Showing 27001 words to 30000 words out of 81312 words
babu bata dogon lokaci suka gama home made pizza sai boiled vegetables da kuma fruits salad din yarima.
Itace ke jera abinci a dining din suka shigo
Shine agaba hannunsa riqeda riqar suit dinsa ta sama farar long sleeve dinsa kamar yanxune yasata
Kallo daya tayiwa hanyar shigowar ta sauke kai tana aje cups din hannun ta.
Shi ko kallon inda take baiyiba duk da acikin idon juna suka fara cikin karo ya wucewarsa sama.
Dagowa tayi tabi bayansa dakallo yana kaiwa qofa zai shiga ya tsaya cak
Tayi saurin dauke kanta shima baijuyoba sai yashige.
Ajiyar zuciya tasaki cikin ranta tana qoqarin daidaita numfashi.
Ammy dake kallonsu tun shigowarta tasaki numfashi tareda nufar hanyar bedroom dinta tashiga.
Wanka yayi yayi sallar magrib yana zaune kan sallayar akayi ishai yafito yaje masallaci dagacan yana dawowa ko shigowa baiyiba hospital yakoma.
Kwance take idanuwanta a rufe amma hawayen daya gani yasashi sanin idonta biyu yakalli nurses din dake tareda shi da sauri suka fice.
Shafa fuskarta yayi ta bude idanuwanta dasuke jajir ta qura masa ido zatai magana ya girgiza mata batareda yabude bakiba.
Share hawayenta tayi daqyar sbd nauyin jikinta cikin tsanani sanyin murya tace,
I love you...i love you and pls always remember it even in the future.
Lumshe ido yayi batareda yace komaiba ya sunkuya yayi kissing forehead dinta murya daqyar yace,
Time to sleep,Gud night.
Lumshe ido tayi tareda gyara lullubinta ya sake kissing dinta yafice bayan yaduba file dinta.
Koda ya isa gida babu kowa a palo sai sultana itama dan tanason ganinsa ne.
Yana ganinta yasan dawowarsa take jira yayi kissing hannunta yace,
Gud night ammy jeki kwanta nadawo.
Murmushi tayi tareda miqewa ta fuskanci qofar bedroom dinta harzata wuce tace,
Gobe inason kayi mana booking flight zamu wuce Libya nida rumanah zuwa jibi,
Kuma inason kafin natafi da ita tasan matsayin aurenta sbd idan munje ba dawowa zamuyiba acan inason tasamu sabuwar rayuwa dan haka kanada zabin iya sauwaqe mata kafin jibi muwuce.
Tana gama fada bata juyoba ta shige dakinta.
Cak ya tsaya bakin stairs din tun lokacinda tafara magana harta gama yana waiwayowa tana shigewa.
Qofar dakinta yakalla kafin ya haye yana isa daki ya kashe wayarsa data damesa da ringing batareda yaduba mai kiranba.
Tubewa yayi yafada toilet yayo wanka yana fitowa yagama shirin kwanciya ya kwanta.
Gari na wayewa ya qarfe tara saura ya sauko cikin shirinsa sbd yanada tiyata har biyu yau.
Motsi yaji dakinsu amah yasa ya tsaya tareda waiwayo qofar tareda tunanin meyasa basu tafi school ba har time din.
Tura qofar dakin yayi daidai zata fito saura kadan suyi karo tayi sauri matsawa gefe cikeda jin nauyin rigar dake jikinta ta bacci sbd ganin Carolina taje kaisu amah school tareda driver yasa take gyaran koina kafin caro din tadawo ta rage aiki.
Qura mata ido yayi tsawon mintuna kafin yakalli hannunta ya dauke kai yafice ko gaisuwarta bai tsaya amsawaba.
Saidata tabbatarda ya fice ta dago kai tareda kallon qofar ta daga hannu daqyar taci gaba da aikinta.
Bayan tagama gyaran dakin sultana harzata fita cikin kulawa takira sunanta.
Dawowa tayi ta zauna gabanta cikin ladabi ta amsa.
ki shirya gobe insha Allah zamu wuce Libya,
Rumanah duk Wanda qaddara da jarabawar ubangiji tasama ya rungumeta da imani Allah baya taba bari ya wulaqanta shiyasa nake miki kyakkywan zato sbd ke mai hkr da yarda da qaddarace dan haka ki yarda da qaddarar dazatazo miki dangane da aurenki insha Allah zaki samu kwanciyar hankali da kwakykyawar rayuwa Libya.
Gyada kai tai jiki asanyaye sbd dama tasan aurenta bamai dorewa bane.
Miqewa tayi ta fice.
Tausayinta sultana taji saidai tasan raba auren shine yafi a rayuwar rumanah din sbd maheer bazai taba daukarta amatsayin mataba dan haka gwara ya sauwaqe mata su tafi can ko karatu tasamu tayi har Allah yakawo Wanda zaisota sbd tasan sunyiwa rayuwar rumanah illar da har abada basa fatan tasan sune sukayi mata wannan illar dan kuwa qiyayyarsuce zata ture girmansu a idonta shiyasa takeson ta nesantata ma kwata kwata da mineelik idan tana tareda maheer batai nesa da mineelik ba kuma shikansa idan yagano wannan sirrin saiya tsani sultan da ita kanta mahaifiyarsa.
Rumanah na fitowa tacigaba da ayyukanta jiki asanyaye harsuka gama ta nufi daki tayi sallah azahar tananan zaune Shiru akai la'asar tayi ta fito suka hau aikin abincin dare.
Suna gamawa Carolina ta nufi dakin suhailat tafara aikin gyara sbd washe gari da safe akace za'a sallamota tadawo gida.
Itadai rumanah Suna gama girki ta nufi dakinta tayi alwala tayi sallar magrib tana idarwa tafara hada dukkanin kayanta ta shiryasu a akwatinanta biyu tana gamawa ana kiran sallar ishai tasako wata alwala tazo tayi sallah.
Bayan tagama abinci tafito taci daqyar sbd ko yunwa ba bataji ta dauki apple daya takoma daki.
Tana shigowa ta tube tashige toilet tayo wanka ta zauna sanyaye gaban mirror spray na Prada tadaure dogon gashinta ta zauna zugum.
Qarfe takwas su amah sukai dinner Carolina tashige dasu tayi musu wanka sukai shirin bacci kafin suka fara karatu da tab dinsu daganan kowannensu bacci yayi gaba dashi.
Sultana sai qarfe tara da rabi tayi dinner sbd ganin maheer baidawo da wuriba.
Tana zaune palon tana kallon news qarfe goma da rabi yashigo yana waya.
Ganinta zaune yasashi dakatarda wayar ya kashe gaba daya ya zauna gefenta yana gaidata.
Ciro komai na tafiyarsu yayi ya miqa mata sosai gabanta ya fadi da ganin itada rumanah nedai zasu tafi,
Duk da wani sashe tanason raba auren amma batayi zaton zai barsu su tafi tareba tayi zaton itakadai zai siyowa ticket din.
Karba tayi tareda ajewa gefenta tace,
Wane time ne flight din?
9:00am""""yafada yana miqewa.
Abiyoka da dinner dinka?
Girgiza kai yayi batareda yajuyo ba yace,
Abani fruits kawai.
Ajiyar zuciya tasauke sbd zancen dazata fada amma ta daure tace,
Idan takawo ka rubuto mata sallamarta sbd nunawa sultan sheda nan gaba.
Juyowa yayi yakalleta kafin ya juya ya wuce.
Yana shiga dakinsa tubewa yayi yafada wanka.
Dakanta ta isa kofar dakin rumanah din ta tura ahankali tashiga da sallama.
Miqewa tayi da sauri ganin sultana dakanta tazo kiranta cikeda kunya dajin nauyi ta durqusa sbd rigar bacci kawai ajikinta.
Ganin tanajin nauyi yasata dauke kai tace,
Kije ki kaiwa maheer fruit.
To ammy'""""tace ahankali cikin nutsuwa.
Idan kin kai kindawo inajiranki adakina.
Sake gyada kai tayi.
Saida ammyn ta fice ta miqe ahankali tareda daukar doguwar riga mai ma6alli biyu agaba da hula tasaka tafito ta nufi kicin.
A qaramin tray ta zuba ta dauki qaramar wuqa ta nufi saman.
Sanin baya palo yasa ta murda tashiga ta isa qofar bedroom dinsa ta daga hannunta dake rawa tayi knocking ahankali.
Jin shiru harso uku yasata murda tashiga
Duhune sosai adakin shiyasa ta tsaya cak tsakiyar dakin.
Ba zato taji anriqo hannunta tayi saurin rintse ido numfashinta na fita da sauri.
Bedside lamp ya kunna tagansa tsaye gabanta cikin sanyeda dogon wandon bacci fari qal amma baisaka rigaba murdadden jikinsa a bayyane ya kafeta da lazy eyes dinsa tuni jikinta yasake daukar rawa ta aje tray din kan table din tsakiyar dakin ganin zai kufce mata.
Yana ajewa ta Juya taji hannunsa yariqo nata ta tsaya cak.
Dawo da ita yayi ta baya ahankali bayanta yahadu da qirjinsa.
Rintse ido tayi numfashinta na tsananta fita ya zura hannunsa daya ya balle botins din rigarta lokaci daya ta zame qasa ta fadi
Sake rintse idonta tayi da qarfi amma ko hannu daya bata daga.
Juyo da ita yayi suka fuskanci juna yana kallon fuskarta yasa hannu ya zame rigar baccinta
Rigar na barin jikinta tasaki kuka ahankali ya jawota yasaka cikin jikinsa lokacin kukanta ya tsananta
Sai kawai ya dauketa ya nufi gadonsa da ita akaro na farko ya hada bakinsa da nata.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationš”_
*21*
Not edited
Sanin batada ikon gardamawa yasa bata gardamaba ta rintse idanuwanta ahankali tareda Jan wani irin numfashi jin hannuwansa sun sauka a qirjinta,
Sakin bakinta yayi ahankali ya dago lazy eyes dinsa yakalli idanuwanta dake rufe
Ya kai bakinsa saitin kunnenta ya furta mata wata kalma ahankali ta bude jajayen idanuwanta sai cikin nasa ta lumshe ido tasake budewa yakai bakinsa ahankali yayi kissing idonta na dama tareda cusa kansa cikin wuyanta yana giga mata dogon hancinsa nan tsigar jikinta duk ta miqe
Yasake dagowa ya kalleta hannuwansa na 'dago masa kanta idonsa cikin nata ya Dora bakinsa anata ta rufe ido ahankali sbd jin inda hannunsa ya nufa.
Duk yanda takeda juriya saidata zubarda hawayen wahala sosai musamman data tabbarda ta fita daga cikin sahun 'yan mata har abada.
Lumshe idanuwanta tayi hawaye suka gangaro tareda kallon qofar bathroom dinda yashiga.
Har lokacin jin hannunwansa da kisses dinsa takeyi ajikinta Wanda suke qoqarin ruda mata kwakwalwa saidai ko tashi bazata iyayiba sbd ba qaramar gajiya ya sauke akantaba ta rufe ido bacci yayi gaba da ita ahankali.
Qurawa kansa ido yayi ta cikin mirror tareda rufe ido yabude yasake kallon fuskarsa ya fitarda numfashi tareda mamakin kansa da yanayin dayakejin kansa.
Wanka yayi yafito daure da towel batareda yakalli gadon datake kwanceba ya nufi gaban mirror yayi amfani da hand dryer ya busarda gashinsa ya saka wasu kayan baccin ya nufi gadon.
Kwantawa yayi ya qurawa fuskarta datai jajir ido dagayen eyelashes dinta duk sun nannade da hawaye sbd kukan datayi duk da bamai sauti bane kukan,
Suhailat bata taba masa kuka ba idan suna making love ko a first time dinsu kuwa.
Rufe idanuwa yayi tareda shigewa dovet.
Qarfe takwas sultana ta fito palo cikeda mamakin rashin ganin rumanah din zuwa gaidata.
Zama tayi tareda kallon Carolina dake jera breakfast a dining tace takira mata rumanah.
Aje aikin tayi ta nufi dakin rumanah da sauri tana budewa bata gantaba tadawo cikin ladabi tace tana toilet.
Gyada kai sultana tayi tareda miqewa takoma bedroom dinta.
Bayan mintuna tasake fitowa sbd ganin time din tafiyarsu yana matsowa tasake aikawa still tana toilet cikeda mamaki ta nufi dakin da kanta saidai har toilet taduba babu rumanah.
Duk inda ake saka ran ganin rumanah Carolina taduba batanan hakan yasa sultana zauna palo cikin fargaba tafara qoqarin kiran wayar maheer amma no answer.
Ahankali yabude idanuwansa cikin wata irin kasala yana kallon agogo ya dafe goshinsa cikin mamakin bacci mai nauyin daya hanasa tashi.
Gefensa ya kalla yaga har lokacin bacci take dunqule cikin duvet gashinta duk a barbaje kan pillow.
Fita duvet din yayi ya sauka gadon ya nufi toilet ganin yayi latti sosai yasa bai tsaya wanka ba yayo alwala yaxo yatayarda sallah.
Yana gamawa ya dauki wayarsa daketa fidda blinking alamar kira
11 missed call daga hospital yasan suhailat ce aka sallama
Sai 9 missed call daga ammy
Miqewa yayi yafada toilet.
Yana shiga tailet ta farka ta bude idanuwanta ahankali sbd nauyin bacci dana kukan datayi tana ganin baya dakin tafara qoqarin miqewa ta sauko daqyar riqeda bargo tana rufe jikinta tajawo rigarta ta barci dake tsakiyar dakin yashe.
Tana daukar rigar yana bude qofar toilet yafito daure da towel,
Kasa dagowa tayi bare ta juyo saima rawa da jikinta keson dauka.
Shareta yayi ya nufi gaban mirror yana goge gashinsa sbd Sam bayajin damuwar komai ko gajiya ras yakejin kansa.
Ganin kamar hankalinsa baya kanta yasa tayi saurin zura rigarta ta cikin bargon amma still kasa miqewa tayi.
Wayarsa tayi blinking yaga kiran ammy ne yayi saurin kallon agogo yaga har tara takusa Sam yamanta da tafiyarsu.
Shiryawa yayi cikin white shirt and blue jeansy trouser ya daure gashinsa ya dauki wayarsa ya nufi qofa,
Zai fita ya tsaya batareda yajuyo ba yace,
Saura 40min jirginku yatashi.
Yana gama fada yafice daga bedroom din.
Qofar ta kalla bayan ya wuce ta rintse idanuwanta ahankali tareda fitarda numfashi ahankali kafin ta miqe ta taka daqyar ta dauki doguwar rigarta ta zura kan rigar baccinta ta nufi qofa tana qoqarin daidaita tafiyarta duk da zafinda takeji.
Saukowa taringayi ahankali harta gama saukowa ta nufi dakinta
Tana kaiwa tsakiyar palon tayi ido hudu da sultana zaune ta zuba mata ido cikeda mamaki.
Sunkuyar dakai tayi idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin kunya da nauyin ammyn.
Juyowa sultana tayi ahankali cikeda mamaki takalli inda yake zaune yayi tamkar baimasan da isowar rumanah dinba ya danna kira asibiti.
Kasa maida kallonta tayi kan rumanah sai kawai ta miqe ta nufi dining.
Jiki sanyaye ta qarasa daki tafada toilet sai kawai tasaki siririn kukan kunya da ciwon da jikinta ke mata.
Wanka tayi da ruwan zafi sosai kafin ta lallaba ta fito tayi sallah ta shirya cikin sauri sauri ta fito kai sunkuye.
Kallonta ammy tayi cikin sanyin murya tace,
Kizo kiyi breakfast mutafi munyi latti.
Kai ta daga ta nufi kicin a darare ammy tabita da sabon kallo harta shige tasake juyowa takalli maheer dako gefensu yaqi kallo,
Mamakin duniya ne ya taru akanta gashi Sam ko fuskarda zatai masa wata magana yaqi bata bare taji makomar rumanah daga garesa.
Daqyar ta iya shan tea da biscuit ta fito daidainan Carolina tagama fitar mata da kayanta zuwa mota.
Kodata fito ammy ta nufi waje sbd sunyi latti sosai dan haka ba kowa a palon saishi azaune yana waya
Qofa ta nufa riqeda qaramar jakarta tana qoqarin wucesa yakara mata qafa ta kwashi wani mugun tuntube ta fada masa ya aje wayar hannunsa tana qoqarin tashi ya matseta da hannunsa daya tareda kallon cikin idonta ya dauke gira daya cikin izza yace,
Ance kitafi ne?
Kallonsa tayi da sauri kafin ta Girgiza kai.
Hannunta yakamo yasaka mata wata Leda tareda sakinta ya miqe yafita batareda ya waiwayo ba.
Bayansa tabi da kallo kafin ta dawo da idonta kan ledar daya saka ahannunta taga magungunane
Sake dagowa tayi takalli qofar fuskarta da mamaki.
Qofa ta nufa ta fito tana sake damqe ledar maganin a hannunta ta nufi motar da tagansu.
Driver ne zai kaisu dan haka dukkaninsu baya suka shiga yana tsaye yana kallonsu aka tayarda motar
Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa idonsu yashiga cikin na juna tayi saurin sauke kai tareda sake damqe ledar maganin daya bata.
Suna fita yafidda key ya nufi hospital sbd tuni suhailat ta damu dayazo daukarta
Shikuma ji yake da bayada aiki sosai ammynsa xaibi Libya sbd damuwar sultan yasan haryanxu tana ranta.
Yana isa asibitin yahadu da doctor dinda ke kula da suhailat sukayi magana da sauran rubuce rubuce suka nufo gida.
Tun ahanya takeson tambayarsa maganar rumanah saidai zuciyarta na gargadin bakinta da furtawa sbd sanin bazaiso maganarba karma ta bata masa rai da kiran sunan an aura masa baiwa.
Suna isa gida ta tararda komai fes tashiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin simple kaya marasa nauyi ta nufi bedroom dinsa.
Cikeda mamaki ta tsaya tsakiyar dakin tana sake bude hancinta sbd dakin wani qamshi yakeyi na dabam Wanda ta tabbar bana maheer bane.
Zama tayi bakin gado ta rafka taguma tana wasi wasin tunani
Ganin qamshin zai iya buga zuciyarta yasa ta miqe tabar dakin sbd dama bayanan yana ajeta ya koma asibiti.
Sun isa Libya da qarfe shida na yamma motocin masarautar mahaifanta sukazo daukarsu cikin qanqanin lokaci suka isa babbar masarautar mai tarin dukiya da adalci
Masarautar mineelik saidai ta nuna musu girma da iko tareda dukiya wadda ta hada data mulkin mutanen da ba'a gani sbd dukiyarsu nada alaqa data mutanen daba nasuba amma a fagen adalci da qaunar talakawa da basu yanci basu kamosu ba ko kadan.
Saida suka sauka fadar sultan jalaluddeen suka gaidashi tareda gabatarda rumanah amatsayin matar yarima maheer yasawa aure albarka kafin suka isa babban sashen sarauniya salma matar sultan jalaluddeen mahaifiyar sultana zaarah.
Sosai aka hau hidimarsu duk da manyanci daya kama sarauniya salma tayi farin ciki da murna sosai ganin rumanah amatsayin matar yarima maheer sbd lurada nutsuwarta.
Sashe guda aka ware musu acikin part din sarauniya salma mai daukeda palo da bedrooms guda biyu dasukaji gyaran tsadaddun decor.
A babban palon s salma sukaci abincin dare tareda ita kafin kowannensu ya nufi dakinsa.
Tubewa tayi tashiga wanka ta jima tana dumama jikinta kafin tafito ta shirya cikin kayan bacci tayi sallolinta harzata kwanta taje ta dauko ruwa tazauna bakin gado tareda fiddo maganin daya bata tasha takwanta cikin qanqanin lokaci bacci yayi gaba da ita.
Bacci tayi sosai mai dadi sbd gajiyardake jikinta bata farkaba sai bayan sallar asuba ta tashi tayo alwala tayi sallah tasake komawa ta kwanta.
Qarfe tara ta tashi tayi wanka tashirya tafito cikin doguwar riga black mai adon red sequence stones.
Dakin sultana ta nufa ta tararda ita tana waya tajira harta gama ta gaidata cikin girmamawa.
Cikeda kulawa sultana ta amsa tareda cewa,
Ya jikinki?
Shiru tayi takasa bata amsa sbd nauyi.
Shikenan tashi kije zansa afara kulawa dake harkiji sauki sosai sbd haryanxu jikinki bai nuna kin warkeba.
Kamar munafuka ta fito sbd tsananin kunya da nauyin ammyn datake ji musamman data riga tasan tabbas ammy tasan meya faru tsakaninsu.
Kodataje gaida s salma acan tayi breakfast dinta har akazo kiranta ta tashi tabisu tanaji tana gani aka hau gyaranta da gashinta kullum cikin sakata cikin ruwan zafi da wasu irin magunguna ake kuma kullum sai anbata 'danyar madara tasha cup daya da safe gashi aiki ko daya anan batayi saidai idan taji jikinta yayi tsami da yawa taje dakin sultana tahau aikin gyara mata kayan wardrobe da wankin toilet duk da akwai masuyi amma wani lokacin tafison tanayi.
Satinsu biyu tasaba sosai da kowa,
Sultana mamakin rumanah takeyi bata taba tunanin zataga rumanah tasake hakaba shiyasa ba bata lokaci tasa aka dauko wani Mexican malamin wata collage yana zuwa koya mata karatu.
Sosai tayi fresh abinta ta dire dakyau kyawunta tuni yaqarasa bayyana sbd Hutu da gyaran da ake mata kamar kullum.
Wanka tafito ta shirya cikin kayan bacci riga da wando tazauna bakin gado tareda jawo bedside drawer taqurawa ledar da kullum saita kalla ido tareda lumshe fararen idanuwanta tanajin hannunsa ajikinta lokacinda zai saka mata ledar ahannu.
Sake lumshe ido tayi tareda zamewa ta kwanta ahankali tana jin wata irin kasala.
Sosai ta warke takoma tamkar batai ciwoba sun cigaba da rayuwarsu kamar da tuni tafara zuwa aikinta hankalinta kwance sbd ganin maheer yamanta da wata maganar aure da aka daura masa,
Abinda yake damunta yake hana mata bacci wani bi 'dayane,
Maheer Sam bai cika nemantaba kamar da ataqaicema yarage sha'awa sosai sbd wasu lokutan tana lure da inda baya taba mata da yanxu yana tabawa saidai ita Sam bataso musamman nonuwanta Sam batason yana yawan tabasu sbd batason suyi laushi da wuri gashi dama shayarwa tafara lausar mata dasu.
Ada Sam basu damesaba shima amma yanxu yanason tabawa tarasa meyasa hakan.
Wannan karon sbd ganin uwar datasha dakuma tiyatar da akai mata yasa tayi allurar shekara biyu sbd tahuta mahaifarta tasake qwari.
Fitowarsa wanka kenan daureda towel wayarsa tayi ringin yakalli wayar kamar bazai daukaba saikuma ya daga.
OK kawai yace ya aje wayar ya shirya cikin kayan shan iska ya sauka.
A palo ya tararda baqon nasa yadauki remote yana canza tasha yace,
Uhumm.
Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace,
U wanted to