Showing 81001 words to 81312 words out of 81312 words
ido atake dukkanin jamar gurin mamaki da tsoro yakamasu musamman maheer dabaisan da hakanba yakalleta da sauri saiyaga tana qoqarin danne abinda takejine dan daidaita nutsuwarta yafasa maganar dayayi niyya ya damqe hannunta dake cikin nasa sbd har lokacin a tsaye suke taredasu ammy da jakadiya da masu tsaron lafiyarta.
Cikin wata irin budaddiyar murya sarkin fada haroun ya bude wata irin zungureriyar takarda mai daukeda tambarin masarautar mineelik dake daukeda saqon assultana yafara karantowa kai tsaye da qarfin muryarsa yanda kowa zaiji.
"""" NI SARAUNIYAR MINEELIK UMMU-RUMANAH BULAMA AYAU SHA BIYU GA WATA NA BIYAR A SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NA SOKE KARAGAR MINEELIK DAN KAWO QARSHEN MULKIN ZALINCI INA GABATAR MUKU DA SABUWAR KARAGA GA WANNAN MASARAUTA...HAKA KUMA AYAU SHA BIYU GA WATAN BIYAR SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NI UWAR MAGAJI SARAUNIYA UMMU-RUMANAH NA SAUKA KAN MULKIN MASARAUTAR MINEELIK TAREDA 'DORA SABON SARKI ABDALLAH ABDALLAH AMMED""
Atake dukkanin gurin yadauki wata irin kabbara da koke koken farin ciki da sbd wannan wani irin babban alamarine yazo musu na sauyi daga mulkin azaba musamman Abdallah Abdallah ammed mahaifin khaleefa mutum ne dazai kawowa rayuwarsu sauyi na adalci gashi shikansa baisanda zancenba.
Tsit aka sakeyi lokacin wasu irin majiya qarfin bayi kusan goma sha biyar suka ciccibo karagar mineelik Wanda keda wani irin girma tareda hularta.
Wani irin baro mai tsananin girma da fadi daukeda wani irin mahaukaciyar tukunta mai tsananin tiriri yaran negasi kusan su ashirin da biyu suka turo aka ajiye tsakiyar filin harabar.
Ta lumshe idanuwanta dasuka fara rufewa suna gani dishi dishi ta budesu daqyar ta iya 'daga hannu ta bada umarni atake haroun yabada umarni aka 'daga karagar aka saka ciki atake tafara nitsewa tana narkewa cikin ruwan dalmar tun tana gani dishi dishi sbd jinin daya balle hancinta atake idanuwanta suka rufe ruf ta yanke jiki ta zube gurin jini na qarasa balle mata ta hanci da bakinta.
#mamuhgee