Showing 60001 words to 63000 words out of 81312 words

Chapter 21 - Tarayya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

17 Dec 2024

247

     "Jamal kasonka shine mafi nauyi a raqumi sbd kaine zaka bamu gudunmawa mafi girma a cikin tafiyar,
abinda zai faru idan kuka isa dajin domin jiranta akwai tsoratarwa daga muyagun aljanu da dabbobi masu firgitarwa da suke yawo cikin dajin,   

     matakin farko zai farane daga kwanaki uku kafin bayyanarta zaku kasance kamar makiyan juna a ranar farko,
Zakiji tsana da qarfin son kashe juna mai qarfi na shigarku saidai karku bari hakan yaci qarfinku sbd dayafi qarfinku zaku kashe junanku cikin rashin imani.

rana na biyu kuwa bazaku ga giftawar tsuntsaye ko wata dabba ko dayaba ko wni iri har kukan namun dajin bazaku ji ba.

a rana na uku da zata bayyana wani mugun zafi da kishirwa zai buwayeku kamar zaku mutu, domin zaku ji har cikin jikinku zai koma kamar babu ruwa da jini a ciki, zuwa yamma ko dare zata bayyana, kai Jamal aikinkane kutsa kai cikin dajin domin haɗuwa da ita duk rintsi duk tsanani babu waiwaya.

                    Shiru sukayi cike da al'ajabi suke kallon kallo sabida jin abinda zai faru dasu wanda suke gani kamar faɗar bokane,

            Kallon bokan jamal yayi cikin nutsuwa yace.
"Wannan indai shine sharuɗan mun amince.

         Murmushi boka yayi sannan yace,

Tafiyace mai zuwa babu tabbacin dawowa abin bautarku ya kubutar daku.

           "Toh ni dai har yanzun abinda nakeson ji shine me zamu mata musamu dauko dukiyar mu mallaketa" Inji Amari.

          Kallon Jamal bokan yayi cikin murmushi ba shi yayi tambayar ba amma ya maida idanunshi kan jamal,

ɗaukar duwatsunshi yayi ya watsa har lokacin idanunshi nakan jamal,  juyawa yayi yace,

"Lokacine zai nuna mana abinda zai faru ynz zan baku wasu madaurin dantse ku ɗaura gudun karku cutar da kanku.

"Wannan zai kareku daga cutar da juna, sannan babu wani abinda zai cutarku nagama daku sai ranar da yasamu nasaran isa birnin Sarauniya mineelik, zamu karasa aikinmu nakarshe."

     Mikewa sukayi baki ɗaya suka fita koda suka isa bakin kofa, kallon jamal yayi cike da tausayi, sannan yace.
"Duk bayan lokaci mai dan tsayi ina son Babbanku yazo ya faɗa min cigaban da kuke samu."

Kallon 'yayansa yayi ya jinjina kai cikin muryar jarumta da bankwana yace,

Abin bauta yasa musake haduwa.

     Haka sukayi bankwana dashi suka tafi.

              ****
  Tunda suka tafi, kaman yanda bokan ya faɗa musu haka ya faru, sabida sun ɗaura ɗanbar wani kudiri a ransu, ranar farko, suna kwance sai suka fara jin shashekar kuka, kamar na yaro kaman na babba haka aka cigaba da razanasu da wani irin mahaukacin kuka, kafin aka samusu dariya irin na bantsoron nan, can da dare yayi tsakiya, sai kana kwance a cikn tantinka za'a zo ana kiranka daga kan ajani aka fara,

yana kwance ya dunkukune a marufinshi yaji an tsaya abakin tantinsa ana cewa.
"Ajaniiiiiiiiiii"
       D'auke numfashinsa yayi cak, tsabar tsoron, haka aka kewayasu ana razanasu.

            Wasa wasa sai da suka kwashi fiyye da wata biyar ana tsoratasu da abubuwa a gurin tuni suka saba da rayuwa adajin sbd dama dukkaninsu sunsaba da rayuwa a daji dan haka yanzu gida suka dauki dajin sbd burinsu abune dazasu iya komai akansa.
lokacin da suka cika wata shida Ajani yaje ya faɗawa boka abinda ya faru, nan ya zauna ya faɗa mishi abinda zasuwa Mineelik dazaran ta faɗa soyayya da Jamal. Bokan ya cigaba da cewa,


" Matuƙar mukace muna son dukiyar baxata bamu cikin lumana ba. Karshe rabaku xatayi da ɗan uwanku amma idan mukayi haka toh babu wata damuwa sannan zan nema muku abubuwan da zakuyi amfani dashi, karka bari ɗan uwanka yaji labarin dan matukar yaji bazai yarda yayi aikin ba."

      Gyaɗa kai ajani yayi sannan yabar garin ya koma dajin, nan suka cigaba da zama ga tsoratasu da ake ga kwanakin kamar baya tafiya, duk sun kaqu da faruwan haka,

    Da zaran sun zauna hiransu kenan, akan yanda zasu juya dukiyarsu da suka samu, daga gareta, a hankali lokacin yana tafiya wasa wasa sai gashi har saura kwanaki bakwai zata bayyana,
   ......

       Bayan kwana huɗu wata rana da safe suka tashi da mugun faɗa kaman zasu kashe junarsu, kaman dai yanda bokan ya faɗa musu, karshe rabuwa dasu Jamal yayi ya koma gefe dan ya hassaso wannan rigimar yana cikin alamomin bayyanarta nan yatunatar dasu nan kowa yayi nesa da 'dan uwansa suna fidda wani irin gumi najin wani irin qarfi mai razanarwa na son kashe dan uwansa.

rana tabiyu kuwa sun tashi da babu giftawar tsuntsaye ko ɗaya tareda wani irin tsoro mai firgitarwa dayake shigarsu wanda suka tabbarda natane amma haka suka dinga daurewa cikin wata irin jarumta.

        Rana mafi tashin hankali shine ranar bayyanarta tsananin zafin da ake yaja sukaita fad'uwa, gashi sun shanye ruwansu, dakyar Jamal ya mike yace.

"Yaku Y'an uwana wannan itace rana mafi hadari ageremu saidai ina fatar mana samun nasara."

Daqyar su kojo suka rarrafo gurinsa suka rungume juna cikeda tsoron rabuwa da juna saidai burinsu ya zarce komai.

Daqyar suka rabu da juna yana rangaji yana faduwa yana tashi sbd yunwa,zafi da qishirwa dake neman lahantasu ya nausa dajin inda ranar suka fara ganinta baisan inama yake jefa qafafunsa ba sbd azabar dayake ji cikin hanjinsa da cikinsa.

 Duhun dare nayi yana isa gurin saidai ba'a cikin hayyacinsa ba sbd tuni yafara ficewa hayyacinsa atake ya yanke jiki gurin yafadi yana fitarda numfashi daqyar.


    Ahankali kunnuwansa suka fara jiyo amo da sautin sarqar zinarin qafarta sanye take cikin kaya ruwan makuba fuskarta na fitarda wani irin annuri duk da cikin duhune atake yaji wani sanyi na yaye masa yunwa da wahalarsa suna barinsa ahankali.

   Cikin wani irin takun nutsuwa da wata irin haiba ta nufo hanyar taku kadan tayi ta tsaya cak tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta.

A hankali ta juyar da kanta tahangosa kwance ba alamar yana numfashi.

A hankali takalli jikinta ahankali ta rikide ta sauya zuwa wata kyakkyawar bafulatar baqar Ethiopia sarqoqin jikinta na zinari suka koma duwatsun dandaye masu qaramin kyau ta nufosa numfashinta na wani irin sarqewa sbd wannan shine karo na farko data taba ganin wani biladama wadda take tabbarda shine Wanda ta dibi shekaru da qarnika tana jira.

A hankali ta durqusa gabansa tareda daga daga dogon hannunta ta ta6a goshinsa atake ya bude idanuwansa yana kallon fuskarta bai san lokacin da ya sume ba,
ruwan dake cikin goranta ta fulanin daji ta ɗauka ta watsa mishi, a hankali ya buɗe idanunshi sai akan fuskarta.

        Cikin idanunta ya kalla kamar wanda aka ɗiga mishi ruwan gold, lumshe idanunshi yayi.

    "Sannun ko" tace mishi...

Wani irin sauti yaji daga muryarta wanda yakusan sake sumar dashi yayi wani irin jarumtar daidaita numfashinsa da nutsuwarsa yayi kalar wanda ke cikin tsananin wuya ya daga mata kai daqyar alamar amsawa yana jan numfashin qarya daqyar.

Kasa wata maganar tayi tasauke kai tana kallon qafafunsa dake cikin takarmin fatar damisa.

           Sunkuyar da kanshi yayi ahankali kwalla na zuba daga idanunshi cikin muryar tsananin damuwa da baqin ciki rayuwa yace.

"Me yasa kika taimakeni?
me yasa baki barni na mutu ba?  na gaji da rayuwar duniya gwara na mutu nabar duniyar nan."
     
        Kallonsa tayi cikin sauri da nutsuwa da laushin murya tace,

"Koma Ya-yane dai rayuwarka tana da amfani,
ka daina cire tsamani da rayuwa, dan ko badaɗe ko bajima zaka amfani rayuwarka tana da amfani."

               Kuka ya fashe da shi yans kwaɗa kanshi da bishiya yana cewa,

"Kaicon rayuwa dan ina maraya shine bazanyi rayuwa kamar kowa, gwara mutuwata."
Duk ya jiwa kanshi ciwo,

tausayinshine da mamakin bil adamane ya kamata musamman ace yaganta mace cikin wannan dajin da tsakar dare amma bai nuna shakku ko tsoro da fargaba ba kodai yasan da fitowartane?

Satar kallonta yayi yaga alamar tunani da nazarinsa takeyi yasan dole yayi dubarar hanata zarginsa hadiye wani mugun yawu tareda zabura gefe jikinsa na wani irin mazari ya nunata da hannunsa dake mugun rawa a tsorace da rawar murya yace,

Ke...keee...ke wacece?
Me...mee kikeyi anan ke daya?

Kallonsa tayi ahankali cikin nutsuwa ganin yanda yarude yake neman zaucewa atake tasaki numfashi mai Sanyi tasaki murmushin daya sakasa zubewa kan gwiwoyinsa.

cikin sanyi murya tace.
"Nima marainiyace kiwo yakawoni kusadanan 6atan hanya yasakani shigowa nan hanyata nake nema amma nakasa ganewa.

Cikin dubara yayi baya alamar tsoro ya buga kansa da bishiya sosai nan take yafadi Jini na fita goshinsa.
 
Hannu ta daga ahankali zata shafa ciwon danya warke ta dakata sbd karya sake tsorata idan ya farko.

         Tashi tayi ta fara niman ganyayyaki tashiga haɗa mishi magani, tasaka mishi a ciwon,
   
           Sun ɗauki kwanaki biyu a gurin tana kula dashi, tun ranar da duka haɗu sukayi magana bata ce mishi kome ba, tsakaninta dashi ido duk abinda majinyaci ke bukata take mishi. Zaman kuramen da suke ba karamin, haifar musu da wani shakuwa yayi ba, dan zata zauna a fakaice tana kallonshi, ko shi yayita kallonta, da zaran sun kama juna take kowanensu zai shiga kame kame, ba yanayin da suke yana tafiya da wani irin tsari na musaman,

Jakarsa ta kaya ya bude ya buga tantin rumfarsa itace take kwana aciki shikuma yana kwanciya da wajen.

       . . A hankali suke iya faɗawa junansu magana ko kuma hira sama sama, a wata safiya ya tashi ya zauna dake ciwon jikinshi ya warke yace mata.
"Zan koma cikin gari, amma baki faɗa min sunanki ba, ni dai sunana Jamal ni maraya ne, zanje sake komawa gurin dangin iyayena dana gujewa.

           Kura mishi ido tayi cikin nutsuwa tace,

"Nima marainiya ce bani da kowa,sai kai da na haɗu da kai gashi zaka tafi kabarni Sunana Mineelik."

Wani irin bugawa qirjinsa yayi sbd ambatar sunan kawai musamman duka kwanakin yayisu ne babu ko kyaftawar ido bare bacci sbd yasan rayuwarsa na tsakanin mutuwa da rayuwane idan yabari yayi kuskure dan qanqani taganosa.

     Cikin tausayawa yace.

Bakyason nabarki cikin dajin nan ne na zauna?
   
     "Zanyi fatar haka idan ta kasance amma bazan maka dole ba." tace mishi.

           Shiru sukayi, suka cigaba da satar kallon juna, a hankali shakuwar da sukewa juna ta sake samun matsaya na musaman ma inda ta rikiɗe ta koma soyayya mai matukar ɗaukar hankali,  tare suke farautar abinda zasu ci, idan zatayi wani abu zama yake ya kareta, gabaki ɗaya jamal ya sadaukar da lokacinsa sabida ita,, musaman suke zama suyita hira da zaran yaga ta fara alamun jin barci zai barta ta shiga ta kwanta yana gadinta.

Tausayinsa ne mai tsanani yashiga rayuwarta sbd kaf baida abinda yake sai kulada ita tamkar sarauniya duk da baisan wacece itaba tabbas zata taimaki rayuwarsa kodan soyayyarsa data ginu a zuciyarta.
#mamuhgee
[7/30, 7:38 PM] ummul aulad: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_



*38*
_a gaggauce_
_not edited_
Haske writers association.

A gaggauce
Not edited.
Zaune suke dukkaninsu gaban boka aqoob dayayi shiru cikin jinjina mataki na qarshe dazai fada musu sbd aljanun dayake aiki dasu sune suke fada masa komai gameda sarauniya mineelik sbd suna cikin maqiyan farko na sarki penya.

Kallonsu yayi 'daya bayan daya
Dukkaninsu kowanne ashirye yakeda karbar matakin qarshe 'din sbd yanxu sunkai iya maqurar ganin cikar burin sbd Jamal dasukaga yafara shiga hanyarda bazata bulleuba su duka.

Wasu irin qananan wuqaqe farare tas guda shida masu kamar azurfa ya fitar daga wani irin rami ya ajiye agabansu tareda kallonsu yace,

Wannan wuqar dafin jinin penya ce wadda duk duniya ita kadaice zata kashe sarauniya mineelik,
Kowannenku zai soketa da wannan wuqal agurare daban daban saidai kuma dafin zai illatatane bazai kashetaba matuqar ba masoyintane ya soketa da ita kuma ya zamto shine zaiyi mata suka ta qarshe da wannan wuqar to tabbas wannan ne kawai zai kasheta...idan Wanda takeso fiyeda komai bai soketaba to tabbas kusani sukarku zata illatane amma bazat mutuba Wanda kunsan rashin mutuwarta na nufin rayuwarmu mu duka dan haka wannan matakin na qarshe yafi kowanne hadari.

Cikin zalama da qosawa kojo yace,

Jamal bazai taba qi hakan ba koya gardama zamuyi amfani da qarfinmu mu sakasa.

To bayan wannan kuma idan ta mutu to masautarta zata bace daga duniya babu Wanda zai sake ganinta saidai idan Wanda take tsananin so ya sadu da ita to tabbas idan ta mutu masarautarta tariga ta bayyana har abada tazama ta bil adama ta tashi daga duniyarsu.

'Daure fuska amari yayi zaiyi magana da sauri kojo ya dakatar dashi yana cewa,

Munriga munkawo yanzu babu abinda zai gagara yamaida mu baya ga wannan tafiyar Jamal dole zai sadu da sarauniya mineelik.

Wasu sabbin madaurin damtse na wani tsarin boka yabasu kowannensu ya daura tareda 'daukar wuqa 'daya na Jamal kuwa cikin fata amari ya nade masa ya soka qugunsa suka miqe.

Yonas dake qoqarin soka tasa cikin takalmin fatar damisarsa yaji hannunsa na wani irin qaiqayi yayi saurin dubawa zai sosa saiyaga rubutu na bayyan a hannun nasa yayi saurin kallon mahaifinsa yaga idanuwansa rufe alamar saqone yake ruboto masa dan sanar dashi wani abin.

Da sauri ya maida kallonsa ga tafin hannunsa yafara karanta saqon.

"" idan buri ya kammala kawai da datti ake ashare komai da komai""""

Jinjina kai yayi cikin rashin tausayi yakalli bayansu kojo dasuka gabansa dan yafahimci saqon meyake nufi yana nufin idan ankammala su kashesu nan take.

Suna fitowa qofar gidan boka aqoob sukaga wani irin gini mai matuqar tsawo da kyawu tareda girman dabasu taba ganiba mutanen gari sai fitowa kallo akeyi ana nufar hanyar da ake hango masarautar
Atake cikin gaggawa suka hau raqumansu suka nufi hanya sai tun daga nesa suke hango babu daji sai masarautar kawai da girmanta yasa ta zamto kamar tana cikin ganin ne.

Suna isa bakin qatuwar qofa mai girman gaske suka taru su biyar suka tura qofar tabude suka shige cikin wani irin mamaki mai rikita tunani da nustuwa sbd girma da kyawun masarautar babu kowa koina tsit saidai komai fes tamkar yaune aka ginata.

Harabar gurin suketa rarraba idanu suna kallo cikeda far in ciki mara misaltuwa sbd burinsu yacika saura qiris su mallaki sauran duniyar.

Wasu furanni masu qamshi yonas ya tsinka ya shinshina ya lumshe ido cikin farin ciki ya daka wani tsalle tareda sakin ihun farin ciki.

Kojo kuwa mahaukaciyar qofar daya tabbatar ta fadar da karagar ke cikine ya nufa ya saka hannu biyu yatura qofar ta wangale atake dukkaninsu sukai mutuwar tsaye ganin karagar dake wani irin daukar ido duk da kasancewarta kalar baqa mai adon zan zinari.
Girman fadar suka kallon cikin wani irin farin ciki madaukaki da sauri suka nufi kujerar kusan atare kowanne na burin kaiwa ya hau Jamal yasha gabansu cikin wani irin yanayi na damuwa da bacin rai.

Tsayawa sukayi dukkaninsu kallonsa saidai ganin kamar hawaye cikin idanuwansa yasasu tamvayarsa cikin gaggawa.

Yaja baya tareda zubewa kan gwiwoyinsa murya na rawa yace,

Ina roqonku da karku cutatar da ita domin kwadayin arzikinta kubari zankarbar mana ta hanya mafi lalama da yardar ta.

Wucesa amari yayi ya nufi karagar yana banzatarda zancensa sbd har abada babu Wanda zai shiga tsakaninsa da wannan taskar arzikin.

Dukkaninsu babu Wanda yabi takansa sbd babu alamar gudu ko ja da baya a wannan alamarin nasu.

Cikin wani irin gunjin kuka ya durqusa a gurin suka waiwayo suka kallesa ajani ne yadawo gabansa ya tsaya cikin kulawa yace,

Meke faruwa munyi alqawarin duba damuwarka idan kafada.

Kallonsu yayi cikin wani irin gunjin kuka mai ciwo ya girgiza kai yana cewa,

Ayau na hada shimfida da sarauniyar aljanu Wanda na tabbarda hakan wata sabuwar qaddara rayuwa ke nufi dani saidai kuma hakan y juyar da ra'ayina bazan iya cutatar da itaba sbd a duniyarsu hakan wani babban alamari mai tsananin girma yake nufi dan haka ta tafi wani gurin bauta bazata dawoba sai bayan kwana uku sbd abinda yashiga tsakanina da ita zatajene domin dawowa duniyata gaba daya dan haka nake roqonku karkuyi abinda zai barmu da masifar da bazata tsaya akanmuba kawai.

Cikin tsananin farin ciki da jin dadi suke kallonsa atake dukkaninsu suka sheqe da dariya mai qarfi cikeda farin cikin ganin komai ya tabbata qiris yarage.

Kallonsu yake daya bayan daya yana mamakin dariyarsu cikeda fargaba.

Sake kutsawa cikin masarautar mai girma sosai sukayi kowanne na taba abinda ya burgesa duk wata zalamarsu da kwadayinsu ya fito nan suka ringa shiga dakuna da gurin shaqawata da sassa daban daban babu tsoron komai aransu.

Shikuwa ke6e kansa yayi daga garesu yana zullumi da tunanin manufarsu daya kasa ganowa yadai San dole sunada qudirin cutatar da ita.

Ranar data cika kwana uku a makeken lafiyyan dakinta dake turakarta ta bayyana lokacin yana zaune tsakiyar daki cikin tsananin tashin hankali da damuwa.

Kallonsa take cikin tsananin farin ciki da wani irin yanayin jin dadi takira sunansa cikin qauna da soyayyarsa.

Da sauri ya miqe tareda juyowa bata tsaya bata lokaciba ta rungumesa da qarfi tana sake ajiyar zuciya cikin farin cikin kasancewa dashi har mutuwarsu.

Rintse ido yayi sbd tuno abinda yafaru ayau tsakaninsa da 'yan uwansa.

Wuqar da boka yabasu suka fitar masa da yasa suka basa tareda yimasa bayani yayi saurin wurgi da wuqar yace,

Aikuwa idan har nine Wanda kawai zai iya kasheta har abada bazata mutuba.

Cikin takaici kojo ya kallesa yace,

Baka isa ka rusa mana shirinda muka share shekara da watanni muna sadaukar da rayuwarmuba.

Kabarsa yagama bulayin shirmen son wadda ba jinsinsa idan yagama shirmrn mafarkin zaidawo hayyacinsane lokacinda tagano manufarsa ta aikasa gurinsu dede"""cewar amari dayafi hasala da zancen.

Yonas ya sake dauko masa wuqarsa ya saka masa cikin hannunsa yace,

Idan bakayiba mu zamuyita sukarta harsai ta mutu koda zamu dauki shekara dari ne saidai kasani tana warkewa karasa yan uwanka dasune rayuwarka har abada sbd kashemu duka zatayi kuma harda kai aciki.

Ajani dayafi kowa qaguwa dasu mallaki masarautar ya matso gabansa ya tsaya cikin tabbarwa yace,

Zabi yarage naka kazaba 'yan uwanka ko soyayyarda bazata doreba har abada sbd ba jinsi dayaba dan haka kashirya tana dawowa zamu qarashe aikinmu idan baka yi yanda akaceba kana kallo zata kashemu.

Tafiya sukayi sukabarsa tsaye da wuqar ahannu yana kallo cikeda wasi wasi saidai bazai iya bari yarasa yan uwansaba sbd sune rayuwarsa sunayiwa juna wani irin so da qauna mai qarfi.

Zamewa yayi daga jikinta jin kamar wani abu a gabanta kallo daya yayi mata yayi baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login