Showing 9001 words to 12000 words out of 81312 words

Chapter 4 - Tarayya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

17 Dec 2024

238

yakesone babu takura sbd dukkaninsu sunada ilimi da wayewar bawa junansu freedom batareda damuwar komaiba.

Hakan yasa ba laifi ya tsaya akayi duk wani biki daza'ayi aka daura aure aka kawo amarya.

Abu 'daya daya sani shine haihuwar da'akeson yayi rututu kamar ta awaki bazai yitaba sbd atsarinsa 'yaya uku zuwa hudu sun ishesa sbd gidansa da familynsa suxamto yanda yakeso baya sha'awar yara da yawa bare ayi zancen mata biyu Wanda shi yana ganin Sam bazai iya ya kwana da wancan yazo yakwana da wannan ba koba komai baya tunanin zaiso mata biyu dole 'daya zaiso so babu mgnar adalci agurin Dan haka Sam babu tsari bare mafarkin auren mata biyu arayuwarsa koba komai shi mutumne mai tsananin qyanqyami haka Allah yayisa.

A ranarda aka kawo suhailat aranar yayiwa sultan yanda yakeso yayi kwanan aureda ita
Satinsu biyu suka tattara suka koma Georgia shida suhailat.

Suhailat tasan Sam babu so atsakaninta dashi saidai wayewarta da iliminta tareda zamantowarta free yasa yakejin dadin zama da ita kuma shima sbd yanada wadataccen ilimi da wayewa yasa Sam babu ma alamar datake nuna baya sonta as far as suna respecting juna dakuma respecting ra'ayoyin junansu ya ishesu zaman aure sabanin wasu mazan dake nuna qiyayyar mace qarara Wanda hakan ba halin namiji mai ilimi bane so pls marubuta mu gyara Sam duk namijin dayakeda ilimi da wayewa baikamata ariqa sashi yana nunawa mace tsana afiliba da kyararta,idan yanada ilimi to yayi amfani dashi.


Wata uku da komawarsu ciki ya 6ullo nan saqo ya isa masarauta farin ciki da murna suka kama koina sai sadakar maqudan kudade akeyi da kyaututtuka baga masarautar ba kawai duk 'yan mineelik duk wani mai arziki kyauta da sadaka yakeyi na farin cikin insha Allah za'a samu magaji amasarautar dazata hanasu zamantowa qarqashin wata azzalumar masarautar.


Lokacinda cikin ya isa haihuwa suka dawo gida ranar haihuwa kaf koina ba wani hayaniya ko 'yan kasuwanni basu firfitoba hakadai ake zaune zaman jira baga sultanba baga 'yan fadaba baga 'yan gariba,

Masarautun dasuke abokantaka datasu masarautarma yau duk cikin jiran haihuwar suke suna adduar samun namiji.

Bayi kuwa sunsan yau qaddara tasasu yin laifi saidai wani kan badai nakaba shiyasa kowa ya nutsu anata addua.

Sultan dai yau yasan 'yancin masarautarsa ya dangana ne da abinda za'a haifa shiyasa yau tsit yake yana lazimi cikin ransa.

Sultana zaarah nacan sashen da ake kar6ar haihuwar sbd haihuwar tazo da gardama
Su jakadiya sai shar6e zufa akeyi ga kuyangi da bayi ajere kofar sassan haihuwar sai gumin wahala da fargaba sukeyi sbd sunsan yau duk aka haifi mace 'daya daga cikinsu ne zaije isarda mummunan saqonda qila abakin lafiyarsa ko ransa shiyasa gabaki 'daya a tsure suke da fargaba tareda adduar samun namiji.
#mamuhgee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡

*8*
Yini guda cur masarautar tayi cikin zaman jiran haihuwar suhailat,
Maheer kuwa duk yanda kowa ya 'daga hankalinsa bai 'daga nasaba sbd yasan dukkaninsu damuwarsu ba akan lafiyar matarsa yakeba sai akan abinda za'a haifane yazamo namiji,
Shi tausayinsa akan suhailat din ne duk da yasan tanada dauriya sbd zama da ita yanxu yasa yasake sanin halayyarta tanada juriyar danne abu ta 6oyesa acikin ranta duk qwaqwarka yanada wuya ka gano abunda ke ranta shiyasa take matuqar basa tausayi sbd shikuma mutum ne da idan bayason Abu baya iya tsayawa basa kulawarda yakamata,
Tasani babu sonta aransa amma baya nuna mata wasu halayansa ke nuna mata saidai son rayuwarsa yasa dukkaninsu jin dadin rayuwar aurensu sbd sunayintane very romantic sbd maheer romantic life is one of the best abinda yafiso arayuwarsa.

Zaune yake a lafiyyan palonsa dake sashensa idanuwansa a lumshe kwata kwata bayan hot coffee dayasha dasafe har lokacin baici komaiba duk da ankawo abinci daga kicin din sashen ammynsa anjere masa dama kaidarsane bayacin abincin kowane kicin saina sashen mahaifiyarsa.


Lokacinda limamin masarautar yakammala kiran sallar magriba daidai lokacin suhailat tayi wani yunquri tareda wahalallen nishi cikin tsananin azaba baby yafado.

Su sultana da sarauniya adama tareda sauran 'yaya mata na zuriar gidan dake kusa duk sunzo suka miqe kusan atare kowa na kallon quryar 'dakinda suhailat din take ciki.

Bayi da kuyangi tuni suka sake gyara tsayuwa suna hadiye yawun fargabar meza a fito ace anhaifa.

'Daga jaririyar mai karbar haihuwar tayi tareda kallonta taga mace ce aka haifa
Ta 'dago takalli jakadiya tana ha'do sabon gumi ta miqa mata jaririyar.

Karbar jaririyar jakadiya tayi tana kallonta yanda take canyara kuka ta qura mata ido tareda sauke nannauyar ajiyar zuciya tamiqawa masu gyarata ta fita tana tattaro kuzari ta iso gabansu sultana ta tsaya tareda sunkuyardakai tace,

Allah yaqaramiki hkr da lafiya uwar 'dakina Allah ya albarkaci yarima da samun 'YA MACE.

Wata irin 6oyayyar ajiyar zuciya sarauniya adama tasauke zuciyarta na cika da wani irin farin ciki amma afili kallon dakinda suhailat take ciki tayi tace,

Akimtsa uwar da 'yar amaidasu sashensu
Jaririyar akawomin ita nizan kaiwa sultan.

Sultana ganin adama tayi mgn yasa ta 'dagawa jakadiya kai tareda cewa jakadiya akula sosai da suhailat ta juya ta fice kuyanginta na bayanta.

Lokacinda labarin haihuwar yagama isa koina sultan baice komaiba yace akaiwa maheer 'yarsa yayi mata huduba.

Bayan maheer yayi mata huduba aka maidawa sultan 'yar yasa mata suna AMATULLAH.

Ba laifi anyi shagalin suna duk wani gata anunuawa suhailat da 'yarta duk da dai tana saneda ba wani farin ciki kowa keyi da haihuwar ba.

Adama kuwa sbd jin dadin ansamu mace ba namiji ba har wani soyayya take nunawa amatullah.

Watansu 'daya maheer yakoma itakuma ta tafi Mali ganin gida kafin daga can takoma Georgia tasamu maheer.

Bayan komawarsu suka cigaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kuma sosai maheer keson amah 'dinsa sbd yarinyar babu abinda tabaro nasa na kamanni shiyasa koyaushe take sake shiga ransa.

Ta bangaren suhailat kuwa saidai tacigaba da sawa kanta dangana da hkr saidai tunda yanason 'yarta hakan naqara saka mata nutsuwa da kwanciyar hankali.

Tunda suka koma cikin dubaru sultana ke 'Dan lurarda suhailat akan kada tayi family planning.

Tunda suka dawo yamaida hankali ga rayuwarsa yamanta da wani batun samun magaji da sultan keso.

Shekarar amah 'daya da sati biyu aka sake tabbatarda ciki jikin suhailat nan aka sake shiga 'doki da duqufa addua da sadakoki akan Allah yabiya buqata.

Wannan karon saida cikin ya tsufa sultan yasa suka dawo akaro na biyu ranar naquda akayi jigum jigum jiran tsammani
Allah mai yanda yaso tasake haihuwar 'ya mace.

Ita kanta suhailat tayita adduar Allah yabada 'da namijin sbd tafara hangowa kanta da 'yayanta kyara nan gaba.

Kai tsaye sultan yace kar akawo masa jaririyar akaiwa maheer yayi mata huduba da suna gabaki daya.

Yarima yayiwa 'yarsa huduba yasaka mata suna fammah.

Wannan karon babu wani shagali ganin haka yasa yarima ya tattarasu suka komawarsu.

Shekarar fammah daya da wata uku suhailat tasake samun ciki wannan karon ma sultan bai cire raiba yace sudawo
Satinsu biyu da dawowa ta haifi mace amma 'yar kwana biyu da haihuwa ta rasu ganin haka suka komawarsu sbd wannan karon Sam ita suhailat yanxu ta rage jin dadin masarautar sosai sbd sultana ce kawai ke qaunar 'yayanta sai adama dake yimusu soyayyar dole.


Ayanxuma tana 'daukeda ciki tsoho sultan yace suyi zamansu harsai ta haihu anji me ta haifa saigashi ankuma samun mace shine sultana taje tafada masa.

Ganin wankin hula na Neman kaisa dare yasa ya yanke hukuncin yarima zaidawo gida atara masa barori koda za'asamu qaruwar ta hanyarsu.

Basu dawo Ethiopia ba Mali suka wuce acan gidansu suhailat sukai hutunsu na kusan sati biyu cikin jin dadi sbd gidansu gidan wayayyin mutane ne masu ilimi gasu amah ma sunason nan 'din sbd suna sakewa sosai ga qaunarsu da Granny's dinsu suke musu.

Daga Mali komawarsu sukayi Georgia tareda yaransu sukaci gaba da rayuwarsu.

Maheer duk cikin yaransa uku babu kamar amah acikin ransa yana tsananin qaunarta Wanda suhailat ke adduar Allah yasa ko kwatankwacin rabin qaunar dayakewa amah tasamu daga garesa.

Maheer da family dinsa wata irin rayuwar turawa ta jin dadi sukeyi babu damuwa babu takura.

Yaransa sun taso cikin turawa da yanayin rayuwar turawa dasuka ga iyayansu aciki
yanayin fatarsu dakeda sirkin yellow da brown kawai zaka zaka kalla kace musu black Americans batareda kasan asalinsu ba.

Baby AMNAH Nada shekara biyu tasake samun ciki wannan karon yazo mata da laulayi da nauyin jiki sosai shiyasa ta rage fita aiki sosai dakuma kula da gidan ta 6angare 'daya ga amnah babu lafiya yarinyar tun tana jaririya take fama da pneumonia Wanda idan ya tashi yana wahalarda yarinyar sosai hakan yasa iyayenta ke tsananin qaunarta.

Yau tun safe jikin nata yatashi sosai sbd kwana tayi yau bada sweater da socks ajikintaba.

Koda Carolina ta shirya amah da fammah shirin zuwa school sukai breakfast
Amah ta nufi hanyar palon dadynsu da gudu tana cewa,

Dady we're running late pls come out.

Fitowarsa daga wanka kenan 'daureda White towel yajiyo muryar amah 'din ya lumshe ido ya bude yakalli agogo yana cewa,

Amah will kill me today for this.

Kallon suhailat yayi data fito daga dressing room 'dinsa daukeda kayanda sabon towels guda uku zata kai toilet yace,

Ki taremin ita na shirya zata cikamin kunne ne da surutu nakasa shiryawa.

Aje towels din tayi bakin king size bed din dake cikin qaton hadadden bedroom din nasa ta nufi qofa tana cewa,

Amah nima wlh bazan iya da surutunki ba.

Tana fitowa amah na kama handle din dakin.

Kamo hannunta tayi tana cewa,

Let's go and check on amnah before your dad comes out....

Tsayawa tayi tareda 6ata fuska zatayi kuka
Suhailat tayi saurin janta suka nufi room 'din yaran dake tsare dakomai na yara.

Saurin isa tayi gurin amnah dake kwance agadonta tana fusgar numfashi daqyar.

Daukarta tayi da sauri tareda dubata taga ciwontane yatashi cikin karaji ta qwalawa Carolina kira jikinta na rawa.

Da hanzari Carolina ta iso tana cewa,

Yes ma'am.

Cikin daga murya rai amatuqar 6ace tace,

Are you trying to kill my poor baby by letting her sleeps without any sweater and socks?

Arikice takalli suhailat cikin rudewa tace,

I'm sorry ma'am but I.......

Just shut up I don't want to hear your stupid silly excuses
Hw can you be so careless and.....


Keep quite suhailat''''' sukaji daga bakin qofar dakin ta juyo takallesa cikin takaici tace,

Baby pls.....

I said keep quite suhailat"" yasake fada yana kallon yanda Carolina ke sheshekar kukan fadanda suhailat tayi mata yace,

Why do you always wants to make things worst? Yanxu kinxo kinsamu halinda amnah take ciki instead kiyi saurin bata taimakon gaggawa kintsaya hayaniya and you seriously know hw much I hate that,
Ga yara basu wuce school ba kinanan kina fada kinkasa tsayawa kiji wat was trying to say.

Hawaye ne yaciko idon suhailat takallesa lokacinda ya juya yafice yana zuwa palo su amah suka bisa mota suka shiga ya wuce yafara ajesu school ya nufi gurin aikinsa.

Bayan fitarsa share hawayenta tayi ta miqawa Carolina amnah tace,

Quickly remove her pampy and dress let me go and change we're taking her to the hospital.

Lokacinda suka fito tuni jikinta yaqara rikicewa tun a mota takirasa.

Tsaye suke ya zuba dukkanin hannuwansa a aljihun trousers dinsa fuskarsa sai wani irin kwarjini da glowing takeyi sbd kyan fata da hutu yana sauraron bayanan wasu new doctors da aka kawo asibitin wayarsa tayi ringin yakalli nurse din dake tsaye riqe da kayansa na theatre da wayarsa tareda wasu folders din patients din dazaiyiwa aiki ya miqa mata hannu ta miqo masa wayar yana ganin suhailat ce ya rufe idanu ya bude tareda dauka yana komawa office dinsa na qurya.

Sanin bayason hayaniya da tashin hankali yasa ta daidaita nutsuwarta tareda share hawayenta tana 6oye kukanta tace,

Baby my amnah is leaving me wlh I can feel it....

Rufe ido yayi ya bude Wanda yazamo 'dabi'arsace yin hakan duk zaiyi mgn sbd tattaro maganar kasancewar baifiyason dogowar magana.

Jikin ne?

Eh baby kwata kwata she's not breathing she's loosing it....

Bring her to hospital yanxunan.

Muna hanya already.

Kashe wayar yayi tareda mayar da hannuwansa aljihu ya rufe ido.

Suna isowa akayi gaggawar fara bata taimakon gaggawa ta hanyar saka mata oxygen saidai tariga tayi nisa sosai mintuna talatin da zuwansu Allah yakarbi ranta.

Cikin jinjina alamarin doctors din dake kanta suka gama rubuce rubucensu tareda kallon maheer da suhailat ke jikinsa tana kuka sukace,

Sorry doctor maheer we lost her.

Wani irin kuka suhailat tasaki tana qanqamesa
Rintse idanuwansa yayi ya rungumeta yana bubbuga bayanta batareda yace komaiba.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡

*9*
Bayan rasuwar amnah sosai suhailat tashiga damuwa shikuma gashi bai iya ya ake lallashi ba bare
Iyakacinsa idan zai fita yanasaka yin breakfast idan yadawo suyi dinner sbd bai cika lunch agidaba.
Hakadai ta dangana tacigaba da rainon sabon cikinta.

Sultan yayi yayi yaqara aure yamaqi dawowa qasar shiyasa yadauki mataki kaitsaye akansa.

Sultana tashiga damuwa matuqa jin amnah ta rasu batareda sun ta6a ganinba saidai a hoto kawai gashi tanason zuwa amma sultan yasa doka.

Jakadiya kuwa sosai tafara shirya shiryen na kullum tana sashe sashe duddubawa cikin dubara sbd sotake saita ringa fahimtar halayyarka sbd kar asamu magaji ta macenda batada nutsuwa ko ma'ana.

Kullum cikin kwantarwada suhailat hankali sultana take hardai taga ta warware itama hanakalinta ya kwanta.

Lurada jakadiya sultana tayi ta kalleta bayan ta kori dukkanin bayinta dake sashen sbd maganar datakesonyi da jakadiyar.

Rumanah ce kawai a bedroom din ammyn tana aikinta hankali kwance.

Cikin muryar bada umarni tace,

Inason sanin hukuncin da sultan ya yanke akan maheer sbd nasan me shirunsa yake nufi.

Sunkuyar dakai jakadiya tayi wani zufa ya tsatsafo mata cikin sanyin jiki da sanyin murya tace,

Sultan yabada umarnin atanadarwa yarima sa dakoki har biyar akillacesu zai dawo bazai komaba yanxu sai ansamu qaruwa daga garesu.


Tashi zaune sultana tayi cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da takaici taringa maimaita innalillahi.

Kallon jakadiya tayi tana qoqarin ganin damuwarta bata rinjayetaba murya amatuqar sanyaye tace,

Har kin tanadesu 'din?

Tukunadai ranki ya Dade saidai nima ina cikin tsananin fargaba da tsoron yanda zata kaya sbd aurensa ma ta yaya akasamu yayi bare yanxu mata har biyar.

Rintse idanu sultana tayi tareda budesu jajir tace,

Idan kin zabesu kafin ki gabatarwada sultan su ki gabatarmin dasu inason naga matanda wasu daga cikin jikokina zasu fito ajikinsu.

Jakadiya na fita ta bada umarnin abuga qararrawa atara mata dukkanin wata kuyanga dake masarautar.
Nan tafara dubasu cikin layi harbasa qirguwa sbd yawansu amma takasa samun 'daya dazata ware duk wadda takalla saitaga komai gyara da kulawar daza'ayi mata batakai matsayinda yarima zai hada shimfida da itaba.

Da haka ta sallamesu tace gobe kowanne yayo wanka su sake zuwa subi layi.


Tana gama gyaran bedroom din tafito tazo gaban sultana ta durqusa cikin girmamawa tace,

Ammy nagama kinada buqatar wani abu?

Kallonta sultana tayi da idanuwanta dasukai jajir sbd baqin ciki ta girgiza mata kai.

Ganin halinda ammyn take ciki yabata tsoro ta miqe hartakai qofa ta waiwayo cikin damuwa murya asanyaye tace,

Saida safe ammy.

Asanyaye ta isa dakinsu ta tararda daga mamani har nuratu basu dawoba ta tube taso watsa ruwa amma jin batada gajiya kuma batai wani aikin wahalaba tayi kwanta.

Tana qoqarin juyawa nuratu tashigo amatuqar gajiye ta zauna bakin 'yar katifarta tana cewa,

Rumanah wlh tsufa da wuri zai kamani sbd wahala.

Murmushi rumanah tasaki ahankali kafin ta tashi zaune tace,

Me kike gudu da tsufa da wuri?

Harararta nuratu tayi tana zame kayanta tace,

Ke kuma mekike yiwa sauri da tsufa?
Nifa rumanah banason tsufa da wuri sbd bazan ta6a cire rai daga hangowa kaina wata irin kyakkyawar rayuwa,
Ke nifa har mafarki nakeyi nazama wadda tafi kusanci ga Wanda wai zai mulki masarautarnan anan gaba,
Kuma kinsan menene?
Mace nake gani amafarkina koda yaushe saidai adon zinarai dake jikinta tana hanani ganin fuskarta....

Mamani dake shigowa tayi saurin qarasowa ta riqota tana washe dukkanin haqoranta tace,

'Yarda zaki haifawa yarima ce......

Fusgewa nuratu tayi da qarfi tana cewa,

Barni da zancenki mamani koyaushe bakinki baya tsayawa mmatsayinsa..

Sake washe baki mamani tayi tace,

Nuratuna dama nasan tuntuni jikina nabani kece zaki fitardani cikin wannan qasqantacciyar rayuwar,
Jikina nabani kece za'a zaba amatsayin sa 'dakar yarima.....

Dariyace taxowa rumanah tayi saurin rufe baki sbd gudun masifa da balain mamani dazata iya kwana tana surfa mata.

Cikin takaicin halin mahaifiyarta nuratu takalleta tace,

Lallai mamani bakya sona tunda harkike fatar nazama baiwarda za'a riqa kwana dani ina haihuwa ana karbe 'yayan.

Cikin saurin mamani tace,

Kibar maganar baiwa daga ranarda kika hada shimfida dashi kintashi daga baiwa sbd duk Wadda ta haifo magaji sultan ya 'yantata daga ranar kuma ita za'a miqawa matsayi dakuma kujerar zaman uwar sarki sbd tariga ta haifo sarki,
Duk Wanda taso nadawa yayiwa danta riqon qwarya shi zata nada har 'danta ya girma abasa kujerarsa,
Idan kika haifi namiji nuratu babu Wanda zaki bawa riqon kwarya kece zakiyi mulkin da kanki,
Kece zaki hau kujerar sarauta da kanki,
Kece zaki mulki dubban 'daruruwan sarakuna da daulolinsu,
Kece zaki zama mace ta farko dazatayi mulkin wannan masarauta da aka tsani haihuwar mata.....

Kasa riqe dariya rumanah tayi tasaketa tana kallon mamani data watso mata mugun kallo tayi saurin hadiye dariyar.

Nuratu ma dariyar tasaki tana kallon mamani kafin takalli rumanah suka saki wata dariyar.

Mamani tayi mugun hasala tayo kan rumanah nuratu tayi saurin riqota tana cewa,

Haba mamani nah kece fa uwar sarauniya nuratu kuma kakar magajin sarautar dariyafa kawai mukeyi ta farin cikin wannan mafarkin naki mai dadin gaske kokuwa 'dayar mamar magajin sarauta.

Dariya suka qunshe suna kallon juna suna kallonta.

Ganin sun maidata mahaukaciya yasa qyaci ta fice ahasale.
#Mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡


*10*
Bayan fitarta rumanah taja abun lullubewarta tana murmushi tace,

Nuratu kinfa karyawa mamani gwiwa daga kawai tana mana fatar samun jin dadi da 'yanci idan kika zama sarauniya....

Kallonta nuratu tayi cikin tsananin sanyin jiki tace,

Rumanah ke kinamin fatar nazama baiwarda za'a riqa kwana da ita tana haihuwa Ana karbe yayan idan nazama haka me naqaru dashi arayuwata bayandai ta tabbata naza baiwa tahar mutuwa...

Qarasowa da sauri rumanah tayi ta rungumeta ganin hawaye na zubo mata tace,

Nuratu bana miki fatar wannan rayuwar ko amafarki bare afili,
Keda mamani kune 'yan uwana kullum fatana da adduana musamu kubuta atare mukoma ga asalinmu domin kuwa saimun koma asalinmu zangano nawa asalin.

Cikin sanyin murya nuratu tace,

Rumanah bawa baida ra'ayin kansa ko abinda yakeso sai Wanda uwayen gidansa suka yanke akansa,
Shin kina tunanin qaddara zata iya zuwa kaina aza6eni cikin masu zuwa shimfidar yarima?

Girgiza mata kai rumanah tayi cikin son qarfafata tace,

Insha Allah bazamu ta6a wannan rayuwarba nuratu.

Rumanah ammy bazata ta6a bari kiyi wannan rayuwarba saidai ni banada tabbaci saidai Allah ya dubi rashin gatana.

Jiki sanyaye zuciya fal da tunani da zullumi suka kwanta har mamani tadawo cikin dare ta kwanta babu Wanda yayi bacci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login