai rumanar idanuwanta a rintse suke
Kowa ya fice sai ammy da suhailat dake bayanta tsaye rungume da abeel zuciyarta na rauni.

Ahankali ya zauna kusada ita bakin gadon ya riqo hannunta ya damqe cikin nasa tareda qurawa fuskarta ido
Ahankali ta bude idanuwanta dasukai jajir ta kallesa zuciyarta na harbawa da sauri,

Zuciyarta qoqarin kallonsa takeyi a matsayin a iyayensa sukayiwa nata iyayen kisar ganganci da rashin imanin abinda ke cikin mahaifiyarta saidai kuma Sam zuciyarta takasa jin sauyi ko tsanarsa dan kuwa itama tana masa wani irin so ne Wanda bazata iya ganin laifinsa akan abinda maifinsa ya aikataba saida kuma batajin zatabar jinin duk Wanda ya zuba ya zube a banza sultan abdulshams zai dandani kalar nata rashin imanin.

Juyar da idanuwanta tayi kan ammy dake tsaye tana kallonta da idanuwanta dake bayyanarda tsananin damuwa da tashin hankalinda take ciki.

Ajiyar zuciya tasauke ahankali idanuwanta na cikowa da hawaye sbd itace ta rasa iyayenta,itace baiwa a dah,itace uwar da aka kashewa 'da tun kafin tafita daga radadin naqudarsa data wuni tana saidai ba itace abin tausayiba sune abin tausayin sbd yanda take jin zuciyarta dakuma sanin abinda ya samarda karagar mineelik batada tabbaci akanta da abinda zata iya yi sbd wani irin fushi,xafin zuciya, qunci,rashin tausayi da bushewa takeji a zuciyarta dan ita kanta ayanxu tasan tanada hadari sbd yanda takejin tamkar mineelik na cikin jikinta saidai soyayyar wainda take so da qauna tananan daram cikin ranta musamman shi daya zamo tamkar shine fitar numfashinta.

Ahankali ta miqawa ammy hannu.
Cikin tsananin farin ciki da 'doki ammyn ta qaraso ta zauna gefenta 'daya tareda kama hannunta cikin tsananin sanyin jiki tace,

Rumanah ki.......

Girgiza mata kai tayi ahankali ta bude baki tace,

Ke uwace agareni kuma zaki cigaba da zama uwata ko wane irin mataki na taka,kome nazama bazan ta6a iya cutatardake ba laifin da aka sakaki kikayi koda badason rankibane wannan tsakaninki ne da ubangijinki bazanso wannan maganar tashiga tsakaninmuba.

Kasa riqe hawayenta ammy tayi sbd kunyar rumanah ta miqe da sauri ta fice hawaye nabin fuskarta.

Qoqarin maida kukanta takeyi saidai takasa sbd radadin datake ji mai zafi na mutuwar da iyayenta sukayi
Da sauri ya rungumeta yanajin zafin ganin yanayinta tasaki wani irin kuka mai ciwo tana qanqamesa.

Suhailat dake tsaye tanason yimata sannu da jiki ta juya ta nufi qofa jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta na qoqarin jin zafi saidai tayi saurin kawar da hakan sbd ganin rumanar batada lafiya tana buqatar kulawarsa saidai duk yanda taso dannewa saida idanuwanta suka ciko da hawaye ta qanqame abeel ajikinta tana qara sauri dan isa gefenta.

Baice mata komaiba saida tayi kukan iya yanda zuciyarta keso kafin tayi shiru tana sakin ajiyar zuciya ahankali.

Dago fuskarta yayi yana kallonta ahankali ya shafota cikin sanyin murya yace,

I love you ummu-rumanah bulama maheer abdulshams.

Kallon cikin idanuwansa tayi akaro na farko dataji Kalmar na bata tsoro saidai tasan maheer 'dinta har abada bazai ta6a iya cutatar da itaba.

Lumshe ido tayi ahankali ta bude tace,

Ummu-rumanah nasonka tun kafin kace kanasonta saidai inason kayi min alqawarin zaka soni a duk halinda nashiga,
Bazaka gujeniba,
Kaine farin cikina soyayyarka itace qwarin gwiwata karka.......

Hannunsa ya dora a bakinta yana mata wani irin kallo yace,

Shihhhhhh get some rest now sbd gangar jiki da ruhi tare suke rayuwa tare suke barin duniya.

Kallonsa tasakeyi tasaki wani irin numfashi mai sanyi tareda sake komawa jikinsa ta kwanta.

Da kansa yakaita toilet tayi wanka ta fito tana duba closet dinta taga sabbin royal gowns 'dinda aka kawo mata ba adadi kowacce da kalar sarqoqinta nakai dana qafafu da hannuwa tareda wuya.

Doguwar English gown tasaka har qasa mara hannu takallesa lokacinda yasake shigowa dakin ya riqo hannunta suka fito palonta na farko har zuwa dining inda aka jera abinci fiyeda kala biyar da mamaki take kallon dining din sbd ganin duk girmansa ancikasa da kalolin abinci da fruits ga masu tsaronta mata da aka kawo tun daga palonta na farkon shigowa har wannan din sai wasu irin samudawan guards da aka zuba tun daga qofar part din dazagayensa har zuwa hanyar dazata rinqa kaita zuwa fada.

Kallonsa tayi yasakar mata wani murmushi ahankali tareda jawo mata kujera ta zauna tana kallonsa fuskarta daukeda qaramin murmushin qarfin hali sbd har lokacin zuciyarta cike takeda radadi sosai takejin kamar ana babbaka jinintane ana qunarsa mai laifi kadan take nema ta dau mataki akansa saidai kasancewarsa tareda ita yasa take iya control din yanda takeji saidai kamar abin nason yafara mata yawa.

Cikin nutsuwa sukaci abincin duk da kadan taci tasha maganinda aka aje kan dining din daga negasi.

Harsuka gama cin abincin idonsa nakanta sbd sosai ya lurada sauyi atareda ita saidai zuciyarsa naqara jaddadawa kanta arayuwa babu abinda zai rabata sonta.

Kasancewar bata fara sallah ba yasa yakaita daki yasake kwantar da ita ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa yace,

Inason sanin abinda yafaru tsakaninki da ammy.

Kallonsa tayi kafin ta dauke kai tana sake sawa zuciyarta qin ganin laifin ammyn kai tsaye tace,

Sultan ya kashe iyayena da taimakon ammy da jakadiya.

Cikin wani irin mugun yanayi na mamaki yake kallonta
Ta zame ta sauka gadon ta nufi bakin window ta tsaya.

Gabanta ya zagayo ya tsaya yana kallon cikin idonta ta rintse idon tana dauke kai.

Ahankali ya bude baki zaiyi magana ta bude idanuwanta dasukai ja ta katsesa cikin sanyin murya da cewa,

Bana maka wani kallo na daban a zuciyata bayan Wanda nake maka na mahadinta ko Allah baya kama wani da laifin wani....

Shiru tayi tana tauna Kalmar dazata fada cikin qarfin hali tace,

Na yafewa ammy sbd Allah da soyayyarta gareni da kasancewarta mahaifiya kuma kaka ga mutane biyu danafiso ayanxu fiyeda rayuwata dakomai,kai YARIMA MAHEER ABDULSHAMS da ABEEL HASSAN......

Cikin sanyin murya dake nuna baqin cikin dayake ciki ya furta,

Sultan f....

Bai qarasaba tace,

Kayi hakuri.

Ta juya masa baya cikin wani irin zafi datakeji a zuciyarta ta rintse ido tasake cewa,

Kayi hakuri.

Kasa motsi yayi sai idanuwansa dasukai jajir yana jujuya kalmarta ta yayi hakuri....zata dauki mataki akan mahaifinsa kenan.... No not possible...tokuma ko Ba itace akan mulkiba tana buqatar justice.....

Ficewa yayi sbd jin kamar numfashi na masa wuyar ja ko gani sosai bayayi sbd tashin hankalin dayake ciki.

Suhailat dake tsaye gaban windonta taga fitowarsa daga sashen na rumanah ta 'dauke kai tareda barin jikin windon sbd gujewa ganin damuwa.

Yana fita ta zauna bakin gado tareda dafe kanta ta rintse idanuwanta kanta na mata wani irin ciwo.

Koda dare yayi duk yanda taso bacci kasawa tayi sbd kewar iyayenta da 'yayanta.

Koda gari ya waye qarfe goma wata zungureriyar takardar saqo daga alqalamin sauraniyar mineelik ummu-rumanah bulama ta isa hannun sarkin fada haroun inda saqon yake cewa ayau angama karbar duk wani bayani akan asalin sarauniya ummu-rumanah daga baiwa mamani dan haka ayau za'a yanke mata hukunci.

Atake aka buga sanarwa koina ya dauka qarfe goma sha daya jama'a suka taru ana jiran isowar assultana.

Cikin wata irin royal gown tafito red mai adon golden gashinta koina rufe da adon sarqar farin zinari wasu irin samudawan guards ne maza da mata taredasu Jakadiya a bayanta ta fito suka nufi fada.

Cikin nutsuwa na wani irin miskilanci ya yasha gabanta yana kallonta guards din bayanta suka nufosa ta 'daga musu hannu tareda juyowa cikin nutsuwa ta kalli Jakadiya tace,

Duk Wanda yasake gangancin tare mijina aduk lokacinda yakeda buqatar magana dani yana ganganci da rayuwarsane a sanarda kowa.

Cikin tsananin ladabi dukkaninsu suka sauke kai suna tuba.

Ta juyo ta kallesa cikin nutsuwa tace,

Ina kwana?

Kallonta yayi kafin ya watsawa su jakadiya wani mugun kallo atake suka ja baya sukai 'dan nesa kadan dasu.

Ya kalleta cikin ido yace,

Bazaki yankewa mamani hukuncin kisaba that's an order amatsayin na mijinki
Ba mamaniba har kowama bazaki yankewa hukuncin kisaba nin......

Sultan ne bakason a kashe ba mamani ba"""ta fada tana kallonsa cikeda fargabar abinda zaice.
#mamuhgee

Sorry manage.
[8/3, 7:40 AM] ummul aulad: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_



*40*
_Not edited_
Kallonta yayi yana sake kafeta da manyan idanuwansa ransa na qoqarin 6aci da zancenta zuciyarsa na qoqarin hana faruwar hakan ya bude baki zaiyi magana ya fasa ya kama hannunta da qarfi ya jata part din ammy dake kusa
Tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta cikin sautin dake nuna bacin ransa yace,

Me kika fada yanxu?

'Dauke kai tayi kai tsaye tace,

Kana qoqarin kare sultan ne akan laifukanda yariga ya aikatasu ne cikin son rai da ganganci saidai kuma nariga nayi alqawarin duk Wanda ya cutatar da wani sai anbi masa haqqinsa sbd wannan shine adalcin assultana,wannan shine banbancin mulkin son rai da adalci....duk Wanda ya kashe a kashesa wannan shine hukuncin a musulunce.....

Riqota yayi da qarfi ransa na qarasa 6aci yace,

Kina tunanin na hanaki hakane sbd sultan yana nahaifina?
Kisa dai matuqar ina raye kuma da aurena akanki bazan ta6a bari kiyiba ko adama kin kashetane a lokacinda bana kusa da bazan taba bari ki kashetaba and da.....

Qwacewa tayi tana kallonsa tace,

Nice na kashe adama kana qoqarin cemin mai kisa ne????
Bayan kasan mutanen nan sun cancanci kisa tako wane sashe na sharia,
Anyiwa iyayena kisan wulaqanci da son rai,
Anyiwa 'dana kisar son rai da ganin dama duk basune masu laifiba nice danake shirin qaddamar da adalci wa kaina amma y.......

Idan kina maganar abeel Hussain ne ni mahaifinsa nabarwa Allah duk Wanda keda saka hannu nabarsa shida ubangijinsa maganar iyayenki kuma amatsayina na mijinki nake baki umarnin kibarwa Allah bazaki qara yankewa kowa kisar wulaqanciba ki tabbatarda idan kika sake hakan ni maheer abdulshams mungama zama tare abakin aurenki gabak......

Cikin tashin hankali suhailat dake palon basusan da itaba tayi saurin katsesa da cewa,

Abu abeel ka.....

Shut up and stay out of this suhailat"""""yafada ransa a matuqar 6ace.

Rumanah datai mutuwar tsaye tana kallonsa idanuwanta sun kada jajir suna zubo hawaye zuciyarta takai qololuwa gurin tashin hankali da baqin ciki ta bude baki cikin baqin ciki tace,

Basaika datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai........

Fixgoto yayi da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki 'daya ya kasheta jitake zuciyarta kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.

Cikin tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake zaune cikin tunani abinda yake faruwa.

Da sauri ta taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.

Rungume rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.

Kasa tsayawa yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da maganganunta.

Suhailat dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin 'ya da uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer 'din.

Shiru ammy tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,

Maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login