Showing 54001 words to 57000 words out of 81312 words

Chapter 19 - Tarayya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

17 Dec 2024

250

ayi adalci ayanke hukunci daidai yanda yakamata.

Atake mutane suka fara kallon kallo da hayaniyar abinda aka fada nan mamaki ya kama sultan kenan har akwai wainda zasu iya tambayar hukuncinsa su qalubalanci yanayin mulkinsa
Atake yace aje a kama Jakadiya arufe ya 'daga hukuncin zuwa gobe duk me hannu aciki kafin faduwar rana baya duniya.

Lokacinda akaje aka kama Jakadiya aka rufe
Sultana kuwa rufe sashenta akayi tareda aje masu tsaron qofar da doka mai qarfi daga sultan babu Wanda zai shiga gurinta ajira hukuncinsa zuwa gobe.

Lokacinda zancen ya isa kunnen maheer kai tsaye gurin sultan yanufa akai masa iso lokacin anwatse sai gobe a shaida hukuncinda zai iya yankewa.

Kallonsa yarima yayi cikeda takaici da baqin cikin yanda yasan sultana bazata aikata hakan ga yayansa ba amma ya yarda haryana iya tunanin yanke mata hukunci
Kai tsaye yace,

Amatsayina na uban magaji zan kar6i mulkin mineelik har lokacinda zai girma ya karbi da hannunsa.

Wani irin murmushin takaici sultan yasaki batareda yakallesaba yace,

Mulkin mineelik da za6ar mai mulkin na mutum 'dayane yanxu dan haka ka rasa damarka,
Mahaifiyarka kuma koni bazan iya kubutarda itaba idan har bincike ya nuna da hannunta aciki.

Yana fadar haka ya shige tabarsa zaune idanuwansa na kadawa jajir.

Duk inda tashin hankali yake masarautar na ciki dan shi kansa sultan jinjina alamarin yake aransa yana jaddadawa yana kuma fatar bincike yasa kar asamu hannun sultana aciki.

Acikin daren babu kalar azabar daba'a bawa mamaniba tace Jakadiya tasaka ta.

Jakadiya aka hau bawa baqar azaba amma daqyar take iya furta babu saka hannunsu aciki.

Acikin daren saqon neman sulhu da sassaucin hukunci yazo daga masarautar Libya dakuma wasu masarautun duk sai alamarin yasake girmama ya sake cabewa sultan gashi komene adaren ne sbd gobe dolene zai yanke hukunci.

Nuratu datun jiya take kuka da tashin hankalin halinda mamani ta fada koda bincike yazo kanta ba qaramin rikicewa tayiba saidai tafada musu komai na dangane da zancen dasukaji su Jakadiya nayi da sultana itada rumanah akan basuso ta haifi namiji.

Atake aka kaiwa sultan wannan zancen hankalinsa ya matuqar tashi saidai har lokacin yanada wasi wasin zancen ga asirinsu na 6oye daya fara shigowa cikin zancen Wanda tonuwar dolema yayi gaggawar yanke hukunci sbd kar maganar ta bankado atake ya yanke hukuncin kisa ga dukkaninsu ukun gobe.

Acikin daren hankula suka masifar tashi jin anyekewasu sultana hukuncin kisa washe gari.

Duk wata zuriar masarautar tun acikin daren suka fara isowa musamman 'yayan sultana da kuka sunyisa na zuci dana fili hankalinsu amatuqar tashe yake.

Yarima maheer Kansa ya rufe adaki duk yanda yake tunanin masifar ta wuce nan abu 'daya yasani bazai mahaifiyarsa ta fuskanci hukuncin kisar wulaqanciba.

Kwance take lamo idanuwanta jajir ko kukan bata iyayi duk abinda yake faruwa bata saniba sbd ta hana abar kowa shigowa gurinta.

Ahankali taji antsaya akanta batareda tadagoba ta lumshe ido tareda budewa taji muryar suhailat cikin wani irin yanayi tace,

Nazo neman alfarma agurin sbd kece kawai zaki iya tsayarda abinda ke shirin faruwa.

Tashi zaune tayi ahankali batareda takalli suhailat dinba
Itama suhailat sauke kanta tayi sbd batason kallon rumanah dan ganinta ke tuno mata da ba itace zuciyar mijintaba.

Hawayene suka gangaro mata tasaka hannu ahankali tashare taci gaba da cewa,

Nice uwar datai rashin abu biyu lokaci daya kuma zuciyata cike takeda neman adalci,
Ina roqonki amatsayina na uwar data rasa 'da da mahaifarta akan adalci zanso ganin anmin adalci saidai bazanso akashe Wanda bashine mai laifinba sbd mai laifin zai cigaba da aikata 6anna aboye har wadda tafi wannan.

Cikin dasashiyar murya da sanyi tace,

Adalcin nima nake nema amatsiyana na marainiyar da aka raba da iyayenta dakuma uwar da aka rabata da 'danta tun bata gama warkewa daga zafin naqudarsaba.

Asubar fari yashigo dakinta idanuwansa da yanayinsa suka karya mata zuciya ta dauke kai daga kallonsa tareda mayarda kanta kan gwiwoyinta.

Tsayawa yayi agabanta zuciyarsa cikeda baqin cikin kasancewarsa shine zai roqi wani yabasa sarautarda shine ya gada saidai yasan kubutarda ammynsa na nufin ya karbi sarautar ayau yazamo shine zai yanke hukunci sbd yagano sultan sbd 6oye wani sirrinsa yakeson yanke hukuncin da gaggawa ayau.

Kallonta yayi da idanuwansa dasukai jajir yace,

Inason kibani sarautar mineelik ayau.

Kallonsa tayi da sauri da jajayen idanuwanta dake budewa daqyar sbd kumburi.

Juya mata baya yayi yace,

Ki shirya ina jiranki kafin lokacin yanke hukuncin su ammy yayi.

Ficewa yayi tabisa da kallo zuciyarta na harbawa.

Cikin wani irin yanayi na sabon tashin hankali ta 'dauki abeel hassan ta fito palo takalli nuratu dake rakube tun acikin daren tana jiran fitowarta tayi kuka har batada qarfin yin wani.

Kai tsaye tace,

Meke faruwa?

Da sauri nuratu ta tashi ta zube gabanta tana hawaye tace,

Ina neman afuwa akan shaidar dana bayar akan sultana da jakadiya gashi zasu rasa ransa sanadin shaidata saidai wlh ina rantsuwa da rayuwata mamani bayin kantabane sakata akayi saidai wlh bansan wayake sakataba dana fada nan fitardasu sultana dan haka ashirye nake da daukar hukuncinki.

Da wani irin sabon baqin ciki da takaici takalli nuratu saidai takasa cewa komai ta nufi qofa ta fice kai tsaye sashen suhailat ta nufa.

Zaune take a dakinta taqurawa akwatinanta data saka Carolina hadawa ido idanuwanta jajir.

Tsayawa gabanta rumanah tayi tareda miqa mata abeel hassan idanuwanta na cikowa da hawaye tace,

Duk duniya ayanxu kece kawai na yarda dake akan 'dana sai Ammy dan haka ina riqonki daki riqesa har sai lokacinda kikaji zuciyarki ta gamsu da adalcin dazan baki,
Na miki alqawarin duk Wanda yakeda hannu aciki ayau zai fuskanci hukuncinsa.

Ficewa tayi kai tsaye ta nufi sashenta tashiga wanka zuciyarta na wani irin zafi tana fitowa tagansa tsaye cikin 'dakin idanuwansa jajir ya kalleta ta 'dauke kanta tareda isa gaban madubi ta zauna.

Cikin zafi ya jawota gabansa cikin 'daga murya yace,

Me kike nufi da abinda kika fadawa suhailat?

Bata kallesaba tace,

Kubutarda uwata.

Sakinta yayi da sauri tareda kallon cikin idonta yace,

Kinsan abinda kike fada?
Kinsan abinda hakan ke nufi?
Bana buqatar ki shiga komai abu 'daya nace kiyi shine ki bani matsayin danace inaso....

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta cikin rawar murya tace,

Nima bana buqatar ka saka kanka cikin ha'dari dan haka bazan taba baka mulkin mineelik ba koda hakan na nufin rasa rayuwatane....

Riqota yayi da qarfi tareda girgizata yace,

Idan kina sona bazaki taba bari ataba mahaifiyata ba sbd itace rayuwata dan haka dole zaki bani mulki.

Hawayen dasuka cika mata idone suka gangaro mata ahankali tace,

Namaka alqawarin babu abinda zai samu uwar data haifi halitta mafi soyuwa arayuwata kozan rasa raina.

Shiga jikinsa tayi ahankali tareda rungumesa hawaye na tsinke mata.
Rintse ido yayi tareda rungumeta ahankali ya furta,

KECE RAYUWATA UMMU-RUMANAH BULAMA.

Dagowa tayi takallesa hawaye far in ciki na tsiyayo mata saidai bazata iya cewa komaiba.

Ruwan kan table din dake tsakiyar dakin ta dauka tareda kaiwa bakinsa tana tsiyayar hawayen tausayinsa dana kanta.

Ahankali yasha yana kallon cikin idonta.

Ahankali ta furta,

Karka gujeni kome zanzama arayuwa dan allah,
Ko bayan raina kayi kayi alqawarin tunawa dani.

Lumshe ido yayi jikinsa na mutuwa idanuwansa na fara gani dishi dishi a firgice yake kallonta sbd gano wani abune tabashi saidai kafin yayi wani yunquri ya zube kan gadon ta durqusa ta gyara masa kwanciyarsa tareda shafa fuskarsa ta miqe.



Dukkanin wani maison sheda hukuncin sultan na cikin qasar da wajenta sun hallara sultan na fitowa guri yayi tsit ya zauna kan kujerar mulkinsa atake aka fito da mamani da jakadiya dukkaninsu babu mai iya tsayuwa sbd azaba da 'daurin dake jikinsu.

Kukan baqin ciki Jakadiya takeyi sbd irin mutuwar tozarcin dazasuyi tareda sultana.

Mamani na ganin masu jiran umarni sun tsaya akansu da takobuna suna kashe ido sbd laifi da qyallinsu hankalinta yatashi tabude ido daqyar tanason magana kaleeb ya take mata kai.

Ana jiran ana fitoda sultana cikin wani irin ama aka sanarda fitowar uwar magaji.

Atake kowa yayi tsit sultan yayi saurin kallon qofar
Tafito cikin wata irin doguwar ethiopiany royal gown red colour mai tsananin tsawo da adon black stones wuyanta da kanta na kyallin farin zinari kallo 'daya zakayi mata kasan tana cikin baqin ciki.

Cikin wainda ke tareda ita Dan tsaron lafiyarta ta kalli gefen daya jiki na rawa ya fidda bayananta dake rubuce jikin fatar rubutu ya miqawa sarkin na'din sarautar mineelik.

Budewa yayi tareda fara karanto da qarfin muryarsa yanda duka alummar dasuka halarci gurin zasuji.


"" NI UMMU-RUMANAH BULAMA MATAR YARIMA MAHEER UWAR MAGAJIN MINEELIK AYAU KWANA 'DAYA DA NADIN SUNAN MAGAJIN MINEELIK NA SAUKE SULTAN ABDULSHAMS ABDALLAH DAGA MULKIN MINEELIK NA KARBA HAR ZUWA RANARDA 'DANA MAGAJI ABEEL HASSAN ZAI KARBI MULKI DA HANNUNSA.."""

Tsit koina yayi sbd firgici da mamaki
Sultan da adama kusan atare suka miqe tsaye tsabar firgici.

Ammy da ake fitowa da ita kadan ya rage ta yanke jiki ta fadi sbd jiyo sanarwar.

Jiki na rawa sarkin nadi tareda duk sauran sarakuna da wazirai suka miqe ta nufi kujerar mulkin mineelik gabanta da numfashinta na fita da sauri
Sultan dayayi mutuwar tsaye ya zare hular mulkin ya miqawa sarkin gida atake aka dauko kayan rantsarwa aka rantsar da ita atake ta zauna kujerar mineelik aka saka mata hular.

Lumshe jajayen idanuwanta tayi wani irin baqon yanayi mai qarfi na shigarta
Wani irin qarfin zuciya da taurin zuciya taji yana shigarta tsawon lokaci ahaka duk anyi tsit anajiranta.

Ahankali ta bude idanuwanta dasuka bushe nan take tagyara zama takalli inda sultan yake zaune yana kallonta cikin isa shima yanajiran jin nata hukuncin ta juyo takalli indasu mamani suke cikin daga murya tace,

Akawo abinda mamani tafiso aduniya.

Cikin gaggawa aka jawo nuratu aka durqusar tsakiyar gurin kai tsaye tace,

Ku yankata agabanta uwarta idan bata fadi Wanda yasakataba cikin seconds uku.
#mamuhgee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: _*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_



*35*
Not edited
*Asalin Labarin mineelik*

Soyayya da cin Amana haÉ—i da Yaudara suka, kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836. Mafarin rigimar daga mutane huÉ—une, jigogin masarautar, Musaman Sultan Jamal wanda shi ya haifar da kome....

Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa, yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami, wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham, fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi mutune magananne, da kuma son raha,
"Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba."

"Wai shin Jamal baka gajiya da magane, haba tun da muka fito kaiÉ—ai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana hakuri haka dan yunwa muke ji." inji Kojo.

"Shi kenan kojo nayi shiru kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba."

Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar sauran.

Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, É—an tafiya kaÉ—an sukayi É—ayansu amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace.
"Ku dakata naga wani abu, kamar Zinari."
"Amari nima nagani tsoron siffar abin yasani shiru gashi can kamar mage ko?" Inji Jamal,

Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me É—an nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine babbansu, cikin fushi yace.
"Dalla kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al'ajabi da ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito muje."
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
"Na rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma ni sai naga abinda ya turewa buzu naÉ—i"

Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,

Cikin laluma kojo yace.
"Shikenan zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman zinariyar."

Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka kunna wuta suna shan É—umi,( bawai dan lokacin sanyi ba'a mutanen da suka kuna wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)

Zama sukayi a gurin, sannan suka ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi, sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.

Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar dasu.

Asalinsu wadanan, Fataken yan garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo É—aya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,

Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daÉ—in zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.

Sai Autansu Jamal wanda ya kasance mutum ne hakuri da juriya ga barkwace da iya zama da mutane, kuma yana da shiga rai dan duk inda ya zauna sai kasamu ana alfahari dashi, sai dai yana da abun dariya dan idan yazauna kusada kai sai ya cika maka cikinka da barkwace da raha.
Wannan kenan....
Washi gari da safe duk suka tashi, nan suka karya a gurguje suka shiga dajin, niman zinarin nan, har rana takusan faÉ—i basu gani ba, tsurawa dajin ido amari yayi yace.
"Jamal jiya ba'a nan muka ga kyalin zinarin mai sufar mage."

GyaÉ—a mishi kai Jamal yayi cike da bashi kwarin gwiwa, murmushi Ajani yayi sannan yace
"Amari zan tura kojo gari ya sayo mana kayan aiki sai mun tono wannan zinarin na yarda da kai."

Cikin farin ciki Amari ya rungume Ajani yana cewa,

Yene dan uwa.

Gurin tantinsu suka dawo suka ciro kuÉ—i silalar akabawa Kojo, yaje ya sayo kayan aiki.

Tafiya ce ta wuni guda dan haka ya haye rakuminshi ya kutsa cikin gari, bai isa ba sai da duhu ya fara rabawa, sannan ya isa gidansu anan ya kwana washi gari ya shiga kasuwa ya sayi abinda suke bukata wanda, na kayan tono,

Yana gamawa ya aza kayan akan rakuminshi,sannan yabar garin,

Tafiyar kaman dai yanda yazone sai da dare ya fara ya isa gurinsu dan ba iyakar kayan aikin yasaya ba, har da kayan abinci yasaya musu,

Zama sukayi a gurin suka ci abinda ya kawo, sannan suka shiga hira yanda zasu tono rijiyar zinarin.

Suna gurin har dare ya farayi sannan suka shige tantinsu.
****
Washi gari suka je inda suka hango zinarin suka shiga tonoda kwashe kasa, a hankali suka ta aikin tono har dai sukayi nisan zango ga dare yayi dole suka hakura zuwa gobe.

Washi gari ma haka suka cigaba da tonon ba dare ba rana har sai da suka shafe kwanaki goma sha takwas da yini daya babu zinarin babu labarinshi karshe hakura sukayi da tono, duk suka zauna jigum, cike da bakin ciki Amari ya fashe da kuka, wanda ya kashe jikin yan uwanshi, rarrashinsa suka shiga yi, kafin yayi shiru mikewa yayi yace.
"Dole sai na isa ga, Ebo sarkin bokaye dan shine zai iya duba min abinda idanuna ya gani."

Cikin son mara mishi baya suka mike take suka nufi cikin gari, dukda dare ne haka bai hanasu tafiya ba, har suka shiga garin gidansu suka nufa, suka kwana washi gari suka tashi dukkansu suka nufi gidan Ebo.

Sarkin bokayen garin, tun daga bakin kofar gidanshi suka hangoshi kwarjale, irin wanda mahajata ke raɓawa akafaɗarshi hannunshi rike da sandar tsafi, goshinsa yashafa bakin gari, inda yaja jan gari a goshinsa,

"Lalle lallae da zuwan sarakunan karnin farko, barka da zuwanku, a koda yaushe k'addara kamar zare ce mai kaifi, amma shahara da É—aukaka tana biye a bayanta ku shigo ciki."

Jikinsune yayi sanyi, zama sukayi akan fatar zakin dake shimfiÉ—e, a tsakar É—akin, shi kuma ya koma kan kujeranshi.

"Ina jinku."
Yace musu, tunda suka É—auko niyyar zuwa gurinshi, yaji haka ajikinshi sai dai lokacin da ya hangosu yaga tagomashin É—aukaka wanda yake É—auke da duhun na ban mamaki.

Cikin zakuwa Amari ya buÉ—e bakinshi zaice wani abu m, take bokan ya dakatar dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login