Showing 57001 words to 60000 words out of 81312 words
ya kalli Ajani, ya masa alamun yayi magana.
Cikin nutsuwa ya faɗa mishi abinda suka gani.
D'auko wata yar jaka yayi, ya buɗe bakinta, ita wannan jakar da fatar jimina akayita, sabida ajiyar abubuwa kananu.
Wasu duwatsune a ciki wanda suke cakuɗe da wuri, wasu kalamai bokan yayi sannan ya jijjiga duwatsun ya watsa, a tsorace yakalle su baki ɗaya sake ɗiba yayi ya watsa, a firgice ya mike yace.
"Shin kungatane?"
Suma atsorace suka kalli juna, sannan suka kalleshi, kaman haɗin baki suka ce.
"Wa kake nufi?"
Komawa gurin zamanshi yayi a nutse, yace.
"Sarauniya Mineerlik?"
"Mineerlik kuma? Sarauniya kuma ai mu bamu ganta ba, kawai mage muka gani ita kuma ta zinarice."
Suka faɗa mishi haka a tsorace.
"Tabbas ita kuka gani, itace tafito dan sau ɗaya take fitowa ashekara, kuma ta tafi bazaku sake ganinta ba sai wata shekara idan da rabon haka kuma ko wace shekara da kalar siffar datake fitowa amma tabbas k'addaranku ce takaiku gurin har kuka ganta."
Shiru sukayi cike da damuwa, suka shiga kallon juna Kojo shi yayi karfin halin tambayar bokan yace
"Wacece ita haka.?"
"A'a ɗan saurayi wannan duniyace ta taskar arziki, daula ce ta musaman Sarauniya Mineerlik sunanta sunan kujeranta."
"Toh Ebo taya zamu sake ganinta? Tunda ake kaddaranmu ce ta haɗamu da ita domin kuwa wannan zinarin saimun mun mallakesa" Inji Ajani,
Gyara zama yayi cikin yarda da abinda zaice.
"Wato wannan dajin da kuke gani ba daji bane, kamar sauran da dazuzzuka, shi ɗin alkarya ce ta aljanu ko nace muku duniyar aljanu ce, shi yasa yake cike da abubuwan al'ajabi, masana tarihi sun tabbatar da cewa, babbar masarautane a gurin me ɗauke da babbar fada na sarkin aljanu Penya, shine mamallakin fadar da kuma alummarsu ta aljanu, lokacin da cutan ajali yazowa penya sai ya bar wasiya, koda ya mutum Kalsh shine shine magajinshi, alakacin matar Kalsh Sultana Neelah tana ɗauke da tsohon cikin, haihuwa ko yau ko gobe....
Bayan kwana biyu jikin mai martaba penya yayi tsamari, haka duk wasu likitotin gargaji suna fama dashi, tashin hankali yayiwa Kalsh yawa domin a lokacin aka sanar mishi, Sultana Neelah tana, kan gwiwa,
Hankalinshi yayi matukar tashi, ana cikin haka Sarki Penya ya mutu, hankalin Kalsh yayi matukar tashi ga rashin Uba ga matar a wani hali gabi ɗaya sai ya shiga kiɗima, ana hidima kai mahaifinshi amna shi ya koma kofar ɗakin karɓan haihuwa, ya zauna.
Sai da Neelah tashafe kwana biyar sannan ta sami nasaran haihuwar Y'arta mace, mai tsananin kyau wacce tunda ake haihuwa azuri'ar ba'a taɓa samun y'a kamar yarinyar ba, sai dai abin takaici kwanar Sultana Neelah ta mutu sakamakon ciwon cikin haihuwa, gashi a ranar aka bawa Kalsh mulkin garin, ga murna ga bakinciki, fito mishi da Yarinyar jakadiya tayi ta zube a kasa cikin kuka tace.
"Sultan ga yarinyar nan, ta rasa uwarta a daren jiya."
Idanunshi cike da zubda kwalla ya karɓi Yarinyar ya ɗagata ga Alummarshi yace.
"Sultan Kalshe Penya, Nasamu Y'a mace naka mata Suna Mineerlik, haka kuma kujeran mulkina shima sunansa kenan Mineerlik, da fatan ku sanya mata albarka."
Cikin maɗaukakkiyar murya alummar aljanu sukace mun ji mun amince da abinda kace munawa Sultana Mineerlik, Barka da zuwa da kuma albarka ya cika rayuwarta."
Juyawa Sultan kalsh yayi rike da jaririyar, zuwa cikin gida ya isa har ɗakin da gawar Sultana Neelah, yana shiga ya zuɓa gwiwarshi cike da zubda kwallah yace.
"Neelah kin ɗaukar min alkawari baki cika ba, Ina soyayyar da kika fada min zamu shimfiɗa ina kaunar da kika min alkawarin zamu nunawa abin ciknki Neelah ya zaki tafi kibarni da ɗawainiyarta, Ina soyayyar da kika min alkawari min, abar kaunata kin tafi kin barni da kewarki da soyayyarki wanda yake tankar gubace a gareni."
Kuka yake cike da damuwa da ɗimauta, ruwan kwallar dake zuba daga idanunshi yana sauka akan fuskar mineerlik, a hankali ta buɗe idanunta tana kallon mahaifinta, sai ta rufe, sabida ɗigar kwalla, jakadiya ce tazo amshi Sultana Mineerlik a hannunshi wacce take motsi da kuka kasa kasa, na alamun yunwa, dan har tasaka hannunta abakinta....
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_
*34*
Not edited.
Arazane sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo 'daya idanuwanta na sake bushewa cikin gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai lokaci 'daya ya 'dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido.
Numfashin wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai magana rumanah ta 'daga hannu batareda takalleta tace,
Duk Wanda yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene.
A gigice adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin takoma ta zauna zufa na karyo mata jikinta na wata irin tsuma.
Tayar da ita akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma tabbarda yankata din za'ayi.
Ahankali rumanah ta 'dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya 'daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,
Gimbiya adama ce.
Cak kaleeb ya tsaya sbd harya 'dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya'dan yanketa.
Arazace sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan haka zatafi rashin tausayi da imani.
Sarakunan dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.
Rufe ido rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar 'danta da iyayenta tana mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,
Ni sarauniya ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau agaban mijinta da 'yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda qannen magajin mineelik.,
Baiwa mamani arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita Kofi 'daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu.
Sultan abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.
Arikice sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana 'daya cikin mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin 'yar qasaba ta saukesa akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama'ar dasuke shakkar ko kallon inda yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni arayuwa...
Yanxu ta karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu da balain da aka binne shekaru tun kafinsu.
Kama adama akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake suka fara yiwa adama jan wulaqanci.
Jikin ammy ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai sbd matuqar tafara mulkinta ayau da zubarda jinin wani to tabbas zaiyi wuya bata zamewa mutane abin tsorobas.
Qoqarin isa gurin rumanah din tayi aka dakatar da ita ta hanyar tareta tayi saurin kallon rumanah data rufe idonta tanajin wani irin baqon yanayi shigarta.
Cikeda rashin imani da tausayi kaleeb ya daga takobinsa yacire kan adama data mutu tana ihu da fizge fizge.
Tsit gurin yayi sbd tsoro da firgici sbd duk mulkin sultan ba'a taba kashe mutum agaban alumma ba sai yanzu nantake kowa yaji tsoro da fargaba tareda tashin hankali na shigarsa atake kaleeb ya 'daga takobinsa dake 'digar jinin adama sama ta bude idanuwanta ahankali takalli jinin dake diga qasa ahankali tasauke ajiyar zuciya ta miqe tsaye.
Cikin wani sauti da babban sauti sarkin na'di yace,
Dogon zamani MINEELIK ASSULTANA UMMU-RUMANAH UWAR MAGAJI.
Juyawa tayi wasu irin samudawan masu bata tsaro da kuyankinta mata suka mara mata baya tashige.
Tafiya kadan tayi ta tsaya cak sbd abinda takeji ajikinta
Wani irin abu takeji kamar yana tafiya da motsi ajikinta ta dafe qirjinta da takejin yana quna.
Ammy tayi saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta 'daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin 'dagota suka gansa kansu idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.
Cikin wani irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar dake tattare da wannan karagar.
Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,
Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.
Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.
Ammy dake zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK.......
#mamuhgee
Kuyi manage na fitane so mu kama gobe.
[7/30, 6:33 AM] ummul aulad: *_TARAYYA_*
_wattpad@mmamuhgee_
_Haske writers association💡_
*36*
_Not edited_
_A gaggauce_
Mineelik nada kwarjini da wani irin haske na tsananin kyawu Wanda yasaka Sam babu mai ganinta daga haifinta sai mai kulada ita shiyasa bakowane yasantaba musamman daya zamto itace kujerar mulkin mineelik ayanda abin yake mahaifinta yariga yayi amfani da wani irin sihiri akan karagar da sunan mineelik yanda ko bayan mutuwarsa babu Wanda zai iya raba mineelik da karagarta kuma barinta a nahiyar na nufin mutuwar duk Wanda ke nahiyar kuma babu Wanda yasan da hakan sai ita mineelik din da mahaifinta sbd ganin bai haifi namiji ba yasa aka fara farautar karagar mulkin.
Mineelik na zama cikakkiyar budurwa qannan mahaifinta su hudu suka hada kai suka kashe mahaifinta mutuwar wulaqanci sbd wani irin zalamar son hayewa karagar saidai bayan kashesa suka kashe junansu agurin sbd kowa nason shine zai hau.
Lokacinda mahaifin mineelik zai mutu saida ya shafawa karagar jininsa dake zuba na suka hudu dasukai masa cikin tsananin azaba da taurin zuciya tareda fushi mai tsanani ya daf karagar yace,
Ni penya maqagin wannan karagar ayau jinina ya zuba sbd wannan dazata zamewa duk wani makusanci agareta masifa ayau ina mata baki mai hadeda tsinuwa duk Wanda zai hauta tazamo ajali mai masifa agaresa matuqar ba MINEELIK-ASSULTANAH bace take kanta har ranar dazata na'da wani akai da kanta sbd jinina da aka zubar akanta daga wannan qarni nawa ta haramta ga dukkanin qarni masu zuwa.
Lokacinda mineelik ta fito bayan mutuwar mahaifinta aranar duk Wanda ke bousk yaganta sukaga zallar kyawun halittar dabasu taba ganiba saidai cikin rashin sa'a fitowarta tasaka rayuka da dama mutuwa dan kuwa wani irin haskene da maganadisu atareda ita dake jan mutane zuwa gareta Wanda wannan abin shine atareda karagar mai janyo mutane da rufewar zuci da ido akan hawanta.
Ranarda mineelik tahau karagarta amatsayin assultana aranar akayi wani irin tashin daya faru aranar shine koda gari ya waye duk Wanda ke nahiyar babusa.
Tashin hankali data shiga shine tabarwa datayi alamun mulkintane bazaiyi kyawuba sbd karagar tayiwa jininta qarfi kasancewarta mace.
Ita kadai tayi rayuwa mai tsayi,shekaru masu tsayi batareda kowaba,
Kadaici,qunci,baqin ciki da kewa sune abokanan rayuwarta sai karagar wadda ahankali take zuqe mata tausayinta sbd babu wani Wanda za'a yankewa hukunci a zubarda jininsa shiyasa abin yake cinta itakadai makari 'dayane mahaifinta yasanarda ita na wannan karaga shine soyayya mafi qarfi amma idan idan sadaukarwar abu mafi soyuwa tashigo.
Sanin kaf acikin duniyarta babu Wanda zai iya ko 'dago kai yakalleta sbd kwarjininta bare ya iya samun soyayyarta saidai ta tabbatarda wannan azarbabin da gaggawar tareda rashin tsoro da kwadayin sai bil adama.
Wannan shine burin
Hakan yasa ta rufe daularta babu wanda yake ganinta sai ita tafara fitowa duniyar bil adama domin kuwa babu abinda take buqata da tsananin buri kamar soyayyar da babu irinta a qarnin.
Aduk shekara da kalar suffan datake fitowa saidai bata taba dacewaba amma alqawarine bazata daina neman soyayyaba harsai ta mutu.
Shiru sukayi dukkansu kowanne najin zuciyarsa a bushe babu wani tsoro ko fargaba sbd dama nema suka fita duniya dan haka su sunga zinari kuma bazasu danganaba harsaisun mallaki wannan karaga Ajani ne ya gyara zama yayi gyaran murya yace,
"Toh shi zinarin yana tare da ita kenan?
Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da tabbarda abinda zai fada yace,
"Ita da kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.
Kallon kallo suka shiga yiwa junansu saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin idon aqoob yace,
Shirye muke da mallakar wannan dukiyar kota halin yaya koda soyayyar tatace mun shirya nema.
Murmushi bokan yayi yana jinjina qarfin zuciya da buried tareda rudu irin nasu sannan yace,
"D'ayanku zai faɗa soyayya da ita amma kafin nan sai kunyi jiran shekara ɗaya, wanda haka zai kasance kamar ganganci da wasa da rayuwarkune sbd hadarin dajin dakuma tsawon lokacin dakuma mataki uku masu matuqar hadari,
idan kuka tsallake mataki uku da zai faru kafin bayyanarta toh tabbas soyayyar ɗayanku zai kulu da ita, sai dai ba soyayyar bace mai muhimmanci dukiyarce mai mahimmanci domin sonda zai gwada mata shi zai sanyanta buɗe mishi alkaryanta da taskar mineelik.
Kallon juna suka sakeyi kowannensu idanuwansa acikeda rashin tsoro ajani yace,
"Toh boka matakai uku da zamu bi dan samun kusanci da ita menene fa'idar haka."?
Mikewa bokan yayi tsaye, ya shiga zagayesu har ya tsaya a tsakiyarsu murmushi yayi yace,
Zakusansu da sharadin taskar arzikin tamuce muduka.
Kallonsa sukayi cike da mamaki da jinjina kwadayinsa saidai zasu iya yin komai da mallakar taskar kojo ya kallesa yace,
"Mun amince, zamu raba da kai.
Dariyar jin dadi yayi yace,
Tareda yarana biyu za'ayi wannan tafiyar tareda rubuta sheda a faifan fatar raqumi da jinin dukkaninmu za'ai rubutun kowa zaibada nashi arubuta a ajiye tarihi ya shaida wannan taskar arzikin mineelik tamuce mu duka.
Babu musu kowanne yafitarda 'yar qaramar wuqarsa dake some a qafafunsu suka 'diga jininsu a 'yar qwarya akai rubutun atake ya ratayesa a bangon dakin.
Yaransa biyu suka shigo yonas da haji yakallesu yace,
Gasunan kuma tabbas akwai haske mai disashe duhu akwai duhu mai disashe haske.
Dayake zuciyoyinsu a shirye suke sun kafe kwaɗayi da son zuciya ya rufe musu ido ba tare da wani bata lokaciba suka amince Jamal dake gyara zaman wuqaqensa dake shanye da dafi kala dabam dabam na macijai da kunamu harma da dafin kada yace,
"Tunda nine zan fara aikin kwada soyayyata dole kasona yazamo mafi nauyi a raqumi.